Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
nasu ƴaƴan gasu dai
gabaɗayan su aiki suke yi but har yanzu fear da aka yi installing masu tun yarintar su tana nan bata fita
ba dan haka basu iya yin abu kai tsaye daga matan har mazan har da ma dai su iyayen sun kasance masu
son hutu masu yawon buɗe ido ƙasa daban daban most of the time suna barin yaran ba tare da masu
tsaro ko duba su ba saboda sun yarda da tarbiyar da suka basu sun kuma san ba zasu yi abin da zai janyo
masu matsala ba.
Bayan ta gama tunanin rayuwar su sai ta kalli Bahajjatu ta ce
"Alright shi da kan sa zai karɓo miki maybe ma ya kawo da kan sa dan na san dai shi za'a wa kwalliyar
kuma ba zai kyautu a ce an yi abu dan shi ba sannan bai gani ba"sai tayi dariya itakuma ta murmusa kafin
ta ce
"A'a fah Umma ni ba ni zan yi gyaran ba ajiyewa kawai zan yi zuwa wani lokacin"ta faɗa tana mai juyar
da fuskar ta sai Umma ta yi dariya ta ce
"Kan ku ake ji yaran nan muma mun yi wannan har ma wanda ta fi naku za ma ku dawo kan hanya
ne"daga haka ta fita abin ta ta nufi hanyar ɗakin Zaid dan ganawa da Hajiya Madina sabida basu sami
damar yin magana ba a daren jiya sakamakon tsalawa da dare yayi kuma a lokacin prof ke sanar da ita
batun tafiyar wanda ta ga bai kyautu ba ta kira ta a daren kai tsaye shi yasa ta bari har yau dan ta mata
bayanin abin da zai mayar da su gidan
On reaching there ta hango ta zaune tana danna wayar ta kamar dai abu mai muhimmanci take yi a
wayar sai ta yi sallama ɗagowa tayi ta amsa mata sallamar haɗe da cewa
"Hajiya har kun uso da wurwuri haka"?ta faɗa tana mai ajiye wayar a gefe.amsa mata ta yi tana mai
zaunawa ta ce
"Eh har fah mun iso Hajiya,mun tashi lafiya"amsa mata tayi suka tambayi junan su how their night went
bayan hakan ne Hajiya Zeenat ta sanar da ita cewa komawa Nigeria zasu yi ta kuma sanar da ita dalilin
komawar su but bata gaya mata har da dalilin maganin Zaid da zasu karɓo ba ya sa zasu tafin
"Toh da ƙarfe nawa jirgin naku zai tashi"?tambayar da Hajiya Madina ta mata kenan sai ta numfasa kafin
ta ce
"Ya ce jirgin ƙarfe tara na safen nan zamu bi shi yasa ma na yi saurin zuwa ina ganin ya sanar da Dr ai"
"Eh toh ba shakka maybe sun yi maganar but tafiya da wurwuri haka short notice Allah dai ya kai ku
lafiya,kuma kika ce 1week kawai zaku yi"?amsa mata Hajiya Zeenat tayi ta ce
"Eh,ni kaina na rasa me yasa ya kasa sanar da ni tun da wuri sai tsakiyar dare nima ban shiryawa tafiyar
ba but kin san halin prof komai sharp sharp ne"sai suka ɗan dara dan gaskiya prof duk da tsufar sa na
tsayin shekaru dan a wasu yankin mutum mai shekarun sa ba su iya yin abubuwan da yake yi but shi
sakamakon agility na sa da tun yana ganiyar shekarun sa ya kasance a jinin jikin sa sai abin ya bisa har
tsufar sa ko a asibitocin sa in har aka kawo wasu cases da su yaran yake basu wahala wato young doctors
da ke aiki a nan,shi ake kira shi ke iya handling hakan ya sa sunan sa bai bar yaɗa asibitoci ba dan
banbancin su da Dr Maher shi ne shi prof komai na ƙarfi ne wanda Bilkisu ta kwaso shi a wannan fannin
dan itama haka take komai na ƙarfi ne bata damu wai she is tiny ba all she knows shi ne in har ta saka
hannun ta a jikin mutum da sunan surgery ko treatment bata ɗagawa sai an sami sakamakon da ya
gamsar da ita while a fannin Dr Maher kuma komai nashi cikin sanyi da lumana yake yi dan shi gani yake
lokacin aikin ƙarfi ya wuce a wurin sa dan haka yake barin young doctors na taking over a asibitin sa
iyakar sa ya basu shawarwari masu amfani shi gani yake yanzu ƙarfin sa lies only in his wife's wish kuma
shine yawace yawacen da suke yi wanda shi kuma Dr Zaid ya ɗauko sa a fannin lumana sai dai shi bai da
sanyin jiki when it comes to work he is very active..
Ɗan hira suka taɓa suna cikin hiran ne wayar Hajiya Zeenat ya ɗau ruri,cirowa tayi daga jakar ta ta duba
sai ta ga mai kiran murmushi tayi ta kara a kunnen ta ta ce
"Gani nan zuwa prof kaii ni Allah nagode ma"ta kashe wayar tana tashi tsaye Hajiya Madina ma tashin
tayi tana dariya ta ce
"Ba dai har ya gama ba"
"Hmm ya gaman kenan shi fah prof akwai asassawa wallahi musamman in ya ga ina ɗaga mai
ƙafa"dariya suka yi suka tafa sannan Hajiya Madina ta fara fita ita kuma Hajiya Zeenat ta nufi gadon Zaid
ta kalle shi kafin ta ce
"InshaAllah zaka farfaɗo Zaid cikin hukuncin ubangiji"addu'ar da ta mai kenan ta fita.
A daidai bakin ƙofar ɗakin suka yi kiciɓis da prof yana magana da Dr Maher jiran su suka yi har suka
kammala wanda a nan suka yi bankwanan sai sun dawo dan babu wanda zai kula da Zaid in suka ce
rakiyar su zasu yi.
Cab ne ya kai su har airport bayan ƴan wasu mintuna jirgin ya tashi addu'a suka yi daga haka suka shiga
tattaunawa akan batun abin da zai kai su Nigeria wanda muhimmin abin shine maganin Zaid da zasu
karɓo,wanda already sun yi wa Dr Ruzu bayanin komai kuma yayi fixing masu appointment wanda shine
dalilin dawowar su cikin gaggawa ba tare da sun shirya ba dalili na biyu shine extensive injury da wani
yayi sustaining wanda daga Dr Afzal har sauran doctors sun kasa sanin yanda zasu yi suturing for almost
a month ana fama da shi da an ɗinke nan sai chan ya kunce da an ɗinke nan chan ya kunce wanda daga
baya dai barin sa aka yi dan an gano cewa cutar Human immunodeficiency virus ne da shi(HIV) saura
kaɗan ma ya shiga Aids dama duk mutum mai wannan cuta in har ciwo ya ji kokuma aka ce aiki za'a mai
toh akan sami matsaloli irin haka sai ayi ta ɗinke ɗinke amma ya rinƙa kwancewa a rasa dalili(Toh dalilin
shine jinin jikin su ya rigada ya lalace da ƙwayar cutar wanda a taƙaice dai jinin sa ba mai ƙarfi bane
kuma duk inda mutum ke ciwo jini yana ɗaya daga abubuwa da ke taimakawa healing process a nan sai
aka sami akasi jinin ya zama marar inganci madaɗin ƙwayoyin sinadarai da ke jinin da ke taimakawa dan
ciwon ya warke ya rufu ba tare da an sami matsalar invasion of foreign bodies ba sai ya kasa aiwatar da
aikin nan instead sai ciwon da ake ƙoƙarin warkarwa ya rinƙa faɗaɗa yana buɗewa saboda jinin da ke
taimakawa wun circulating a area of injury is infectious and non sterile daga haka sai a rinƙa cewa
mutum na da ƙan jiki,kokuma a ce ai gado yayi dan duk ayarin gidan su haka suke in sun sami matsalar
da ya yi necessitating surgery toh ko an yi ba'a dacewa daga haka maganar so called "our village people"
will come to play a nan za'a fara suspecting ana blaming ancestors da cewa they cast a strong powerful
curse a family na wani ko na wance gashi nan ɗa ko jikar wani ya sami hatsari an ui ɗinki sau ba adadi
amma abin bai yi ba in ba mutanin su ba wa zai janyo wannan rashin dacen blah blah blah sai a ƙarshe in
akwai mai zurfin tunani sai ya ce ko dai gwada jinin sa za'a yi dan a ga meye musabbabin ƙin zaman aikin
da ake mai toh sai a nan ne za'a gano wai yana da cutar sai kuma zagi da hantara ya dawo kan sa a fara
jeopardising nasa a community forgetting that mutum na iya contacting cutar ta hanyoyi daban daban).
They arrived safely and Bilal was the one that picked them daga airport yana ta zumuɗin jin ko Zaid ya
farka ne amma bad answer ɗin nan ya samu wato not yet sai mood ɗin sa ya chanza a nan ya tambayi
lafiyar twinien sa har gida bai bar su sun yi sukuni ba sai da motar ta tsaya suka fito suka yi cikin gida
inda gabaɗayan family ɗin ke jiran dawowar su daga jamil da matar sa haɗe da baby zarah,Lukman da
sauran ma'aikatan gidan farinciki ne ya luluɓe su ganin familyn na su all present except baby doctor da
ke chan ƙasar samin lafiya.
Welcome pleasantries aka yi exchanging daga nan baby zarah ta nufo grannyn ta ɗaga ta tayi tana mata
wasa har dai ta haura da ita sama tana mata tsiyar kar ta ƙwace mata mijin ta dan idanun nan irin na
Bilkisu ta kwaso dara dara,dariya kawai jama'ar falon ke ta yi har shima prof ɗin.
A ranar dai sai chan wuraren 10pm suka kwanta inda su Jamil da matar sa suka koma gida yarinya ta
tafi wun iyayen ta ta ƙi ita kuwa Hajiya Zeenat ta ce ai sai ta yi dan ba ta kwana mata a gida salon mijin ta
ya ve yana so an yi rarrashin amma ta ƙi ji da bori da botsarewa aka danƙwafar da ita aka saka ta baccin
dole da haka suka koma gida dan Hajiya Zeenat ta sanar da su in dai yini ne guda ta yarda ƴaƴan su su yi
mata amma kwana baza ta lamunci haka ba ta raini iyaye ta raini ƴaƴan su ba zai saɓu ba..
Basu kwanta ba sai da Hajiya Zeenat ta shirya mai komai na washegari dan Dr Ruzu zai fara visiting kafin
ya tafi asibitin wanda ya kai su har ƙarfe 12 na dare sai a lokacin suka kwanta,washegari da wurwuri ya
shirya shi kaɗai yayi tafiyar sa zuwa HRR&T dan tun 7am ya bar gida bai kai ba sai 8am a hakan ma dan
ya saka speed a tafiyar kenan saboda yayi ya gama ya wuce asibitin dan ganin in case ɗin nasu ne in
kuma na referring ne sai a yi providing referral means dan abin na worsening each day.
Yayi nasarar zuwa har ma ya gana da shi ya kuma mai bayanin dalla dalla Alhamdulilah ya bashi
magungunan game da prescription da yadda za'a yi administering komai ya mai bayani suka yi settling da
girmamawa suka rabu and yhe very good and sweet paer of it Dr Ruzu ya sanar da shi cewa matuƙar aka
fara mai medication yadda yayi prescribing in less than a week yana iya farfaɗowa abin nan ba ƙaramar
daɗi ta yiwa prof ba dan har kasa ɓoyewa yayi sai da ya kira Hajiya Zeenat ya labarta mata komai ai ko
har guɗa tayi dan murna mata ba'a rabasu da budi'a sai da ya tsawatar mata akan godiya zatawa
ubangiji da ya ɓullo masu da waraka a sauƙaƙe ba guɗa ba sai a nan ta ta ɗan dawo kan hanya ta shiga
yiwa Allah kirari daga bisani ta rinƙa gode mai..
Daga nan asibitin sa ya tafi inda ya ga patient ɗin ya kuma yi ƴar bincike binciken da yakamata daga
bisani ya gano cewa dole ne ayi referring nasa zuwa wata ƙasar dan method of surgery da za'a mai ya
danganci fannin amfani da metal seal dan shine mafita a gare sa,an rubuta masa referral later an damƙa
mai a hanun sa kuma an yiwa relatives ɗin sa bayanin komai dan haka aka saka masu kwanakin
discharging nasu.
°°°°°°°°°°°°°°°°°
Tafiyar su Hajiya Zeenat da kusan awowi uku zuwa huɗu Bilkisu ta farfaɗo sai bata ga kowa a ɗakin ba
dan haka ta shiga ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta zauna tana laluɓar wayar ta,ƙunna wayar tayi sai
ga kira nan da sabuwar lamba kuma kamar lambar Nigeria ne dan haka sai ta ɗauka muryar ta a ɗan
shaƙe tayi sallama,bai amsa ba sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa da
"Wa'alaikumul salaaam baby na"!!har jan salam ɗin yayi kawai saboda farincikin ɗaga wayar sa da ta yi.
Ko a magagin bacci ta tashi sarai zata shaida mammalakin muryar wanda ba kowa bane face Dr Aslam.
From no where ta ji wani baƙin ciki ya kawo mata ziyara sai ta danne dai bata ce komai ba dan tana son
sanin dalilin sa na ƙin zuwa duba su bayan an dawo da su daga ƙauyen nan kafin su zo nan ƙasar.jin bata
ce da shi ƙala ba sai shi ya mata magana
"Baby ya jikin ki da fatan dai kin farfaɗo garau babu wata damuwa kuma"?shiru tayi kamar bata jin sa
shi kuwa ya san tana jin sa amma halin izza da jin kai irin nata ba zai taɓa barin ta ta amsa mai ba ko da
kuwa amsawar mai muhimmanci ne sai kawai ya cigaba da maganar sa
"Ɗazu Dr Afzal ke sanar da ni cewa Abban mu zai dawo nan Nigeria kuma zai zo asibiti saboda akwai
wani babban case da muka kasa handling properly shine na tambayi Dr Afzal ɗin ko ya jikin ki ya ce min
da sauƙi but i wasn't comfortable so i asked him to give me your phone digits da na karɓa kuma ban
zauna ba sai yanzu shi yasa na kira ki da fatan dai kin warware sosai"?da alama dukkan abubuwan da ya
faɗi daga zuciyar sa suka fito but ta yaya iyayen ta zasu tafi Nigeria amma bata da masaniya akai ko lafiya
Allah ne masani.
Bai yi fushi ba sai ya kuma cewa
"Baby ina son visiting ɗin ki saboda lokacin da abin ya faru na sami labari but my dad send me to clear
up something a wata ƙasar for almost a month ina chan i couldn't communicate with anyone dan jin
yadda jikin ki yake na yi ƙoƙarin kiran ki but it wasn't reaching through,da na dawo Kuma na ji labarin
barin ki ƙasar zuwa germany i wanted coming but our twin bro asked me not to worry too much ya ce
min kina cikin ƙoshin lafiya and he told me that you have regain consciousness shi yasa na sami sauƙin
damuwa ta but still ina da niyar zuwa ganin ki kafin ki dawo dan na san laifuka na sun yi yawa"!!ya ida
maganar yana mai lowering muryar sa ƙasa maimakon ta ji haushin da take ji a kan sa ya rafu sai ta ji
kamar ƙara ninka mata haushin sa aka yi a ran ta dan abin lura shine tun da ya fara maganar in banda
kalmar "ki" da yake amfani da shi baya furta komai toh me yake nufi?zai ce bai san tare da Zaid suka
sami matsalar ba kokuma tsabagen wulaƙancin da cin fuska ce urin ta Aslam ya sa bai nuna damuwar sa
akan shi Zaid ɗin ba?bata tsaya jiran shawarar da zuciyar ta zata bata ba sai kawai ta shiga balbale sa
kamar dai yadda take a da
"Dakata mana Aslam..so kake ka ce min baka da masaniya akan cewa ba ni kaɗai na sami wannan
matsalar ba amma har da Zaid?so kake ka gaya min an baka details na komai da ya faru da ni but an
manta a sanar da kai ciki har da Zaid?koko tsabagen i don't care halin ka ne kake son nunawa a wannan
situation ɗin ma?mutumin da tun da abin nan ya faru ko inda kansa yake bai sani sannan wai baka
tambayi nasa lafiyar ba ka dage kana son sanin ya tawa lafiyar.toh ka sani ko wani ɗan adam na da jini a
jikin sa yadda kaje jin ka ruɗe ka damu da son sanin lafiya ta ni kaɗai toh shima Zaid ɗin miliyoyin mitani
ne ka mararin jin lafiyar sa ba ma mutum ɗaya tal ba dan haka ka ga mallam sai anjima you just spoil the
moon"..zata kashe wayar ya dakatar da ita
"Wait... Waitttt..tsaya,haba baby wannan zafin rai irin taki har tsoro take bani.yanzu saboda Allah bany
kin min adalci kenan?i am here sick and hungry of you just your face alone amma kika yi attacking ɗi na
da maganar wannan mai kama da basamuden marar tsarin kallon?baby kin fah sani ba dan Allah Zaid
yayi selecting naki a matsayin wacce zai tafi outreach da ita ba sai dan ya wahal da ke ya kuma ƙuntata
min dan ya san na riga shi shiga a wurin ki kuma na fisa komai duk fah shi yasa ya yi hakan sai gashi a
hanyar ƙuntata min cikin ruwan sanyi Allah ya nuna mai he can deal with him duk wayon sa da dabarar
sa yanzu fah alhakin zaluntar mu ke bibiyar sa in ba haka ba ta yaya kawai zai zo ya ɗauke li ya kai ki
wata uwa duniyar dabbobi da jakai da sunan outreach kawai dai Allah ne ya kama sa shi yasa ma ni ban
tsaya ɓata lokaci na dan sanin ko ya nasa jikin yake ba"..ran maza ya ɓaci dan shi tunda ta fara maganar
yake hasashen kamar haƙar Zaid ya cimma ruwa dan yadda ta iya rufe idanun ta ta burbuɗa masa masifa
akan Dr Zaid Maher toh lallai in har ba wata abu ba ce a tsakanin su ba ba zata yiai haka ba.
Tun da ya fara aibata da muzanta haɗe da kushe Zaid da halittar sa sai kawai ta tsinci kanta cikin wani
irin yanayi wanda daidai Aslam na dasa aya a surutun sa ita kuma ta datse wayar dan bata son ƙara jin
muryar sa a take ta saka sa a black list ta wurga wayar kan gado ta koma da baya ta kwanta tana nazarin
maganganun Baha so take ta tantance ta cire magana ɗaya mai amfani amma ta kasa haɗa maganganun
ta maida su kalma ɗaya mai ma'ana ita kanta bata san me take ji game da Zaid ba taysayin sa ne ke
ɗawainiya da ita kokuma a'a damuwa da shi da lafiyar sa tayi kokuma wani abin ne na daban Allah ne
kaɗai masanin wannan abin da take ji a zuciyar ta dan she become over reactive whenever is about Zaid
itama bata san dalili ba.wani juyi tayi akan gadon tana cigaba da tunanin ta sai ta ji sallama ɗago kanta
tayi dan ganin ko waye sai ta Ammi ce tashi tayi ta zauna a kan gadon tana mai gaida Ammin amsawa
tayi ta tambaye ta ya ƙarfin jiki
"Baby dama zuwa nayi in sanar da ke cewa Umman ku da Abban mu sun tadi Nigeria sakamakon wani
aiki da ya taso wanda dole sai Abban ku na nan"ta ɗan yi briefing mata komai kamar dai yadda suka
sanar da su sai