Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ya koya mata iya zama da miji shi kuma ya auri ra'ayin ran sa haba
yarinya baki fi haka ba amma zuciyar ki sai ƙarfin tsiya na gaji ba zan mutu da baƙin cikin Bilkisu ba
haba"ta faɗa muryar ta na nuna tsantsar ɓacin ran ta.
Dafe ta Hajiya Madina ta yi kafin ta ce
"Yanzu mafita zamu nema daɗin abin lafiya ƙalau suka dawo ƴar matsala ce da rashin fahimta wanda
nake da tabbacin ba iyakar sa ba kenan dole akwai wani abin da ya mata da ya tunzira ta har ta ɗau
wannan hukuncin faɗa ne bata yi ba"sai Hajiya Zeenat ta juyo ta mata wani kallo kafin ta ce.
"Dan uban ta har ajwai wani abin da mijin ta zai mata ne ta kasa riƙewa ta yi handling da fuskar fahimta
sai dai ta mai fitsara?wai me ke damin yaran yanzu ne me suka ɗau auren nan ne?gani suke in an ɗaura
masu aure shikenan ta zamo matar sa ta mai girki ta yi kwalliya in lokacin buƙatar sa ya taso ta saukw
mai shikenan auren babu respect babu fahimta babu sanin matsalar juna sai tsagwaron selfishness da
son kai da yayi wa yaran yanzu yawa haka ake auren"?.
Ɗan murmushi Hajiya Madina tayi ta ce
"Hajiya Zeenat ki saurare ni da kyau kin ga yaran nan...,sanin kan ki ne ko da tsiya ko da bori by now sun
san kan su in ba dan haka ba babu yadda za'a yi Bilkisu ta ɗau zafi har haka baki ganin kishi ne ya saka ta
yi mai abin da ta mai?ni fah ban ga laifin ta ba hasalima shi ke da laifi sama da tsawon lokaci suna tare
dole ya san halayyar ta na kishi dan haka saboda ta yi fushi da shi har ta hukunta sa hakan ba laifi bane
duk son sa da kishin sa ya saka ta aikata hakan ba wani abin ba dan haka ni dai in zaki fahimce ni mu fitar
da hannun mu akan yaran nan aure ba abin wasa bane ya wuci gaban a yi wasa da shi haka sanin kan ki
ne mata da miji sai Allah duk wani borin da haukar da zasu yi wallahi wataran ba tare da sanin mu ba
zasu daidaita kan su yara ne su ko marasa ilimi da za'a ce sai an natsar da su an nuna masu abin da ya
dace da akasin hakan?dan haka ni zan ma Dr magana kema ki ma prof magana mu fita harkar su mu
zuba masu ido dan yanzu jira suke su ga abin da zamu yi upon hearing what happened amma in muka
bar su zasu yiwa kansu faɗa so i suggest we leave them alone iya inda zamu iya yi masu magana shine in
muka ga abin na taɓarɓarewa bai gyaru ba sai mu nuna masu dama chan ido muka zuba masu ba wai
dan bamu san abin da suke yi ba i think this suggestion is okey"!!kallon juna suka yi sai Hajiya Zeenat ta
yi shiru tana tunanin in ba dan kyakyawar alaƙar da ke tsakanin ahalin su da na Dr Maher ba da ko shi
Zaid ɗin bai saki Bilkisu ba mahaifiyar sa zata saka sa sakin ta dan rashin hankalin da ta yiwa ɗan ta...
Har gate suka rako su Hajiya Madina na daɗa jaddada mata kar ta ce da Bilkisu komai ta bar ta dan
itama babu abin da zata wa shi Zaid ɗin nasu ido ne for the main time..
Da suka dawo gida ne ta ke ma prof bayani sai ya ce da ita
"Ai abin da kuka yanke shi zamu bi dan da bai da kyau da baku yanke hakan ba ku kuka fi mu sanin zafin
su dan ku kuka ɗau cikin su kuka haife su kuka raine su har kawo yanzu kin ga kun fi mu sanin abin da ya
dace da su"sai ya ɗan murmusa kafin ya ce
"Ni da aka nunawa banbanci ɗazu wai ban san zafin rasa ɗa ba"yana murmushi yayi maganar sai Hajiya
Zeenat ta harare sa cikin wasa ta yi hanyar bayi tana mai ce da shi
"Whatever"dariya yayi itama da ta shiga bayin dariyar ne ya zo mata sai ta tuno da ɗaga hankalin da tayi
ɗazu Allah dai ya kawo sassauci cikin lamuran ƴaƴan nasu..
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*_This page is urs friendy Ahumaggahress mi love u te quiro mucho mucho💋_*
*31*
*_The blame games_*
Ko da suka dawo gida pretending gabaɗayan su suka yi kamar basu da masaniya akan abin da ya faru ko
hanyar ɗakin Zaid bata bi ba suka nufi ɗakin su hankali kwance ta shiga yi mai bayanin shawarar da suka
yanke akan matakin da zasu ɗauka game da matsalar ƴaƴan nasu amsa ya bata da
"Ina ganin da mun yiwa yaran nan faɗa saboda prof ya sanar da ni abin da ya faru according to baby
doctor sai na ga bai kamata mu bar su ba we should at least let them know their faults and improve ko
ya kika gani"ɗan murmushi ta mai mai gamsarwa kafin ta ce
"Dr ban hana ba kuma ban ƙi ta taka shawarar ba but ka sani fah yaran nan babu ɗan 18 years daga shi
har ita sun mallaki hankulan kan su babu fa'ida in mun ce zamu masu magana nake ganin in muka zuba
masu ido muka yi biris kamar bamu san komai ba da kansu zasu shirya dan babu daƙiƙi cikin su believe
me Dr this is the best way and a perfect way and method of punishing them both amma yi masu magana
will not solve the issue and at the same time punish them"shiru Dr Maher yayi yana sauraron ta kafin
daga bisani ya miƙe yana unbuttoning rigar sa yana faɗin
"Toh sauran family members ɗin kuma fah ya zamu yi masu bayanin shawarar da muka ɗauka"?tashi
tayi tana taya sa cire rigar nasa sai ta ce.
"Family meeting zamu yi gabaɗaya nan da chan gidan su Dr sai mu haɗu a yi bayani dan kowa ya san
abin da ake ciki ka ga ba za'a sami wani leaking grounds ba"riƙo hannun ta yayi ya ce
"Kamar da yaushe kenan kike ganin ya dace ayi meeting ɗin"?
"Eh toh,ko gobe ne da yamma dan ka san emergency ne kuma akwai abunuwan yi during the day time
but zuwa yamma an gama komai an dawo gida sai a yi cikin sukuni ko ya ka gani"gyaɗa mata kai yayi
kafin ya ce
"I will compose the message and make sure it communicate to everyone"gyaɗa kai tayi ta ce
"Nice Idea"sai ya ce
"Kenan ba zamu yi involving yaran ba kenan"harara ta danƙara mai tana girgiza kai ta ce
"Just yanzu yanzun nan you acted so smart and i was praising you yanzu kuma kana son sako shiririta
kamar ba da kai nayi maganar plan ɗin ba u don't know when you will ever become serious Dr"dariya ya
mata dan dama so yake ta sake kar abin ya cigaba da damin ta kamar yadda shi yake damin sa dan ya so
a ce ɗan sa na tare da matar sa by now he should have at least start a family amma bawa baya gujewa
ƙaddarar sa duk yadda ka so in Allah ya rigada ya tsaro maka dole kayi haƙuri ka karɓi ƙaddarar taka..
°°°°°°°°°°°°°
_9am_
Juyin farko da tayi kenan bisa kan gadon ta tun bayan da ta tashi tayi sallar asubahi ta
koma,sequentially ta buɗe idanun ta ta sauke saman fuskar Bahajjatu dake zaune saman sofa tana video
call da Bilal..
Wuf ta miƙe daga kwance ta ce
"Baha ke ce"?sai a sannan ta juyo da fara'a saman fuskar ta ta ce
"Beelove ni ce har kin tashi"?sai ta sallami Bilal ɗin dan ya zame masu addiction matuƙar ya isa wun aiki
sainya kira ta sun yi hirar mintuna biyar sannan su yi sallama haka itama in ta kai office ɗin ta sai ta kira
sa sun yi good luck wishes..
Cikin fara'a fuska ba yabo ba fallasa ta nufo ta tana ƙoƙarin mayar da wayarta cikin jakar hannun ta
wanda da ganin ta ka ga wacce zata tafi wurin aiki.
Da zuwan ta Bilkisun ta sauko daga kan gadon ta ta nufo Baha ɗin tana zuwa ta rungume ta sai kuka ita
kuwa Baha da ta san kwanan zancen sai ta ƙyale ta ta rinƙa risgar kukan ta dan a jiya bayan su Ammi sun
bar gidan babu Afzal a kusa ta tafi ɗakun Zaid ɗin ta gan sa cikin tashin hankali a nan ta damu ta shiga
tambayar sa sai ya kasa sanar da ita ainihin matsalar yayi shiru har ta gaji da tambayar sa ta fito sai Afzal
ɗin ne ke sanar da ita ɗan abin da ya sani sai tayi mamaki toh yau da safe ta shirya har zata wuce wurin
aiki Ammin su ta tsayar da ita ta mata bayanin abin da ya faru tsakanin yayan ta da aminiyar ta ta kuma
sanar da ita dalilin da ya sa mahaifin su yayi distributing masu family meeting message kenan..
Sai da ta yi mai isar ta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ita dai Baha ƙala bata ce da ita ba har
dai ta matsu ta ce
"Baha ba zaku tambaye ni matsala ta bane ko dan yayan ki ne baki son ganin laifin sa kema"?sai Baha ta
saka surprising face ta ce.
"You are unbelievable Beelove,yanzu dan kin yi kuka kamar baby Zarah har jira kike yi in tambaye ki
dalilin kukan ki sannan ki sako yaya na ciki?ai ko ba komai Beelove na san kukan ki na kewata da kika yi
ne wanda nima kin san na yi kewar ki sosai kukan ce bata kusa shi yasa ban yi ba kuma na san yaya na
shi ke da laifi dan jinyar sa ya sa bamu haɗu ba amma ki sani ni ba goyon bayan sa nake ba dan na fi
kowa jin kewar ki sam yaya bai kyauta ba"!!..sake baki Bilkisu tayi tana kallon bakin Baha da ke rero
waɗannan kalamai sai ta ce
"Yanzu Baha fahimtar da kika wa kuka ta kenan"cikin rashin damuwa da maganar ta ce
"Yes or don't you miss me as well"?idanun ta kyar saman fuskar ta yayin da take yi mata tambayar sai
Bilkisu ta zamo totally speechless ta kasa ce ma Baha komai.
"Toh na ga lafiyar ki Beelove ni zan tafi ayyuka sun taru min a office da yawa sai dai in na dawo zan zo kin
ji"?bata tsaya sauraron ta ba tayi gaba abin ta ita kuna Bilkisu ta shiga ruɗu yanzu Baha so take ta ce da
ita bata san ma'anar kukan ta ba ko me?me yasa bata ba maganar muhimmancin ba ko a jikin ta..
Wani sashin zuciyar ta ne ya bata amsa da
"Ai duk laifin Zaid ne dan shi ya sa Baha tayi ma magana ta kallon wofi because ta fi kowa sanin halin
Baha ko damuwa ta gai saman fuska ta sai tayi magana amma wai ina kuka kuka sosai but Baha ta ce da
ita ai saboda ta yi kewar ta ne,yes nayi kewar ta but damuwa ta daban"...
Kallon hanyar toilet tayi sai ta miƙe ta nufi hanyar toilet ɗin da nufin yin wanka sai dai kasa yin wankan
tayi dan bayan ta kammala cire kayan baccin ta ta tsaya da nufin saukewa kan ta shower sai ta shiga
tunanin moments ɗin su ita da Zaid,.
"Ya ilahi wai nikam ya zan yi da son Zaid?ina zaman zama na rayuwa ta cikin sauƙi kawai ya shigo min
ciki ya hargitsa sannan yana son yin tafiyar sa"..tana ƙunna shower ɗin ruwan na fara zubo mata ta tuno
da unforgettable moment ɗin nan da ya mayar da ita mace sai ta ji hawaye na son zubo mata at the
same time tsigar jikin ta ya tashi ga zazzafar son sa da ke huda gaɓoɓin jikin ta..
Wannan wanka dai ba na daɗin rai aka yi sa ba dan duk saukar ruwar dake fitowa daga cikin shower ɗin
nan sai ta tuno sa mijin ta sai yanzu kewar sa ke kuma kama ta..
Sai da tayi da gaske sannam ta kammala wankar ta fito dan kar ma ta cigaba da tunanin sa sai tayi
saurin zurma doguwar rigar ta bayan ta saka inner wears ɗin ta ta ɗau wayar ta ta sauko ƙasa tana
fargabar ganin fuskar Umman ta dan it was a narrow escape for her a jiya..
Babu kowa a parlor sai ma'aikatan gidan da ke gyare wurin da aka gama cin abinci kenan har suka yi
breakfast babu wanda ya neme ta.
"Ai duk laifin Zaid ne ban taɓa experiencing fushi daga wun iyaye na da yaya na ba sai a kan ka duk wai
ba'a ga laifin da kai kayi ba sai ni ake ta blaming".
Haka ta koma ɗakin ta ran ta na mata ba daɗi,zama tayi ta kira mai masu girki ta wayar ta ta sanar da
ita abin da take so a kawo mata.
Ajiye wayar tayi bayan ta duba time aunty Zee ta ce mata zata zo yau but har yanzu bata zo ba kuma a
halin da take ciki bata da wani da ya fahimce ta sama da ita aunty Zee ɗin dan haka take ganin ta sami
hope at least ba duka family nata bane suka juya mata baya ba..
Not too long aka kawo mata breakfast ta zauna da nufin farawa sai dai abin mamaki banda tuno fuskar
Zaid a lokutan da suke cin abinci tare babu abim da take yi ƙarshe ma da abin yayi yawa sai ta hau
hasaso sa tare da ita a yanzu ma har dai fuskar sa ya fara yi mata gizo bata ankara ba ta ji abu na bin
fuskar ta ko da ta kai hannun ta sai ta ga wai hawaye ne ke bin fuskar ta sai ta mayar da cokalin ta jingina
da gadon ta ta shiga rafka kuka ba ji ba gani tana ta maganganu marasa ma'ana
"Duk kai ka janyo mana,na gama tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance yadda zamu rinƙa gudanar
da activities ɗin mu amma ka wargaza mana duk laifin ka ne duk kai ka jawo mana wannan abin yanzu
ina wannan halin amma babu kai kusa da ni duk pains ɗin ni kaɗai nake ɗaukar sa kai babu ruwan ka
baka ma san ina yi ba and i believed you i trusted you i gave you my body,my heart and my soul i
thought you will take care of it amma i was very wrong na tafka babbar kuskuren da na daɗe ina gudun
tafka sa a rayuwar aure na,my dignity my virginity i gave it all to you thinking that you will respect me
after that but sai kayi proving min cewa kai ɗin cikakken namiji ka kira min sunan wata a daren farkonna
da kai ka rinƙa faɗin kalamai masu taushi akan ta gaba na fah,gaban ido na ina kwance a jikin ka ko
shakka ta baka ji ba baka yi respecting ɗi na ba ka raba ni da mutunci na sannan ka juya min baya me ya
sa Zaid?why??why did you choose to punish us in thus hard way?sarai ka sani na ƙi jinin jin sunan
yarinyar nan amma ka rinƙa maimaita sunan ta kamar abin bautar ka"!!!..kuka take yi tuƙuru duk idanun
ta sun kumburo sun yi ɓulu ɓulu kamar an daɗa mata girmar su ba ƙaramin raɗaɗi take ji a ran ta ba dan
ta gama mafarkin washegarin daren farkon ta zai dasa tarihi mai tsafta a zuciyar mijin ta she endured the
pains of a virgin lady wacce karon ta na farko da haɗuwa da namiji zata ji raɗaɗi ta kasa riƙe zafin har sai
ta fitar da muryar ta fili amma ita ta danne ta bar wa kanta duk dan ta saka sa yin alfahari da ita amma
ga abin da ya mata bai ma damu da abin da ya mata ba ya zage ne kawai yana maganganu akan wata
Asma'u
Tsabar baƙin ciki a nan ta kwanta har baccin azaba yayi gaba da ita wanda har cikin baccin ma banda
blaming Zaid babu abin da take yi a ganin ta duk shi ya ruguza masu rayuwar auren su da ta jima tana
tanadi.
Uwa uwa ce duk fushi faɗa da rigimar da zaku yi da ita dole ta damu da son sanin lafiyar ka,.ko a jiya
danne zuciya Umma tayi ta fita harkar Bilkisun har zuwa wayewar yau da za'a yi breakfast aka ce za'a
kirawo ta amma ta hana ta ce a bar ta yarinyar da bata iya zama da miji ba ai har iyayen ta ba iya zama
da su zata yi ba dan haka ko bayan sun watse sun tafi wuraren aikin su ya rage daga ita sai ita a gidan ta
rinƙa saƙawa tana warwarewa ƙarshe dai ta yanke hukuncin zuwa ɗakin ta dubo ta in yaso sai ta ce faɗa
ta zo yi mata dan kar ma ta ɗauka ko damuwa tayi da ita.
Zuwan ta ɗakin ke da wuya sai ta gan ta kwance a ƙasa fuskar ta duk ga alamar hawaye nan sun bushe
gefe ga abincin ta nan bata taɓa ba sai kuma ta dawo jin tausayin ta she knows that she overreacted
yesterday and today amma dole ne ta nuna mata rashin gaskiyar ta ba wai dan tana ɗiyar ta shikenan ta
rufe ido ta ce zata goyi bayan ta ba as a good mother she have to correct her daughter's misconception
akan zaman ta da mijin ta..
Hawaye ne ya cicciko idanun Umma sai ta miƙe ta bar ɗakin dan ita ta san raɗaɗin kishi saboda a fagen
kishi sam Bilkisu bata kamo ta ba amma yanayin rayuwa ya sa dole ta sassautawa kan ta sai gashi duk
addu'ar da ta rinƙa yi akan kar Allah ya sa Bilkisu ta yo gadon ta sai da ta yi nata kuma har da son taɓa
mata ƙwaƙwalwa yake dan ko a baya da ita tayi nata kishin Allah ne kawai ya taimake ta ya sa har yanzu
suke tare da Prof ba dan haka ba da ba'a ma haifi Lukman ba dan her past was a hectic one sai dai yanzu
ya zamo past kuma tana fatar Allah ya yayewa Bilkisu wannan mummunar kishi da ke ɗibar ta dan
mazan yanzu basu da tabbas ba kowa zai ɗauki shashancin ɗiya mace ba bare ma a ce tana ƙarƙashin sa
sai yadda ya ga damar yi da ita..
************
Bai farka daga baccin da ya ɗauke sa saman sallaya ba sai wurare ƙarfe