Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 74

81K to 84K   out of 221.1K words

tana kallon sa cikin sigar da bata san yanda zata alaƙanta sa ba.

Firgigit kamar an tsungule ta sai ta ga kamar baccin da take yi har yanzu bata farka ba haba in ba a
mafarkin ta ba dama ta yaya Zaid zai yin yunƙurin yin wani abin ai sai dai a mafarkin dan haka ta saka
kan ta zata fita ta kuma jin alamar faɗuwar abu wani juyin bori tayi a zafaffe ta buɗe idanun ta gaban ta
na tsananta bugawa tana fargaban abin da zai biyo baya in har bai yi alama ba toh gaskiya ba zata taɓa
yafewa zuciyar ta ba for making her imagination go beyond her limits.



Sharewa tayi ta yi kamar zata fita sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon jin numfashin mutum kamar yana
gasping sai ta juya a rikice tana baza idanun ta dan ganin daga inda numfashin ke fitowa bata san lokacin
da ta dira a gaban sa ba sakamakon ganin ɓarin flower verse a gefen gadon sa,saurin yaye comforter ta
yi hannun ta na ɓari tana gama yaye comforter ɗin sai ta ga shi ke numfashin kuma taimakon gaggawa
yake buƙata dan haka ta fita cikin gaggawa bata tsaya ko ina ba sai a ofishin likita da ƙarfin ta ta shiga
office ɗin tana ta kwala mai kira a rikice ya fito daga cikin bathroom da shigar sa kenan yana tambayar ta
ko lafiya ta rasa me zata sanar da shi sai kawai ta shiga kirawo mai room number tana faɗin

"405...405..405."ganin ta ruɗe sai ya ce da ita
"Is okey let's go"da gudun ta ta fita shima ya biyo ta suka ranƙaya zuwa ɗakin da shigan su ya riga ta
zuwa kan gadon.ganin Zaid yayi yana jacking yana gasping da sauri da sauri sai ya cire mai mask ɗin ya yi
regulating device da zai rinƙa bashi iska,fita yayi cikin hanzari ya nufi office ɗin sa babu jimawa ya dawo
shi da wasu doctors biyu a nan ne aka buƙaci baby doctor da ta fita girgiza masu kai ta shiga yi tana kuka
tana faɗin ba zata iya fita ba,hayaniyar da ke fitowa daga ɗakin ne ya janyo hankalin Hajiya Madina da
Hajiya Zeenat da ke kwance a ɗakin masu kula da majinyata fita suka yi gabaɗayan su zuwa hanyar da
hayaniyar ke fitowa,ko da suka tafi sai suka ga abin tashin hankali wato Bilkisu ce ke faman risgar kuka
while ga doctors nan uku a ɗakin da Zaid yake kamar dai so suke su yi stabilizing nasa sai Hajiya Madina
ta ɗan janyo Bilkisu tana tambayar ta me ya faru.

In banda kuka babu abin da take yi hakan ya sa Hajiya Madina jan ta suka bar wurin a inda Hajiya Zeenat
ta tsaya tana hango abin da ke gudana a ɗakin duk hankalin ta a tashe yake ko me ya sami Zaid ɗin sai
Allah dan haka zirga zirga ta shiga yi a bakin ƙofar Hajiya Madina dai bata dawo ba dan bata jin zata iya
cigaba da witnessing abin da ke faru sai ta tsaya tana rarrashin Bilkisu kawai.



An hour + kafin doctors ɗin su sami damar saisaita Zaid dan sun fahimci cewa ya farfaɗo ne kuma da
ƙarfin sa ya farfaɗo dan kuwa so yake ya farka gabaɗay sai dai ciwon da ke kansa wanda ya janyo masa
surgery bai warke ba dan haka dole komai sai a hankali zai saba da shi they were able to seduce him dan
ya koma bacci kuma he is calm shi yasa suka fito a nan Hajiya Zeenat ta tare su tana tambayar su ko me
ya faru shi babban likitan ne ya yi inviting ɗin ta zuwa office ta bi sa cikin hanzari.bayan sun zazzauna ne
ya kalle ta at first moon face ya saka sai daga baya ya murmusa da smiling face ɗin ya ce da ita

"I must say,congratulations your son just regain consciousness and he is in good state of mind he will
wake up in not less than an hour or more with full strength and ability what a surprise i guess"!!faɗaɗa
murmushin sa yayi yayin da Hajiya Zeenat ta tafi ƙasa tayi sujjada bata ce da likitan komai ba sai da ta
ɗago sannan ta kalle sa fuskar ta jiƙe da hawaye idanun ta sun yi ja ja zir tana dariya tana fidda hawaye
ta ce da shi

"Thank you,thank you doctor,thank you"!!shima murmushin ya mayar mata da shi yana girgiza mata kai
ya san tana cikin farinciki dan haka bai ga laifin ta ba dan ta zage tuƙuru tana kuka.daga office ɗin ɗakin
zaman su ta nufa inda ta ga Hajiya Madina na rungume da Bilkisu tana rarrashin ta ita kanta mai
rarrashin ta take nema dan haka ta ƙarasa shiga ɗakin ta ce cikin muryar kuka

"Hajiya tashi ki ma Allah godiya our Zaid is back"ba ita kaɗai ba hatta da Bilkisun sai da ta razana dan
maganar a matsayin abin almara ya zo masu da mamaki da al'ajabi sai suka tashi tsaye baki ɗayan su
hawayen Bilkisu ya ƙafe yayin da Hajiya Zeenat ta buɗe baki cikin mamaki tana son yin magana amma ta
kasa Hajiya Zeenat ta gane state of shock da ta shiga dan haka ta matso kusa da ita ta riƙe kafaɗun ta ta
shiga girgiza ta tana cewa

"Yes yess Hajiya Zaid is back for good yanzu na fito daga ofishin Dr kuma ya sanar da ni cewa Zaid ya
farfaɗo kuma any moment from now yana iya farfaɗowa cikin ƙoshin lafiya abin godiya ne ga Ubangiji"!!
sai ga hawaye sharr na fitowa daga idanun Hajiya Madina cikin farinciki da jin daɗi ta rungume Hajiya
Zeenat ta saki kukan farinciki petting bayan ta Hajiya Zeenat ta shiga yi tana ƙara tabbatar mata da cewa
eh Zaid ya dawo masu irin farinciki da suka tsinci kan su a ciki understatement ne sun manta da Bilkisu a
ɗakin wacce ta yi suman tsaye sakamakon jin an ce Zaid ya farka a nan ta bar su ita kuma ta nufi hanyar
ɗakin da Zaid yake.

An saka dokar kar wanda ya shiga ɗakin har sai ya farka amma ita kam kai tsaye ta shige ta rinƙa bin sa
da kallo tana jin wani abu a ran ta game da farfaɗowar Zaid a haka ta zauna gwiwa a sage ta kafa mai
dara daran idanun ta waɗanda suka chanza launi zuwa jajjaye saboda kukan da ta yi saƙe saƙe kala kala
take yi a zuciyar ta mafi akasarin saƙe saƙen sun ta'alaƙa ne ga mafitar rayuwar ta in Zaid ya farfaɗo ya
kuma gane cewa shi da ita sun zama ma'aurata wanɗanda zasu rinƙa zama inuwa ɗaya tun farfaɗowat sa
har izuwa ƙarshen rayuwar su ya zai karɓi maganar?shin da wani siga zai fahimci maganar?zai amince da
ita kokuma a'a?zai ma yarda ya ɗauke ta a matsayin abokiyar rayuwa ta har abada?waɗannan tanbayoyi
sun tsaya mata a rai she knows that tomorrow will be her wedding day ranar da ba zata taɓa mantawa
da shi ba a rayuwar ta saboda tambari ne that will signifies a new life,a new beginning and a new world
to her.but is she well prepared and ready to accept it?sai ta kuma kallo sa ta ga yadda yake fidda
numfashi a hankali har yanzu bata san me take ji game da shi ba it's somehow mix the chemistry is over
reactive reaction ɗin na boiling ko wani ɓangare da saƙo na jikin ta,kanta ne ya fara ɗebar chaji sai ta
tsagaita da tunane tunanen ta cigaba da kallon sa.



_1:00am_

Suna a haka shi yana baccin sa ita kuma ta kasa runtsawa tana ta bin sa da kallo already nervousness ya
gama yi mata dabaibayi ya hana ta sukuni,tana kan kallon nasa sai ta ga ya fara juyawa da kansa idanun
sa a rufe ruf sai ta tashi ta matso kusa da shi tana gyara mai abin numfashin da aka saka mai ɗazu sai ya
dakata daga juyawar da yake yi ya tsaya da kan sa a wu ɗaya itama sai ta natsu kamar mai son haddace
wani abu kusan 5 minutes bai motsa ba sai ta ji ran ta ya fara mata ɗaci ɗaci ta ji ɗakin ya mata wani iri
dan ta gama sadaukarwa ba gaske bane kawai yaudarar ta idanun ta ke yi sai ta haƙura ta koma kan
kujerar ta kafe sa da idanun ta wanda zuwa yanzu sun ƙara girma sakamakon takura da suka samu daga
gare ta dan kuka ne ba kaɗan ba tayi ɗazu ga rashin baccin da bata yi ba ga tunani duk sai suka taru suka
haddasa mata damuwa dan har barkono barkono idanun ta ke mata amma bata cire tsammanin sake
haɗa kwayar idanun ta da Zaid ba.



Gradually,synchronously ya buɗe idanun sa kaɗan sai ya maida ya rufe duk bata lura ba sai da ya kuma
buɗe su a karo na biyu ya sauke su kanta duk bata sani ba sai da ta ji a jikin ta kamar mutum ya kafe ta
da idanu sai ta yi wuf ta ɗago with the hope of seeing him fully awake,.

Gani tayi kamar idanun ta gizo yake mata ɗan murza su tayi ta tsaya sai ta ga still ita yake kallo abin bai
mata ba sai ta rufe idanun ta for a moment ta buɗe su taga ita ce dai yake kallo dan haka sai ta shiga
pinching hannun ta but the reality is well set shi ɗin ne dai ba mafarki ba ba kuma imagination ba sai a
hankali kamar mai sanɗa ta fara takawa kaɗan kaɗan tana kallon fuskar sa sai ya bita da idon ta kuma
dawowa ta gaban sa still ya bita da kallo sai ta dawo gaban sa ta tsaya shima idanun sa suka tsaya a kan
ta ya tsura mata idanu kamar bai taɓa ganin ta ba.

She was out of words sai kawai ta juya cikin hanzari ta fita ta nufi ɗakin iyayen nasu ta gan su zaune dan
tun da ta bar ɗakin suka neme ta suka rasa sai Hajiya Madina ta fita duba ta ganin ta a ɗakin Zaid ya sa ta
girgiza kai ta dawo ta sanar da aminiyar ta abin da ta gani sai suka zauna zaman jiran farfaɗowar sa basu
koma baccin ba.

Da shigar ta cikin extreme euphoria ta ce

"Umma Zaid..Zaid ya tashi..wallahi ya tashi baya baccin..idanun sa a buɗe suke zo muje ki gani"tausayi
ta bama iyayen nasu dan sun gano mummunar son Zaid ya gama kamata har yana shirin illata ta ba tare
da ta sani ba.

Sai da ta ja hannun Umman sannan suka biyo ta zuwa ɗakin Zaid ɗin suna fatar ganin abin da Bilkisu ta
faɗa.



Ko da suka shiga ɗakin ganin sa suka yi a zaune jingine kaɗan da gadon idanun sa lumshe yana fitar da
numfashi kaɗan kaɗan sai suka ga kamar a mafarki.ƙarasa isowa kusa da gadon Hajiya Madina tayi tana
mai son gasgata abin da idanun ta suka gane mata.da isar ta hannun ta na ɓari ta ɗaga ta kai kan kafaɗar
sa sai ya buɗe idanun sa kamar an wanke mata ido dan ganin sa shi kaɗai sai ta yi saurin kiran sunan sa

"Zaid baby..Zai..ddd..are you really back..."duk a hargitse take maganar dan haka ya juya mata idanu
alamun eh sau ta rarumo sa ta rungume tana mai sakin kuka haɗe da faɗin

"Zaid..ka yi baccin doguwar zango ba tare da ka sani ba..you were unconscious for almost a month har
ana ce mana zaka kai 3-4months kafin ka farfaɗo..baby i was in great hell of pains i was hiding it not to
worsen the situation"sai ta yi bursting into tears shi kuma ya kasa faɗin komai amma yana jin wani abu a
ran sa but he can say it out dan haka yayi shiru yana sauraron ta har dai Hajiya Zeenat ta zo kusa da su
tana mai taɓa kafaɗar Hajiya Madina akan ta daina kukan da take yi bai dace ba sai ta daina kukan ta
ɗago tana kallon sa kamar an ce da ita za'a ɗauke mata shi yayin da Bilkisu ya ƙure sa da idanu tana
kallon duk wani motsin sa har dai tayi wani tunani ta bar ɗakin,ɗakin ta ta koma not minding what the
time is kawai ta shiga kiran layin Bilal sau biyu tana kira yana ƙarewa ba tare d an ɗaga ba,bata haƙura
ba ta ƙara kiran sa cikin magagin bacci ya ɗauka yana tambayar ko wanene dan bai duba lambar ba

"Apple wake up you rascal"ta faɗa with great excitement a muryar ta.

A rikice Bilal ya tashi haɗe da buɗe idanun sa da kyau ya ce

"Apple ke ce?what happened?is brother In-law awake"??duk a jere ya mata tambayoyin.

Bata san lokacin da ta sake dariyar murna da jin daɗi ba sai ta ce
"Bilal Zaid is back..Zaid ya farfaɗo am happy..am just excited and i feel that i can't take the whole
happiness all alone that is why i call you ate you happy"??tayi tambayar da eagerness a muryar ta sai
yayi saurin bata amsa ya ce

"Damn your second thought apple of course am happy..how could you even think that am not
happy..of course i am apple na ma fi ki farincikin farfaɗowar brother in-law"!!murnar su suka yi tuƙuru
suna tsaka da celebration ɗin Bilal ya ce mata

"Apple gobe fah shikenan zamu daina duk waɗannan wasannin da muke yi because you will become
Mrs Maheer and the bond between us will be weaken"sai mood ɗin su ya chanza su duka dan yanzu ta
tuno cewa da zarar an ɗaura auren shikenan duk wata ƙaƙƙarfar alaƙar da ke tsaƙanin ta da twin brother
ɗin ta sai ta ji hawaye na bin fuskar ta sun ɗau lokaci a hakan kafin daga bisani ya daure ya ce

"Apple don't worry muna tare a zuciyoyin mu ko da bamu tare a zahiri kin ji"?amsa mai tayi tana share
hawayen ta

"Na ji Bilal kuma na maka alƙawari ko da bamu tare son ka a zuciya ta daban take ba zan iya haɗa ta da
kowanne ba you are special to me"kasa yin shiru yayi har sai da ya furta mata

"Apple am gonna miss you please don't forget about me"tarar numfashin sa tayi ta hanyar ce mai

"Common Bilal stop talking like that it makes me feel like crying already"sai ya ɗan murmusa ya shiga
teasing ɗin ta ita ma tun bata biye mai har ta fara mayar mai da martanin tsokanar da yake mata.a haka
suka ƙarar da ragowar daren basu ajiye wayar ba har sai da ƙarfe 4:30am ya buga a agogon ɗakin Bilkisu
sai ta mai bye bye ta ajiye wayar.she was lost in her thought dan haka bata ma san lokacin da bacci mai
nauyi gauraye da daɗi ya ɗauke ta ba.



_7:09am_

A lokacin ta farka shaf ta sha'afa bata yi sallar asuba ba dan haka a hanzarce ta sauko daga kan gadon
tana addua'r tashi daga bacci haɗe da yawning,sauri sauri tayi alwalar ta fito ta tada sallah ta makara ba
kaɗan ba shi yasa tayi saurin tada iƙama ta sallame raka'oi biyun ta zauna addua bata bar abin sallar ba
sai da ta ɗau mintuna kusan talatin sannan ta sallame ta miƙe tana folding praying mat daga bisani ta
shige toilet tayi wanka ta fito abincin ta ta tarar a kan table da aka saba ajiye mata abinci da
magungunan ta dan haka shiryawa tayi cikin usual wear ɗin ta wato doguwar riga maroon colour sai
bata yafa mayafin ba ta ɗaura kawai,.

Zama tayi ta buɗe abinci kallon abincin tayi for a moment kafin tayi bismillah ta fara cin abincin,ba wani
yawa wanda ta ci ta tufe ta ɗau magungunan ta sha.har ta kwanta sai ta tuna da bata gan sa ba dan haka
ta tashi ta nufi hanyar ɗakin sa babu komai a ran ta ta tura ƙofae ta shiga haɗe da yin sallama ba'a amsa
mata ba dan haka kan ta tsaye ta shiga tana raba idanu dan ganin inda yake sai dai bata yi nasarar ganin
sa ba dan kuwa an fitar da shi an yi transferring nasa zuwa wani well equipped room da bashi special
care tunda ya farfaɗo sai ta ruɗe ta rasa me ke mata daɗi ina kuma ya tafi ta ma kanta tambayar sai ta
shiga duba sa ta zaga ɗakin babu shi ta shiga bubbuga toilet door ɗin tana kiran sunan sa bai amsa ba sai
ta fito a birkice tana neman sa ji tayi an jata gefe sai ta ɗago a tsorace.

Ganin Bahajjatu tayi ashe ita ta ja ta gefen sai ta kalle ta tana son tambayar ta inda aka kai Zaid sai dai
Bahajjatun ta riga ta dan sanar da ita tayi fuskar ta tam cike da murmushi tace

"I know tambaya ta zaki yi inda Yaya na yake,fine yana chan ɗakin da aka chanza mai very close to
yours dan ana saka ran ma an kusa sallamar sa nan da sati biyu sai dai ya rinƙa zuwa check up after 3
months"sai yanzu ta sami relief ta sauke ajiyar zuciya zata yi magana Bahajjatun ta riga ta ta hanyar
rangaɗa mata guɗa sai ta shiga rera waƙar

"Tazama tazama tazama ɗauko riga tazama tazama ɗauko hula tazama tazama ɗau takalmi tazama"a
haka fah ta rinƙa nanata wakar tun Bilkisu bata fahimrar inda waƙar ta dosa har ta fara harbo jirgin sai ta
buɗe idanun ta ciki mamaki tana mai cewa

"Baha ban gane ba"sai Baha ta ce da ita cikin raha

"Ina nufin daga kimanin mintuna arba'in da suka wuce kin zamo mata kuma suruka wato dai kin zama
matar babban yayan mu Dr Zaid Maher Mahmud kuma kin zamo suruka a wun Dr Maher Mahmud da
Hajiya Madina Maher at the same time kin zamo sister in-law ɗin mu"da annashuwa shimfiɗe a kan
fuskar ta ta ƙarasa maganar..

Abin a fizge ya zo mata dan haka sai da ta ɗauke wuta na wucin gadi kafin ta dawo hayyacin ta ta ce

"Baha kina nufin an ɗaura auren ne already"?dariya tayi ta ce

"Of course mana an ɗaura auren ku in fact ana ɗaurawa Bilal ya korawo ni ya sanar da ni cewa baku
jima da gama waya ba shi yasa bai kora ki ba dan kar ya hana ki bacci so presently you are officially Mra
Zaid Maher and wani abin da baki sani ba shine we all will be leaving zamu tafi mu bar ku tare saboda ya
farfaɗo kuma yana iya motsa jikin sa kaɗan kaɗan no need ma zaman mu,jirgin 8pm na daren gobe zamu
tafi dan Abba ma ya ja mana kunne akan mu yi mu dawo since you are now married you can take care of
him kin ga tafiya ta kama mu ba tare da mun shirya ba beelove"abin mamaki

28 / 74
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted