Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 74

150K to 153K   out of 221.1K words

ba..

"Listen ban san matsalar ki ba but ko ma menene you should talk to me and not ignore me"wani kallon
haushi da mamaki ta bisa da shi wato bai ma san abin da ya mata ba

"Hmm just let go off me"

"I won't you have to tell me say your problem out speak it out am all ears"harara ta mai kamar zata fitar
da idon waje

"Hmm Zaid you suck...you suckkk..."rumtse idanun sa yayi yana jijjiga kai kafin ya ce

"I know i do suck but tell me,,me ya faru kika min abin da kika min"??..

Tana faman sauke ajiyar zuciya tana kallon sa kamar ba zata yi magana ba

"Zaid why?me yasa ka min haka?sarai ka san abin da ka yi bai kamata ba but yanzu kana kare kanka wai
baka san abin da ya faru ba"kamar zata yi kuka dan son sa ne ke artabu a zuciyar ta amma bata jin zata
iya cigaba da share sa.

"Tell me ban san me na maki ba i swear"wani kallo ta kuma mai kafin ta fizge jikon ta daga nasa cikin
ɓacin rai ta ce

"Baka sani ba ko?jiya saura kaɗan Umma ta mare ni duk dan saboda kai,my brother is angry with me all
because of you and you are telling me you don't know anything"??kallon ta yake yi cikin rashin fahimta
sai ya ce

"But who caused it?ke ce kika janyo dan da kin saurare ni all these wouldn't have happened but you
didn't listen to me"..

Kallon mamaki ta mai kafin ta ce

"Now you are also blaming me too"da ƙarfin sa ya ce

"Yes it's all your fault"da masifa ta ce

"This is not my fault it's all you fault you caused it all"

"Are trying to frame me or what"?kallon you must be kidding me ta mai kafin ta ce

"Are you trying to insult me"?da low tune tayi maganar ya buɗe baki kenan zai bata amsa sai suka ji an
turo ƙofar ɗakin dukkan su suka mai da hankalin su wun ƙofar dan ganin ko waye..
*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*32*
Wacce suka gani a bakin ƙofar ne ya saka su baki ɗayan su sauke ajiyar zuciya cikin tsoro da fargabar ta
shigo a ƙurarren lokaci lokacin da bai dace ba ta yi saurin duƙar da kan ta ƙasa tana faɗin

"Ki gafarce ni Hajiya wallahi ban san komai ba kawai shigowa nayi na ɗauka ke kaɗai ce a ɗakin shi yasa
na shigo kai tsaye ki min afuwa ranka ya daɗe ka min haƙuri ba da niya ko manufa na shigo maku haka
nan ba"sauke numfashi Bilkisu tayi tana kallon matar nan sai ta ce da ita

"Ba komai ajiye abincin ki tafi"jiki na ɓari ta ajiye kamar ana tsungulin tatayi gaba har da tuntuɓi dan
ganin laifin kan ta ta shiga gani da ta nace da yin sallama da bata shigar masu ɗaki haka ba..

Tana saukowa Hajiya Zeenat dake zaune saman two seaters hannun ta riƙe da tablet tana yin
transaction ta hango Alawiyya dake saukowa suƙuƙui kamar mai cuta sai ta ɗan karance ta kaɗan tana
nazarin me kuma ya kai ta ɗakin Bilkisu dan ta direction ɗin ɗakin ta fito sai dai yanayin ta na nuni da
wani abin ba daidai bane.

Har ta gifta zata tafi kitchen Hajiya Zeenat ta kira sunan ta

"Alawiyya zo nan"a firgice ta juyo duk tunanin ta baby doctor zata balbale ta ne dan ta kutsa mata kai
cikin ɗaki ba tare da ta bata izini ba but luckily enough for her tana juyowa ta ga uwar gidan ta ne sai ta
sauke ajiyar zuciya ta dawo da baya tana faɗin

"Wallahi hajiya har kin saka ni jin tsinkewar gaba,duk tunani na hajiya ƙarama ce"jin haka sai Hajiya
Zeenat ta gane zargin ta ya zamo gaskiya kenan sai ta gyara zama tana mai kallon Alawiyya da kyau

"Ke ban son shirme gaya min,me ya faru da hajiya ƙaramar"??ta tsare ta da ido dan kar ma ta sami
damar lauya maganar sai ta shiga inda inda kamar marar gaskiya sai da Hajiya Zeenat ta tsawatar mata
sannan ta natsu tayi mata bayani

"Hajiya,abincin Hajiya ƙarama na kai mata ɗakin ta na duba ta can balcony bata nan sai na yi sallama
ban ji amshi ba sai kawai na shige kai tsaye dan nayi tsammanin baccin ta koma yi saboda lokacin da ta
kira ni tace in zo in kawo mata abinci daga bacci ta tashi,toh Hajiya in gaya maki ina tura ƙofar ban fah
lura ba na saka kai na shige da niyar in ma baccin take sai in zo in maki magana a tashe ta baccin yayi
yawa haka nan amma abin kunyar da na janyowa kaina ya sa na kasa faɗin komai Hajiya"sai kuma tayi
shiru alhalin Hajiya Zeenat ta kasa kunne tana jiran jin zance amma Alawiyya tayi shiru.

Ɓata fuska Hajiya Zeenat tayi dan tasan halin Alawiyya ita ɗin yarinya ce mai kawaici da rashin son
gulmace gulmace shi ya sa nasu yazo ɗaya da Hajiya Zeenat ɗin.

"Kina ƙarasa gaya min ne ko kuma in bar ki har Hajiya ƙaramar ta zo ta isko ki da bala'in ta"?ai jin
wannan sai ta ce

"Haba Hajiya a yi haka,a'ah bari dai in gaya maki,,kin ga da na shiga ɗakin sai na gan ta tare da shi mai
gidan nata a tsaye kamar dai ma magana mai muhimmanci suke yi da juna shiga ta ce ta katse masu
maganar da suke yi,wallahi Hajiya duk kunya na ji ga tsoro na hana su ƙarasa maganar su sam ba da wata
manufa nayi hakan ba wallahi abinc...."nata bar ta ta kai ayar zancen ba dan ta sami abin da take son ji
dan haka ta dakatar da ita ta hanyar ce mata

"Is okey ya isa haka nan tafi abin ki zan yiwa Bilkisun magana dan kar tayi fushi"har ƙasa ta duƙa tana ma
Hajiya Zeenat godiya kafin ta tashi ta bar wurin.

Bin ta da kallo Hajiya Zeenat tayi kamar ita ce Bilkisun har ta ɓace sannan ta dawo da idanun ta saman
tablet dake hannun ta tana girgiza kai at the same time tana murmushi ita kaɗai...

Dama sai da Hajiya Madina ta yi maganar nan ta ce mata da miji duk borin da zasu yi ba lallai bane mu
san lokacin da zasu shirya ba hakan kuwa gaskiya ne dan gashi tun ba'a kai ko ina ba da tigimar har an
fara siɗaɗewa ana zuwa ganin juna a ɓoye.

Murmushi mai ƙayatarwa tayi tana jijjiga ƙafar ta dan abin nasu yanzu dariya yake bata kamar dama
wani ne ya ce da su suyi faɗar da suka yi..

"Allah ka ƙara haɗa mana kawunan ƴaƴan nan namu ka basu zaman lafiya da fahimtar juna dan suna
lacking fahimta a zaman nasu..

Gyara ƙafar ta tayi bisa kujerar tayi positioning tablet ɗin tana murmushi sai ga fuskar Hajiya Madina
yayi appearing a screen.

"Kai aminiya ya naga annuri ne bisa fuskar ki ko dai yarinyar nan ciki ne da ita"??dariya cikin ƙasaita
Hajiya Zeenat tayi tana faɗin

"Ko ɗaya wallahi ai mu da ganin ranar ɗaukar cikin nan sai dai mun gani"da amusement Hajiya Madina ta
ce

"Kina nufin me kenan"cikin halin ko oho ta ce

"Ai shekaranjiya yaran nan suka haɗe humm"abin ita kanta da take faɗa ya bata mamaki bare Hajiya
Madina da ke sauraron ta sai ta ce

"Bilkisun ce ta sanar da ke"?girgiza kai tayi ta ce

"Ina fah zata faɗi gaskiya,ai ta san bata da gaskiyar ne tsabar hauka ne da rashin tunani ya sa ta yi abin
da tayi"saurin katse ta Hajiya Madina tayi tana jujjuya mata yatsa ta ce.

"ia mu ne marasa gaskiya Hajiya Zeenat"da mamaki ta ce

"Mu kuma"?gyaɗa mata kai tayi kafin ta ce

"Can you imagine,bamu fah tsaya mun saurari ainihin dalilin yarinyar nan ba fah kawai muka ɗau mataki
kenan in har a daren washegarin dawowar su ne suka sami matsalar nan kamar yadda ta faɗa to lallai
akwai ɓoyayyen lamari dan ban ga alamar rashin jituwa ba a tsakanin su saman fuskar Zaid da safen nan
ba dan ya shigo gaida ni har ya so yayi min maganar matsalar amma na kauce mai ban bari yayi ba,dole
zalintar yarinyar nan yayi i just pray ba fin ƙarfin ta yayi ba ta ga ba zata iya zama da shi ba again ya kuma
ƙara mata takaicin maganar wata ba a daren farkon su ba dan har in dai wannan ne dalili then i must say
Zaid bai da hankali"ran ta a ɗan ɓace ta ida maganar sai Hajiya Zeenat ta ce mata

"Ni kam duk ba blame games ɗin nan ba wannan damuwar su ne amma ki sani yanzu da haka right
now,,Zaid na gidan nan chan ɗakin ita Bilkisun"!!mamaki ƙarara saman fuskar Hajiya Madina ta ce

"Ban gane ba aminiya"darawa Hajiya Zeenat tayi kafin ta amsa mata

"Yanzu kuwa zaki gane"nan ta sanar da ita exactly abin da Alawiyya ta sanar da ita.

Wani shewa suka yi sai Hajiya Madina ta ce

"Bana kusa da ke da mun tafa,ai dama na gaya maki duk borin da zasu yi mata da miji ne matsalar sai in
har basu san junan su ba amma matuƙar suka sani toh fah ba faɗa ba ko yaƙi suka yi zasu dawo su liƙe ne
yanzu ke da ke gidan kin ma san lokacin da Zaid ɗin ya shigo maki gida"!?girgiza kai Hajiya Zeenat tayi
tana mamakin ƴaƴan nasu

"Kin gani,dan haka ƙala kar ki ce da su su gama sulhunta kan su su gyara babu ruwan mu ciki but kafin
nan ya aka yi kika san abin da ya faru wa ya sanar da ke"?murmushi tayi ta ce mata

"Zainab matar Jamil"cikin son jin labari ta ce

"Gaya min mana"tas ta mayar mata da zancen ta ɗora da

"Sam ni ban yi tsammanin kishin Bilkisu ya kai har haka ba duk fah ta haukace da yawa"..gyaɗa kai Hajiya
Madina tayi ta ce

"Manta su kishi ai haƙƙun ne dan tayi kishin sa ba laifi bane but mu dai zuba masu ido what goes around
comes around"murmushi Hajiya Zeenat tayi sai ta ce

"Wai fah tare suke ni abin ma har yanzu dariya yake bani ki ga fah yadda yarinyar ta ta zaƙe ita fah sam
babu ita ba u shi but ko me ya canza ta"da dariya ta gama maganar wanda har sai da Hajiya Madina ta
taya ta dariyar

"Ai bar su kawai zasu gane kuren su mu suke son rainawa hankali su mai da mu ƙananan mutani"dariya
suka kuma yi kafin daga bisani suka yi sallama.har suka gama wayar nan mamakin Bilkisu da Zaid bai bar
ta ba...




A nan ɗakin Bilkisu kuwa bayan fitar Alawiyya iska Bilkisu ta furzar cikin son kare kan ta ta ce

"Please in ka san blame games ka zo playing da ni har gidan mu just go away i don't want to hate you
more"zafi take ji cikin ran ta dan yayi putting blind face to matsalar yana son ce mata bai san me ya faru
ba kenan itace mahaukaciya mai ɗaukar son sa da kishin sa a kan ta tana yawo da shi..
Harɗe hannuwan sa yayi bisa ƙirjin sa yana bin ta da kallo dan mamakin ta ya kasa barin sa mutum da
mood swing haka da tana da ciki ne ma sai ya ce ɗaya daga cikin changes da ke samin mata kenan in sun
yi conceiving amma ita babu but she gets irritated easily.

Yana kallon ta ta gama maganar da zata yi shi dai nashi ta bashi chance su yi magana ya ji damuwar ta
dan dole yana son tafiya Yola washegari kuma bai son tafiya da damuwar Bilkisu a zuciyar sa.

Takowa yayi kusa da ita ya durƙusa ya kawo hannun sa ya haɗa da nata yana kallon ta tun bata son
kallon sa har ta mayar da hankalin ta kan sa ta shiga kallon sa sai a yanzu take ƙare masa kallo tsaf a
tsanake.

Kyawun sa da kyawun shigar da yayi ta ke yabawa a ran ta sai kuma kishin sa ya biyo bayan yabon sa da
take cikon ran ta dan ba ƙaramin kyau ya mata ba ko ina zai tafi da yayi wannan irin adon she just pray
ba fita zai yi tana roƙon Allah ya sa dan ita yayi adon..

Ɗago idanun ta tayi ta sauke saman fuskar sa ta tsare sa da ido shi kuma sai ya ɗauka ko attention ɗin
ta ta ba sa dan haka ya fara magana cikin lumana da son samin mafita

"Bilkisu ki saurare ni ki bani breathing space in maki bayanin matsalar da ya kawo mana kai but ba zan
iya explaining kai na ba har sai na san damuwar ki ki yi haƙuri ki sanar da ni matsalar me na maki da kika
ɗau wannan matakin a kai na"?ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon ƙwayar idanun sa tana so tayi
fushin da shi amma ba zata iya ba.



Idanun su cikin na juna ta girgiza kai tana mai juyar da kan ta gefe sai yayi saurin riƙo fuskar taya dawo
da shi direction ɗin nasa fuskar suna kallon juna sai ya girgiza mata kai ya ce

"Kar mu fara da haka baki zaki buɗe ki min bayani,sam bana son hayaniya Bilkisu but you made me raise
my voice on you why"?kallon sa tayi idanun ta na cikowa da hawaye sai ta fara magana cikin karayar
zuciya

"Na san ba ni kake so a,na san ba a hayyacin ka aka haɗa mu aure ba na san ba so na zaka yi ba ko a
wani duniyar,amma ka sani nima ba yin kai na bane zama tare da kai,ban taɓa mafarkin zama inuwa
ɗaya da kai ba dan bamu da kyakyawar fahimtar juna,,,a ranar da na bari abu ya shiga tsakani na da kai a
ranar ka yi manifesting min real you...,,ka nuna min tsana tsantsan,,,ka mim kora da hali Zaid,you should
have been patient da na bar maka rayuwar ka at a twinkle of an eye ba sai ka nuna min ƙarara tsanar da
kake min for a very long time ba"shiru ta mai bata cigaba da maganar ba sai ya ɗan ɗago daka
tsugunnen da yayi height ɗin sa ya zo daidai da nata yana bin ta da kallon da shi kaɗai ya san ma'anar sai
ita kuma ta sauke kan ta ƙasa dan hawaye ne ke son zubo mata kuma bata so ya ga weakness ɗin ta.

Cikin sanyin murya ya shiga yi mata magana kalmar farko sai da ya saukar mata da kasala

"Baby,,..you see....bana son ki saka wani abin a ran ki after what happened between us that night....nayi
ƙoƙari dan in ga na gane damuwar ki amma baki bani chance ba...a yanzu da muka haɗu kuma kina son
mayar da maganar wani abin daban can you please spot out the main point of concern to me ban san
laifin da na maki ba"..idon ta ta zuba mai har ya gama maganar sa sai ta hau girgiza kai tana cire hannun
ta cikin nasa ta matsa baya kaɗan haɗe da ture sa daga jikin ta

"Zaid,,,ka faɗa min irin tsanar da kake min...please tell me"!!!abin ya ɗaure masa kai shi tambayar ta yayi
amma ta juyar da maganar zuwa kan sa sai ya ce

"Bilkisu bana son wani blame games anymore just tell me,mai na maki"?idon ta ya canza launi ya
ƙanƙance dan ba ƙaramin kuka ta sha ba..

"Baka san laifin da ka min ba"?muryar ta chan ƙasa tayi mai tambayar sai ya girgiza kai yana mai ƙara
riƙo hannun ta cikin nasa

"Zaid......,,my first reunion with you.....you didn't even remember me...wata fah ka rinƙa kira...sunan
wata ka rinƙa nanatawa sama da abin da zan iya ƙirgawa...i....i...gave you something precious in my life
but....you handled it carelessly...duk saboda ka tsane ni Zaid....you broke me into pieces....you made me
hate you a hate that has no limitations a hate that is created out of trust...the hate you gave me was a
massive one...baka san abin da ke rai na ba akan rayuwar mu amma you diminished everything you
changed our fate you spoiled everything and i hate you for that i hate you for tarnishing our future my
future i hate you for that Zaid"sai ta shiga dukar sa a ƙirjin sa tana kuka dan ta kasa riƙe hawayen ta dan
abin na mata ciwo duk sa'iln da ta tuno kalmar da ya faɗa mata na cewa _yes i have feelings for her and
you can't do anything about that_ sai ta ji ran ta na mata zafi dan da a ce bai nuna mata abin da yake
buƙata daga gare ta ba da ba zata ji zafin sa sosai ba amma ya nuna mata halin su na maza ya sami abin
da yake nema daga gare ta ya ji ta ishe sa..



Bai hana ta ba dan ya san huce haushin ta take yi kuma hakan ya fi da ta zauna da damuwar sa cikin ran
ta tana kallon sa a matsayin weird person and not gentile..

Dan ƙashin kan ta ta bar sa ta daina dukan nasa ta kuma ture sa tana share hawayen ta,

A yanzu ya ƙara fahimtar sunan Asma'u ne bata son ji kwata kwata kenan saboda ya kira sunan Asma'u
ne ta birkice masa a ranar har tayi punishing nasa haka..kallon ta yayi ya ce

"Did you not like Asma'u"??rumtse idanun ta tayi da ta ji ya kirawo sunan Asma'un daɗin wani abin
takaicin ya kuma rura mata a ran ta by calling Asma'u's name

"Baki son jin sunan Asma'u ne"??cikin bala'i ta ce

"Get lost just go to hell i hate you"halbin sa tayi da pillow dake kusa da ita daga haka ta tashi ta bar masa
ɗakin tayi shigewar ta toilet,zama yayi a ƙasa yana tunanin ta yadda zai ɓullowa lamarin Bilkisu dan in ya
bar ta a haka abin zai yi mata yawa dole ya fahimtar da ita alkhairin da Asma'u ta mai a baya da dalilin sa
na son sanin lafiyar ta he have to create an atmospheric understanding between them dan baya son
hatred ɗin da Bilkisun ke da shi akan Asma'u yayi yawa itama ai mutum ce kuma yarinya she should be
treated as a human and not an enemy..



Tashi yayi ya nufi bakin ƙofar toilet ɗin ya manna kunnen sa sai ya ji shiru hakan ya saka sa yin magana

"Bilkisu i have to get going ina son tafiya Yola gobe na so mu tafi tare da ke but bana son in takura maki
dan na lura baku da fahimtar

51 / 74