Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   64 / 74

189K to 192K   out of 221.1K words

zage ya
rinƙa kwasar mata abubuwan da ya san zasu faranta mata rai dan farincikin da ta saka sa ciki bai san da
me zai saka mata ba..

Da ido ta rinƙa bin sa da kallo har suka kammala suka bar mall ɗin bini bini kaɗan sai ya tambaye ta
hope she is fine babu wani discomfort sai tayi faking murmushi ta nuna mai babu komai har suka iso
masaukin su sallah suka yi sannan ya ɗau wayar sa ya kira Dr Hussain yana ɗagawa ya ce

"Man ya naga international number"da fara'ar sa ya ce

"Mannn muna dubai,,maganar ka ta zamo gaskiya my wife is 3 weeks pregnant"sai suka saka shewa
suna sharing joy ɗin abin ita dai ta zama mutum mutumi..

Suna gama wayar ya sake trying layin Hakim ai kuwa ya shiga dama shine suka daɗe basu yi waya
ba..,rumui rumui suka gaisa sai da suka kai ƙarshe ya ce da Hakim ya kira Ammi ya sanar da ita cewa ta
kusa zama granny sai kuwa Hakim ya fasa ihu yana jin daɗi wai ya kusa zama uncle murna kamar ya
janyo su kusa da shi..
Hakim voice of every body a familyn sai kuwa ya shiga spreading news da ɗumi ɗumin sa sai dai Zaid ya
kashe masu wayoyin su ya ce yau ɗin ranar love ne in washegari yayi sai su buɗe wayar su bi voice
messages suyi responding haka ta rinƙa yin murmushin dole ba dan tana so ba dole ta biye mai ranar
suka rinƙa baje kolin soyayya amma hankalin ta sam baya jikin ta but she knows what she will do is the
best kuma zasu yi benefiting gaba ɗayan su...

Kiran sunan ta yayi bayan sun fito daga wanka yana goge jikin sa ita kuma tana zaune gaban mirror

"Sugar,are you satisfied?kin san masu ciki da buƙata"halbin sa tayi da foam da take goge fuska da shi
sai ya matsa yana dariya ita kuma tana murmushi..

Rungume ta yayi ta baya yana faɗin

"I love you my girl"ta ɗan murmusa tana faɗin

"I love you more my hero always remember that"suka yi ma junan su murmushi suna kallon kan su ta
mirror..



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim



*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*
*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



_This page is a give away to all Iya Ruwa Fidda kai fans masu yin comment daki daki i❤u guyz_



*39*



*_Dilemma_*




_Ƙauyen koma_



Tun ranar da yayyen Asma'u suka wa mahaifiyar su magana akan ta yarda su tafi da Asma'u cikin birni
dan samin kwanciyar hankalin ta ta ƙi yarda ta saurare su basu kuma tuntuɓar ta ba sai suka bar ta dan
ta sauko ta yadda zata amince da ƙudirin su..basu sake neman ta da zancen ba sai bayan kwanaki shida
suka kuma tunkarar ta da zancen ta so ƙyale su amma suka roƙe ta da ƙyar da siɗin goshi ta amince da
sharaɗin duk wanda yace yana son ta da aure su tabbatar sun sanar da shi hallayar ta da kuma cikin dake
jikin ta dan kar a dawo ana abin dana sani..

Amincewa suka yi suka yarda da haka suka kirawo Asma'u suka tasa ta gaba masu faɗan baki nayi masu
ji kamar su make ta na ji sam bata ɗau halayyar su ba Mudan ya rigada ya gama lalata masu rayuwar
ƙanwa...
Ita dai murna ne duk ya mamaye ta da farinciki ko ba komai zata bar ƙauyen su ta huta da tsangwamar
jama'a dan itama takaicin kan ta take sam sai yanzu take nadamar halayyar rashin ɗa'ar ta bata san
wataran yana iya dawo mata a karkace ba sai yanzu da duniyar ta juya mata baya ta nuna mata iyakar
ta..

A yadda suka tsara tafiyar bayan kwanaki biyu daga ranar da mahaifiyar su ta amince zasu yi tafiyar dan
haka ta shiga harhaɗa kayayyakin ta cikin ghana most go da aka siyo mata sabo komai nata na buƙata ta
tattara ta saka ciki bata muradin dawowa ƙauyen har abada kuma ta ma kanta alƙawari akan kafin su
yafi sai ta tafi gidan su Mudan ta ma mahaifiyar sa rashin mutunci sannan ta mai maganar da sai ya
gwammace mutuwar sa dan ba zata ɗau kayan takaici ita kaɗai ba,Mudan ya gama yi mata cuta cuta
mafi muni a rayuwar ta ya illata mata rayuwa sam ba zata taɓa barin sa ya cigaba da morar rayuwar sa
cikin jin daɗi ba addu'a take Allah ya ɗauke ran sa bayan ya gama azabtar da shi..



Chan cikin dare ana washegari zasu wuce ta yi satar hanya ta fita ta yi tafiya mai ɗan tsayi sannan ta isa
gidan su Mudan,luckily enough sai ta ga mahaifiyar sa na fitowa daga ɗakin sa da bokitin ruwa a hannun
ta sai ta ji kamar ana motsi dan haka ta haska fitilar hannun ta sai ta ga Asma'u

"Wa nake gani haka kamar ma'u"cikin fitsara da rashin kunya ta ce

"Ni ce mana baki gani ne da dare"?cikin tsinkewa da lamarin Asma'un ta ce

"Ke kuma me ya jefo ki gidan mu cikin daren nan ko dai yawon ta zubar ɗin kika zo yi a nan toh ai sai ki
ƙara gaba dan kin jefa min rayuwar ɗa cikin matsala da damuwa"ai kuwa buɗar bakin Asma'u sai cewa
tayi

"Ke kama kan ki wallahi ba sanyi nayi ba har yanzu ina nan da rashin mutunci na kamar da,sannan da
kike faɗin yawon ta zubar har ke kina da bakin gaya min ina yawon ta zubar?tsaf kin san ni kin san gidan
mu kuma kin sa bamu da shegu a gidan mu da tarbiya ta na taso amm wannan macuci azzalumi maci
amanar wanda ya yarda da shi ya san yadda yayi ya tozarta ni ya ɓata min sunan a ƙauyen nan ya ɓata
min sunan a gidan mu ya ɓata min tarbiya ya gama lalata ni ya maida marar kunya sannan zaki zo kina
faɗin ni ce na jefa mai rayuwa cikin matsala har akwai babbar wacce ta shiga matsala sama da ni ne?ni
da aka zalinta aka yiwa cikin shege?toh wallahi bara kiji in gaya maki baba lantana kin san Allah
ɗaya,,birni zan tafi ina tafiya Allah ya sa na haife wannan asararen cikin turo maku shi zan yi in yi aure
nan kuma bana fata Allah ya ba ɗan ki lafiya ubangiji Allah ya dawwamar da shi cikin wannan baƙar hali
da yake ciki kuma Allah ya kawo ajalin sa bayan ya gama azabtar da shi da wannan ciwo da yake
yi"...baki hangame idanun waje mahaifiyar Mudan ta ke bin Asma'u da kallo dan bata san rashin kunyar
ta zai kawo kan ta ba.

Kaf abin da Asma'u ke zazzagawa mahaifiyar Mudan duk a kunnen sa yana ji kuma yana nadamar rashin
abin kirkin da ya aikata a rayuwar sa gani yake yadda Asma'u ta juya mai baya ta zaɓi ɗan birni abin da
ya mata a ganin sa shine daidai sai dai kuma abin da shi aka mai sai ya ga kamar haƙƙin ta ne ke bibiyar
sa hakan ne ma ya sa yake roƙon Allah ya bashi lafiya dan ya je ya bata haƙuri ya kuma ce da ita ya
amince zai aure ta tunda shi ya lalata ta..

"Ma'u ki dubi girma na ki dubi shekaru na ki gasa min maganganun rashin ɗa'a haka"?kallon hadarin
kaji ta mata ta ce

"Ban sani ba"tana gama faɗin haka ta ja doguwar tsaki ta yi kamar zata bangaje ta ta wuce cikin ɗakin
da Mudan ke ciki yaye labulen tayi ta riƙe ƙugu tana karkaɗa jiki tana aika mai da kallon tsana.

Duk ya zabge ya rame ya zama wani iri kwance kamar marar rai sai dai bakin sa ya fara buɗewa yana iya
buɗewa yayi magana ƙasa ƙasa.

Kallon sa tayi ta ja tsaki kafin ta fara zazzaga mai maganganun da suke kamar garwashi ne a gare shi
duk abin da take gaya mai ya san laifin sa ne shi ya janyo hakan kuma babu ƙarya cikin bayanan ta..

A ƙarshe ta ce da shi

"Baka fah ga komai ba Mudan sai rayuwar ka ta fi haka salwanta sai rayuwar ka ta ɗaiɗaicr sai ka
wulaƙanta fiye da yadda ka wulaƙantar da ni sannan ka mutu mutuwar wulaƙanci mugu azzalumi maci
amana Allah ya isa tsakani na da kai Mudan"kamar zata yi kuka haka ta ƙarasa maganar sannan ta bar
ɗakin mahaifiyar sa na kallon ta tana jin wani iri sai yanzu take jin rashin daɗin da Asma'u ta daɗe tana ji
sai ta rasa me ya hana ta ganin hakan tun fari....



Tana kuka tana haɗa ƙafar ta haka ta nufi hanyar titi ta tari a daidaita ta nufi gidan mai gari dan yi mai
bayanin abin da ya faru da ita da kuma asalin abin da ya faru wanda bata sanar da shi ba a baya da take
zaryar tafiya gidan..

Goma saura na dare ta iso gidan mai gari abin ya basu mamaki ganin ta cikin wannan dare kamar tayi
ɓatar hanya amma abin da ta tafi masu da shi ne ya jijjiga su suka gane cewa lallai bata da laifi a matsalar
da ya sami likitocin birnin da suka taho masu rashin wayo ne ya saka ta aikata abin da tayi dan haka mai
gari ya mata fatar alkhairi akan Allah ya sa iyakar matsalar ta kenan kuma Allah ya inganta mata rayuwar
ta,bari masu magana tayi akan duk ranar da ɗan birni zai zo a sanar da shi gaskiyar lamarin sannan a
nemar mata afuwar sa a bashi haƙuri akan gazawar ta wurin kuɓutar da shi daga faɗawa tarkon Mudan.

Abin gwanin tausayi haka ta bar gidan tana kuka ta kama hanyar gidan su ba wata tazara bace tsakanin
gidan nasu da na mai gari ba shi yasa ko da ta fito bata sami adaidaita ba ta taka da ƙafa ta koma gida...



A saɗaɗe ta shige gidan godiyan ta ɗaya babban yayan ta bai dawo daga cikin gari da ya tafi ba tun safe
dan haka ƙofar gidan a buɗe yake an bar shi saboda da shi,a ɓoye ta shige ta kwanta bisa katifar ta tana
jin wahalar ta ya ɗauke daga washegari in suka bar ƙauyen bata kuma waiwayo ƙauywn sai har ta zama
wani abin a rayuwa ta yadda in ta dawo mahaifiyar ta zata san cewa ta gyaru ta natsu....
A ranar da zasu tafi ta shirya cikin shigar mutunci ta saka kayan ta wanda ta fi so fiye da sauran kayan
ta ta ɗan yi ado ta saka hijabin ta sabuwa wanda yayan ta ne ya ɗinka mata akan in zasu tafi ta saka shi...

Ɗakin mahaifiyar su ta tafi ta tsugunna har ƙasa ta gaida ta,kamar ba zata ansa ba sai ta amsa da
ƙyar,kuka ta saka mata tana roƙon gafarar ta akan ta yafe mata ƙilla tafiyar kenan in bata dawo ba ta
yafe mata sai tausayin ta ya kama mahaifiyar nasu har dai ta ji ya kamata ta tausaya mata dan duk abin
da ya faru da bawa muƙaddari ne ba shirin bawan ba..

Jan ta a jiki tayi ta shiga rarrashin ta itama tana kukan da ƙyar dai suka yi sallama ta raka su har wurin
shiga mota dan a ƙofar gidan su motar da suka yi shata ya zo suka loda kayayyakin su ciki suka yi sallama
da mahaifiyar su suka shige ita kuma da sauran yayyen Asma'u suka koma ciki..



Tafiyar awowi uku da rabi ne ya kawo su cikin birnin Adamawa inda suka ɗau mota ya kai su har
anguwar da zasu tafi gidan ba wani babban chan chan bane tsaka tsakiya ne amma yana da kyau kallon
gidan Asma'u ta rinƙa yi tana jin daɗi itama zata zauna a birni ko goge goge ne ta amince zata na yi a
gidan muddin zasu bar ta ta zauna a gidan..

Ƙarasawa ciki suka yi da yake shi ɗin ɗan gida ne an san shi suka yi gaisuwar sannaya ya masu bayanin
ko wacece Asma'u a gare sa ta gaida su gaisuwar mutunci suka shiga ɗakin sa na gadi ya nuna mata inda
zata zauna ta shige da kayan ta ta ajiye ɗakin mai ɗan girma ne ba laifi akwai tsari daidai
gwargwado,akwai wani katifa kamar sabo ne sai dai ba fil ba amma bai ji jiki ba..

Shigowa yayi ya ce da ita ta fito su tafi cikin gidan su gaisa da ƴan gidan,tashi tayi suka bar gefen nasu
suka tafi ciki aka masu iso suka shiga cikin falon mai kyau da fasali suka zazzauna a ƙasan kafet ɗin inda
babu jimawa Hajiyar gidan ta sauko fuska ba yabo ba fallasa suka gaisa ya mata bayanin wacece Asma'un
da kuma matsalar da yake tattare da ita amma ya ɓoye mata rashin jin da Asma'un tayi a rayuwar ta a
ƙauyen su, kuma gaisawa suka yi da Asma'un ta karɓeta a matsayin ƴar aikin da zata ɗauka a cikim gidan
dan duka ƴaƴan ta mata sun yi aure sai dai jikoki da kan zo mata hutun ƙarshen mako su tafi ranar lahadi
toh shine ta ɗauke ta a matsayin wacce zata na kula da yaran in sun zo sannan on normal basis zata na yi
mata ƴan share share da goge goge amma banda girki dan ita ke girkin ta da kan ta...

Godiya sosai suka mata daga Asma'un har yayan nata da karramawar da ta masu..



Tun daga ranar Asma'u ta ke aikin ta a gidan tun ƙarfe 7 na safe zata bar gefen su ta tafi sashen Hajiyan
ta mata aiki da yake mijin Hajiyan ba zama ya cika yi ba yana yawan tafiye tafiye dan haka ta waya
Hajiyar ta mai nayanin Asma'un ya nuna in har ita hankalin ta ya kwanta da yarinyar toh ta bar ta ta
zauna...
Ƙalau suke zaman su a gidan at the same time tana ganin canje canje a jikin ta sakamakon girman da
cikin ta ke yi wani lokacin takan zauna ta yi kuka tana nadamar rayuwar ta gashi yadda duniyar ta mata
juyin masa amma har da hakan tana godiya ga Allah da ya sa ta zo nan gidan ta kuma gode da irin rufin
asirin da ta samu a gidan haɗe da karramawar da ƴan gidan ke mata,wasu ranakun hutun har da iyayen
yaran kan zo gidan su kai har yamma sai su tafi su bar ƴaƴan a haka a haka har suka ɗan saba da ita
ganin irin kula da gidan da take yi dama kowani wargi wuri ya samu yanzu da Asma'u ta ga rayuwa sam
babu wanda zai kalle ta ya ce ta taɓa tsula rashin kunya a ƙauye sam ta natsu daga aikin ta sai zaman
ɗaki wasu lokutan ne ma jikokin Hajiyan kan ja ta akan ta zo suyi karatu in mallamin su na isalamiya ya
zo da kaɗan kaɗan tun tana jan baya tana jan jiki har ta fara sakin jikin ta babu wani abin da zata ce da
matar nan sai addu'a dan sam bata nuna mata tsangwama ko kaɗan...



A haka cikin Asma'u ya kai har tsawon wata uku da ɗoriya ya fara fitowa sarari dan haka Hajiyan ta bata
shawarar canza kayan sakawa ta rinƙa saka dogayen riguna dan sune zasu sake mata a jiki ita da kan ta
ta bata wasu kayayyakin yaran ta da sukan tattaro su aiko da su akan a bayar da su sun tsufar masu,sai
ta ba Asma'u su ita kuma ta rinƙa godiya.

Bata rasa ci ko sha ba komai dai Alhamdulillah yana tafiya mata daidai dan har shawarar fara zuwa
awon ciki Hajiya ta bata akan cikin albashin ta na ko wani wata ta rinƙa cirewa tana tafiya awon da haka
ta ɗau shawarar dan ko wani wata ana bata dubu shida a hakan ma dole ne dan cewa tayi ga wun zama
ga abinci har da kyatuttukan bazata ita ba zata iya karɓar wani kuɗin aiki ba toh sai da Hajiyar ta dage
sannan ta amince ta fara karɓa saboda Hajiyar na jin daɗin zama da yayan Asma'u saboda amanar sa da
gaskiyar sa gashi ta gwada Asma'u ta hanyoyi da dama kuma duk gwajin da take mata bata taɓa faɗi ba
shi yasa ta amince ta yarda da ita har take jan ta a jiki......




**************



A nan ABJ kuwa tun da Aslam ya sami labarin cewa Zaid da Bilkisu sun shirya sun koma gidan su da zama
abin bai mai daɗi ba shi so yayi ya same ta a matsayin matar auren sa dan gani yake sam Zaid bai san
yadda ake kula da mace ba duba da yadda yake da izgilanci da jin kai sai yake ganin sam ba zai iya nuna
soyayya ba shine ya fi dacewa da ita ba shi ba amma bayan dogon nazari da shawarwarin da mahaifin sa
ya basa akan ya rabu da Bilkisu ya fitar da tunanin ta a ran sa dan ba ita kaɗai bace mace akwai waɗanda
suka fita kyau da ilimi ya cire ta a zuciyar sa kawai dan ta auri wani already kuma ya san wannan ɗin ba
sakin ta zao yi saboda shi ya aura ba,,wannan shawarar mahaifin nasa yayi amfani da shi ya cire Bilkisu
da ƙyar a zuciyar sa dan har mafarkin ta yake yi duk ya damu ya dami kan sa ganin haka sai iyayen sa
suka yanke shawarar yi masa aure da wata ɗiyar ambassador aminin mahaifin Aslam ɗin ne na kusa
yarinyar na ajin ta na ƙarshe a wani jami'a chan ƙasar Cairo tana karanta tsumi da dabara wato
Economics.

Ko da labarin ya iso sa bai wani nuna ya yi maraba da zancen ba kuma su iyayen basu janye ba dan so
suke su mai auren gata dan ya more rayuwar sa..



Kamar wasa dai haka aka haɗa su dole ita dai yarinyar dama kamar tunkiya take in an ce yi nan nam
zata yi bata da wani matsala ko damuwa girman falo girman cikin gida ne babu wayo sosai ita bata ja da
maganar ba shima ɗin da ƙyar aka tanƙwasa sa ya fara zuwa ziyartar ta in ta zo hutu da kaɗan kaɗan dai
suka fara sabawa har dai suka fara sakin jiki da juna inda daga haka ne aka tuntuɓe su da batun in sun
shirya sai a yi batun auren amsawa suka yi dan haka aka saka biki ba tare da an ja lokaci ba kwata kwata
wata ɗaya ne cif wanda in aka yi da watanni biyu za'a yi na su Afzal da Baha.

Ko da su Pro da Dr Maher suka ji taya Dr Aslam ɗin murna suka yi suka kuma yi mai fatar samin happy
home ya masu godiya tun daga

64 / 74