Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 74

9K to 12K   out of 221.1K words

hana ta fita dan abin kamar wani sabon abu a duk lokacin da
zata tafi dubo patient ɗin ta muddin dare yayi toh tsoro ba zai bar Hajiya Zeenat ta amincewa ɗiyar tata
zuwa dubiyar ba sai an sha fama shi yasa bata ƙaunar gaya mata tana da morning theater sai dai ta ce
theater ɗin zai yi commencing by 1-2pm dan in dare yayi ta bar ta ta tafi dubiyar patient ɗin ta.



A yau ɗin ma dramar kenan gashi apple ɗin ta na son jaza mata dan haka ta yamutsa fuska ta yi shiru
abin ta ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat ta yi saurin miƙewa ta isa kujerar kusa da tata ta zauna ta fara
taɓa jikin ta duk ta ruɗe



"Baby jikin ne?ina ke damin ki?ba dai sanyin air split ɗin theater ɗin nan ne ya maki yawa ba"?duk ta
ruɗe wanda hakan ya janyo attention ɗin sauran family members ɗin suka mai da duban su ga baby
doctor.,ita kuma ganin hankalin umman ta ya tashi ya sa ta ɗan sasauta tamke fuskar da ta yi ta ce



"Babu ko ɗaya umma"daga haka ta yi pim haka fah yayan ta Lukman ya rinƙa tambayar ta ƙarahe
hawaye ta fara matsewa daga idanun ta ta miƙe ta ce da twin brother ɗin ta



"Apple ungo zo ka raka ni"ta wurgo mai maƙullin motarta ya cafe ya na mata alamar ya zata mai haka
daidai lokacin ya ke samin damar ganawa da Bahajjatun sa itama kallon tashi mu je kawai ta mai dan
bata jin wani doguwar surutu dan kar ma a gane faking fushin ta take yi,



Zai yi gardama ta ce mai

"Ka tashi mu tafi kawai kokuma wallahi in jaza ma babu abin da ya shafen"ta juya baya ta fara tafiyar ta
sumsum ya miƙe ya sallame su wai sai sun dawo yaya Luk kawai ya amsa yana murmushi dan ya san
borin gwal ɗin gidan ya tashi yau babu ji babu gani.



Bayan sun fita babu daɗewa ya kammala cin abincin sa ya ma iyayen na sa goodnight dan ya ba wa
Abban su space ɗin rarrashin Hajiya umman su sakamakon chanjin yanayi da ta shiga tun bayan fitar ƴan
biyun ta Abban su kaɗai ya amsa goodnight ɗin yayin da umman ta kyaɓe fuska Lukman na barin wurin
ta saka ma prof kuka mai haɗe da shesheƙa tana cewa
"Prof ka ga yadda Bilkisu ta bar gidan nan kamar fah ran ta a ɓace yake ta fita na ɓatawa ɗiya ta rai ka
kirawo min ita ta dawo in rarrashe ta i didn't mean to offend her emotions"sai kuka shi kuwa da ya san
halin abin shi ya san darun ta sarai yanzu akan ƴaƴan ta sai ta fita hayyacin ta in har ita ke da laifi toh
babu sukuni har sai sun daidaita dan haka ya ɗaga ta suka bar falon suka wuce bedroom ɗin su inda ya
bata assurance ɗin cewa komai zai yi daidai ai Bilkisu mai hankali ce da kyar fah ya rarrashe ta akan da
safe zata bata haƙuri har da kwanciyar bacci amma tana ganin ya ɗan yi nisa a baccin sa ta miƙe ta koma
falon zaman jiran dawowar su duk ta rikice..




_Back to Dr Maher's house_



Da ya shiga ciki da tarikicin Hakim ya fara karo suna mai sallama tsaƙi ya ja ya wuce ya rasa dalilin da ya
sa muddin Hakim ya dawo gida duk gyaran da za'a kwana a yini ana yi ma gidan tas sai ya hargitsa shi in
aka yi magana ya ɓige da cewa experiment yake yi shi a dole ga kwararren scientist hatta da kula da kan
shi ma sai Ammin su ta yi kamar zata mai wanka da kan ta kafin ya yi dan shi in ta tashi ne bai ƙi sai 12
ɗin dare ba dan tsabagen aikin dan a gaskiya shi ɗin haziƙi ne akwai brain ba laifi a ko da yaushe jiye mai
da yayan shi ke mai shine yadda matar shi zata iya zaman haƙuri da shi dan fah shi kullum a cikin utilizing
time yake kamar sanƙiran hanzari..yana da wani abin da yake so yayi inventing dan haka yake cikin
charging kwakwalwar shi babu ji babu gani.



"Hakim!!! Hakim!!! da ɗan ƙarfi ya kira shi yana mai banko mai ƙofar ɗakin sa.duk dai bata sauya zani ba
dan nan ɗin ma kacakaca da kaya da ƙyar ya kutsa ya shiga ciki ya hango shi kan reading table da babbar
computer system ɗin sa gefe ga manyan pamphlet babu iyaka ɗan tsayuwa yayi a kan sa na mintuna
kafin ya ɗan taɓa shi,a ɗan firgice ya ɗago suka yi ido huɗu da yayan na shi.



Bambancin su tazarar shekaru ne dan kamannin su sak iri ɗaya ne da juna.

Miƙewa yayi yana murmushi ya cire glasses ɗin da ke idanun sa masu rage mai kaifin haske ya gaida
yayan nashi



"Good day big bro wallahi tun ɗazu nake ta jiran ka ka dawo akwai wani chemical combination ne da ya
shige min i couldn't sort it out"!kallon sama zuwa ƙasa ya mai kafin ya matso da doguwar hancin sa gab
da jikin ɗan uwan ya shiga sunsunawa sannan ya ɗago ya tsaya ya ce da shi
"You stink go get shower sai ka dawo mu cigaba da magana and make it snappy coz i will be going
out"daga haka ya juya ya fita leaving Hakim a tsaye yana shafa kanshi yana murmushi kafin shima ya
wuce toilet ya fara wanka..




Shima wankan yayi ya fito kenan ya tararda missed calls har huɗu bin kiran yayi ya sanar da cewa nan da
15 minutes yana zuwa sauri sauri ya shirya ya fita ya manta shaf da ɗan uwan sa da ya ce mawa ya same
sa.



Da sauri ya fita daga gidan ya wuce iyayen su da ke zaune a pool side har lokacin kiran sa suke yi amma
ya wuce yana mai cewa



"Yanzu zan dawo"motar shi ya shiga ya fige ta sai asibitin da zuwan sa cikin sauri ya sa aka yi setting mai
theater suit saboda emergency caesarean section da zai yi.



Babu wani time dan haka aka yi saurin haɗawa yayi changing zuwa kayan aiki wani Dr Mark ne ya yi
assisting ɗin shi suka yi lafiya suka gama lafiya bayan ƴan observation aka wuce da matar zuwa ga post-
op room sannan ya koma office ɗin sa ya ɗan yi relaxing..




Kiɗa ya saka a motar ta yi saurin mangare hannun shi ta chanza zuwa wani wa'azi sannan tayi lowering
volume ɗin chan ƙasa zai taɓa ta hayayyaƙo mai



"Kana taɓawa zaka fita wannan motata ce ba taka ba yauwa"! Ta jingina kan ta da kujera tana tunanin
yadda tafiyar ta su zata kasance. interrupting ɗin ta yayi ta hanyar magana



"Apple kenan kun shirya da brother in-law"!? Wani kallo ta kwashe shi da shi ta juya kai kawai ya kuma
ƙoƙarin furta wata kalmar ta riga shi

"Apple wallahi kana takura ni"shiru yayi dan yau kam laifin asibiti na son shafar kowa..ƙala bai kuma
cewa ba har sai da suka isa asibitin ya zaga ya buɗe mata ƙofa ta fito ya mayar ya rufe suka tako har cikin
asibitin tare da yake dare akwai restricted movements sai ƴan tsiraru da ba za'a rasa ba.
Gaisawa suka yi da receptionist ɗin ta masu barka da dare suka wuce ciki,ɗakin patient ɗin ta ta wuce
apple ɗin ta na bayan ta,ƴanuwan patient ɗin ne suka gaida ta ta amsa cikin girmamawa shima Bilal ya
gaida su suka amsa suna mamakin kamanin su kallon yayan ta suke mai since shi ɗin jibgege ne tun daga
girman jiki har tsayi ya fi ta sai suka kasa yin shiru har sai da suka tambaye ta

"Doctor wai wannan ɗin ɗanuwan ki ne"? Kallon junan su suka yi suka murmusa dan an saba yi masu ire
iren waɗannan tambayoyi



"Eh ɗan uwa na ne"!sai suka ce daga gani ai sun shaida,dariya kawai suka saka daga haka ta tambayi
matar patient ɗin ko ya farfaɗo

"Eh doctor ya farfaɗo ɗazu ba ki nan sai ɗayan likitan nan ne ya zo wucewa daidai ya farfaɗon sai muka
kirawo shi shine ya zo ya duba shi"! da mamaki ta tambaye ta

"Wani likita kenan"?



"Wannan ɗin nan doctor ZM naji ana kiran shi ko menene"!

Ɗan exclaiming ta yi ta ce

"Oh yeah shi,ok toh yanzu ya jikin nashi"?

"Alhamdulilah doctor har fah ƴar hira muka yi da ya farfaɗo"suka ɗan dara kafin ta jadadda masu kar
fah su takura mai har sai ya taso da kan sa suka amsa mata haɗe da yi mata godiya daga haka ta sallame
su.



Fitowar su kenan ta ja shi zuwa office ɗin ta ta zaunar da shi ta fara mai tambaya

"Apple,wai am i that bad"?natsuwa yayi ya bata hankalin sa kafin ya amsa mata da

"Not at all apple me yasa kika yi wannan tambayar"?ɗan shiru ta yi kafin ta miƙe tsaye tana ɗan zagawa
na wasu lokuta sannan ta cigaba da magana



"Apple ka san tafiyar nan ba da niyya ta za'a yi shi ba"!!juyawa yayi ya kalle ta kafin ya ce

"Ban gane ba apple"zama tayi ta ƙura mai ido kamar wacce ke son fiddo Wani abu a kallon da take mai
"Apple Zaid mugu ne he must have planned something bad da ya sa ya matsu sai mun yi wannan
outreach ɗin tare i don't trust him"a nan ta kwashe labarin abin da ya faru da safen ta sanar da shi



Madaɗin ya nuna damuwar sa sai ya share ya ce mata

"Apple kin san dai da brother in-law na da mugun hali da tuntuni an gano hakan but ni nake ga kawai
hanyar shiryawa yake nema if not ban ga me zai sa ya bar family ɗin shi da career ɗin shi a nan ba ya tafi
wannan dajin Koman dan ya maki mugun abu ba"shiru tayi tana kallon shi kafin daga bisani ta miƙe ta ce
mai



"Tashi mu tafi ypur brain always boot about bank stuffs baya nuna maka reality da ke gaban ka talking
to you is always a waste of time apple"wucewa tayi ya biyo ta yana dariya.



Suna hanyar su ta fita bata sani ba ta bangaje shi da sauri ta furta

"Oh goodness am so sorry"ɗagowar da zata yi ta gan shi a tsaye wani mugun takaici ne ya ziyarci zuciyar
ta kamar ta gasa mai magana sai dai ta share ta yi gaba yayin da Bilal ya tsaya suka gaisa dan ya baƙanta
mata ya rinƙa jan Bilal ɗin da hira dan dai kawai ya bar ta tsaye tunda ya san bata night driving definitely
Bilal ɗin ne ya kawo ta kuma ya san in har yana wurin ba za ta iya magana da ɗan uwan nata ba gashi
Bilal ba laifi akwai surutu kamar alƙalin aku.bai tashi releasing ɗin Bilal ba sai da ya ga ta gaji da tsayuwar
sannan ya ce da shi

"Ga fah ƴaruwar ka chan na jiran ka"shaf ya manta da ita a tsaye da gudu gudu ya ƙarasa wun ta yana
bata haƙuri ya yi saurin buɗe ƙofar motar ƙala bata ce da shi ba ta shige suka kama hanya yayi ta
magana komai bata ce da shi ba ya bata haƙurin har ya gaji haka suka dawo gida ta riga shi shiga tarar da
Hajiya Zeenat ta yi a zaune ta yi mamakin rashin baccin da bata yi ba 9:34pm amma bata yi barci ba ta
manta sun yi faɗa da umman na ta kafin ta fita



Da ganin shigowar ta ta miƙe ta nufe ta tana ce wa

"Baby kin yi fushi da ni ki yi haƙuri i was so concern about your health shi yasa nake tsoron barin ki kina
fita da dare ga sanyin yau yayi yawa please forgive me baby i never meant to offend you am sorry"!!
rungume ta tayi tana ce mata



"Haba umma sau nawa nake hana ki zaman nan akan wani fake anger ɗi na and i know that you cried
why are you behaving like a baby"?rungume ta tayi itama sosai dan tana tsoron rasa ɗiyar tata akan
condition ɗin ta shi yasa tafi tsaurara mata ƙaidoji.Bilal da shigowar shi kenan ya gan su zai yi magana ta
yi pulling daga jikin umman su ta fara tafiya

"A word from you will increase my anger ba zan yi having conversation da kai ba sai gobe"ta ce da
Hajiya Zeenat

"Umma je ki kwanta sai da safr na gaji"..



Ta yi shigewar ta leaving them staring at her inda umma ta balbale shi me yasa zai ɓata mata rai shima
ɗin wucewa yayi Hajiya Zeenat ma ta wuce bedroom ɗin su tana sababi..




Bayan ta shirya cikin kayan bacci ta yi setting laptop ɗin ta ta ɗanna kira babu jimawa yayi connecting
aka ɗauka wata kyakyawar budurwa ce sanye cikin chiffon mini top babu ɗan kwali a kan ta ta yi sallama
tana murmushi



"Wa'alaikumul salam"

"Beelove ya kije ya apple ɗi na"?



Harara ta danƙara mata ita kuma ta kece da dariya tana cewa

"Haba Beelove wai laifin me aka miki ne yau na ji apple na complaining temper ɗin ki yau ya ɓaci"!tsaƙi
ta yi ta ce



"Rabu da shi zan yi maganin shi ne ai yanzu ba wannan ba yaushe zaki dawo Baha"?ɗan dariya ta yi
kafin ta ce

"Don't tell me you are missing me already"



"Yes i am kuma akwai maganar da nake son yi da ke shi yasa na matsu ki dawo"!



Ɗan juya ido tayi kafin ta ce
"Nan da 5 days kayan ne ban ga taste ɗi na ba da tun jiya na dawo"da murna ta ce



"Alright till then sai da safe headache na dami na yau surgery huɗu na yi i need to rest"daga haka suka
yi goodnight..




**************



A lissafi saura kwanaki 6 su tafi outreach ɗin su wanda har lokacin babu wata kyakyawar maganganu ko
alaƙa mai kyau tsakanin su amma da haka ake kan bakan za'a yi tafiyar outreach zuwa Adamawa.



Da safen ranar wacce ya kasance asabar,al'ada ce ta gidar akan duk asabar haɗuwa ake yi wu ɗaya a yi
spending saturday ɗin tare da juna dan haka bayan sun gama breakfast suka shirya zasu tafi Nija Motels
dan cikasa ranar,prof ne da Hajiya Zeenat cikin shigar kayan beach iri ɗaya nashi na maza nata kuma na
mata hatta da kalar iri ɗaya ce babu bambanci da hulunar cowboy sun mammaka a ka za'a yawon buɗe
ido chan ma Dr Maher da Hajiya Madina shiga iri ɗaya suka yi kamar dai irin na su Prof suka haɗe a gate
cikin motocin su komai an yi packaging ɗin shi an saka masu a mota horn suka yi wa junan su suka hau
kan titi babu wasu drivers dan ba su buƙatar su tafiyar holewar su ne masu kallon asiri are not
needed,ƴaƴan kamar su fashe dan haushi haka dai suka bar su kowa ya cigaba da sabgar sa..



Fitar su babu daɗewa Hajiya Madina ta kira Bilkisu a waya wai sun manto earpiece ɗin su a gida da
headphone ɗin Dr Maher dan Allah ta je ta ce da Zaid ya kawo masu yanzu.



"Oh ni Bilkisu i can't say no to this woman in ba haka ba a rasa wanda za'a kira ya je aike sai ni"haka dai
ta fito daga gidan su ta saka slippers ɗin ta fito daga gidan su ta shiga cikin gidan su Zaid duba shi ta yi
bata gan shi ba ta cigaba da zagaya gidan har dai ta iso pool side inda ta hango shi kwance saman couch
ɗin pool ɗin idon shi manne da sunglass gefen shi apple ice ne ga hand towel a gefen shi daga shi sai
boxers babu riga a jikin shi,gwalalo idanun ta tayi tana ƙoƙarin juyawa kenan ta ci karo da mai aikin gidan
zai kai mai wani drink ɗin kafin ta hana shi magana har ya rigata



"Hey goodmorning baby doctor how may i help you"?runtse idanu ta yi tana jin haushin sa ai ko ya miƙe
jin an kira sunan baby doctor
Neman rigar shi yayi ya saka cikin hanzari yana roƙon Allah ya sa bata gan shi a haka ba



"What could she be doing here"ya tambayi kanshi.

Kasa ba ma mai aikin amsa tayi kawai sai ta cigaba da tafiya da nufin in ta koma gida sai ta aiko Bilal ya
faɗi saƙon amma tana fara tafiya ta jiyo muryar shi cikin ɗan fushi yana cewa



"Hey me ya kawo ki gidan mu by this time"? bata juyo ba amma ta tsaya haushin ɗaga mata muryar da
yayi ta ji sai ta ce mai



"Gidan masu gida dai, kuma ni Ammi ce ta ce in sanar da kai sun manto earpiece da headphone ɗin su
ka ɗauko ka kai masu"tana kaiwa nan ta wuce tana tsaƙi..



Mamaki yake yi ga wayar shi nan kusa da shi babu missed calls ko ɗaya bare ya ce kira suka yi bai ɗauka
ba suka kira ta toh me suke nufi na aiko ta by this time ga Hakim nan a gida ba'a kira shi an aiko shi ba
sai ita lallai there parents are up to something



Tsakin yayi shima ya saka takalman shi dan dubo masu abin da suka ce sun baro a gidan,



Ita kuma da ta koma gida ta rufe ƙofa ta shiga zirga zirga tana ƙoƙarin calming kan ta in any way possible
dan kuwa tun da ta gan shi ɗazu har yanzu yanayin da ta riske shi ya ƙi daina yi mata gizo da kyar ta
yakice abin ƙarshe ma shiryawa ta yi ta wuce zuwa gidan yayan ta Jamil dan ta rage wani abin tunda
ayyukan ta na ranar are less daga chan sai ta wuce zuwa hospital ɗin may be zata rage damuwar da ke
ɗawainiya da ita.



Shi kuwa da ya koma cikin gidan dan ɗauko masu saƙon su ya duba ya gani sai ya chanza kayar sa zuwa
ƙanana ya fito da saƙon a hannun sa ya wuce zuwa wun motar sa ya shige ya ja har chan kiran su yayi a
waya dan jin inda suke suka mai kwatance ya tafi.abin haushi sai yi suke kamar wasu yara gaida su yayi
kan shi a ƙasa ya miƙa masu saƙon ya juya zai wuce sai ya ji muryar Ammin sa tana cewa
"My boy please ka tafi ka dubo min lafiyar baby doctor dan umman ku ta ce tun jiya bata ji daɗi ba
gashi na aiko ta wun ka ban sani ba sanyi ya taɓa ta please go check on her huhh"rasa abin cewa yayi
dan he can't believe that his parents are for real,girgiza mata kai kawai yayi ya wuce



Jan motar yaje yi kamar motar ce ta aike shi bai tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan su yana fita daga

4 / 74