Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*25*
*_Conspicuous_*
Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare
yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma
baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da
lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta
tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin.
Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar *_"IYA RUWA FIDDA KAI"_* amma
bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin
magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin
dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da
za'a iya alaƙanta kalmar da ba..
Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa
hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta
ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura.
Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga
nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka
tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin.
Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe
hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba
tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata
na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya
kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time
ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai.
Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in
tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na
nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin
highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa
jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta.
Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane..
A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga
flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa
A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower
vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar
akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita..
Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru
ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of
separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa.
Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba
they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba?
A wannan karon da ya kalle ta sai ya ji yana son kwanciya next to her maybe zai sami sauƙin raɗaɗin da
yake ji a ran sa dan haka ba tare da wani doguwar tunani ba ya saki hannun ta ya tashi daga zaunen da
yake ya dawo kan gadon ya kwanta a left side adjacent to her ya juyo fuskar sa daidai nata fuskar yana
kallon ta.
Akwai wani maganaɗisun da ke ingiza sa yin abubuwa da dama da bai gama yin shawara da zuciyar sa
akan halascin su ba amma yana jin in bai yi abin ba toh kamar a takure zai kasance wannan ne dalilin sa
ma na barin ɗakin sa ya shigo nata kenan ba tare da ya tsaya yayi doguwar tunanin abin da zai yi ba
sannan yanzu da yake zaune ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta next to
he,kuma ikon Allah sai ya ji faɗuwar gaban da yake experiencing ya ragu kusan kashi talatin cikin
ɗari,yana kallon nata ne yana tunanin zuci har bacci mai naiyin gaske ya ɗauke sa wanda bai san ba a
ɗakin sa yake ba dan he feel very comfortable and free a inda yake sanadiyar samin lafiyayyiyar baccin
da yayi kenan..
_5:14am_
A daidai wannan lokacin ne ya juya da nufin gyara kwanciyar sa sai kuma ya dakata daga komawa baccin
dan ya ji different scent ba kamar wanda ya saba ji ba in ya juya a ɗakin sa,a hankali ya shiga buɗe
idanun sa har ya gama buɗe su duka sai a nan ya fara tuno abin da ya faru da shi a daren jiya,dafe goshin
sa yayi yana mai lumshe idanun sa kusan mintoci kafin ya buɗe su ya juya ta ɗaya gefen sa sai ya ganta
kwance lafiya ƙalau tana kwasar baccin ta juyawa yayi ya ɗauko remote ɗin air split na ɗakin ya rage
yawan shi dan yana gudun wani abin da zai janyo mata ƙaruwar zazzaɓin da take ciki already.
Tashi yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin,ba sallah take ba bare ya tashe ta sai kawai
yayi tafiyar sa zuwa ɗakin sa ya yi alwala ya zo yayi sallah..
Wani baƙon lamarin da ya same sa shine yadda ya taƙarƙare ya rinƙa yi mata addu'ar samin lafuya haɗe
da yi mata addu'ar tsari daga yin wani rashin lafiyar dan shi kaɗai ya san yadda ya ji a jiya da ta shiga
halin nan sam baya so ya kuma witnessing..
Sai da haske ya fara haska ɗakin nasa sannan ya tashi daga saman sallayar nasa ya dawo kan gadon sa
ya kwanta daga haka ne wani session ma baccin ya kuma yin awon gaba da shi kuma a cikin wannan
baccin nasa ne ya rinƙa mafarke mafarke marasa daɗi dan kaf abin da ya faru da shi ne a dajin nan ya
shiga dawo mai sai ya shiga karkarwa yana haɗe jikin sa wu ɗaya at the same time yana karantar add'uar
tsari da kariya bai farkan ba haka bai daina yin add'uar ba har sai da hotunan mummunar ranar takau
daga baccin sa sannan ya cigaba da yin baccin duk ya gama haɗa zufa gashi ya rufe kan sa da blanket
kuma ba ƙaramin zufa yake yi ba..
Juyawar ta ke da wuya taji ƙarar wayar ta sai ta fara laluɓo wayar har da ta kai hannun ta kan wayar ba
tare da ta duba sunan ba ta ɗauka haɗe da karawa a kunnen ta ta kwanto ta gefen da ta ɗauko wayar
idanun ta rufe da ragowar magagin bacci cikin muryar ta ta ce
"Hellooo"..haka ta ja kalmar wanda ya saka Umma kallon aminiyar ta Hajiya Madina sai suka ɗan yi
murmushi dan dama sai da Ammi ta hana ta kiran ta ce da ita maybe fah basu tashi ba amma Umma ta
ce ita kam tana jin yin waya da su..
Jin ba'a ce komai ba sai ta kuma maimaita kalmar
"Hello"sai a wannan karon ne aka amsa
"Goodmorning Mrs Zaid Maher"muryar da ta ji ne haɗe da sunan da aka kura ta da shi ga kuma
ƙamshin da ta ji su suka haɗu suka saka ta warewa da kyau ta tashi a birkice tana zazzaro idanu waje
cikin rikiɗewa ai a sittin ta ce
"Umma please can i call you back in the next 15minutes"??tayi tambayar gaban ta na faɗi sai Umma ta
ce mata
"Yeah...sure...why not...just..just take your time okey baby bye"wani irin ajiyar zuciya ta sauke idanun
ta na daɗa buɗuwa da kyau kan ta na sara mata kamar ta kwana biyu tana rashin lafiya.
Dafe kanta tayi ta zauna kam gadon tana son tuno abin da ya faru jiya..
Iya abin da take iya tunawa shine jiya sun yi sai da safe ita da Zaid kuma distance dake tsakanin su da
ɗan tazara tana kwance ne shi kuma daga bakin ƙifar ya sallame ta but how come take jin ƙamshin
turaren sa a saman gadon ta gashi nan dai babu alamun mutum ya shigo dan gadon is neat babu wani
canji daga yadda yake..
Ganin zata wahal da kan ta garin nemo amsar da bata san inda zata samo shi ba ya sa ta tashi ta nufi
hanyar bayi dan gyara kanta.
Wanka tayi ta gyara jikin ta sannan ta fito ta buɗe closet na kayan ta duk ta ma rasa abin sakawa sai
kawai ta ɗau wata bum short da one single hand shimi ta saka ko bra bata saka ba da ta gama saka
kayan sai ta ɗauko wata doguwar riga mai hula orange colour blended with red touches ta saka ya kuwa
sauko mata har ƙasa sai ta nemi room slippers ta saka kasancewar babi inda zasu tafi ranar dan next
checkup nasa sai washegari zaman gida zasu yi a yau..
Turare kala kala ta feshe jikin ta da shi sanna ta ɗau wayar ta tayi dialing digits na Umman ta,tana tafe
da wayar a hannun ta har ta iso falon ta nemi wuri ta zauna haɗe da ɗauko remote ta ƙunna tv,tana
ƙunna tv Umma na ɗaga wayar sai ta riga ta yin magana ta hanyar ce mata
"Umma na ina kwana"dariyar manya Hajiya Zeenat tayi kafin ta ce
"Bilkisu kenan shikenan cikin waɗanda zaki manta har da ni a ciki baby?,,ki ce kawai in kama baby Zara
dan ina ganin in kuka yi naku ƴaƴan hana su zuwa wun mu zaku yi tunda gashi tun yanzu kun manta
mu"murmushi tayi kaɗan kafin ta ce
"Umma ni na isa,,wallahi ba haka bane Umma kin ga jiya gabaɗaya ban yi baccin daɗi ba rashin lafiya duk
ya saka ni gaba dama kwanannan kawai managing kai na nake yi dan bana so Zaid ya zama demoralize
saboda ni but am really sick please Umma ki min haƙuri inshaAllah hakan ba zai kuma faruwa ba kin ji"?
tun da ta fara wannan maganar babu gaɓar da ya taɓa Umma sai inda Bilkisu ke faɗin"jiya bata yi baccin
daɗi ba kuma ganaɗaya satin managing kan ta take yi" what does that implies?
Cikin jan wani irin ƙara Umma ta ce
"Baby you pregnant"tari Bilkisu ta shiga yi har tana wani shiɗewa tsabar mamakin abin da Umma ta faɗi
kuma ya zo mata ne kai tsaye daga sama.
Sorry Umman ta shiga yi mata sai Bilkisun ta tari numfashin ta ta hanyar ce mata
"Umma is not what you think,,ban da lafiya ne saboda monthly cycle ɗi na was about coming ne and
jiya da na ce maki ban yi baccin daɗi ba,cramps nake ta experiencing a bacci na shi nake nufi ba abin da
kike tunani bane"sai kuma anmashuwar fuskokin su ya kau Hajiya Zeenat ta kalli Hajiya Madina suka
girgiza kai su duk tunanin su ko sun kusa zama grannies ne especially Ammi da yanzu ta ɗora buri akan
babban ɗan ta Zaid tana bala'in son samin jika daga gare sa time is flying any moment za'a wayi gari
babu su and she can't help her self but say it out to her friend wato Hajiya Zeenat and she made her a
promise that inshaAllah ba zasu bar duniyar ba ba tare da sun ga jikokin su ba waɗannan kalamai kaɗai
ke kwantar mata da hankali..
"Kina nufin har yanzu baki fara jin alamomin masu ciki ba baby"?da mamaki ta ce
"Strange Umma,,why are you asking me such question"??kamar jirar ta Umman take ta ce
"Saboda na matsu in sami jika why are you people delaying it"??ya salam su kam Allah ya albarkace su
da iyaye sai ta ce
"Umma in dai har irin tambayar da zaki na yi min kenan toh i wi stop picking your calls i promise
you"babu alamar wasa a muryar ta sai suka kuma kallon juna suka girgiza kai sai Hajiya Zeenat ta ce
"Fine na daina kuma ba zan sake ba but ina dai fata baby ba planning kuke yi b?dan Allah kar ku bi
hanyar yaran zamanin nan masu cewa sai sun gama enjoying honeymoon kafin suyi conceiving please
kar ku mana haka mu muna buƙatar jikoki as soon as possible"shiru Bilkisun tayi tana sauraron
mahaifiyar tata cikin rashin sanin abin da zata ce da ita dan abin nasu ya fara takura mata 2 days back
Ammi ta yi nata part ɗin and now,,her mom is portraying her own pattern..
"Oh ya Allah Umma,dan Allah ki daina ke da Ammi have to stop all these things you are doing,seriously
kuna takura ni i can't please,,,sai anjima i will call you when the need arises"ɗiff ta kashe wayar ta ajiye
saman kujerar haɗe da kwantar da kanta saman pillow dake bayan kujerar,shiru tayi tana tunani..
She was lost in her thinking har ya fito bata lura ba tana kan tunanin abubuwan da ke faruwa da ita a
ƴan kwanakin nan ga matsananncin son Zaid da ke juya ta ga asassawar iyayen su da wanne zata ji..
Ya kai minti ɗaya tsaye kan ta bata sani ba shi kuma a nasa tunanin gani yake kamar she is still in pains
shi yasa take zaune haka..
Zama yayi a same chair da take zaune ya kai hannu ya taɓa gefen wuyar ta sai ta buɗe idanun ta a ɗan
birkice sai ta ga shine hakan ya janyo mata baƙuwar yanayi tun ma bai tambaye ta ba kenan ina ga in ya
tambayi health ɗin ta.
"Good morning"da ɗan murmushi ta ce
"Morning"sai ya kuma tambayar ta yana mai kawo hannub sa kusa da goshin ta
"How was your night"?imagine Zaid is a good pretender kamar ba ɗakin ya kwana ba sai ta bashi amsa
da
"Alhamdulilah"ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
"Your health"??sai a nan ta haɗa ido da shi dan shima abin da yake so kenan,so yake ya haɗa ido da ita
ko zai sami wani amsa cikin idanun nata dan shi ya rasa gane abin da ke damin lafiyar tunamin sa.
Cikin sanyin murya da ke tattare da tsantsar so da ƙaunar sa ta ce
"Alhamdulilah nagode"sai suka yi shiru suna kallon juna kafin daga bisani ya tambaye ta
"Waya...da wa kike waya..na daɗe a nan baki sani ba"cire idanun ta tayi daga nasa tana gyara zaman
rigar ta sannan ta bashi amsar tambayar sa cikin unexpected response
"Hmmm i see,,me kuma ya sa kake son sanin ko da wa nake magana"?wani irin kallo ya mata mai nuna
tsantsar mamakin sa da irin amsar da ta basa har ma da tambaya a ƙarshe.
Bai so amsa mata ba but wani sashe na zuciyar sa na ingiza sa akan dole ya amsa mata dan haka ya ce
"Babu,kawai gani nayi hankalin ki ya koma kan wayar gabaɗaya"!!ƴar murmushi tayi sannan ta rausayar
da kai gefe kafin ta ce
"Da Umma na yi wayar"sai ya gyaɗa kai yana mai kai hannun sa kan teburin da ke mafi kusa da
ita,landline ya kira ya masu ordern breakfast har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalle ta cikin kulawa ya ce
"Sorry ban tambaye ki abin da kike so ba na bayar da ordee,what would you like"??kallon sa tayi kafin
ta miƙe tana tafiya a hankali zuwa ɗakin ta ta ce da shi
"Abin da zaka ci shi zan ci ko ka manta a ƙarƙashin ka nake"??ta juyo ta mai kallon da ya saka jikin sa
sakewa,kasala ce ta sauko mai a bazata ba zato ba tsammani ya ji kawai ita yake son kallo sai dai kafin
yayi wani yunƙuri har tayi shigewar ta ciki.
"Damn it...Zaid common man up man up..."ya furzar da iska mai ɗauke da ɗumi daga bakin sa dan
hucin iskar alama ce ta yamayin da zuciyar sa ke ciki but why all these me ya sa haka me ya kawo haka
he thinks he should visit a doctor seriously..
Da dariya ta ƙarasa shigewar ta ɗakin dan ta san ta ƙunna sa dan dolen sa ma ya ji a jikin sa saboda ta
san yanayin maganar da ta mai sai ya ji wani abin all she need is for him to realise and keep her in his
head kuma ba zata iya yin hakan ita kaɗai ba dole sai da sanin sa da kuma yardar sa..
Kwantawa tayi bisa kan gadon ta tana jin wani sassanyar annashuwa na shigar ta from no where,juyi
tayi tana tuno wasu moments da suka yi tare da shi most especially jiya da ya nuna damuwar sa gare
ta,tunowa tayi da lokacin da ya ruɗe a jiyan yana ta tambayar ta ko me ke damin ta sai ta tsinci kan ta da
yiwa kanta dariya lallai ta shiga sabuwar duniyar da bata san da akwai shi ba a duniyar nan the feelings is
extraordinary abin ya mata nauyi da yawa tana buƙatar mai taya ta riƙon abin da take ji a zuciyar ta..
Tana duniyar tunanin ta ne ta ji an turo ƙofar ɗakin kamar ba'a son turowa hakan ya tabbatar mata da
Zaid ne dan shi kaɗai ke tare da ita a gidan.
Tashi tayi daga kwanciyar riginginen da tayi tana mai kallon sa da murmushin son da take mai shi ko
shagala yayi yana kallon ta yana jin wani abu na fizgar sa sai dai yayi ƙoƙarin controlling kan sa dan yana
ganin kamar yana overreacting da yawa.
Gyaran murya yayi game da riƙe ƙofar ɗakin yana mai sauke mata idanun sa cikin wani salo hakan kuwa
yayi tasiri a kan ta dan kallon yayi affecting nata sosai sai dai itama