Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   45 / 74

132K to 135K   out of 221.1K words

ya
tari taxi ya ce a kai sa gidan su,..

Bayan sun iso gidan ne shima gate man ɗin su ya taya sa kwashe kayan sa jar yake mai barka da
dawowa dan lallai ya tsallake rijiya da baya ya so sanar da shi kamar ya ji muryar mai gadin gidan su
Baby doctor na ma wata barka da dawowa sai dai ya kwaɓi kan sa dan ya san a gaban idanun sa aka
ɗaura auren su ƙila wani dalilin ne ya sa basu dawo tare ba shi nashi ido ne kawai...



Bayan shigar sa gidan ne ya kai ɗakin sa sai ya ga komai ya canza masa babu abubuwa da dama a
ɗakin,kenan an kwashe an kai su chan gidan.

Wanka yayi da warm water ya zo ya biya sallolin da ake bin sa da ya gama ya sauko ya haɗawa kansa
quacker oat ya koma ɗakin sa.a nan ya sha bayan ya gama ya ɗauki magungunar sa ya sha sannan ya
kwanta yana tunanin ta jefi jefi daren su na jiya na dawo mai,juyawa yayi ya gyara kwanciyar sa yana
cigaba da tunanin ta har dai ɓarawon ya sace sa,ba shi kaɗai ba har ita baby doctor kasa bacci tayi da
wuri tana ta tunanin sa da abin da ya faru tsakanin su da ƙyar da kukan wahala baccin gajiya da dole ya
ɗauke ta...



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_
*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*




*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*29*



*_The ZM Residence_*



Maƙil yake cike da jama'a wanda mafi akasarin su family ne sai closed friends,gidan ba ƙaramin ado aka
mai ba duk inda ka juya walwalin hasken ƙwayayen wutan lantarki ne kaloli daban daban masu bada
ma'ana da ɗaukar ido,shagali ake yi ba ƙarama ba dan cikin mahalartan wannan taro har da abokan aikin
waɗannan couples,fannin families daban na friends daban ana ta walwala da fara'a dan ƙiyasta irin
annashuwar da waɗannan ahali ke ciki ba makusantan su ba har waɗanda ba kusa suke ba sun san irin
farincikin da suke ciki ƴaƴa har biyu daga abin alkhairi sai a dawo da su ranga ranga har sai da aka
dangana da fitar da su ƙasar waje dan samin lafiyar su sannan a ce duk sun dawo hayyacin su ga wata
babbar alaƙa da ta kuma ƙulluwa a tsakanin ƴaƴan nasu ai dole ma su yi farincikin wannan rana.

Ba nan kusa suka ɗauki liyafar tarbon ƴaƴan nasu ba dan a yadda suke communicating da su sun nuna
masu cewa daga su sai su ne babu outsiders but sun gayyato family friends dan yayi serving as a surprise
to them.
Hajiya Zeenat ce riƙe da wayar ta a hannu tana ta faman trying layin Bilkisu amma sai dai a ce da ita on
another call ta cigaba dai da trying dan ta san ba wani kira babyn take yi ba kawai a divert aka saka
numbern ta but why abin da ta kasa ganewa kenan sai ta shiga trying na Zaid,ta yi sa'a nasa ya tafi sai dai
ba'a ɗaga ba har ya tsinke sake gwadawa tayi nan ma ba'a ɗaga ba sai hankalin ta ya fara tashi ta bar
inda take tsaye ta nufi inda prof yake shi kuma yana kan gaggaisawa da mutani,tana zuwa yayi sighting
tashin hankalin da ke tatyare a fuskar ta sai ya ce da baƙin yana zuwa.

Tana nufo sa shima yana zuwa towards her direction duk hankali tashe,colliding suka yi a hanya sai ya
riƙo hannun ta zata yi magana ya jawo ta gefe gudun kar ta saki magana gaban guests ɗin su.

Hankali tashe ta shiga yi mai bayanin abin da ya faru shima sai nasa hankalin ya tashi har ya so fin nata
but yayi ƙoƙarin suppressing nasa dan kar ya sage mata gwiwa ya ruƙo ta da kyau yana faɗin

"Yanzu ki kwantar da hankalin ki zan aiki Jamil ya dubo mana ko akwai matsala ne da ya sa jirgin su bai
iso ba but please do me a favour,don't let anyone know about this kin ji"??kallon uku saura kwata ta mai
kafin ta shiga girgiza kai tana faɗin

"Prof you know nothing about the pains of a mother a duk lokacin da aka ce da ita ɗan ta na cikin
damuwa kawai faɗin lafuzan bakin ka kake yi dan suna maka daɗin faɗi"tana kaiwa nan ta bangaje sa
tayi wucewar ta tana ƙoƙarin controlling hawayen ta dan tun ɗazu take ji a jikin ta kamar na lafiya ba sai
dai ganin lokacin flight arrival na su bai kai ba sai ta share amma ganin har awa ɗaya ya shafe babu su
babu alamun su sai hankalin ta ya fara tashi gashi wayoyin su duk babu mai ɗauka hakan ya kuma ɗaga
mata hankali shi yasa ta fara neman Dr Sulaiman amma ga abin da ya sanar da ita sai ta ga kamar ba
damuwa yayi ba..



Nemar Hajiya Madina ta shiga yi dan tana ganin maybe ita ta samo masu mafita dan kamar su iyaye
mazan nan ba damuwa suka yi da matsalar da iyaye mata ke ciki ba ko a reaction ɗin sa bata ga alamun
damuwa ba..

Hango ta tayi tsaye da Afzal tana magana da shi sai tayi saurin nufo su,tana zuwa ya matsa dan basu
wuri sai Hajiya Madina ta juyo tana kallon ta da mamaki ta ce

"Hajiya Zeenat lafiya kuwa na gan ki haka kamar kina cikin wani damuwa"!!..ajiyar zuciya Hajiya Zeenat
tayi kafin ta ce

"Ina na ga lafiya Hajiya Madina,,sarai kin san yau yaran nan zasu dawo kuma a ƙa'ida ya kamata ma a ce
by now sun dawo har an kusa kammala liyafar nan tare da su but har yanzu a ce babu su babu alamar su
sannan dukkan su babu mai ɗaukar waya?ita Bilkisun ma da fari wayar ta na shiga ɗauka ne kawai bata
yi but now....,her phone isn't reaching through and na Zaid...na kira ya fi a ƙirga but baya picking and ina
ji a jiki na kamar ba lafiya ba na ma prof magana amma sai ce min yayi wai in jira har ya tura Jamil airport
ya ji ko lafiya...ta yaya hankali na zai kwanta"..shiru Hajiya Madina tayi tana digesting maganganun
aminiyar tata but sai ita kuma ta fahimci maganar ta wata siffar
"Ban ƙi taki ba but don't you think you are over exaggerating?yaran nan fah ba ƙananu bane bare a ce
dole sai mun takura su ba kina dai gani kullum muka kira su they are always busy kin dai san halin yaran
zamani bare yanzu da suke jin kansu ɗanye sun sami lafiya the will always be like a glue ko ina suna tare
dan hayaƙin newly wedded couples bai bar su ba har yanzu fah amarcin su suke ci so i see no reason
why you should be disturbed dan babu tantama they must be doing something important you know irin
bedroom cuddles ɗin nan da maybe basu yi ba da safe due to tafiyar da zasu yi yau maybe shi suka tsaya
yi a wani wurin kafin su iso gida dan sun san in sun dawo jama'a zasu masu yawa ba lallai bane su sami
time ɗin junan su ba and they must have been tired late at night and they can't do anything so sun
zaman yi a wani wurin don't you think maybe wannan shine dalilin su"??kallin ta Hajiya Zeenat tayi haɗe
da girgiza mata kai kafin ta ce da ita

"Duk wai babu wanda zai fahimce ni ne?this is a very sensitive issue ba abin wasa ba..about their
cuddling ai duk wannan can follow dan ba tangible reason bane da za'a ce shi ya hana su ɗaukar waya ta
ba"..ɗan murmushi Hajiya Madina tayi ta dafe kafaɗar aminiyar ta

"Hajiya Zeenat ni fah ban ga wani abin ɗaga hankali ba,yaran nan fah sun mallaki hankulan su,dole suna
tare da junan su by now and ke kanki kin san ba a ƙarƙashin mu suke ba yanzu they are on their own su
ke da ikon kan su namu da su yanzu shine nu tsawatar masu in suna son bin hanyar da bai dace ba but
bamu da alhakin shigar masu rayuwar auratayyar su just like that...so calm down and just relax
inshaAllah komai zai zo mana da sauƙi i know yaran nan na nan lafiya kawai saurin ruɗewa ce irin ta mu
but is okey"juyar da kai Hajiya Zeenat tayi gefe sai ga hawaye na bin kuncin ta ba komai take tunowa ba
sai wahalar da ƴaƴan suka shiga not quite long da irin jinyar azabar da suka yi na dole duk tsoron ta ba
dai wani abin ne ya same su ba wanda ya sa har suka kasa ɗaukar kiran ta..

Juyowa tayi tana share hawayen ta da handkerchief a ruɗe ta ce da Hajiya Madina

"Toh ki kira mana layin shi Zaid ɗin maybe yayi picking"!!!sauke numfashi Hajiya Madina tayi dan ta ga
hankalin aminiyar tata ba ƙaramin tashi yayi sai ta ce

"In har Zaid bai ɗau kiran ki ba toh ni wacece da zai ɗau nawa kiran?uhmm?ki daina ɗaga hankalin ki
dan ni na san ƙalau suke kawai tsantsar saka abin da kika yi ne a ranki ya sa kike ganin kamar ba lafiya
ba"..Juyawa kawai tayi ta bar Hajiya Madina tsaye ta shiga neman Bilal bata gan sa ba har ta gaji da
neman sa sai ta yi karo da Lukman da ke waya.

Da zuwan ta bata tsaya jiran ya kammala wayar ba ta taɓo shi sai ya juyo ya ga ita ce yayi saurin
sallamar wanda yake wayar da shi ya sauke wayar daga kunnen sa

"Umma lafiya na ga kamar kina cikin damuwa"sai ta fara magana cikin karayar zuciya

"Lukman ƙanwar ka da mijin ta ba su ɗaukar kira na kira su sama da a ƙirga basu ɗau kira ta ba na ma
Abban ku magana bai ɗau abin da muhimmancin ba na ma Ammin ku magana bata yi reasoning da ni ba
ya suke so in yi"??sai ya shiga duhu but ya jawo ta suka bar wurin dan Hajiya Zeenat in har hankalin ta ya
tashi ko a taron dubban jama'a ne ba ko wani lokaci take iya controlling kanta kar ta nuna a gaban
mutani ba..
Suna zuwa gefe ya riƙo hannun ta yana faɗin

"Yanzu Umma na me kike so a yi"?sai ta share hawayen ta ta ce

"So nake ka fara kiran min su in ji ko lafiya sai su sanar da kai abin da ya tsayar da su a hanya"gyaɗa
mata kai yayi yana mai fiddo wayar sa,ƙunnawa yayi sai ya laluɓo numbern Bilkisu yayi dialing amma
abin mamaki har ya ƙaraci ringing ba'a ɗaga ba ya kuma dialing amma nan ma still ba'a ɗaga ba shima sai
ya ji hankalin sa ya fara tashi zai kuma dialing ta dakatar da shi

"Bar ta haka,yanzu ka kira layin Zaid mu ji"bin umarnin ta yayi ya dubo numbern Zaid ya shiga kira kusan
sau huɗu ba'a ɗaha ba sai ya kira ɗaya layin nasa nan ma ba'a ɗaga ba.

Tashin hankalin da ta shiga ciki har ya ninka wanda ta shiga ɗazu,a ruɗe ta fara magana da Lukman

"Luk kana ganin anya lafiya kuwa baka ganin kamar suna cikin matsala ko wani abin ne ya same su"??
riƙo ta yayi yana girgiza mata kai ya ce

"Umma calm down i will find out just compose yourself nothing of such is gonna happened okey trust
me"girgiza mai kai tayi daga haka ya sake ta ya kama hanyar zuwa neman Bilal.



A fannin prof kuwa bayan Hajiya Zeenat ta bar sa tsaye kiran wayar ƴaƴan nasu ya shiga yi sai dai basu
ɗaga ba sai ya duba Dr Maher da ƙyar ya hango sa a nan yake sanar da shi abin da ya faru sai yayi shiru
abin sai lokacin ya shige sa sai ya shiga neman layin Zaid but ba'a ɗagawa duk hankulan su tashe ga
mutani duk sun matsu su ga baƙin germany but har yanzu shiru wasu har sun fara ƙananun maganganu
wai an tara su sannan yara basu zo ba wa ya sani ko gado iyayen su suka yi wun yawon baje soyayya a
wurare maybe tafiyar su suka yi wani wurin dan ɓarje soyayyar su su kuma an bar su nan kamar marasa
abin yi,a kunnuwar Dr Maher Muhammad,duk maganganun nan yana jin su sai ya juyo ya kalle su sam
basu san yana kusa da su ba sai suka shiga kame kame but he have caught them already kuma dole ya
mayar masu da martani

"Alhamdulilah dama kyawun ɗa ko ƴaƴa muddin ƴaƴan halas ne toh su gaji iyayen su kuma MashaAllah
ba gadon zina suka yi ba gadon tsantsar so,yarda da aminci mai tsafta suka yo dan shi mu iyayen su suka
ga muna yi kuma abin alfaharin mu ne ƴaƴan mu su fi mu ba su yo gadon su daidai mu ba,na san kun
fahimce ni sosai right"??shiru suka yi cikin jin kunya da nauyin sa dan tun da suke mu'ammala da shi
basu taba ganin sa yayi displaying ɓacin ran sa a fili haka ba he is always gentile and silent but gaahi yau
mai basu amsa daidai su wato Dr Sulaiman bai ba su ba sai shi kan sa lallai sun janyowa kan su dan haka
suka buɗi baki da nufin ba shi haƙuri amma shocking interruption suka ji daga gare sa

"Is okey kuna iya tafiya gidajen ku and gobe ba jibi ba kuyi evacuating min asibiti dan mutumin da bai
da ƙima a idanun ku bai kamata ya cigaba da ciyar da ku ba kamata yayi ku tafi ku nemi wanda is capable
enough responsible and waɗanda ƴaƴan su nasu yo gadon iyayen su ba su baku muhalli a ƙarƙashin
inuwar su"yana kaiwa nan ya ce da prof
"Zo mu tafi Dr Sulaiman"haka suka wuce mutanin nan leaving them standing idol,bayan sun wuce su ne
prof ya dakatar da Dr Maher

"Dr amma wannan hukuncin yayi masu tsauri da yawa kuma ka yanke hukunci cikin fushi you shouldn't
have done that"kallon sa Dr Maher yayi kafin ya ce

"Prof ka fah ji abin da suke faɗi ƴaƴan namu zasu aibata haka su ce da su wai gado mu suka yi?kenan
mune iyayen banza marasa kamun kai ko?toh ai yayi tunda yanzu nayi setting nasu free suna iya yin duk
yadda suke so"yana gama faɗa haka ya ce da shi

"Mu tafi airport"mamakin sa prof ya ji dan bai saba yin hakan ba,girgiza kai yayi kafin ya shiga motar sa
shima Dr Maher ɗin ya zaga ya shiga,tada motar Prof yayi ya ja suka bar new residence ɗin ƴaƴan nasu..



Zaune suke kusa da pool side ɗin gidan suna faman soyewar su kamar babu gobe,hira ta yi masu daɗi
sai dariya suke yi buɗar bakin sa kenan da nufin yin magana amma ya ji muryar yayan sa sai ya juyo yana
mai ɓata tai dan sam baya son abin da zai yi distracting masa hirar sa da apple ɗin sa hakan ne ma ya sa
ya ce da ita su gudo su zo nan dan nan ne kawai babu hayaniya amma binciken ƙwaf irin ta yayan sa ya
sa ya gano su a nan..

Kallon ta yayi kamar wani sokon mata ya ce.

"Apple am coming ki bani minti biyu i need to see yaya Luk"gyaɗa mai kai tayi tana murmushi.

Tashi yayi ya nufi inda yake yana ɓata fuska shi dole gashi auta ya tsaya a tsaye ya ce

"Yaya Luk me kuma ka zo har nan wurin masoya"?ba lokacin shirme bane dan haka bai biye mai ba ya
ce.

"Yaushe kuka yi magana last da Bilkisu"?sai ya shiga taitayin sa ya ji faɗuwar gaba ya riske sa sai ya
shiga tuno rabon su da yin waya

"18 hours ago"jijjiga kai Lukman yayi ya ce

"Ba su ɗaukar wayoyin su and this is past 10 ya kamata sun dawo by now"sai Bilal ya ruɗe kafin ya ce

"What happened brother,ko dai an sami matsala ne da flight ɗin su"???..

Girgiza kai Lukman yayi kafin ya ce

"Duk ba wannan ba yanzu ka zo mu tafi airport mu dubo su any other thing follows later"shi da yake
jimamin rabuwa da masoyiyar sa sai ya ma manta roƙon ta yayi mintuna biyu har ya bi Lukman ɗin sai ya
jiyo muryar ta tana cewa

"Bilal ina zaka tafi"?sai a nan ya tuno sannan ya dawo da ɗan sauri ya ce
"Apple Bilkisu da brother In-law basu ɗaukar wayar kowa zamu tafi dubo su ne yanzu bari mu je"ai tuni
itama ta ruɗe ta shiga ruɗu tana cewa

"Zan ni ku"sai ya girgiza mata kai yana faɗin

"No apple you can't follow us ki tafi wun su Ammi na san yanzu they must be disturbed ki yi calming
nasu har mu dawo okey"??ɗage mata gira yayi daga haka ya bar ta nan ya nufi yayan sa suka wuce zuwa
wun motar Lukman ɗin..

Kamar ta kurma ihu jin banzayen kalaman da ke fitowa daga bakin wasu mutani da suka zo wucewa ta
pool side ɗin sai maganganun banza suke yi akan iyayen su,haushi ne ya kama ta sai ta daka masu tsawa

"Enough,,enough of all these rubbish...you are in our home not yours...so you either maintain silence
and enjoy the party or you leave silently no body forced you to attend the party....ingrate humans
arrrhggg"da ihun dai still ta kai ƙarshen ayar zancen nata mai ɗauke da masifaffen tune..

Sum sum kamar annamimai suka wuce ta,halbin su da glass table cup da ke hannun ta tayi ta shiga
gyara jelar baƙar rigar ta da ke share wuri sannan ta ui tsaki ta wuce itama..



By now Hajiya Madina hankalin ta ya fara tashi da rashin ɗaukar wayar da ƴaƴan nasu basu yi ba ga
rashin isowar su wurin akan time gashi har 11 saura kwata dole tayi protecting respect da dignity na
families ɗin su dan haka ta nufi wun MC ɗin ta amshi microphone ta shiga yi masu bayani

"Assalamu alaikum,ina fatan zaku bani aron lokutan ku da hankulan ku actually this party was supposed
to be over by 11pm but due to inconveniences and unavoidably reasons we couldn't conduct it and time
is not by our side,we are really sorry for the short comings we never planned for that but it happened
we are deeply sorry for snatching your time from you and halting your activities and duties,the couples
are still not present due to some little flight problems i hope and pray that your hearts will be good
enough to forgive us for not fulfilling our words,i never wanted saying

45 / 74