Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 74

21K to 24K   out of 221.1K words

ci
su daga haka ta basu kyaututtukar su sannan ta raba su gida uku a inda tayi mixing ɗin yaran ɗakunan
uku ta ce da su washegari gasa za'a yi duk group ɗin da suka lashe gasar za'a basu kyauta mai girma dan
haka ta raba masu inda zasu yi bita yaran suka tafi da murna da ƙudirin lashe gasar washegarin iyayen su
sai murna suke ashe dai ƴaƴan su na da hazaƙa cutar da kansu suke ta yi basu sani ba wai suna kishi.



Bayan fitar iyayen suka cigaba da hira tare da zulfa'u a inda take ce mata har karatun boko zata fara koya
masu kaɗan kaɗan murna sosai zulfa'u tayi ko ba komai sun sami hasken duhun kan da suka daɗe a ciki
suna tsaka da hirar su mai gari ya aika a kira baby doctor dan haka ta tafi ta same shi a falon shi yana
zaune shi da Dr Zaid hira suke yi,suka gaisa ya jinjina ma ƙoƙarin ta na ranar da godiya dan matan shi sun
sanar da shi komai cikin jin daɗi da farinciki dan haka ya mata godiya ta musamman



"Haba ai ba komai yi wa kaine kuma ai ƙanne na ne babu komai ai mune da godiyar karamcin da kuka
mana na bamu muhalli a ƙarƙashin inuwar ka Allah ya saka da alkhairi".



hira suka taɓa har zuwa ƙarfe tara na dare jifa jifa yake saka masu baki dan shima ya ji daɗin sabuwar
rayuwar da ta ke son kawowa ahalin gidan,9:15pm suka yi sallama ta wuce ko da ta koma tea kawai ta
sha da cupcake ɗaya ta kwanta bacci.




**************

_Next day_



Kamar jiya haka yau ma ya kasance sai dai a hanyar dawowar su ya ɗan ja ta da hira

"Jiya kin yi ƙoƙari i must say good job"ta kalle shi cikin mamaki dama ya iya complement hmm
"Thank you"daga haka suka cigaba da tafiya sai dai a daidai bakin titin suka yi karo da Asma'u tana
tahowa babu tsari



"Ɗan birni"ta kwala mai kira suka dakata suka juya kallon ta a hujajjan ta ke tafe da zuwar ta ta yo kansu
kamar zata faɗa masu da sauri Bilkisu ta dakatar da ita ta hanyar saka hannu tsakanin su da ita



"Malama kina da matsala ne"?kallon raini ta mata kafin tace

"Ni da ɗan birni nake magana ba ke ba"

Murmushi ta yi ta ce

"Ai duk ɗaya muke ni da shi dan haka in kina da abin cewa faɗi ina jin ki"

Abin ya bata haushi dan haka ta ce

"Chan maki ban da lokacin ki"ta juya ga Dr Zaid ta ce

"Ɗan birni sai ka zo anjima ai zaka zo koh"? Sai yanzu ya san bata da tsari sosai sai dai bai jin zai iya yi
mata faɗa dan haka ya girgiza kan sa ta juya ta yi tafiyar ta.



Kallon sa Bilkisu ta yi ta ce

"Allah ya shirya"bai amsa ba sai ya haɗe girar sama da ta ƙasa ya ce



"Ya zaki rinƙa yi ma budurwa ta ɓatanci a gaba na wannan ai cin fuska ne"dakatawa tayi da tafiyar da
take yi ta juya tana kallon shi ido cikin ido ta nuna shi da yatsa ta ce

"You?her?budurwar ka"? Sai kawai ta fashe da muguwar dariyar da bata taɓa yi ya gani ba dan haka sai
abin ya bashi mamaki dan haka sai ya sake jiki yana kallon ta abin gwanin sha'awa he never knew she is
this beautiful ita kuma sai dariya take mai babu ƙaƙƙautawa dan abin ya bata dariya ta yaya zai ɗau
wannan ballagazar ya ce budurwar sa ce hala bai da labarin saurayin ta Mudan ne taɓdijam abin abin
bada dariya ne ɗagowa tayi ta ce

"Sorry forgive my manners but i can't help it but laugh"ta cigaba da dariyar sho kuma kamar zombie ya
rinƙa kallon ta...............
*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

#vote

#comment

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*6*



Yana cikin duniyar tunanin sa bai san lokacin da ya ce da ita

"You look cute"ba,kawai sai ta dakata da dariyar ta natsu amma da ragowar murmushi a kan fuskar ta
wanda hakan ya saka shi gano cewa abin na yawo a kan ta still.

Toh amma menene na dariyar?koh dan ya kira Asma'u da budurwar sa shi yasa take ta mai dariya?but
ai Asma'u kyakyawar yarinya ce bata da aibu.shi fah ba sani yayi cewa Asma'u na da saurayi mai siffar
ƴan daba ba shi yasa ya fara dulmiyawa but nevertheless zai tsawatar wa baby doctor akan me za ta na
yi wa budurwar sa dariya dan haka ya ce



"In kin gama dariyar ki zo mu tafi yamma na yi kuma yanayin ruwa ne".kaiwa nan ya fara tafiya yayin da
ita kuma ta biyo shi a baya suna tafiya yana riƙe da kayan da suka raba ya rage wanda yawan jama'an
yau har ya ɗare na jiya dan haka sun ɗau lokaci sama da na jiya.



Suna tsaka da tafiyar su ta kurame kawai sai ta kuma sakin dariya sai yi take kamar ta sami abin arziƙi
abin harzuƙa shi yayi dan haka ya tsaya ka kalle ta kafin ya mata wata muguwar tsawa.



"What the heck are you laughing at huh"?shiru ta yi ta haɗe rai kafin ta ce



"Excuse me Dr Zaid Maher baka da right din ɗaga min murya dan na yi dariyar abin da bai fice min a kai
na ba laifin waye?kai fah ka faɗa min cewa wannan ballagazar ita ce budurwar ka yarinyar da babu tsari
babu tarbiya a tattare da ita kai ka sani haka kuma kana gani da idanun ka bata da tsarin da za'a ce ta kai
standard ɗin zama budurwar doctor ba doctorn ma kamar kai mai girman kan tsiya da iyayi,iya nan jijji
da kan ka ya dakata ashe?dan haka ni ba laifi na bane dan na yi dariya dan abin na dariya ne mana ta
yaya zaka ce da yarinyar nan wai budurwar ka kai tsaye,ai kowa ma dole yayi dariyar wannan abin". Tana
isa nan ta yi gaba ta wuce shi shi kuma ya tsaya nazarin kalaman ta dan akwai ƙamshin gaskiya a ciki shi
kan shi ya kasa ganewa da tantance dalili ƙwara guda da yasa ya ke jin kamar akwai wani al'amari da ke
son faruwa da shi game da yarinyar wato Asma'u kenan but ko ma dai menene he don't think Bilkisu
should give that bad impression to Asma'u dan ba dan ita ba da an shafe tarihin sa a doron ƙasa ƙila dan
bata san da haka bane shi yasa but zai gyara mata tunanin ta akan Asma'u.
Shi kaɗan shi yake wannana analysis ɗin har dai ya kamo ta dan dama ba wani sauri take yi ba har suka
shiga taxi suka kai madakatar su babu wanda ya kuma cewa kanzil da suka fito ta riga shi shiga cikin
gidan yana maganar zuci ya ƙarasa ciki shima a inda yake cewa

"Ƙarfin halin yarinyar nan yawa gare shi ita ce da laifi kuma ita ce da fushi"ya cigaba da tafiyar sa har ya
kai masaukin sa inda ya yi wanka ya chanzo zuwa ƙananan kaya zuwa lokacin an kawo mai abinci ya ci ya
fita abin shi ko ina zai tafi.



Ita kuwa da ta shiga ciki dariya ta tuntsire da dan abin gaskiya ya shammace ta ace mutum da izza da
iyayi amma ya ɓige da son wannan fanɗararriyar yarinya kuma yana mafarkin mahaifiyar sa zata lamunci
wannan shirmen tasa.



Har ta gama cin abinci tana alhinin wannan abin yayin da zulfa'u ke tambayar ta dalili sai ta ɓoye mata
saboda yadda suke respecting Dr Zaid ba zai kyautu ta faɗi abin kunyar da ya ke yi ba dan mutuncin sa
ne zai zube wanda hakan ba zai kyautu ba sai ta ce da ita wata mata ce ta ke sanar da ita wai akan mijin
ta zai ƙara aure ita kuma ji take kamar ta yi hauka dan haka wai baby doctor ta taimaka mata su je gidan
su yarinyar ta sanar da su cewa ta gwada mijin kuma ta tabbatar da cewa yana ɗauke da cutar
zamani,kuma a zahirin an yi hakan but sai ta lauya wa zulfa'u instead ta sanar da ita ainihin maganar sai
ta chanza,

Itama dariyar abin ta yi dan matan su akwai duhun kai haka halayyar su take duk baƙon da ya zo sai an
gwada mai ƴar hali..



Chan misalin ƙarfe 5:00pm daidai sai ga tarin yara wai sun zo karatu ciki kuwa har da waɗanda basu zo
ba jiya kenan yaran gidan sun sanar da abokan wasan su akwai kayan kwalam dan haka yaran suka zo
bayan yaran gidan mai gari sun koya masu karatun da aka koya masu jiya,



Murna sosai Bilkisu ta yi dan sun yi bitar karatun jiyan har ma yaran makwabtar sun yi_(abin mamaki
dama akwai yara masu ilimi da basira a dokan daji waɗanda da za'a bincika da yawa in aka saka ido a kan
su aka tsaya masu wallahi za su zama abin alfahari a ƙasar nan baki ɗaya dan baiwar su ta daban ce wato
they are exceptionally genius kan su na ja but due to wasu dalilai irin na rashin gata,rashin abin taimako
wato kuɗin kai yara makaranta,rashin lura irin ta iyaye akan ƴaƴan su na da special talent sai a kasa fiddo
ƴaƴan nan daga duhun da suke, zamani ne na don kai wani mai shi ko da ya lura da hakan daga wun
gifted child ɗin nan ba zai taɓa taimakawa ba sai dai ya kawo na shi ɗan yayi tapping daga wun gifted
child ɗin nan in suka gama su maida ɗan ɗan daba ko ɗan ta kife ya rasa tudun dafawa bayan sun moru
da shi a ƙarshe ma in suka ga yana son kawo masu cikas sai su nemi su salwantar da rayuwar
ɗan,ɗaiɗaiku ake samin na kwarai cikin alumman yanzu saboda son kai da son zuciya yayi yawa Allah dai
ya sa mu fi ƙarfin zukatan mu ya yaye mana son kai dan wasu da na su ya rasa su taimaki wani mai
buƙata gwara sun yi biyu babu wato na sun ya rasa sannan mai buƙatar ma ya rasa)_



"Yauwa toh yanzu tunda mun gama bitar na jiya zamu ɗora da sabo kuma ina so ku tabbatar da cewa
duk a shirye kuke saboda gasae jiya da nace zaku yi ban manta ba ga kyaututtukar ku nan a ajiye muddin
kuka lashe zan baku kun amince"?



Cikin jin daɗi suka ce

"Eh mun amince anti"dariya ta ɗan yi kafin ta masu gyara ta ce

"Idan muna nan wato wun karatun islamiya da malama za ku na kura na idan kuma muka bar nan da
aunty za ku na kira na ba anti ba dan anti wata kalma ce ta daban a yaren ƴan boko wanda na san kuma
kuna son ku ji kuma ku iya yaren ko ba haka bane yaran malama"? Da zumuɗi suka ce

"Eh muna so malama"cikin farin ciki suka fara karatun nasu yayin da iyayen ke jin daɗi dan wannan
bokayen turai da suka zo masu kamar rahama ne a gare su gashi ƴaƴan su na karatun addinin su har ma
da ɗoriyar ta boko ake son yi masu basu da bakin godiya sai dai yi masu addu'ar gamawa da duniya
lafiya,kafin jiya a bawɗe suke bautar su dan rashin sanin ƙa'idoji but tun da suka ga yadda baby doctor ta
ke komai nata cikin tsari da ilimi sai su ka ga ashe sharar fage sule yi a fannin ibadar su dan haka sun
ƙudiri niyar samin ta ta koya masu har da dai sun manyanta dan sun yi ƴa da ita amma ilimi amfani ne da
shi tunda shine ginshiƙin rayuwa dan haka sun yarda su sauke girman kai da kishin fitinar da suke fama
da shi su zo ta koyar da su dan a ganin su kamar dan ilimin addinin da amaryar su wato zulfa'u ke da shi
ya sa mijin su ya fi son ta ba wai dan yana rawar ƙafar ita ɗin amarya bace matar da ta kai watanni
takwas ai ta wuci gaban a ce miji na mata rawar kan amarci sai dai wani dalilin daban wanda kuma a
zahirin gaskiya hakan ne dan zulfa'u akwai ilimi daidai gwargwado bata dai yi zurfi ba amma da babu
gwamma akwai ko da kaɗan ne toh ita duk ta fisu dan tana kiyaye sharuɗɗan addinin ta yadda ya
kamata har azumin litinin da alhamis take yi ga shi ta ƙware wun iya girki da tsafta toh dole mai gari ya
rinƙa mararin ta gata ƴar gidan masu da shi a ƙauyen kuma ita kaɗai ce mai waya a matan gidan dan tun
kafin ta auri mai gari mahaifin ta ya siya mata da shi ta zo dan haka da fari da kishin wayar suka fara ta
fita harkar su suka koma kan kayan kallon da ta zo da shi a nan ta buɗe masu wuta shine ta sami sa'ida
suka rabu da ita aka zo kan haihuwa zasu fara hayayyaƙo mata ta wanke du tass akan ai ita nata mai
kyau ne su da sai da suka kai shekara ɗai ɗai har biyar zuwa shida kafin su haihu ai ita nata ya yi kyau toh
a nan ma ta yi nasarar fidda kan ta suka dawo suna cewa wai hala kyawun ta ne yake ruɗin mai gari toh
a nan shi da kan sa ya tsawatar masu da uwargidan sa kam ta yi ɗiya da zulfa'u dan kwatakwata ba za ta
wuce 20-21 years ba a hakan wai ta tsufa bata yi aure ba dan mahaifin ta ya dage sai ta yi karatun arabic
wanda yake haɗe da na boko primary ita dai ta fi bada ƙarfi a na arabic ɗin dan ta san ko ta zurfafa da na
bokon ba lallai bame mahaifin ta ya yardar mata da na bokon gaba da primary ɗin ba shi yasa tana sauke
Alqur'ani mai gari ya ringa sauran samarin zuwa dan kar ya rasa yarinya mai ilimi a gidan sa ai ko ta yarda
aka yi aure,toh bayan duk waɗannan gadajen zaren da suke ta haɗa mata sai dai ta ce da su su zo ta
koyar da su irin nata ilimin amma fafur suka ƙi wai bata kai wannan matakin ba ta nemi da ta koyawa
ƴaƴan su suka hana sannan ƙananan ƴaƴan ɗakin uwargidan aka saka su a islamiyya wai dan su nuna
mata suma ba daƙiƙai ba ne haka suke ta yi har dai Allah ya kawo su baby doctor gidan..



Bayan sun kammala karatun sun kuma yi gasar group 2 sun lashe sai group 3 kafin group 1 kuma duk sun
sami kyaututtukar su yadda ya kamata a ƙarshe ta sanar da su akan duk ranakun litinin zuwa juma'a za
su na yin karatun boko kuma da yamma a rinƙa ɗorawa da na islamiyya hakan ba ƙaramin farinciki ya
dulmiya iyayyen su ba yayin da labari ya kai kunnen mai gari rasa abin cewa yayi sai dai Allah shi mata
albarka da yaje ta yi,



Shi kuwa uban gayyar ko da ya ji labarin wannan daɗin sauyi na koyawa yaran karatun boko da zata yi sai
ya ga why not yayi convincing Asma'ur sa ta zo ta yi joining tunda shi bai taɓa kawowa a ran shi ya koyar
da ita ba ko ma ya saka ta a makarabtar bokon ba duk zuwan da yake yi ƙauyen ashe daumi kansa yayi
wa wannan dabarar zuwa da baby doctor a da so yayi ya haɗa ta da mutanin ƙauyen ya nuna mata bata
da daraja sai dai ya ga yanzu tana da amfani sosai a gare shi he just pray that Asma'u ta amince dan ya
ga kamar jinin su bai haɗu da Bilkisu ba..



Cikin dare suna hira tare da zulfa'u akan abin da zasu yi ita da Dr Zaid next week ana haka ɗaya daga
cikin yaran ɗakin matar mai gari ta biyu mai suna hafiz ya zo ya yi sallama kamar yadda ymta koyar da su
akan kar su na shiga wuri kai tsaye babu sallama kuma in sun yi su bari har sai an basu izini kafin su shiga



"aunty likita wai ki zo in ji uncle likita yana ƙofar gida yana jiran ki"da mamaki ta kalli time ta ga past 9pm
kuma a ƙofar gida ba ma a cikin gidan ba ko me ya faru.

"Bara na je na dawo ba zan daɗe ba".

"Toh sai kin dawo likiciya".



Fita ta yi ta same shi a ƙofar gidan dan haka sallama ta mai ya amsa sai ta ce mai

"Ka kira ni a ƙofar gida da daren nan lafiya ko"?

Ɗan shiru ya mata yana jin izza izza ita kuma ganin bai da niyar yin magana sai ta juya ta kama hanyar
tafiya dan yau itama nata izzan ya motsa.
"Wait"!!! Ya dakatar da ita.

Inch ɗaya bata ƙara ba ta dakata ya kuma cewa cikin isa

"Ki dawo mana magana nake son yi da ke"!! wani irin juyin isa da mulki ta mai kafin ta ce

"Ban ga alamu ba in ka shirya sai ka neme ni ni kuma in ina da lokaci sai in amsa kiran naka"!!daga haka
ta wuce cikin gida



"What have i just done?alfarma fah nake son nema a wun yarinyar nan,oh gosh thank goodness ban
furta ba whatt"???ya ƙarasa yana godiya ga Allah da bai bashi ikon furta mata niyar sa ba da shikenan
she will definitely look down on him.



Yanke shawarar koyar da Asma'un da kan shi yayi dan yana ganin kamar zata fi amincewa since she
respect and value him a lot dan haka ya bari akan gobe a wun outreach zai sanar da ita ƙudirin sa,daga
haka ya shige cikin gidan ya kwanta,



"Hakan me ya ce da ke ne wai"? Zulfa'u ce ta mata wannan tambayar sai ta bata amsa da cewa

"A'a kira aka mai wai ana ta kiran layi na bai shiga shine aka gwada nashi ɗazu a wun aikin nan shiyasa
ya kira ni dan sanar da ni kin san ba mu samin damar kira dan babu service a nan"cikin hanzari ta tari
numfashin ta ta ce

"Inaa likiciya ai muna samin sabis a nan gidan zo in gwada miki"ta ja hannun ta zuwa cikin toilet ɗin ta
ta nuna mata gefen da zata sami service ai kuwa kamar abin asiri sai full service cikin ɗoki ta danna kiran
umman ta da layin ƙasar waje ya shiga sai dai bata ɗauka ba sai ta kuma kiran layin Bahajjatu ringing
biyu ta ɗaga

"Apple dama zamu gana da ke a cikin dajin nan"! Dariya suka saka tare daga bisani suka shiga hirar su
ta aminai sosai suka

8 / 74