Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ta mai tana ɓarin jiki dan bai mata kama da
Mudan da ta sani ba a baya wannan Mudan ɗin mugu ne dan so yake ya gwada muguntar sa har a kan
ta..
Sai da ya tabbatar tarkon sa ya ɗanu da kyau sannan ya ce da sauran su fito su yanki dajin sannan ya ce
a ingizo mai Asma'u,tana turjewa dan sam bata son ganin abin da zai yiwa Zaid a gaban ta sai dai ƙarfin
maza ya fi nata dan dolen ta ta natsu ta bi su har cikin dajin dan sai a nan ta gane cewa tarko Mudan ya
ɗanawa ɗan birni ba wani jan kunnen da zai yi mai sannan ya raina mata hankali ne kawai yana so yayi
ta'addancin sa a gaban ta in ya so ya ja mata baƙin jini..
Da kukan ta aka illata ɗan birni a gaban ta ta kasa hanawa hasalima sai hukuncin da Mudan ɗin ya mata
dan ta nuna mai bai dace ba abin da ya yi.
Share hawayen idanun ta tayi tana data sanin shawarar da ta bada Mudan ɗin dan ta san da a ce ta ƙi
bashi wannan shawarar ta natse akan ita ya hukunta ta da babu abin da zai janyowa ɗan birni shiga halin
da yake ciki kuma da a ce lokacin da ya ce da ita ta mai alama in sun fito ɗin nan bata mai ba da duk
hakan bai faru ba,,yanzu gashi an ce mata an fitar da su ɗan birni daga ƙauyen rai a hannun Allah...
Kuka mai sauti ta shiga yi tuno da irin hantarar da aka rinƙa mata a washegari da abin ya faru dan an
gano cewa tare suke da Mudan lokacin da ya aikata abin da fari ta so turjewa tayi rashin kunyar ta amma
sai ta ga abin ya fi ƙarfin ta dan ko ta yi bata da mataimaki saboda a daren Mudan ya mata rashin
mutuncin da bata taɓa mafarki ba..
Wani hawayen baƙin cikin ne ya silalo mata tunowa da tayi da abin da ta ji a matsayin sakamakon
rashin lafiyar ta da ta kai sati tana yi.
Kuka sosai ta rinƙa risga dan ta tsani kan ta da in ana tsine masu a gari saboda rashin mutuncin da suke
yi sai ta rinƙa ganin ai ba su ake tsinewa ba masu tsinewar su ke tsinewa kan su.
Ba zata manta ba akwai wata tsohuwar da Mudan ya saukewa mari saboda ita wai dan tana wucewa
tana cin gyaɗa tana wurgi da ɓawon gyaɗar sai ya sauka saman fuskar tsohuwar sai tsohuwar ta ce da ita
_*ƴar nan anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa,kina kallo na ki watso min ɓawon gyaɗa*_
shikenan kuwa Mudan ya ce da wa Allah ya haɗa sa in ba da tsohuwar nan ba ya shiga mata rashin
kunya buɗar bakin ta ta ce da shi _*in duniya ce yara zaku gan ta ai*_ shikenan ya ɗaga hannu ya
shararawa matar nan mari ya ce da ita ita kaɗai zata ga duniya su sun gama ganin ta har sun gama
shawagi a cikin ta.suka yi gaba tsohuwar nan na kallon su har suka wuce ta ɗaga hannun ta sama tana
roƙon sakayyar abin da yaran suka mata sauke hannun ta ne yayi daidai da juyowar Asma'u ta banka
mata harara haɗe da jan tsaki tana faɗin wai fah addu'a take yi,sai suka saka dariya suka yi gaba abin su..
Kuka ta cigaba da yi dan a kullum sai ta tuno da ire iren rashin mutuncin da suka ma mutani a ƙauyen
wanda a ko da yaushe cikin tsinuwar su suke ko da jama'an garin suka ji abin da ya faru suka shiga tsine
mata wai har da baƙon da yake taimakon ta ma ta gwada mai rashin ɗa'ar ta toh ai ta ɗaga tuta gashi
nan Mudan ɗin ya mata abin da ya dace da ita.
Labari bai ɓoyuwa tuni labarin rashin mutuncin da Mudan ya mata a daren ya karaɗe ƙauyen da rashin
halascin da ta ma ɗan birni sannan ga gargaɗin da Mudan ya mata na kar ta kuma shaida sa a matsayin
wanda ta sani babu shi babu ita,abin nan ya ma jama'ar ƙauyen koma daɗi suka rinƙa murna ai Allah ne
ya fara sauko masu da aya kaɗan ma kenan suka fara gani,a nan gidan su kaf yayyen ta ƙyamar ta suke ji
dan hani suke ai ita ta kai kan ta inda abin da faru da ita dan haka ba wani tausaya mata da zasu yi tun
daga ranar suka fita harkar ta sao dai su bi ta da ido.
Dama mahaifiyar ta ba gamawa tayi da muzancin jama'a ba akan rashin tsawatarwa ɗiyar ta da bata yi
akan tana barin ta tana fita suna ta'addanci tare da Mudan kuma ta zuba masu ido duk waɗannan
kalamai su suka haɗu suka haifar mata da damuwa mai tsananin gaske toh da ta ga kwana biyu Asma'un
ta fara hankaki har tana jan jiki da Mudan ɗin sai ta ji daɗi har take iya mayar da magana in ana mata
habaici ko a waje ne amma ranar da ta ji abin da Asma'un tayi ta kuma ji ɗibar albarkar da Mudan ya
mata sai ji aka yi ta faɗi ƙasa sumammiya ƴaƴan ta maza su suka taimaka aka kai ta wata ƙaramar PHC da
ke chan nesa da gidan su a nan suka yi jinyar ta na tsayin kwanaki huɗu kafin a sallame su duk wannan
jinyar ta hana Asma'u zuwa kusa da ita ta kuma ce matuƙar ta kusanto ta toh Allah ya isa ta je cjan ta
sami Mudan ya zame mata uwa,uba da komai na rayuwa...abin ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba sai
kuma a nata mentality ɗin ta ɗau hanya ta bi Mudan har gidan su wai ga abin da maman ta ta faɗa ya
taimaka ya zo su je ya roƙar mata ita ta yi haƙuri ta bar ta ta je kusa da ita in ya so ma sai ya gayawa
maman ta da yayyen ta maganar auren ta a masu aure tunda ga abin da ya faru,.
Buɗar bakin sa sai ce mata yayi
_*"Ai ni banu abin da zai saka ni auren ki ba zaɓar wannan ɗan nasarar kika yi akai na ba har ni kamar
ni Mudan in saka miki doka ki sa ƙafa ki take hmm ai babu abin da zan yi da ke ki je can inda na aika
wannan garan ki aure sa amma ba ni ba dan ba zan aure ki ba*_"kuka ta saka mai tana faman roƙon sa
amma ya nuna mata shi fah sam babu inda zai kai ta ta fitar mai a rayuwa kawai in ba haka ba itama ya
san abin yi da ita..
Tun daga ranar ta shiga tashin hankalin da bata san ranar fitar ta ba sau uku tana zuwa gidan mai gari
wai ko an ji labarin su ɗan birni amma amsar ɗaya ce su ma basu san inda yake ba,takan ƙulle kan ta a
ɗaki ta ci kuka har bacci ya ɗauke ta kamar cikin ƙaya take tsabar tsangwamar da ake mata a garin a cikin
gidan su ma ba zaman daɗi ake yi da ita ba.
Kamar bayan sati uku ta tafi wannan ƙaramar PHC da ke ƙauyen cikin dare ta je dan bata ganewa kan ta
kwana biyu,ko da aka gwada ta aka sanar da ita matsalar da ke tare da ita,ji tayi kamar ta mutu a nan
kasa kukan tayi sai zaman da tayi a wurin kamar marar rai,..
Tana barin wurin ta nufi gidan su Mudan ta sanar da shi abin da ya faru har da ma cikin maye yake
amma sai da ya kashe mata gargaɗi akan kar ta masa wasa da ajiyar sa shi zai karɓi ajiyar sa kuma ta bari
ya kama ta tana wasa da maganar sa sai ya nuna mata ɗaya grfen sa..da kukan azaba ta dawo gidan ta
sanar da maman ta tana daga waje dan bata da ƴancin shiga ɗakin ma,amsat da maman ta ta bata shine
halbin da ta mata da rediyo tana daga cikin ɗakin ta shiga sharɓe kuka tana data sanin haihuwar Asma'u
da ta yi kalamai dai marasa daɗin ji ta rinƙa suƙar ta da shi.
Kwanar baƙin ciki tayi har ta fara tunanin kashe kan ta cikin daren kawai ta huta amma sai ta fasa dan
ta san ƙila ɗan birni ya dawo ya zo ya fitar da ita daga cikin halin da take ciki..
Share hawayen ta tayi a karo marar adadi.ci da sha bata rasa ba amma walwala kam ya ƙaurace mata
dan yayyen ta da suka ji hakan ma kasa yi mata komai suka yi sai ɗaya daga cikin su ne ma yayi ƙarfin
halin zuwa har hideout ɗin su Mudan ya same sa ya lakaɗa masa dukan banza ya kuma ce da shi ko ya ƙi
ko ya so dole in Asma'u ta haife abin da ke cikin ta ya aure ta in ba haka ba shi zai yi ajalin sa,..
Tunowa ta kuma yi da ranar da labari ya zo mata akan wasu sun ma Mudan dukar kawo wuƙa yana nan
a gida rai a hannun Allah murnar da jama'ar garin suka yi bai kai wanda ta yi ba dan tun bayan faruwar
abin bata kuma tsintar kan ta cikin walwala ba sai ranar dan har takawa tayi tsabar farinciki ko ba komai
itama Allah ya saka mata da wulaƙancin da Mudan ya mata cikin ruwan sanyi...
Tashi tayi ta share hawayen ta ta shige koɗaɗɗiyar ɗakin ta mai ɗauke da katifa marar riga ta shimfiɗa
zanin ta ta kwanta a kai tana tunanin ko me zai faru da ita kuma dan mai gari ya kira yayyen ta maza
akan su zo yana son ganin su toh fitan su ne ta dawo tsakar gidan ta zauna zaman jiran su shine da ta gaji
ta koma ɗaki ta kwanta dan bata da jimirin yin doguwar zama tuni sai ta ji tana jin jiri sai dai kwanciya.
A ɗakin ma tana kwance ne amma tana tuno halin da Mudan yake ciki tun ranar da aka mai dukar nan
an ce baya iya tashi kwance yake kamar matacce tunowa tayi da irin kukan da ta rinƙa yiwa mahaifiyar sa
akan ta roƙar mata Mudan ya zo su yi aure amma sai tashi tayi ta bar ta zaune tsaƙar gidan tun daga
ranar ita kuma bata kuma zuwa roƙar ta komai ba sai dai ba ranar Allah da zai wuce da ba zata saukewa
Mudan kwandon Allah ya isa ba...
Bacci ne mai nauyi ya ɗauke ta cikin baccin ne ta rinƙa jin hayaniya kamar tsakanin mahaifiyar su da
yayyen ta maza,da ƙyar ta iya farkawa ta buɗe idanun ta sai ta ji ana faɗin
"In dai Asma'u ce autar mata toh ni na yafe ta ta je chan zata gani a ce ta rasa wanda zata cutar ta rasa
wanda za'a haɗa baki da ita a cutar sai yaron nan,yaron kirki da ya inganta rayuwar ta,sannan ta kwaso
min abin tirr har cikin gida kuma ku ce min in mata rangwami in yafe mata,,anya hankalin ku na jikin ku
kuwa"??hawaye ne ya bi kumatunta sai ta shiga rera kuka a hankali tana rufe bakin ta,muryar yayyen ta
ta ji suna cewa
"Mama wallahi muma ba haƙuri muka yi da abin da Asma'u ta yi ba sai dai tunda har mai gari da kan sa
ya kira mu ya nemi da mu raga mata abin da muke mata a gidan nan sai muke ganin kamar bai kamata
mu watsawa maganar mai gari ƙasa ba,shi yasa muka yanke hukuncin ɗauke ta ma in babban yaya zai
koma wurin aikin sa cikin yola sai su tafi tare in ya so sai ta rinƙa zama tare da shi a nan gidan da yake
aikin gadin sa tunda ya ce ɗakin da yake ciki akwai wani babu kowa ciki kin ga a can ma abin zai fiye
mana sauƙi da a ce mu cigaba da kallon ta ana muzanta ta ga wannan kwallon ɗan iskan bai da niyar
auran ta,in ya so tana haihuwar cikin sai a kawo masa ita kuma ta cigaba da karatun ta tunda tana so
dama chan shi ya hana ta wata ƙila ma sai a dace ta sami wani na garin da zai gan ta ya aura ko ya kika
gani mama"??wani kallo ta bisu da shi kafin ta ce
"Yaro yaro ne ta ina zata taɓa samin mijin aure bayan ta gama ɓata tarihin ta da hannun ta a ce yarinya
ƴar shekara haka amma har ta san ta yi cikin shege sannan wani marar sa'a kamar ta ya ce zai auri jaraba
a gidan sa"saurin katse ta yaran suka yi ta hanyar hana ta ƙarasa zancen ta
"A'a mama kar ki mata wannan bakin inshaAllah zata sami wani nagari da zai riƙe ta da amana ai
hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka yar kawai amincewar ki muke buƙata da addu'ar ki"!!!shiru ta masu
kafin daga bisani ta tashi ta basu wuri dan ta tsani ta tuna da abin da Asma'u ta yi abin na ƙona mata rai
ba kaɗan ba yanzu ko fita bata iya yi tsabar kunyar idon jama'a..
Daga ɗakin ta ji duk wani tattaunawar da suka yi ta kuma matsu ta ji amsar maman su sai dai ta ga tayi
wucewar ta sai ta kuma tsanar kan ta tana kuka haɗe da tsinewa Mudan dan a da duk tsiyar da take yi
yayyen ta basu taɓa tsanar ta ba amma yanzu wai ko kallon kirki baya shiga tsakanin ta da su..
Kiran ta suka yi ta fito jiki na mazari ta durƙusa ƙasa kan ta a ƙasa tana faman share hawaye,kasa ce
mata komai suka yi sai suka ce ta tashi ta basu wuri haka ta koma ɗakin ta jiki sanyaye dan ta san ta
gama amfani a duniya..su kuma suka ƙudiri aniyar kuma roƙar mahaifiyar su akan tafiya da Asma'un dan
sun san yanzu ran ta a ɓace yake amma zuwa kamar bayan kwana biyu tana iya hucewa ta haƙura..
********************
*_7:40pm_*
Ya mata ne a airport tana sauka bayan an gama firfito mata da luggage ɗin ta ta tari taxi ya shigar mata
da kayan ta cikin taxi boot ya dawo ya shige ya ja ta mai kwatancen inda zai kai ta..
Tun da ta shiga jirgin nan take jin kan ta wani iri gani take kamar hukuncin da ta yiwa Zaid ya mai tsauri
amma in ta tuna da kalmar da ya furta mata na "yes i have feelings for her what can you do about it" sai
ta ji hukuncin ma ya mai kaɗan how could he do this to her ta yarda ya shaƙu da yarinyar amma me yake
nufi da kalaman sa ta ɗauka ba wani abu mai kama da so da zai shiga tsakanin sa da yarinyar ta ɗauka
shaƙuwa ce kawai amma sai ta ga abin da yake son fin shaƙuwa at least da ya bari maybe after their
holly matrimonial night sai yayi maganar amma a wannan daren da ya fi mata ko wani dare
muhimmancin dan ta gama tsarawa kanta rayuwar da zata yi da shi irin son da zata nuna mai after their
reunion as a husband and wife but he ruined everything ya ɓata mata duk wasu feature plans ɗin ta by
just calling that girl's name..
Share hawayen da ya wanke mata fuska ta yi tana jan hanci abin takaicin shine wai ta kasa yaƙice son
Zaid cikin zuciyar ta har a yanzu son sa sabo fil yake a rana ita kuma irin nata jarabawar kenan..
Tsayuwar motar ne ya sa ta san sun kawo gidan sai ta fita ta sauke kayayyakin ta ta biya mai taxi kuɗin
sa ya tafi ita kuma ta shiga jan two trolleys ɗin ta ta nufi bakin gate ɗin,danna alarm bell tayi sai ga gate
man ɗin ya zo ya leƙa sannan ya buɗe gate ɗin cikin farinciki da jin daɗi ya fara mata barka da dawowa
dan a gaban idanun sa aka fitar da ita kamar marar rai
"Ranki ya daɗe sannu da dawowa ya hanya ya lafiyar jikin ki"murmushi kawai ta iya yi mai ta girgiza kai
haɗe da nuna mai akwatunan ta tayi ciki,ya san ta sha hanya dan haka ya biyo ta da su a baya tana tafe
tana rangaji dan fah ba warkewa tayi ba har yanzu raɗaɗin da take ji yana kan ratsa ta ƙarfin zuciya ce
kawai irin nata ya sa take danne zafin...
Babu kowa a gidan duk suna chan gidan da aka ce mata wai gidan mijin ta ne,girgiza kai tayi ta tsaya a
kitchen tayi plugging ruwa sannan ta fita ta haura sama zuwa ɗakin ta,ko da ta shiga ɗakin sai ta ga
kusan kashi saba'in cikin kayayyakin ta na amfani babu su ɗakin sai ya mata faɗi sa kai tayi ta wuce zuwa
toilet ɗin ta ta ƙunnan shower da kayan jikin ta ta tsaya tsakiyar shower ɗin ruwan na sauka mata tana
faman risgar kuka kamar ba zata daina ba duk abubuwan da ya faru da su a jiya ne ya shiga dawo mata
duk part ɗin da ta tuno sai ta ƙara sautin kukan ta ruwan ma kamar zafi yake ƙara mata a ran ta..
Kusan mintuna ashirin ta ɗauka tana kukan nan kafin ta kashe shower ɗin ta fita bayan ta cire kaf kayan
jikin tata fito da towel a hannun ta tana son ɗaurawa,kallon wayar ta tayi ta ga yana haske alamun kiran
ta ake yi sai ta kife wayar ta fita.
Ɗauko ruwan da tayi plugging tayi ta tsiyaye cikin bathtub ta bar shi haka nan ta dawo ta kuma sauka
ƙasa ta shiga kitchen ɗin ta haɗa quick quacker oat ta zuba enough milk da sugar kaɗan ta juye cikin
kofuna biyu ta ɗau spoon ta koma ɗakin ta.
Ajiye kofunan tayi saman side bed drawer sannan ta shige bayin ta cire towel ɗin ta tayi hanging
sannan ta rumtse idanun ta ta shiga cikin bathtub ɗin.
Zafin ruwan ne ya shige ta ta kuma rumtse idanun ta tana tuno daren su na jiya..
*_35 minutes later_*
Tana shan kofin quacker oat na biyu kenan amma duk tunanin abubuwa da yawa sun ishe ta jira kawai
take Allah ya bata aron rai zuwa washegari..
**********
Jirgin su bai sauka ba sai kusan goma na dare ya so yin kiran azo a ɗauke sa amma sai ya ga rashin
amfanin hakan dan kashe wayar sa yayi bai san me zai faɗawa Ammi ba in ta tambaye sa abin da ya sa
basu dawo tare da Bilkisu ba dan shi duk tunanin sa ta tafi chan gidan ne sai ya canza tunani kawai