Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 74

126K to 129K   out of 221.1K words

lissafi haɗe da haifar mata da baƙin ciki da tsanar
yarinyar farat ɗaya

"Yesss..i have feelings for her what can you do about it"??cak ta tsaya kamar an dasa ta a wurin,for
almost 1 minute suna a haka duk ran su a ɓace babu wanda ya iya taɓuka komai dan gabaɗayan su faɗar
nasu ya shammace su basu san dalilin da ya saka su yin wannan faɗar ba.

Sai bayan ya gama furta kalaman nan sannan ya dawo hayyacin sa sai ya ɗago kan sa cikin wani hali
halin tsanani da tsagwaran tashin hankali mai tattare da nadamar kalaman sa ya buɗe baki ya kawo
hannu zai taɓa ta kenan ta sauke mai wani razanannen mari da ya gigita sa wanda saura kaɗan ear
device ɗin sa ya fita sai dai bai kai ga fitan ba dan magnetic board ɗin ya manne sosai da kunnen sa..

Ɗauke wuta yayi na wucin gadi he can swear that tunda Ammi ta haife sa bata taɓa laying hannun ta a
fuskar sa da nufin mari ba but yau ga matar sa ta mare sa..

Hannun sa na ɓari ya ɗaga ya fara kawowa kan jikin ta tana kallon sa kamar ba ita ta ɗauke sa da mari
ba sai haki take kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi,hannun sa na taɓa jikin ta ta tsala wani ihu haɗe shiga
kokuwar ƙwace kan ta amma hakan ya ci tura dan damƙa ne ya mata mai tsauri tana ihu yana mata
magana

"kin yi hauka ne ban sani ba Bilkisu?kina cikin normal senses ɗin ki kuwa?i am your husband and you
raised your hand and slapped me what is wrong with you"a tsawace ya ke maganar amma madaɗin ta
amsa mai sai kawai ya ji wani irin zafi na ratsa hannun sa da ya riƙe ta.

Cizo mai ɗankaran zafi ta gatsara mai hakan ne ya saka sa sakin hannun ta dan dole,yana sakin ta ta
ingiza sa tayi bayin haɗe da saka lock again..kuka ta shiga yi fiye da wanda tayi ɗazu ita yake gayawa eh
yana da feelings ma Asma'u what can she do about it..ya salam..



Buga ƙofar yake yi yana kiran sunan ta amma sautin kukar ta kawai yake ji,gajiya yayi dan saura kaɗan
kan sa ya buga tsabar ciwon da yake mai.zama yayi a wurin amma sai ya jiyo muryar ta cikin faɗa tana ce
mai

"Ka tashi ka fitar min a ɗaki kafin rai na ya ɓaci,just leave my room"salin alim ya tashi ya bar mata ɗakin
ya koma nasa ɗakin,neman maganin sa yayi ya sha duk jikin sa yayi zafi yana gama sha ya kwanta a ƙasa
yana sauke ajiyar zuciya dan in yayi wasa maybe ya koma asibiti washegari dan zazzaɓi ne mai tsanani ya
sauko mai...




_8 hours later_
Daga ita sai kayan jikin ta da gadgets ɗin ta,,zuciyar ta a bushe yake dan duk wani abin da zata yiwa
rayuwar ta ta gama yi already babu wani alamun sauƙi a kan fuskar ta takalmin ta ne ya saka sa tabbatar
da zargin sa dan ya daɗe yana jin ana ta kai kawo tsakanin ɗakin ta da waje.

Fitowar sa kenan ya ga har ta kai bakin ƙofar falon zata yi tafiyar ta.cimin sauri ya ƙarasa bakin ƙofar ya
riƙo ta yana mata magana a ruɗe cikin ɗimuwa

"Bilkisu ina zaki tafi,,,huhh?me kike shirin yin haka ne wai?why are you acting likw someone that has
been possessed ko kin manta baki da lafiya ne?ina zaki tafi cikin wannan yanayi"???..motsi ko ɗaya bata
yi ba sai ta natsu har ya kammala maganar sa sannan a hankali cikin slow motion ta cire hannun sa daga
jikin ta a hankali ta juyo da fara'a saman fuskar ta.

Riƙo hannun sa tayi cikin nata hannun tana murzawa kamar babu wani abin da ya faru ta shigar da
idanun ta cikin nasa,tsagwaron son sa ne tsantsa a ƙwayar idanunta sai dai dole ta hukunta sa dan ya san
ita ɗin mai daraja ce kuma tana son dawowa da martabar ta a idanun sa sam ba zata ɗauki defeat ba
hukunci dole ta hukunta sa dan irin tsanar yarinyar nan da ya ƙaru a ran ta ba kamar da ba ya daɗu fiye
da na da chan da bata auri Zaid ba..



"Zan tafi Zaid saboda baka buƙata ta a nan akwai wacce ta fini a gare ka wacce ina ga in har ka kawo ta
nan ko ma cikin rayuwar ka zai fiye maka than zama tare da ni,"numfashi ta sauke kafin ta ce da shi

"But ka san wani abu?....barin ka da nayi ba yana nufin zan bar ka ka ji daɗin rayuwar ka bane..nooo.. I
will be your...obsession Zaid Maher Muhammad i promise you....sai ka zo da gwiwowin ka biyu crying for
my love but it will be too late for you dan kayi wasa da babbar damar da ka samu daga gare ni,you toyed
with me you toyed with my heart for that zan na yi maka addu'ar rasa samin soyayyar ko wace ɗiya
mace kuma idanun ka rufe zaka rinƙa craving ma do amma ba zaka taɓa samu ba"cikin ruwan sanyi ta
mai maganar tana kaiwa aya ta wurgar mai da hannun sa ta saka kai tayi gaba abin ta..



Ko da ta kai airport kasa controlling kan ta tayi sai kuka take kamar ran ta zai fita ta rasa irin son da take
mai wanda yake ƙara mata son sa a duk lokacin da ta tuno sa wannan punishment da take da niyar yi
mai ba shi kaɗai ke ɗaukar raɗaɗin ba ita nata raɗaɗin har ya fi nasa..

Ko awa basu ƙara ba jirgin su ya tashi dan dama jirgin rana zasu bi amma ta san yadda tayi ta sami
morning flight,sarai tana ta ganin kiraye kirayen iyayen su na shigowa wayar ta amma ta ƙi ɗagawa....



*_Few hours later at the airport_*
Bai san abin da ke masa daɗi ba sam ya kasa ganewa kan sa,bai san me ya mata da ya saka ta yi masa
irin wannan abin ba amma ko ma dai menene ya san in suka yi landing dole iyayen su zasu saka ta gaba
dan ta masu bayanin abin da ya faru da ita dan bai san abin da yayi zafi har haka ba ya saka ta cursing
nasa haka ba..

Jirgin ta da nasa banbancin awa biyu ne dan haka landing ɗin su ba wani tazara a tsakani...



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*_Beautiful IYA RUWA FIDDA KAI fans this page is for u where ever u are i luv u xoxo 💋💋_*

_Mamansadeeq i can't luv u less ur last comment shakes me off seriously i laughed,I really luv that
comment tnx alot_

*28*



*_A little bit flash back to koma's village[waiwaye adon tafiya]_*



Zaune take a tsakar gidan su ta rafka tagumi kamar wacce duniyar ta mata atishawar tsaki duk ta fita
kamannin ta babu kyawun bare hasken duniyar ta mata zafi ta mata tsanani ba kaɗan ba a baya ko wani
ya buɗi baki ya ce da ita wata ran zaki dawo abin tausayi ba zata taɓa gasgata maganar ba sai dai a yanzu
da take tsundum cikin zafin rayuwa,juyawa tayi ta kalli ɗakin su inda ta jiyo tari mai ɗauke da amai
wanda ta tabbatar da ba wata bace face mahaifiyar ta,hawaye ne ya sauko mata daga idanun ta sai ta
shiga tari itama dan ba isashiyar lafiyar ce da ita ba sha'ani kawai ake yi dan rayuwar ta mata juyin masa
cikin tanda,..

Tunabi mai zurfi ta shiga yi wanda ya zame mata abin kumallo tun daga buɗewar rana har faɗuwar
sa,bata da abin da ya wuce mata zama ita ɗaya kamar marainiyar da tayi rashin gata a rayuwar ta
tunanin baƙin aibun halin da tayi a ɗan wata ɗaya da ɗoriya take tunowa ita kanta ta san ta tafka babbar
asara da mugun aiki dan abin da ta yi ta san duk mai hankali wanda ya san karamci ba zai kalle ta a
matsayin ƴar halas ba sai dai ma ya bita da Allah ya tsine.wani hawayen ne ya bi kuncin ta ta saka bayan
hannun ta ta share ita dai yarinya ce bata san me ya kamata da me bai kamata tayi ba dan duk abin da ta
ke yi gani take kamar daidai ne shi yasa har rana mai kamar ta yau ko ta fita an nuna ta da baki ko yatsa
bata iya ƙyalewa sai ta mayar da martani ƙarshe ma daina fitan tayi kullum tana gida tana faman jinyar
maman ta dan shi ya fiye mata..



*_Wata ɗaya a baya_*



A hanyar ta ta dawowa daga aiken da maman ta ta mata ne ta hangi motar su Zaid dan ko ba'a sanar da
ita ba ta san ɗan birnin ta ne dan shi kaɗai ta sani mai mota a ƙauyen nasu shi yasa cikin azama ta nufi
hanyar gidan nasu sai dai ko kafin ta ƙarasa shiga ta ji an damƙo ta an yi gefe da ita haɗe da rufe mata
baki,mutsu mutsu ta shiga yi tana son yin ihu sai dai fuskar wanda ta gani ne ya saka ta natsuwa ta kasa
yin ihun tayi shiru.

Cire hannun sa yayi daga bakin ta,bin sa da kallo ta yi kamar ta ga abin ƙi dan ta daɗe rabon ta da shi sai
ta shiga ja da baya dan kar ya illata ta amma wani tsawar da ya daka mata ne ya sakata tsayawa cak ta
juyar da kanta gefe amma ya saka hannun sa da ƙarfi ya juyo da fuskar ta suna fuskantar juna abin da
yake mata gabaɗaya sun zo mata a banbaraƙwai.

Cikin isa da dakiya ya fara yi mata razanannun maganganu kamar haka

"Na lura wannan banzan ɗan nasaran ya zo ya juya maki tunani har kika iya kwana kika tashi ba tare da
kin bibbiyi lafiya ta ba,na ce ba zaki yi karatun ƴan boko ba amma da yake yana da ƙarfin nasara ya zo ya
juya maki hankali da tunani har kika iya tsallake sharaɗin da na saka maki,ni...niiiii....Asma'u...ni Mudan
kike son juyawa baya ko ba haka ba....hahhh...ni na hankali hurɗa da yaron nan amma kika ƙi jin magana
ta ko ba haka ba?iyeee?har kike gudu na kike ɓoye min takun ƙafar ki ko ba haka ba?ni Mudan ɗaya
maganin dubu...in ce ki fita harkar yaron nan amma ki ɗauki ƙafa ki bi sa har gidan mai gari kina koyon
fitsara da rashin kunya haɗe da nasaranci ko ba haka ba?toh bari ki ji in gaya maki a yau,,,ba gobe ba,a
yanzu,ba anjima ba,zaki kai ni har inda wannan tsagerin yaron yake in gama da shi in shafe tarihin sa a
doron ƙasar nan da hannun ki zaki taya ni kashe shi dan ko na kashe sa na kashe banza wofi bai da
amfani a duniya dan tun da ya shigo mana gari shi ke hana mu rawar gaban hantsi shi ga shi wakilin
masu kula da lafiya eyyee?na gama kaiwa bango dan bai taɓa shigowa gona ta ba sai yanzu da na ga
yake ƙoƙarin wuce gona da iri dole in ja masa kunne amma tunda ba shi kaɗai yake abin ba har da ke
kina taya sa dole in share sa a duniyar nan alƙawari na kenan dan haka kizo mu je tun muna mu biyu mu
gama da shi in ba haka ba rayuka da dama zasu salwanta na maki alƙawari"..



Rasa abin cewa tayi tun da ya fara maganganun sa bata taɓa sanin baƙin hali irin na Mudan ya kai har
haka ba a ce har ita kanta da take tare da shi yana neman salwantar da ita lallai mutani sun yi gaskiya da
suke ce mata wata rana zata yi nadamar kasancewa tare da Mudan dan bai da halin kirki yanzu a ce har
ita bai bar ta ba yana son takurawa rayuwar ta..

Wani ihu ya mata yana magana kamar taɓaɓɓe marar hankali

"Keeee Ma'u ina magana ne fah kina min eh ya ne ban gane ba ko baki ji na ne"?haɗiye yawu tayi tana
jin wani mugu mugun tsoron sa na shigar ta sai ta daure ta ce

"Mudan me kake nufi me kake shirin yiwa ɗan birni,ka san bai da laifi a duk wannan rashin haɗuwar
tamu da kai duk laifi na ne wallahi bai da masaniya babu ruwan sa"wani dariyar ƴan daba ya mata kafin
ya tsuke fuskar sa ya fara magana

"Kin ji haushi kenan dan na yi magana marar kyau a kan sa,kenan ran ki ya ɓaci kenan dan na ce zan
kashe wannan banzan gajan da yake son shiga tsakanina da ke"???tarar numfashin sa tayi tana son
gyara mai tunanin sa dan ta san yana iya yin abin da ya ce ɗin
"A'a tsaya ka ji Mudan ni dai kawai ka rabu da zancen wai laifin ɗan birni ne ka mayar da laifin kai na
kuma ina roƙon ka ka min rai kar ka lahanta sa ka yafe mai ni ka min abin da zaka mai bai da laifi ka ji"?
dariyar bosawa yayi kafin ya ce

"Yanzu na gane nufin ki Ma'u wato dai kin amince ke in baki laifin da yaron nan yayi ko"?girgiza kai ta
shiga yi dan tana gudun fitinar Mudan sam bata so wani halaƙa ta kuma shiga tsakanin su..

"Tsaya ka ji ni in za ka yarda madaɗin ka lahanta shi me zai hana ka ja mai kunne kawai amma ka san
ɗan birni ne in ya zo ya kai ƙarar ka ka san babu wanda zai goyi bayan ka Mudan dan kaf ƙauyen nan
tsine maka suke yi babu wani mai son ka ka rufa mana asiri"kallon uku saura kwata ya mata kafin ya ce

"In ja masa kunne kika ce"??sai ta girgiza mai kai kamar zombie sai ya ce

"Yayi..zan aiwatar da hakan...lallai zan ja masa kunne ta yadda ko hanyar da kika bi aka nuna mai aka ce
ya kalla ba zai kalla ba...amma kafin nan tare da ke zamu tafi wun ja mai kunnen"!!tsoro ne ya shige ta
ita sam bata so a ce ya ma ɗan birni ta'addancin sa tana tare da shi ta fi son ya tafi yayi shi kaɗai in ya so
ko daga baya ne sai ta nemi afuwar ɗan birni amma bata son bin sa..

Kiran sunan ta yayi irin na marasa tarbiyar nan sai ta amsa duk tsoron sa ya gama mamaye ta

"Yanzu ki tabbata kin daidaici lokacin fitowar sa kina ganin ya fito ki min alama zan tsaya a nan..ya faɗa
yana nuna mata bayan gidan su wani ɗan loloƙi ne a wurin nan yake son fakewa dan kar a gan sa,kin
gane ko"??ta amsa mai tana mai girgiza kai.

Daga haka bai kuma ce mata ƙala ba ya nufi hanyar loloƙin dan ya gama ƙudirar sai ya kawar da Zaid a
hanyar sa saboda ya gama kai sa maƙura...



Bayan ya wuce ne ta shiga yin kuka ita bata san me yake damin Mudan ba ko tsoron kar a kama sa
baya ji toh idan ɗan birnin ya fi ƙarfin sa fah?idan ya tashi shi ya lahanta sa fah me zai ce?sam ta kasa
samo mafita ɗaya ta yadda duk wani rashin hankalin da Mudan zai yi ba za'a kira sunan ta ba dan ta gaji
da zagin da ake mata cikin gari ana cewa tana ta'addanci tare da saurayin ta duk inda suka kutsa sai an
zage su,yanzu tana son ta fita a harkar sa kwata kwata amma ta yaya gashi yana son taɓa lafiyar ɗan
birni...



Tana cikin tunanin nata sai ta hangi giftawar su Zaid ta ja da baya kaɗan har ta ga shigewar su motar su
kamar ta gudu ta bar Mudan a wurin sai dai da ta tuno maganar da ya faɗ mata na cewa zai ja mai kunne
ne sai kawai ta bi bango a hankali ta mai alama ta bayan gidan na su kamar dai yadda ta saba yi in sun
tafi rashin jin su.

Fitowa yayi yana faman hararar motar yana ƙwafa ita kuma tana bin sa da ido har ta kama hanya zata
wuce gidan su ya damƙo hannun ta ta juyo cikin tsoro ta ce
"Me kuma zan maka ba gashi nan na sanar da kai ba"sai ya aika mata da wani mugun kallo kafin ya ce

"Ce maki aka yi ni wawa ne da zan bar ki ki tafi ba tare da na ja masa kunnen a gaban ki ba"??gaban ta
ne ya faɗi sai ta ce mai

"Yanzu me kake so in maka kuma"?murmushin gefen baki yayi kafin ya ce

"Biyo ni zaki yi mu tafi dan in ja masa kunne a gaban idanun ki"a rikice ta kalle sa tana girgiza kai sai yayi
dariya kafin ya ce.

"Yarinya kin fi kowa sanin hali na au ki biyo ni mu tafi tare au kuma....."ya tsayar da maganar sa yana
mata nuni da cikin gidan su sarai ta gane me yake nufi wato ko ta bi sa ko ya taɓa lafiyar maman ta.

Kuka ta shiga rera mai zata yi magana ya ingiza ƙeyar ta zuwa napep da aka faka gaba kaɗan da gidan su
suna zuwa ya tura ta cikin ɗaya daga napep ɗin dan har biyu ne ɗayan ƴan daban sa ne ɗayan kuma daga
shi sai ita sai mai napep wanda shima ɗan gidan sa ne shi ke kai sa duk inda zai tafi yin ta'addancin sa a
faɗin ƙauyen nan...



Ko da suka hau kan titin sai faman razana ta yake yi da maganganun sa yana daɗa nuna mata in ta
kuskura ta mai wasa da hankali ta kai sa inda ba nan Zaid ke bi ba da motar sa sai ya gyara mata
tunani,ire iren maganganun da ya rinƙa gaya mata kenan ya ruɗa ta har ta ga da ta rasa ran ta da na
maman ta gwamma a je a ja ma Zaid ɗin kunne kawai ai in an yi haka zai fi mata sauƙi in ya so sai su bar
ƙauyen tare tunda ya ce da ita ai zai kai ta birni ya saka ta a makaranta..



Suna tafe tana nuna masu hanyar da motar ke bi dan shi kam Mudan ya sha ya bugu ba kaɗan ba kawai
so ya ke ya ga gawar Zaid ko zai sami salama a zuciyar sa..



Suna kawowa daidai inda motar su Zaid ya tsaya ta gayawa Mudan amma ya ce ba ita zata gaya mai
abin da ya kamata ba shi zai tsara abin da ran sa ke so,shiru

43 / 74
Connection failed: SQLSTATE[HY000] [2002] Operation not permitted