Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ba and about issue na whether or not ita ba taste na sa bane,duk
bai taso ba dan ni na hango abin da su yaran basu hango ba,babu namijin da zai kalli Bilkisu ya kawar da
idanun sa nare a ce har ya mallake ta sannan yayi yunƙurin cewa bata mai ba wannan ƙarya ne babba
ma dan Bilkisu owns everything a proud woman should have ko kin manta hausawa na cewa *_Iya ruwa
fidda kai_*,dan haka ina mai miki albishir da ki shirya tarbon jikar ki ta biyu nan da shekara mai
zagayowa we will be grannies isn't that a perfect picture"?ta faɗa tana mai fallasa farincikin ta da ta kasa
ɓoyewa dan ta gama haɗa komai da yadda zai gudana cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba.Hajiya
Zeenat have no choice but to accept the decision being made by her dearest friend.
Dariyar manya suka yi sai mazan suka kalli juna cikin mamakin ta yaya matayen su suka san abin da ke
zuciyoyin su wanda a halin da ake ciki maganar suke tattaunawa akai dan sun gama da maganar lafiyar
Zaid but Dr Muhammad refuse to reveal his intentions akan makarin rashin lafiyar Zaid dan yafi so ya zo
masu a matsayin surprise gift daga wun sa sai suka ɗan buɗo idanu alamun what?sai suka kuma kallon
matayen nasu sai dai su ba su suke kallo ba hasalima hirar su suke yi.
For a long while tana ta kai kawo daga ƙarshe ta gaji ta zauna haɗe da matsowa kusa da Bahajjatu ta yi
lowering voice ƙasa
"Baha can't you please help me just last help ban kuma roƙan taimakon ki regarding this but please do
me this last favour ki taimaka ki tsallake maganar Ammi ki bar ni na shiga ɗakin nan dan ganin sa wallahi
am restless bana jin ina iya samin natsuwa matuƙar ban gan shi yadda nake so ba please baha do
something i might create a big calamity here"!!a dame ta ida maganar wanda hawaye yayi
accompanying maganar ta ta ƙarshe sai tausayin ta ya kama Bahajjatu but ya zata yi Ammi ta gindaya
sharuɗɗa ita kuma bata shirya amsar faɗar Ammi ba sai ta janyo ta jikin ta tana share mata hawayen
"Beelove ba fah ƙin son shigar ki ake ba a'a,kin ga jiya ɗaya da kika hango sa sai da kika birkice mana
kija yi collapsing har sai da aka maki antidepressant kafin mu sami hutu again apple ya amshi laifin da ba
shi yayi ba a jiyan nan sannan yau Ammi ta ja min kunne dan Allah kaɗai ya san me zai faru matuƙar kika
yi tozali da shi kamar yadda kike son yin kin ga ko ba komai kin jawo min magana da Ammi shi yasa na ƙi
barin ki ki shiga ciki ko daga nan ma kina iya hango shi ba sai kin shiga ba ki ƙara haƙuri wataran zaki
shiga very soon"!ta cigaba da rarrashin ta dan ita dai bata son shiga matsalar Ammi.
Dan ji kam ta ji ta bjmut bata jin tana iya rintsawa ba tare da ta ga fuskar sa ba,kuka take yi sosai wanda
ya sa Bahajjatu tambayar ta ko dai wani abin aka mata da bata son faɗa sai ta ce a'a ta share hawayen ta
a daidai lokacin kiran Bilal ya shigo wayar Bahajjatu saurin picking ta yi ta matso da Bilkisu kusa dan su
gana tare,fuskar sa ne yayi appearing da rabin jikin sa da wanda banda white singlet babu kaya a jikin sa
ai yana ganin fuskar twin sistern sa yayi saurin kife wayar yana tunanin me yasa Bahajjatu zata mai haka
itakuma Bahajjatun da ta ga bai da kaya sai singlet sai tayi saurin kashe wayar dan kar Bilkisu ta gani
saboda lokacin da ta saita wayar ita tana faman goge running tears da ke tsere a kan fuskar ta bata ɗago
kan ta ba shi yasa bata lura ba sai da ta gama ta ga an kashe wayar
"Me ya faru naga kin kashe wayar"!!tayi mata tambyar sai ta bata amsa da
"Babu ina ga matsalar sadarwa ne kin san kayan bature"!jijjuga kai tayi ta share maganar idanun ta na
kan sa ta transparent door da ke ɗakin ita in da zasu mata adalci da sun yarda ta shiga ta gan shi.
Kira ne ya kuma shigowa wayar Bahajjatu ta ɗauka Bilal ne sai ta yi saurin dubawa sai dai ba shi ta gani
ba numbern kelita ta gani kuma video call ne ɗauka ta yi haɗe da ɓata fuskar ta ta ce
"Yes"! a halin taimako da agaji kelita ta fara magana
"Ma'am how are you,how is your brother's health i was informed this morning"!
"Uhumm,,he is fine.anything else"?ta mata tambayar cikin ɓata fuska sai ta ruɗe ta rasa abin cewa tsaki
Bahajjatu tayi ta ce
"Am hanging up"da sauri ta dakatar da ita ta hanyar ce mata
"Ma'am is still on the issue,please do something and save a soul i don't know where to go of i leave here
please help me"hmm lallai wasu dai basu iya samun wuri ba in banda haka ke ba gidan ku ofishin ma ba
na ubanki ba an kore ki amma kamar karya kin ƙi barin wuri sai ta ran ta ya ɓaci a zuciye ta ce
"Hey drama queen i don't have time for your drama as i have said you should evacuate my office
before i return back and that's final"katse kiran tayi tana ta jero tsaki dan haushi da takaici wanda ya
saka Bilkisu tambayar ta ko lafiya amma ta ce da ita ta share maganar kawai,sharewar tayi dan dama ba
a mood na magana take ba so take kawai ta gan sa ko zata sami sassaucin fargabar da ke ɗawainiya da
zuciyar ta..
Miƙewa tayi ta kama hanyar shiga ɗakin ta dan tana ganin ko kwana zata yi ba barin ta Bahajjatu zata yi
ta shiga ɗakin ba,bin bayan ta tayi tana tambayar ta
"Beelove wai ki gaya min wani magana mana"!tana tafe ta ce
"Ina jin ki"!
"Wannan saurayin naki na asibitin ku Dr Aslam ko wa yake?ina yake halan ko bai san baki da lafiya bane
dan tun da aka dawo da ku har aka kawo ku ƙasar nan ban ga ya biyo ba bai kiuma kira ba me yasa"??
dakatawa tayi ta tsaya kafin ta juyo ta zubama Bahajjatu idanun ta kamar zata yi magana sai kuma ta
shiga tunani,.
Aslma?ina ya shiga?ita ta manta da shi kwata kwata saboda last time da suka yi waya da shi ta wayar
Zaid ne kuma a ranar ta mai kaca kacan in kiran ta zai yi ya rinƙa yi ta wayar ta ba wayar Zaid ba dan a
lokacin basu fara jituwar sosai da Zaid ba kuma tun daga ranar bai kuma kiran ta ta wayar zaid ba sai dai
ta nata wayar and if he call bata ɗagawa dan bata da wani sauran magana da shi but still yakamata a ce
ko ba dan personal issues da suke da shi ba as professional colleagues kuma ma'aikacin da ke ƙarƙashin
ta ya kamata a ce ya zo ya gaida su daga ita har Zaid but bai zo ba bai kuma nuna ya sani ba yana
rayuwar sa comfortably lallai ma Aslam za kuwa ya haɗu da ita wani irin mutum ne shi marar sympathy
wa mutani,tana cikin tunanin ta ga hannun Bahajjatu na moving kusa da fuskar ta sai ta ɗan lumshe
idanun ta ta buɗe su
"Bilkisu tambayar ki fah nayi amma kika shiga tunani halan menene"?sauke ajiyar zuciya tayi ta ce
"Babu,about Aslam kuma ki manta shi kar ma ki kuma min magamar sa please ba shine a gaba na
ba"tana gama faɗa ta juya ta fara tafiya sai abin ya ma Bahajjatu daɗi dan dama so take ta kuma
tabbatarwa koh eh Bilkisu na da wani special feelings ma Dr Aslam but thank goodness hunch ɗin ta bai
zama gaskiya ba kuma dama hakan take so dan ita kam bata mafarkin wani ya mallaki aminiyar ta sama
da yayan ta ta san duk rashin fahimtar junan su ne ya sa suke ganin kamar ba zasu taɓa iya zama inuwa
ɗaya ba kuma a rayuwa yanzu *iya ruwa fidda kai* ne in shi bai iya takun sa ba ita ya kamata ta iya in ita
bata iya ba shi ya iya kuma ta ma san dole ne zasu saba dan dukkan su masu sauƙin kai ne kawai rashin
sanin ainihin hallayar juna ya sa suke ɗaukar junan su a matsayin wani yana da jin kai but a hakan ma ita
ta hango rayuwar su nan gaba matsalar dai shine a ɗaura auren but muddin aka ɗaura ko za'a haɗa sama
da ƙasa bai isa ya datse auren ba bai kuma usa ya ƙaro wata ba sai dai ya gama bulaguron sa ya dawo
kan hanya because she knows her friend more than anyone ita ɗin ƴar son soyayya ne kuma ta san zata
samu daga wun yayan ta dan haka bata da wata ragowar damuwa.
Saurin rungume ta tayi tana cewa
"Apple dagaske ba shi bane a gaban ki"?mamakin tambayar ne ya kamata sai ta ce
"Are you alright at all baha"??
"Yes..yess am alright am just happy"
"Happy"?ta maimaita maganar Bahajjatun tana kallon ta sai ta girgiza kai ta cugaba da tafiyar ta har suka
shiga ɗakin bata kuma cewa komai ba sai da suka zauna Bahajjatu ta kuma tambayar ta
"Bilkisu wai ina maganar yarinyar nan da kika ce wai yaya na na so a ƙauyen nan"?sai ta ji ranta ya ɓaci
sakamakon tunowa da Asma'u da ta yi sai ta ce
"Baha ki daina ɓata min rai please i don't wanna hear or say anything about that ingrate"a harzuƙe ta yi
maganar ƙarshe wanda ya bama Bahajjatu damar tantance eh aminiyar ta kishi take yi da so called girl
lover na yayan ta kuma ta hango tsantsar so da takewa yayan nata sai dai in ɓoyewa junan su zasu yi but
ko ma dai menene what goes around comes around zasu gane hakan nan gaba.
Dariya kawai ta yi wanda ya sa Bilkisu kallon ta a tsorace ta ce
"Anya baha ba za'a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ki ba kuwa kafin mu koma gida ba"?wani dariyar farinciki
tayi kafin ta ce
"Friend i saw what you were unable to see for the past few days humm"!!ƙyale ta tayi dan kamar
Bahajjatu ta fara zarewa biye mata bai da amfani.
Chan wuraren ƙarfe 11pm lokacin kowa ya kwanta babu ma masu taya ta kwanan dan an hana mutani
saboda ana takura mata da yawa da unnecessary hirarraki kuma hakan na chaza mata brain jin hakan ya
sa Hajiya Zeenat tafiya gida ita kuma Hajiya Madina ta ce babu inda zata tafi a nan zata kwana sai dai ba
ta gefen ɗakin Bilkisu ba rather ta ɗakin Zaid hakan bai mata daɗi ba but ta san duk yadda za'a yi dole ne
ma kawai ta gan shi yau sai dai a yi haƙuri da Bahajjatu zata tafi ma sai da ta tsaya ta gaya mata wata
magana maganar da ya tsaya mata a rai
"Bilkisu you are in love but you keep on denying it kin fake da cewa damuwa da shi ne ya sa kika kasa
natsuwa again ɗazu mun yi maganar Aslam and you became furious and irritated mun yi maganar
Asma'u sai kika sami mood swing immediately kika yi switching and you responded my question by
saying you don't wanna talk or hear anything regarding her,,,if you don't have or feel anything about my
brother then why did you reacted in such manner?girl don't feel shy i guess abin da iyayen mu suka
hango is finally becoming real and reality dan haka ni dai nawa shawarar shine go for it..go for what you
want and follow your heart i assure you you will never regret your choice goodnight and take care of
yourself as well my brother"!!..
Tafiya tayi ta bar ta da mamakin maganar amma gaske ne wai?ko dai kawai hasashen Bahajjatu ne?but
how a ce kana son mutumin da maganar kirki na tsayin mintuna biyar bai taɓa shiga tsakanin ku ba
sannan har a ce so ya gitta?no. Wannan ma ba gaske ba ne weighing the distance and differences
between the two of them sai kawai ta ga inaa maganganun Bahajjatu shiririta ne ba zai taɓa zama
gaskiya ba dan ita ta san in banda tausayin sa da take ji sakamakon halin da yake ciki bata tunanin wani
abu mai girma wai shi sunan shi so yana son kutse ya shigo tsakanin su haba a'a wannan shurmen baha
ne kawai ba gaskiya ba.
Da wannan tunanin ta lallaɓa ta saci hanya ta rinƙa ɓoye fuska har ta iso ɗakin Zaid babu kowa a wurin
haka ma a ɗakin babu kowa sai shi kaɗai hasken ɗakin is very deem sai da ta kai mintuna biyu a tsaye
tana wasi wasin ta shiga ko a'a shin zata iya hana kanta yin kuka in ta ga halin da yake ciki ko baza ta iya
ba.ƙarshe shahada tayi ta tura ƙofar ɗakin ta yi sallama sannan ta shiga jikin ta a sanyaye duk ta ji
gwiwar ta ya sage,,takawa ta fara yi kaɗan kaɗan tana jin fargaba.
His face is turned laterally ta gefen dama dan ana jujjuya mai position bayan kwana ɗai ɗaya saboda a yi
preventing pressure bed sore saboda is very obvious wa masu long hospitalization.
A ɗarare ta nemi kujerar kusa da gadon ta zauna tana son ganin fuskar sa a hankali ta leƙa tana fargaba
har dai ta sauke idanun ta a kan fuskar sa,gaban ta ne ya faɗi haɗe da tausayin sa dan a normal basis shi
ba mutum ne mai ƙazanta ba yana da tsafta he try as much as possible dan shaving excess hairs a fuskar
sa but yau sai gashi almost half of his face is covered with hairs though ba a ƙazance yake ba but yana
buƙatar gyara,kamar a kira sa ya amsa but babu hali,tuno da rayuwar su ta rinƙa yi tun kafin su tafi
outreach har izuwa ranar da abin ya faru.
According to doctor ya ce ba zai farfaɗo ba sai nan da watanni 3-4 masu zuwa,sai ta ju kamar ruwa
ruwa a kan kumatun ta sai ta kai hannu a hankali ta taɓa ta ga hawaye ne,cire hannun tayi ta shiga rera
kuka kukan da ke da ma'anoni daban daban dan a ƙunshe yake da baƙin ciki,tsana,fansa da wani dalilin
na daban da bata san yaya zata yi classifying ba..
Magana ta shiga yi mai tana yi tana jan hanci idanun kuwa basu daina fitar da hawaye ba dan zuciyar ta
na cikin ƙunci da baƙin ciki.
"Zaid me yasa ka mana haka?ba fah ni kaɗai ka saka a cikin halin damuwar nan ba.Ammi,umma su
Abba,yaya jamil,yaya Afzal da Hakim ga baha ga Bilal yaya Lukman ka san kuwa ka saka kowa cikin
damuwa da tashin hankali..ta ja hanci ta goge hawayen ta cigaba,dan haka ina son sanar da kai Zaid
muddin baka tashi ka kwantar mana da hankali i will never speak to you again did you understand"?
kamar da mai rai take maganganun tsawon lokaci bata san da kanta kawai take maganar ba da ta ga
kuka da surutun ba zai fishe ta ba sai ta shiga yi mai addu'a ta manta dare ya tsala kuma ba a ɗakin ta
take ba dan haka tana cikin addu'ar bacci yayi gaba da ita dan kanta tayi leaning a bedside..
Around 5am ta ji kamar motsin mutani sai ta fara buɗe idanun ta tana ɗaga kan ta a hankali har ta ɗago
completely sai bata ga kowa ba lumshe idanun ta tayi dan yana da kyau in mutum ya farka especially in a
halin figici ya farka kar yayi wuf ya miƙe dan hakan na iya janyo mai ciwon kai da throughout ranar ba zai
sami sauƙin sa ba sai a hankal.
Idanun ta a lumshe ta ji muryar Ammi na ce da ita
"Baby tashi ki yi sallah asuba ta yi"!!a nan ta buɗe idanun ta dan sai a lokacin ta tuno wai ba a ɗakin ta
take ba and 'tashi kiyi sallah asuba ta yi'what does that mean?ohh God bacci tayi a ɗakin sa ko me?ya
rasulillahi,kasa ɗaga idanun ta tayi har sai da ta ji Ammi ta shige toilet sai ta miƙe da gudu ta ƙarasa zuwa
ɗakin ta tana shiga ta ja ƙofar ta saka mai lock ta haɗa bayan ta da ƙofar tana sauke ajiyar zuciya sai
mamakin kan ta take ya aka yi ta kwana a ɗakin sa sai wata zuciyar ta bata amsa da "kin manta abokin
aikin ki ne kuma abokin yayan ki sannan yayan aminiyar ki?ai ba wani abu bane dan kin taya shi zaman
jinya".at the same time other part of her heart ya bata amsa da"maybe saboda tausayin sa da kike ji ne
ya sa kika kwana a chan dan ai ba halin ki da ɗabbi'ar ki bace kawai tausayin sa ne"da wannan amsar ta
sami ƙwarin gwiwa har ta shiga ta yi wanka kafin ta ɗauro alwala ta fito ta saka doguwar arab El-Mondy
gown baƙa mai adon cream colour saka hijabi tayi ta tayar da sallah da ta idar ta yi addu'oin ta sai ta
tsinci kanta da yi mai addu'a in a special way addu'ar take yi fiye da yadda ta ke yiwa kanta a kullum ta
daɗe tana mai addu'ar samin lafiya kafin daga baya ta idar ta kawar da kayan sallan.
Abin mamaki sai ta yafa gyalen gown ɗin ta duba ƙaramar jakar ta da kayan shafawar ta ke ciki ɗaya
bayan ɗaya ta fiddo su duka sai dai abin da take nema bata gan shi ba ƴar ƙaramar tsaki tayi sai ta janyo
ɗayar trolley ta duba still babu abin sai ya ɓata mata rai gashi har shida na safe yayi za'a zo a bata
magungunan ta ciki kuwa har da seductive drug wanda ta san mudfin ta sha shikenan ita da aiwatar da
abin da take so sai dare ko ma washegari dan har yanzu ana bata depressive drug twice daily six na safe
da six na yamma dan brain ɗin ta bai gama settling ba at any time tana iya collapsing saboda daɗewar da
tayi a kwance cikin shock,.
Bata gama tunanin mafita ba ta ji sallama ɗaga kan ta tayi sai ta ga Bahajjatu ne wani miƙewa tsaye tayi
da sauri ta buɗe mata ƙofar gabaɗaya tace
"Hey where us your makeup kit"!??da mamaki Bahajjatu ta ce
"Makeup kit Bilkisu?da asussubahin nan me zaki yi da shi?and wait"!!a nan ta ga shigar ta sai ta dawo
kamar dai yadda take da wato Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman sai abin ya ma Bahajjatu daɗi dan an sami
cigaba sai ta ce
"Ki just bani minti kaɗan zan dawo na baro kit ɗin a gida