Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
duba wannan ba ya shiga nemar mafitar matsalar su wato lalurar Dr Zaid bai fah yi girman kan
shi ya sani ba ko ma da yayi practising ba he went into research ba dare ba rana dan dama Allah
subhanahu wata'ala baya saukar da cuta ba tare da ya saukar da maganin ta ba sai dai in ba'a bincika ba
but ko da a birnin sin maganin yake in har ka bincika zaka samu but nowadays we the children of the
computer age find it stressful,boring,burdensome,annoying and time wasting mu tsaya bincike
especially wai gargajiya sai dai a yi na bature kawai a tsaya jiran adadin da effect zai yi exhibiting but
gargajiya ba da mu ba i mean the real gargajiya not muna gargajiya drugs wanda sau da dama muna da
su,muna da magungunan cututtukar mu a nan kusa da mu but due to uniform habit na mu na i don't
care da ignorance ya sa sam ba mu taɓa sanin komai sai dai mu yi ta ɗura kuɗaɗen mu muna siyo abin
da kusa kullum muke kiciɓis da su but sakamakon ignorance na mu ba mu sanin su ne,the long and short
paragraph containing the bulky note shine mu daina ko ma mu rage son jiki wurin bincike da son sanin
abubuwa a rayuwar mu da zamu ƙaru da su in a positive way mu kasance cikin bincike da bankaɗo
abubuwa da dama da bamu sani ba wanda mu kan mu mun san ba mu kaɗai zamu amfani da shi ba the
entire nation will benefit from a single introvert and unrecognized individual experiment,dan haka am
urging not only us the youth but kowani citizen na ƙasar da yake da ya yi ƙoƙarin shiga chan ciki cikin
research dan samo latest update da related histories ɗin su dan samowa kan mu al'uma mai walwala sai
tare da haɗin kan mu da hannun mu zamu gyara ƙasashen mu either regarding our health,wealth,safety
and security,environment,education and so many other things ina fata Allah zai taimake mu akan
portraying waɗannan ƙananun shawarwari da na bayar Allah ya sa mu dace amin)_
_Next morning_
Da sanyin safiyar ranar juma'a Bilal ya nufi asibitin da ganawa da ƴaruwar da nufin in ya kai wata ɗaya
zuwa biyu zai kawo masu ziyara dan Hajiya Zeenat kam cewa tayi ƙafar Zaid ƙafar baby doctor na barin
ƙasar dan tare aka kai su so dan ta ji sauƙi ba yana nufin zata tafi ta bar sa bane a'a tare zasu koma
yanda aka san cewa a tare aka illata su toh ana fatar a taren za'a gan su sun koma lafiyar su ƙalau dan sai
lokacin zasu samu su hukunta la'anannen da ya kusa kai masu ƴaƴa inda ba'a dawowa,ƙulluwa sosai suka
yi da Mudan sunan sa kaɗai suka ji but anything regarding his personal life affairs basu da labari dan ba
ta shi su ke ba kawai jiran farfaɗowar yaran au suke dan hukunta la'anannen zai fi armaahi in suna cikin
daidan su.
When he opened the door,he felt something strange da bai san dalili ba sakamakon ganin ta zaune ita
kaɗai tana cin abincin ta na safe saboda akwai 6am medication da za'a yi serving mata,on normal basis
haka kawai bata cin abinci irin haka dan in bai manta baa jiyan nan da ƙyar ma ta iya cin dinner dan sai
da aka kai ruwa rana sannan ta tsaƙuri kaɗan ta ce ta ƙoshi but yau,right now she is behaving different
kamar wacce ta shekara bata ci abinci ba me yasa?.
Ƙarasa shiga yayi ya kalle ta kafin ya zauna ya kira sunan ta
"Beelove"!!jin kamar sautin muryar sa ya sa ta ce.
"Bilal"tare da ɗagowa dan tabbatarwa because she has been longing to hear his voice. kallon ta yayi
cikin sigar tausayi sai ya ce
"Na'am apple".da wani irin speed ta jawo hannun sa ta riƙe cikin nata ta fara maganganu
"Bilal i missed you,ya aka yi ka san halin da muke ciki har ka sanar da su umma aka kawo mu nan?kana
ji na?ka san wa buge Zaid?Mudan ne..Mudan kuma yarinyar nan yarinyar da muka yarda da ita ita ce ta
nunawa Mudan hanyar da muka bi shine suka zo..suka zo...suka buge Zaid a ta nan" tayi maganar tana
mai nuna mai occiput ɗin ta sannan ta cigaba da magana cikin ƙaraji
"Bilal i want to do something..i hate that girl i hate her with passion she caused all these misfortune i
hate her"da kuka ta ƙarasa maganar.
Me zai ji ya kuma gani?ba dai suspect ɗin sa bane yake shirin zamowa gaskiya?Bilkisu hauka ke shirin
kama ta ne ko mai?da ya shigo she was eating without manners and now tana narrating abin da ya faru
da su a ƙauyen nan bayan ta kai kusan kwanaki huɗu da farfaɗowa kowa na murnar ta farfaɗo but what
is all this?what is he witnessing?sai ya shiga girgiza ta yana magana
"Bilkisu are you alright?are you back for real?did you remember every single thing that happened?and
she?who is she?waye yayi sanadiyar shigar ku wannan halin Bilkisu tell me"??banda girgiza kai babu abin
da take ta yi tun da ya fara maganar har ya ida sai ta amsa kamar mayunwaciya ta ce
"She is a villager a low class girl that i trusted and thought,the girl that claimed to be pure but she isn't
i...i hate her"!!..ta cigaba da kuka bai gane maganar ba sai ya kuma tambayar ta
"Bilkisu look at me..kin tuna abin da na faɗa maki ya faru jiya?kin tuna kin ga halin da brother In-law ke
ciki wanda yayi sanadiyar collapsing ɗin ki"?girgiza mai kai tayi ta ce
"Yeah..i do..i remember everything..see..am not mad i saw him yesterday..nima tashi nayi na ji na tuna
komai..na ga halin da yake ciki kuma na tuna doctor ya sanar da ni condition ɗin sa har ya sanar da ni
cewa wai matuƙar muna so Zaid ya dawo hayyacin sa na kankat bayan ya farfaɗo na farko sai an
m.a........ "tunawa tayi da cewa she promised not to tell anyone about it saboda tashin hankalin da zasu
shiga sai ya fi wannan da suke ciki dan haka tayi saurin kwaɓon bakin ta jin ta fara sauka a kan layi.yin
shirun ta ya haifar wa Bilal tambayoyi daban daban a zuciyar sa toh menene final sauƙin kuma?ai likita
ya sanar da su komai har da period da zai ɗauki Zaid kafin ya farfaɗo so why is she saying wai akwai zai
dawo hayyacin sa bayan ya farfaɗo na farko?ko dai hucin rashin lafiyar ta ne ya sa take maganganu
barkatai?yes,haka ne ma dan yanayin ta na yau kawai zai nuna maka cewa duk surutan da take yi a cikin
magagin recovering if not wani final farfaɗowa zai yi?she is talking nonsense dan haka sai ya shiga saka
ta breathing in and out haka haka har suka yi shi da ita sau biyar sannan ya ce
"Apple i believe you duk abin da kika faɗa weren't delusional i understand but please don't say you last
word to anyone ki bar shi tsakanin mu ni da ke dan kin san families ɗin mu are passing through a lot
already akan wannan matsalar sayin your last word might ignite the range in everyone's heart so please
make it be our little promise hmm"??idon su cikin na juna ta amsa mai da ido,godiyar ta ɗaya na ƙin
tambayar ta ta ƙarasa sentence ɗin da ta fara ɓaramɓaramar faɗin secrete da ta bar wa kan ta.
"Apple zan tafi dan ayyuka na jira na sosai a office i hope idan na dawo zaki gama jin sauƙi kuma zan
tarar da brother In-law cikin good state of health"?amsa mai tayi da kai sai ya kuma yi mata wani
maganar
"Do me a favour apple"!kallon sa tayi sai ta ce
"menene"?
"So na ke ki taya brother In-law recovering daga shock ɗin nan ta inda in ya farfaɗo kowa zai yi murna
mai ɗorewa ke kaɗai ce kika fi kowa sanin hanyoyin da zai saka shi dawowa a matsayin sa na mutum
because you are like him,a doctor,su Abba ba za su iya ba please help him kin ji"har da saka fuskar
tausayi sai ta amsa da
"Toh zan yi"murna yayi sosai har suka rabu yana jaddada mata kar ta bari kowa ya ji maganar da ta fara
faɗa ɗazu.
Abin na ran sa dan haka da ya kirawo Bahajjatu akan su yi sallama sai ya yi narrating mata komai ƙarshe
ya ɗora da
"Apple ni fah gani nake Bilkisu ta sami matsala a brain na ta dan tana abu wani iri can you believe wai
tana gaya min brother In-law zai kuma undergoing wani matsalar bayan ya farfaɗo?toh a ina ta ji kuma
wa ya sanar da ita hakan?she called a name wai Mudan i guess he is the guy that attacked them kuma ta
kirawo wata yarinya bata faɗi sunan yarinyar ba but according to her is like yarinyar ce tayi causing duka
event da ya faru,but that name Mudan..yana min yawo,zan so sanin shi because i overheard Umma
calling that name rannan da aka masu aiki i don't know but am obsess with that name Mudan".da
alamar tambayoyi ya ƙarasa maganar wanda bai dawo tunanin sa ba sai da ya ji muryar Bahajjatu tana
cewa
"Ni na san Mudan kuma about tunanin whether or not shine guy da yayi attacking su Bilkisu shine..ba
wani ba..kuma daga kai har families ɗin mu kar ku damu matsalar has been handled already ba sai an
ɗau wani mataki ba"shiru tayi ta bar shi da mamaki haɗe da sumewar tsaye har ya kasa tambayar ta me
take nufi da 'it has been handled'??
Ƙoƙari yayi ya haɗa kalmar
"Me kike nufi da it has been handled"??sai ta ɗan murmusa ta ce
"Apple tafi kar jirgin ka ya tafi ya bar ka and about the issue?time shall tell in muna da rai da lafiya
hmm"??bin ta da kallo yake sai ya dai yi shiru yau kan sa na son ƙullewa da lamarin ƙawaye biyun.
Raka sa tayi ya shiga taxi dan Hakim ne zai raka sa dama zuwa airport,kamar kar su rabu da juna tana
ɗaga mai hannu shima haka ko kunyar Hakim ma ba su ji haka suka rabu ta koma ciki su kuma suka tafi,a
motar ya kuma tambayar Hakim ko ya san wani wai Mudan amsa mai yayi da eh ya san shi sai ya
tambaye shi ko yana da masaniya da matsalar da aka ce yaron ya janyowa family na su nan ma amsa mai
yayi da eh ya sani kuma babu wani damuwar son sanin hukuncin da za'a mai dan sun yi handling komai
but sai ya ce da shi ya bar maganar a tsakanin su kar ya faɗawa kowa a cikin family members ɗin su,har
suka isa airport jirgin su ya tashi bai daina mamakin abin da ya ke gani ba..
°°°°°°°°°°°°°°
Around 11am na safe bayan Hajiya Madina ta koma ta yi wanka ta ɗan huta ta dawo asibitin dan bata jin
zata iya samin sukunin kanta without seeing her self next to her son shi yasa ta koma asibitin mamakin
ta Hajiya Zeenat ta ji sai dai da ta tuna har yanzu Zaid bar farfaɗo ba ba ta yadda zata sami kwanciyar
hankali shi yasa suka baje a ta garden ɗin asibiti saman babbar darduma yayin da mazajen su ke ta ɗaya
ɓarayin suna tattaunawa game da matsalolin su.a ƙalla ba a kasara ba sau shida Bilkisu na kai kawo
tsakanin ɗakin ta,ɗakin Zaid da garden da su Hajiya Zeenat ke zaune,kowani moves ɗin ta Hajiya Madina
na ankare da ita duk wasu suspense da tensed looks da ke kan fuskar ta tana ankare so take ta shiga
ɗakin Zaid but an saka mata restriction dan jan kunne Hajiya Madina ta yiwa Bahajjatu akan ta kuskura
ta bar Bilkisu ta silale ta shiga ɗakin Zaid har ta kuma collapsing masu toh zata fuskanci hukuncin ta mai
tsauri ita kuwa ganin ba'a yi discovering ita ba ce ta fitar da Bilkisun a jiya ba ya sa ta ɗau alƙawarin kare
ta daga shiga ɗakin a yau dan a zauna lafiya shi yasa ta fito da ita daidai corridor ta inda zata rinƙa hango
shi but bata bari ta shiga ba..
Matsaowa kusa da kunnen Hajiya Zeenat Hajiya Madina tayi ta rage murya ta ce
"Hajiya kina ganin anya ba za mu yi abin da muka jima bamu yi ba kuwa"?dariyar manyan mata suka yi
wanda ya sa mazajen su kallon su sai suka gimtse suma sai suka basar suka juya suka cigaba da
tattaunawar su ganin haka sai suka ƙara murmusawa...
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
*#COMMENT*
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*15*
Gyara zaman su suka yi Hajiya Zeenat ta ce
"Aminiya ina jin ki me kuma kika gano mana ba dai ƴan samarin mazajen mu na hararar waɗannan
matan turawan bane masu jajayen fuskoki sur pimples da spot ba"?da teasing tune ta ida maganar sai
da Hajiya Madina ta dara dan abin ya bata dariya sosai.
"Hmm ke dai aminiya bari ai ba ta kan su muke ba tukunna su zamu koma masu ne bayan mun gama da
wannan matsalar da ke gaban mu"shiru ta yi kafin ta mai da idanun ta towards direction na baby doctor
wanda har a lokacin ta kasa sukuni sai kai kawo take yi duk hankalin ta taahe sai Hajiya Zeenat ta bi
idanun Hajiya Madina zuwa inda take kallon sai ta ga me take kallo juyowa suka yi a tare suka kalli juna
Hajiya Zeenat na mata kallon ƙarin bayani sai ta ɗan dara kaɗan ta ce
"Hajiya Zeenat me kika hango tattare da yarinyar chan"??sai Hajiya Zeenat ta ɗaga kafaɗa alamun bata
hango komai ba sai Hajiya Madina ta ɗan ɓata fuska ta ce.
"Kai Hajiya Zeenat kar ki gaya min har kin fara gazawa wun gano abubuwa mana,yanzu wai duk budirin
da ke kai kawo cikin asibitin nan ba ki gano komai ba"?ɗaga kai Hajiya Zeenat tayi alamun tunani ta daɗe
a hakan kafin ta sauko da kan ta ƙasa ta ce
"Wallahi Hajiya Madina na kasa hasaso komai ban san dalili ba dan Allah dai ki saka ni a kan hanya dan
ciwon kai kawai zan yi da tinanin nan because i don't think i can bring up anything"!!tafa hannu Hajiya
Madina tayi kafin ta fara zayyano mata maganganu
"Kin ga yarinyar nan Bilkisu,a baya da na yi zaton hala ƙiyayya ce mai tsanani tsakanin Zaid da Bilkisu
wanda har nake ganin anya ba zamu shiga haƙƙin su ba in an haɗa auren nan nasu ba dan duk wata
dabara da tarko da muke ɗana masu dan su hau kai ba su hawa but tun da suka tafi wannan outreach sai
na ga sauyi sosai dan in na kira baby ina bugar ruwar cikin ta akan Zaid sai ta natsu ta rinƙa bani labarin
tambayar da na mata haka shima toh ta nan na fara zargin kamar closeness ɗin su ya daɗu fiye da da
kafin su tafi outreach ɗin a haka har wannan ƙaddarar ta sauko mana,ina iya ce maki tun da aka yi
hospitalizing ɗin su har kawo ranar da baby ta farfaɗo abin mamaki da sunan Zaid ta farfaɗo tun daga
ranar bata da magana sai nashi jiya fah da dare har sneaking tayi ta nufi ɗakin sa sai na ga sun dawo tare
da Bilal tana faman risgar kuka suddenly yau yanzu kuma sai gata tana faman zarya tsakanin ɗakin ta
corridor da ɗakin Zaid hankalin ta sam baya tattare da ita duk motsin ta ina ankare sai nake ganin kamar
fah a matso da auren nan nasu kusa if possible kafin ya farfaɗo su bar ƙasar nan tunda kin ga his
personal care is being taken care of by Hakim but kin ga in yana da mata komai ma zata iya yi mai ba
physical care kaɗai ba hatta da psychological care wanda zai taimaka masa yayi saurin farfaɗowa dan
akwai strong connection tsakanin ma'aurata so i just conclude mu haɗa auren kawai sai kulawar sa ya
koma hannun matar sa ta nan ma zai fi samin kula sama da yadda Hakim ke mai dan Hakim ɗin kan sa
ban gama kula da shi ba bare ya kula da yayan shi,this is my experience ya kika gani"??Hajiya Zeenat da
ta yi suman zaune sakamakon jin maganganun Hajiya Madina wabda ya razana ta a ce ta haifi ɗiya ta
raineta har girmn ta but tana cikin wannan halin bata sani ba ba ma ta lura da hakan ba sai da wata ta
sanar da ita,is she a bad mother then??ta tambayi kanta,taɓo ta ta ji anyi sai ta dawo hayyacin ta firgigit
tare da sauke ajiyar zuciya ta fuskanci aminiyar tata ta ce
"Amma Hajiya kina ganin yin hakan ba zai dawo ya haifar mana da ɗa marar ido ba kuwa?dan na ga
kamar dai har yanzu ba wai jituwar da kike tunani bane ke gudana tsakanin su ba ni na fi ta'alaƙa
wannan halin da take ciki da incidence da ya faru da su a ƙauyen nan dan she is the only one that was
with him a lokacin da abin ya faru so is very possible shock da ta shiga ne ya sa da ta farfaɗo ta ga shi bai
farfaɗon ba ya sa duk ta damu dan kin san ɗiyar taki da sakawa kanta damuwa ni mamakin rashin
damuwar ta ma nayi da aka ce zasu tafi outreach,she didn't complain but still ni dai bana son a ma ɗa na
dole dan kawai baya cikin hayyacin sa kuma yana ƙarƙashin ikon mu kar fah ki manta a tarihin rayuwar
mu namiji mace ɗaya yake fara rayuwar shi da kuma da ita yake ƙarewa so what if we decide to get the
two of them married and it end up that yana da wacce yake so da muradi fah?wacce yake burin aura
kuma ita kaɗai ce tsarin sa fah?sai ya farfaɗo ya ji Bilkisu ce matar sa ba wacce yake son ba kina ganin
za'a kwashe lafiya?anya ba zamu shiga haƙƙin sa ba kuwa Hajiya"?tayi maganar ƙarshe da alamar
jimamin lamarin sai Hajiya Madina ta dara kaɗan kafin ta ce
"Me haka kuma Hajiya?ke fah da kanki kin faɗi cewa a tarihin rayuwar mu namiji da mace ɗaya yake
rayuwar sa dan haka ki sani Zaid bai da wata matar a duniyar nan illah Bilkisu matuƙar ina raye kuma ni
na haifi Zaid a ciki na na raine sa har girman sa toh bai da wata mata a duniyar nan sama da baby either
he likes it or not bare ma ba zai ƙi ta