Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
juna but if you study Asma'u zaki gane cewa yarinya ce marar matsala da
damuwa you will like her she is very simple and friendly believe me"tsakanin sa da Allah yake maganar
dan shi bai ɗau abin a matsayin wani babba ba sai daga cikin bayin ya ji tana ce mai
"Zaid ka tafi mana hala riƙe ka nayi?na hana ka tafiya ne?go...go to Asma'u i never stunted you do i"?
yana iya sensing ɓacin rai cikin muryar ta dan haka ya ce
"Ƙarya kike yi...na san baki son yarinyar nan kuma kina faɗa ne dan you are up to something"abin
mamaki wato bai ma yarda da ita ba kenan yake nufi dan haka daga bayin ta ce da shi
"Duk ba laifin ka bane laifi nane da ban taimake ka ba na bar ka da duk hakan ba zai taso ba"daga haka
ta fito daga bayin yana kallon ta cikin azama ya zo zai riƙo ta banka mai harara tayi waje shima sai ya
biyo ta ya manta ba gidan su bane daga shi sai ita ba tana tafe tana data sanin yardar mai ya haɗa jiki da
ita shi kuma yana faman kiran sunan ta yana ce mata ta tsaya suyi magana amma ko kallon sa bata yi ba
suna falon suka ja burki dan ganin Umma da suka yi zaune nan wurin ita kuwa tana ganin su tayi kamar
bata san Zaid ɗin na gidan ba dama sai ta kalle su da fara'ar ta ta ce
"Hello"kasa amsa mata suka yi sai Bilkisun ce ma tayi ƙarfin halin zama a ɗaya daga cikin kijerun falon
shi kuma cikin jin nauyin Umman yayi da kan sa ƙasa ya zo har gaban ta ya tsugunna ya gaida ta amsa
mai tayi tana tambayar sa jikin sa sai ya amsa da Alhamdulillah daga haka ya tashi ya ma Umman sai
anjima yana kallon Bilkisu dan so yake su yi magana amma ko inda yake bata kalla ba hasalima juyar da
kan ta tayi zuwa wani gefen bai da zaɓi haka ya fita ya wuce.
Duk motsin su a kan idon Hajiya Zeenat yi tayi kamar bata wurin yana fita Bilkisu ta ja wani tsaki mai
ƙarfi kafin ta bar wurin rai ɓace ita dai Hajiya Zeenat abin dariya ya bata dan haka ta dara har da tafe
hannu da wani zai zauna ya bata labarin wannan drama da ake yi mata a gida ƙaryatawa zata yi ta ce ba
gaskiya bane sai dai gashi nan tana gani da idanun ta lallai Bilkisu ta ɗauko da zafi sai dai kamar yadda
suka yanke hukuncin ne akan shawarar zuba masu ido su ga iya gudun ruwan su..
A nan ɗakin ta maganganu ta shiga yi ita kaɗai.
"Bilkisu Zaid ya gama raina ki har ya rinƙa yi maki maganar wata a gaban idon ki duk dan ya raina ki ne
kuma saboda ya gano kina son sa da yawa shi yasa you just have to control yourself ki daure ki cije ki
daina nuna mai damuwar ki a sarari because he will only break you down remember what aunty Zee
told you akan yawan kishin ki she told you that zai janyo maki raini and you see Zaid ya ɗauko hanyar
raina ki Bilkisu do something reasonable try to maintain your formal image try...try...you can just keep
on calming and controlling yourself"furzar da iska tayi daga bakin ta nan take hallayar ta na ainihin Dr
Bilkisu Muhammad Sulaiman AKA baby doctor ya yi resuming back and then she thought of leaving her
old fashioned life and about Zaid zata cigaba da jiran ranar da zai dawo hayyacin sa yayi realising cewa
shima yana son ta she knows that she lost something but definitely ta san wataran Zaid zai gane
muhimmancin ta she just have to let him be for now..
Throughout ranar nan har zuwa dare haka tayi su babu jin daɗi but abu ɗaya take tunowa ta ji sanyi a
ran ta wannan abin kuwa shine ita ɗin matar sa ce ko babu so a tsakanin su aure ya haɗa su and she
promise not to intrude into his affairs har sai ya dawo hayyacin sa..
Da tunanin sa ta kwanta har bacci ya ɗauke ta bata daina tunanin sa ba she misses him she missed
everything about him,kewar sa ne da kaɗaici suka dame ta sai dai ta rantse ba zata kuma zubar da
hawayen ta akan Zaid ba..
**********
Da ya bar gidan su Bilkisu gida ya koma dan fasa fitar yayi ya nufi chan bayan gidan ya zauna a poolside
yana tunani kala kala ga Bilkisu ga Asma'u ya rasa da wanne zai ji ya san Bilkisu matar sa ce and he feels
bad a lokuta da dama especially in suna faɗar nan a baya suna zama peacefully but tun ranar nan da abu
ya shiga tsakanin su ta fara ƙin sa har ya kai tana furta mai kalamai marasa daɗin ji in har ta iya ce mai ta
tsane sa abin da ya mata ya ɓata mata rai ba kaɗan ba dan ta nuna ƙarara and he don't blame her..
A nan ya shiga tuna lokacin da ta rinƙa dasa mai naganganu ta rinƙa nanata mai kalmar hate baya son
tunawa,sam bai san me ya shige sa ba da ya kasa daina kiran sunan Asma'u a gaban Bilkisu ba ko dan
yana tunanin ta ne..
Juyawa yayi saman bed couch dake pool side ɗin yana mai cigaba da tunanin sa as a responsible person
dole ya kare haƙƙin mutanin da ke kusa da shi and Asma'u has once helped him she saved him from that
incidence bai kamata ya saka mata da haka ba bata cancanci haka ba.
Tunowa yayi da ranar da abin ya faru ita ce mutum na ƙarshe da ya gani ya kuma ji tana bashi ƙwarin
gwiwar ya tashi ya yaƙi Mudan and he knows in ba ita ba wa ya taimake su suka bar dajin nan shi ya sa
yake ta son komawa ya san halin da take ciki but yana ji kamar in ya tafi zai ɓatawa Bilkisu rai she might
not be happy with him but dole yayi striking balance between his wife and Asma'u..
Juye juye ya rinƙa yi har azahar tayi sannan ya tashi yayi hanyar masallaci bai dawo gidan ba sai da aka
idar da la'asar yana dawowa ya nufi hanyar ɗakin Ammin sa dan yi mata sallama saboda ya yanke
hukuncin komawa chan gidan because the more he sees Bilkisu's house the more he feels guilty and
baya son hakan kuma yayi tunanin in ya tafi chan maybe Ammin sa ta canza ta dawo masa a yadda ya
san ta because waɗannan attitude da take masa baya jin daɗin su..
Da shigar sa ta nufo hanyar fita dan tana sauri zasu tafi wurin meeting ɗin da zasu yi sai ya ga kamar ma
she get irritated easily by merely seeing him close to her dan haka ya tun kafin ta ce mai wani abin ya
riga ta da
"Ammi please wait...i am here to tell you that zan koma chan gidan"kallon sa tayi zuciyar ta kuwa fal
farinciki ne dan tayi zaton yiwa kan su faɗa suka yi suka yanke shawarar komawa gidan su sai ta ce mai
"Alright...wish you luck baby"babu damuwa akan fuskar ta yayin da take mai maganar sai ya ji guiltiness
ya kama sa why is his Ammi behaving like this kamar bata damu da shi ba..
Tare suka fito ya ce da ita
"Ina zaki tafi Ammi sai in kai ki"murmushi tayi kafin ta ce.
"Don't take the trouble Zaid tafi kawai Allah ya tsare"tana gama faɗar haka ta wuce sai ya tsaya saman
bene na ukun ƙarshe yana wondering halayyar mahaifiyar sa da take nuna mai a kwanakin nan..
Yana saukowa zuwa benen ƙarshen ya hangi Afzal dama tun jiya rabon sa da ita sai yayi saurin kiran sa
"Afzal"tsaya yayi ya juyo saibya ga yayan sa ne dan haka ya dakata yana jiran sa
Ƙarasawa yayi zuwa inda Afzal ɗin yake ya tsaya yana kallon sa kafin ya ce
"Afzal you are also avoiding me huh"?da surprise face Afzal ya ce
"Yaya ni ma isa ma..good afternoon ya jikin naka"?girgiza kai yayi ya ce.
"Jiki da sauƙi"daga haka suka ji muryar Ammi tana kiran Afzal ɗin akan ya zo su tafi.
Juyowa yayi ya kalli yayan nasa yana mai ce da shi
"Yaya bara na tafi in na dawo zan shigo"!!..
Tsayawa yayi kamar an dasa sa a nan ɗin yana mamakin Afzal ɗin
"Are these people for real?na ce da Ammi zan kai ta inda zata tafi amma ta ce a'a but she went ahead
and asked Afzal to take her is she angry or mad at him"?kan sa yayi wa wannan tambayar sai dai bai da
amsar tambayar.
Fita yayi shima ya nufi motar sa yayi ya ƙunna yayi starting kamar ba zai tayar da motar ba ya so su
gana da Abban sa but abin ya ci tura dan yayi kiran har ya gaji bai ɗaga wayar ba dan haka yayi tafiyar sa
ko da ya fito sai da ya kalli gidan su Bilkisu yana jin wani abu na mai yawo amma sai ya share ya ja motar
ya tafi ya san a hankali zasu fahimci juna..
*********
Cikin sauri ta fito tana faman masifa kamar an mata laifi alhalin ba haka bane tsabar masifa ce irin tata
"Kin san Allah zeeya,in baki gyara wannan kuskuren ba har na dawo anjima zaki fahimce ni"tana gama
faɗa tayi gaba ta shige motar ta ta tayar bata tsaya ko ina ba sai guest house ɗin Dr Maher inda a nan ne
suka tsara yin meeting ɗin saboda sirri...
Shiga tayi tana gyara zaman gyalen dake kan ta dan tayi latti kuma wannan yarinyar ce da ta rinƙa
balbalewa ta saka ta yin latti..
Da shigan ta inda suke ta fara basu haƙuri
"Am so sorry am late wallahi wanna zeeya girl ɗin ce ta saka ni yin latti"ta faɗi maganar tana mai
zaunawa idanun ta kan Bilal da bai mai kai gida ba dan da kayan aikin sa a jiki ya zo wurin..
Bayan opening prayers da suka yi Dr Maher yayi introducing main abin da ya tara su a wurin kamar dai
yadda ya sanar masu cikin wasiƙar da ya turo masu.
Meeting ne mai zurfi suka yi kowa ya faɗi ra'ayin sa ciki har da current update da ya faru daga safe
zuwa bayan la'asar ɗin yau duk an bayyana har tafiyar Zaid gidan su Bilkisun duk an sanar da komawar sa
chan gidan sa dake Apo Hills duka an bayyana a ƙarshe dai an yi drawing conclusion akan duk inda suka
juya a ni su a hakan in sun shirya a ƙarshe sai a sanar da su abin da ya faru har aka rabu da su dan
maganar aure ba wasa bane.
A wannan meeting ɗin ne kuma aka yanke watan bikin Bahajjatu da apple ɗin ta abin a bazata ya zo
masu su biyun dan ta dai san bikin yayan ta Afzal ne kaɗai a ranar amma sai gashi yau tana jin wai har da
nata bikin that same day ne how comes.
Iyayen zamani babu ruwan su da wata kunya congratulatory pleasantries suka rinƙa exchanging da
ƴaƴan su har gori suka shiga yi ma Lukman akan yana son zama gwawro ga ƙanin sa nan zai angwance in
the next 3 months amma shi ko budurwar bai da shi dariya ma yayi ya tasho yana mai ce masu shi ya tafi
yana da appointment da wani buɗar bakin Hajiya Zeenat sai cewa tayi
"Zaka ma faɗi gaskiya ne dan kwanan nan ban cika ganewa yawar fitar ka ba"ko a jikin ta tayi maganar
sai ya juyo da mamaki ya ce.
"Umma please"dariya suka mai ganin cinna mai da Hajiya Zeenat tayi ya cinnu har ma yayi responding
ma tease ɗin ta..
Ƙarasa meeting ɗin suka yi aka yi addu'a sannan kowa ya kama gaban sa amma su kam basu ga na
tafiya ba tsayawa suka yi a baya har sai da iyayen nasu suka tafi su kuma suka tsaya a wajen guest house
ɗin suka dasa hira mantawa suka yi da gajiyar da suka kwaso daga wun aiki sai da suka soye son ran su
sannan suka shiga motocin su suka hau kan titi tare tana gaba yana baya da suka iso gida kuwa sai da
suka yiwa juna horn suka yi bue bye sannan kowa ya shige nasa gidan..
*******
_8:50am_
Tsaf cikin shigar aiki ta fito fuskar ta sake kamar bata da damuwa duk ta ɓoye danuwar ta,ɗakin
Umman ta ta nufa dan yi mata sai ta dawo.
Bata ɗakin lokacin da ta shiga sai ta sauko ƙasa ta same su saman dinning suna yin breakfast girgiza kai
tayi wato kora da hali ake mata a gidan su ta salon cin abinci ba tare da an sanar da ita ba..
Ƙarasowa tayi kusa da dinning ɗin fuskar ta sake ta ce
"Ina kwanan ku"sau suka kakle ta duka da wani yanayi Dr Muhammad kaɗai ya iya amsawa dan sauran
were shock sun yi tunanin tun jiya ta tafi gidan mijin ta ne da dare dan basu ji motsin ta ba ashe tana
nan.
Juyar da kanta tayi zuwa ga Bilal da murmushin ta ta ce
"Apple ba gaisuwa ne yau ko baka san ni bane"haɗiye abincin da ke bakin sa yayi ya shiga girgiza mata
kai kafin ya ce
"Goodmorning apple your night"?murmushi ta mai ta ce
"Ban amsawa sai da na roƙa"sai ya ji kamar yayi backing out cikin wannan plan nasu dan shi baya iya
ganin ta cikin damuwa Umman su na kallon su ta san ƙanƙanin abin da Bilal zai yi ne ya ce zai yi backing
off dan haka tayi saurin cewa
"Join us"sai ta girgiza kai tana mai faɗin
"No Umma am late for work sai na dawo"daga haka ta masu sai anjima ta fita tana mai jin ba daɗi a ran
ta duk family nata sun juya mata baya duk saboda abin da tayi kamar laifin ta ne..
Motar da ta sa a wanke mata ne ta shiga ta tayar ta fita bata tsaya a ko ina ba sai asibitin nan da ta fi so
wato Skyline,sliding car glass ɗin tayi ƙasa tana kallon structure ɗin asibitin for a while sannan ta fito ta
ɗau jakar ta ta rufe motar ta shiga takawa a hankali ana gaishe ta fuska sake take amsawa har ta isa
zuwa offishin ta ta shiga.
Zaman ta babu jimawa aka shigo sanar da ita akan surgery da za'a yi dan dama wasu doctor ms ɗin zasu
yi but da aka ga ta iso sai aka ce ita ta zama surgeon ɗin sauran su yi assisting nata sai ta yi murmushi
wato haka zasu yi welcoming nata a asibitin da zuwan ta har zata fara yin aiki..
Sallamar mai saƙon tayi akan sai ta zo ajiye mata file na patient ɗin aka yi ta ɗauka ta buɗe tana karanta
cause of surgery ɗin da ta gama sai ta tashi ta shiga daga ciki ta canzo zuwa scrub na theater dan saura
mintuna talatin a shiga theater ɗin babu wani time sosai.
Kashe wayar ta tayi ta ɗau face mask ɗin ta ta saka tun daga office ɗin ta fito ta shiga theater room ɗin
tayi zaman ta saman wani stool tana kallon time,har kusan 15minutes sannan ta ga shigowar wasu
doctors biyu wanda ɗayan ya kasance Dr Aslam ne ɗayan kuma Dr Josh Jeremiah ne kenan su zasu yi
assisting nata.
Basu ma lura da ita ba da shigar su ɗakin canza kaya suka nufa suka saka scrubs ɗin su suka saka mask
da elbow gloves riƙe a hannun su suka fito suna hira kaɗan kaɗan.
Zama suka yi suna jiran zuwar sauran theater team ɗin.juyawar da zai yi ya hange ta zaune sai yayi
blinking idon sa ai kuwa ya ga ita ɗin ce sai ya tashi tsaye ya cite face mask ɗin sa fuskar sa tab cike da
annashuwa ya nufo ta yana kiran sunan ta
"Baby...baby ke ce"?kallon sama zuwa ƙasa ta mai kafin ta juyar da kan ta gefe dan bata son yana kiran
ta ko kiran sunan ta shi kuwa kamar banza haka ya rinƙa jin daɗi har ya janyo stool ɗin sa kusa da ita
yana tambayar ta
"Baby ya kike ya jikin ki yaushe kika dawo ban sani ba"!!ɗan tsaki tayi ta tashi da nufin barin wurin sai
yayi saurin ce mata
"No am so sorry zauna ni bari in matsa"da haka ya ja kujerar sa baya amma idanun sa na nan saman
fuskar ta bai kuma daddara ba ya ƙara tambayar ta
"Baby yaushe kika dawo ne wai na so zuwa duba ki but i was told that baki dawo ba hope kin ji sauƙi
baby"??kalmar ƙarshen da yayi a kunnen Zaid yayi sa da shigowar sa kenan dan yin assisting a surgery da
aka kirawo sa yi just few minutes ago shine ya haɗu da wannan mummunar kalma daga bakin Dr Aslma
rai a ɗan ɓace ya kalle sa ya ce
"Excuse me"juyowa suka yi baki ɗayan su suna mamakin ganin sa ita bata san da zuwan sa ba tayi
tsammanin ɗaya asibitin zai tafi shi yasa ta zo nan sai gashi yau a nan ɗin yake but how?shi kuwa Dr
Aslam da ya ga wanda ya mai magana sai ya ji wani ƙulun baƙin ciki wai shi Zaid ɗin nan kullum ne sai ya
shige mai gaba a al'amuran sa ne?tsaki yayi ciki ciki zai yi magana Zaid ɗin ya riga sa
"Kar fah ka manta...."sai ya zo gab kusa da shi yayi ƙasa da muryar sa ya kai bakin sa saitin kunnen sa
cikin gayya ya ce.
"She is now mine dan haka sunan babyn nan ba da kai ya dace ba da ni ya dace"yana gama faɗin haka ya
ɗaga kan sa ai kuwa Dr Aslam ya shaƙa dan haka yayi wurgi da hand glove ɗin yayi waje cikin takaici da
jin haushi..
Shi kuma Zaid yayi shigewar sa ɗakin saka scrub ya shirya tsaf ya fito da zuwan sa aka shigo da patient
ɗin dama ya sab assisting zai yi dan haka ya tsaya a position ɗin assistants ita kuwa dama tun da ya shigo
take kallon sa da gefen ido tana ganin abin da ya ma Aslam tayi hamdala bata san me ya ce da shi ba but
ta san ya fita cikin fushi hakan kuma ya mata daɗi dan ba son surutun sa take ba.,tana tsaye a wurin
surgeons ta miƙo hannu aka bata surgical incision knife ko kallon Zaid ɗin bata yi ba bare a yi gaisuwa
har ayi harmonious chats kan ta tsaye tayi incising skin ɗin ta kuma yin incising fat ta