Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ko"?sai tausayin sa ya kama ta mutumin da kullum a cikin raha da fara'a
yake amma yau guda ya zauna in ban da kuka babu abin da yake yi
"Bilal zata warke zata dawo gare mu kamar ma bata taɓa yin rashin lafiyar ba abin da nake so da kai
shine ka tafi ka yi alwala ka zo ka yi nafila ka yiwa ƴaruwar ka addu'ar samin lafiya dan a halin da take ciki
addu'ar mu kaɗai take buƙata a yanzu ba kukan mu ba dan ba zai yi mata amfani ba humm"?alama ya
mata da kai kafin ya miƙe ya nufi toilet duk bai da kuzari ya yo alwalar ya fito ta shimfiɗa mai sallaya ta
fita a lokacin da ya tayar da iƙamar sallar.
Bata tsaya ko ina ba sai part ɗin Lukman he is used to it already samin shi ta yi yana nafila dan haka ta
ja mai ƙofar ta fita ta nufi sashen su a inda ta tabbatar zata sami privacy ta zauna ta yi dialing digits ɗin
Afzal ringing uku huɗu ya ɗauka da fara'ar sa ya ce
"Assalamu alaikum umma na"kamar ta yi kuka haka ta ji sai ta daure ta amsa mai da
"Wa'alaikumul salam ɗan umma ya kuke ya canada"?
"Umma lafiya ƙalau da fatan dai an dawo gida ko"? Yayi tambayar da teasing tune sai ta ce
"Afzal ka mai da mu kakannin ku"yayi dariya ya ce
"Toh ummq in banu yi da ku ba wa zamu yi da"?
Sai ta ce
"Babu Afzal yanzu dai kana ina"? sai ya ɗan yi jim kafin ya bata amsa da
"Umma ina gida but inshaAllah ina son dawowa nan da sati guda saboda ina ji a jiki na kamar Ammi is
missing me and we have not been in touch kusan a week +"..
Jin haka sai jikin ta yayi sanyi dama tsakanin ɗa da mahaifi akwai strong bond da ke taimakawa wun
sadarwar su wanda in ɗaya na da damuwa ɗaya zai ji a jikin sa especially uwa dan haka ta natsu ta
warware mai komai sannan ta ɗora mai da dalilin kiran ta..
Iya ƙololuwar tashin hankali ya shiga bayan ya saurari abin da aka sanar da shi sai ya ce da ita
"Umma ina hanya gobe inshaAllah su kuma Allah ya basu lafiya"!
"Amin sai Allah ya kawo ka Afzal Allah ya kare ya tsare"
"Amin umma sai da safe"!!
Zama tayi tana ta tunanin yanayin rayuwa few weeks back sune a London cikin kwanciyar hankali basu
da damuwa ko matsalar komai sai gashi kwatsam suna tsaka da jin daɗin su kaddara ta sauko masu da
wannan tunanin ta daure tayi alwala ta yi sallah bata rintsa ba dan ta san tana buƙatar ibadan a wannam
gaɓa sama da kwanciyar barcin....
A gidan babban yaya Jamil tun bayan tafiyar su kid sis ɗin sa da aminin sa ya dawo gidan hankalin shi ba
a jikin shi ba duk dabarar da matar sa ta mai dan ganin ya sake ya bi su da addu'ar samin lafiya abin ya ci
tura dan kamar ingiza shi take yi akan ya cigaba da saka damuwar a ran sa sai ta zuba mai ido kawai dan
ita kanta tana cikin damuwar da tashin hankali wanda ita kaɗai ta san yadda ta ke ji.
Bai bar ɗakin da ya rufe kan sa a ciki ba sai chan tsakiyar dare ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita kwance
saman sallaya chan kan gadon ga baby Zarah tana barci sai ya ji ta bashi tausayi it takes a loyal,caring
and kind wife to behave and act exactly the way she does dan haka ya lallaɓa ya ɗaga ta dama akwai
nauyin bacci dan haka bata wani farka ba sai ma ta kuma lamo a hannun sa fita yayi da ita ya kai ta ɗakin
sa ya kwantar da ita ya koma ya ɗauko baby Zarah ya kwantar da ita next to her momma shi kuma ya je
yayi ablution ya zo ya tayar da sallah ya ɗau lokaci mai tsayi yana addu'a ma ƙanwar sa da aminin sa
daga kan sallayar ya hauro ya kwanta shima suka saka baby Zarah a tsakiya ya ja masu comforter haɗe
da kashe lamp ɗin ya tofe masu addu'ar bacci...
********************
Kimanin kwanaki uku aka ɗauka ana monitoring patients ɗin germany kafin doctor ɗin ya yanke
hukuncin kai treatment ɗin zuwa second stage wanda a gefen baby doctor dole ta yi undergoing electro
convulsive therapy ba ƙaramin rikita iyayen ta abin yayi ba dan a gida Nigeria sun gama shirin zuwa ciki
har da Afzal da Bilal ƙin barin Bahajjatu aka yi dan in ta tafi tana iya creating scene a wurin nan kuma
ƙasar turawa ne basu cika son hargitsatsen abu ba sai aka bar ta a gida,..
Suna airport labarin ya same su Hajiya Zeenat ji tayi kamar tayi kuka ne ko ta kurma ihu ne ko kuma ta
zauna ne ta rinƙa rasbihi,shawarar ƙarshe shine ta yi tasbihi dan haka ta yi shiru ta shiga yin tasbihi har
jirgin ya tashi dan bata sanar da Hajiya Madina abin da Dr Muhammad ya gaya mata ba sai ta bar wa kan
ta.
Shi kam abin ba'a cewa komai dan dai duk wasu analysis da diagnosis da likitocin suka yi basu sami
gamsashiyar outcome ba sai ma kamar condition ɗin na daɗa yin gaba dan already akwai concealed
blood da yayi bleeding tun daga ainihin main root ɗin sai abin ya zama somehow bulky har kan ya fara
expanding dan jinin na ta regurgitating ba kama hannun yaro abin da ya rikita likitocin kenan suka ga ya
kamata su yi mai gabaɗaya a wuce wurin wato dai brain surgery za'a mai dan haka nemo iyayen shi suka
yi bature bai da ɓoye ɓoye straight to the main point ya masu bayani sannan ya sanar da su life rate
percentage ɗin in aka yi surgery ɗin either 40/50 ko 50/50 ko mutuwa chances ɗin survival is low which
happens to be as low as 30%..
Tashin hankalin da ba'a saka mai rana daga Dr Maher har Dr Muhammad sumumui suka fito in banda
fargaba babu abin da ke ran su babu mai ce ma wani komai gashi likitan ya basu space ɗin yin decision
har tsawon awa ɗaya da rabi kafin a san abin yi a hakan ne suka zauna shiru babu magana har suka cinye
kusan rabin hour a haka a haka suka kuma shafe hour wanda ganin hakan ya sa doctor ɗin yayi
reasoning da su ya ƙara masu awa ashirin da huɗu amma ya gaya masu cewa suna delaying survival ɗin
ɗan su dan dama ita baby doctor a washegari za'a mata ECT ɗin shi kuma a ranar aka so yi mai sai dai
they can't go ahead with the surgery without the permission of the patient relative which have to be his
parents with their bold agreement and acceptance + signature da za'a yi stamping a yi forwarding to the
board dan a saka a babbar file ɗin brain trauma clients da zasu yi undergoing brain surgery...
Dan haka samin wannan damar suka koma lodge ɗin su gabaɗaya jikin su a sanyaye suke babu jimawa
suka ji kiran su Hajiya Madina akan sun iso tare suka tafi ɗauko su a cab suka dawo lodge ɗin inda aka
masu booking ɗayan ɗakin sai suka koma zaman su na ma'aurata wato kowa ya tare da mijin sa a two
rooms ɗin,su kuma Bilal da Afzal next room ɗin suka zauna su biyu.
Ordern abinci aka masu but kasa ci suka yi duk sun damu su ga ƴaƴan nasu sai dai a cikin situation ɗin
da ake ciki ba su fatan matayen na su su ga tashin hankalin da yaean ke ciki da ƙyar da siɗin goshi suka
yarda washegari zasu tafi asibitin amma fah babu kwanciyar hankali a tattare da su kowa na tsoron da
fargabar abin da zai gani a goben...
_2:50am_
Daidai lokacin da Dr Maher da Dr Muhammad suka fito daga ɗakunan su kenan dan samin mafitar abin
da likitan ya sanar da su ƙarfin hali kawai suke yi ba dan sun shirya ba dan haka bayan doguwar nazari da
hangen nesan da suka yi sun yi arriving a kan zasu yi signing ɗin a yi surgery ɗin su kuma su bisu da
addu'a dan matuƙar babu addu'ar toh ko ma me za'a yi ba lallai bane su yi succeeding a surgery ɗin ba
da haka suka koma suka cigaba da tunanin rayuwa...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
As early as 7am duk sun gama shirin zuwa asibitin dan haka cab ne ya sauke su suka ranƙaya zuwa ciki
abu na farko da suka yi shine samin doctor ɗin suka amshi form ɗin kiran matayen nasu suka yi suka
nuna masu form ɗin kasa ƙarasa karantawa suka yi sai kuka dan haka su mazan ne suka yi namijin
ƙoƙarin saka hannu a papern aka yi submitting zaman jiran likitan suka yi ƙarshe dai ƴaƴan ne suka koma
rarrashin iyayen su har zuwa lokacin da doctors ɗin suka iso aka masu bayani babu ɓata lokaci aka fara
shirin yin surgery ɗin sai kuka Hajiya Zeenat da aminiyar ta ke yi basu tabbatar da cewa situation ɗin
yayi worsening ba sai da aka fito da shi kamar gawa dan bambancin sa da gawa shine shi yana breathing
in-out kaɗan kaɗan apart from that bai da maraba da gawar.
Basu tsaya ɓata time ba aka shigar da shi iyayen na kuka kamar me daga nan aka shigar da baby doctor
ɗaya ɗakin ECT ɗin wanda yake ɗauke da transparent doors and windows ta yadda duk abin da ake yi a
ciki ana iya gani daga waje itama haka aka wuce da ita kamar marar rai sai suka mai da duban su gare ta
har aka ƙarasa da ita ɗakin setting komai aka yi aka yi testing electrodes ɗin suna tsaye a wurin suka ga
an fara dadanna machine ɗin daga haka suka fara witnessing babbar tashin hankalin da basu taɓa gani
ba a rayuwar su.
Bayan jona mata electrodes ɗin aka danna sai ya fara charging yana bada electical spark da ke shiga
directly brain structure ɗin ta suke charging domin bada response ma incoming electrical transmission
daga electrode ɗin hakannis equal to her bodily movement first spark ɗin da ya shige ta kawai sai ta
shiga jijjiga kamar epileptic patient jijjigan yayi rhyming da saukar hawayen gabaɗayan su da ke kallon
procedure ɗin a karo na biyu kuwa hannu Hajiya Zeenat ta saka a baki ta fashe da wani irin kukan ban
tausayi sai Hajiya Madina ce ta rungume ta itama tana kukan Bilal kam kasa cigaba da kallon yayi ya
matsa chan nesa da ɗakin ya shiga risgar kuka mai ƙarfi babu ƙaƙƙautawa ..
Chan ana fama da surgery ɗin Zaid Maher nan ana faman stabilizing baby doctor,a karo na shida da aka
ƙara spead ɗin electrode ɗin ne Hajiya Zeenat ta fasa wani ihu haɗe da zamewa ƙasa numfashin ta ya
ɗauke cak kanta aka yo ana faman jijjiga ta wannan tashin hankalin koh a mafarkin su basu taɓa
encountering da shi ba for crying out loud when will all these be over and done with Zaid is there
battling with his life a surgery room mutumin da shi ke yi wa wasu yau shi ake yiwa,baby doctor na ciki
ba'a san yadda hali zai yi ba anf now Hajiya Zeenat ruɗewa Dr Muhammad yayi sai da aka fitar da shi
daga arena ɗin dan a samu a farkar da Hajiya Zeenat..................
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*11*
Tun da aka fara waɗannan matsalolin na su Dr Zaid da baby doctor ko kusa Dr Aslam bai da labari bai
sani ba kuma bavu wanda ya sanar da shi dan ba ta kan shi ake ba kuma dama ba wayar kirki suke yi da
ita baby doctor ɗin ba ko da kuwa tana daidai gaɓar da akwai service yayi nasarar kiran ta toh ba ɗaga
kiran take yi ba sai dai ta ƙyale dan mugu mugun haushin sa take ji haka kawai ta tsani ganin lambar sa
da sunan sa in yana kira abin suƙin kuma shine uban gayyar ma ya daina kiran sunan Dr Aslam ɗin in
suna tare bata san dalili ba...
Wata alhamis ya shirya na musamman ya tafi gidan su baby doctor dan sanin ko ana jin labarin su dan
fah shi ya ƙudiri aniyar cewa da zarar sun dawo daga outreach ɗin zai mata magana a turo kawai a yi a
wuce wurin dan shi babu ranar Allah ta'alah da zai waye bai ji son babyn ya daɗu a ran shi ba dan gaskiya
bai taɓa soyayya ba bai san ya ake yin ta shi yasa da ya fara da baby doctor ya ke jin in bai mallake ta ba
toh lallai akwai matsala duk rashin bashi muhimmanci da bata yi bai dame shi ba hasalima gani yake yi
duk cikin so ne dan bata da baƙi a wurin sa komai tayi daidai ne bat laifi a cewar sa ma in suka yi auren
zasu saba ne kaɗan kaɗan...
On reaching there ya riski labarin ai ƙalau suke kuma ba wani matsala ko damuwa kawai rashin samin
lokaci ne hakan sai ya haddasa masa tunane tunane marasa kan gado da fasali sai yake ganin yanzu
shikenan tana chan tare da Dr Zaid abokin hamayyar sa suna chan tana faman yi mai murmushi ko ma
heart killer laughter ɗin ta sai ya ji wani baƙin ciki da ɓacimn rai duk sun ziyarce shime yasa ma tun fari
bai amince zai bi su ba ai da ya ce shima zai tafi dan he is sure that Bilkisu is not well secured with Dr
Zaid hakan ne ya sa ya yanke shawarar da dawowar su zai saka mahaifin shi a gaba a yi mai yiwuwa dan
yana ganin rayuwar turai da ya ke kan turbar yi ba zai kawo mai hanya mai ɓillewa ba domin kuwa
cutuwa yake yi dan shi jiran ta yake yi ta fara son sa amma sai abin ke nema ya fi ƙarfin tunanin sa dan
instead ta faɗa tricks ɗin sa sai ya ga kamar ƙara bata chances yayi na baje kolin soyayya da Dr Zaid
which he doesn't welcome it..
Duk matsalolin da ya faru ɗin nan kama daga incidence ɗin da ya faru a koma har dawowar su gida na
tsawon 2 weeks ɗin nan har tafiyar su germany bai da labari dan kafin nan mahaifin sa ya tura sa zuwa
ƙasar Oman domin yi mai wani babbar assignment wanda hakan zai ɗauke shi sama da wata guda har
ma da ɗoriyar sati biyu,bai so ba but ya tafi da zumar in ya dawo zai sanar da mahaifin sa komai dan shi
ya matsu bai mallaki Bilkisu ba.....
°°°°°°°°°°°°°°°°°
A nan gida kuwa bayan tafiyar su Dr Maher da Dr Muhammad Hajiya Zeenat da aminiyar ta Hajiya
Madina sun ci kukan su sun ƙoshi ƴaƴan su duk ba su cikin sukuni aka rasa wa zai tsawatar wa wani dan
babu ranar gogewar wannan ɓakin babi da ya buɗo masu har sai ranar da Allah yayi sauƙi zai ziyarce su a
zuriar,
Misalin 7pm Hajiya Zeenat ta fito cikin shigar doguwar rigar abaya silver mix da mayafin ta ƙarama ta
yafa dan su basu yarda da hadisin bononon mutani ba na cewa dan ka hayayyafa ka yi jikoki shikenan ka
tsufa ba su dan gudun kalmar tsufar ma ya sa auke hole rayuwar su su je chan ƙasar su je chan ƙasar dan
fah basu yarda sun tsufar ba in ya kama ma wani tafiyar har da surikar Hajiya Zeenat ake yin shi tun kafin
ta sami ciki sai su ce ai ciki baya hana jin daɗin rayuwa toh ko da ta haihun ma zarah ta kai 8months tare
ake tafiyar da ita da baban ta in suka tafi a miƙa ta hanun nanny su kuma su hole rayuwar su acewar
Hajiya Zeenat idan har zee na ma jamil waɗannan abubuwa toh tabbas babu wata macen da zai kalla ta
burge shi dan matsalar matan arewa ne na wai dan ka yi aure an gama amarci an sami ƙaruwa shikenan
sai mace ta mai da kanta babbar ƙarfi da gadara toh ita bata amince da wannan haɗubar ba ta fumi
yarda da rayuwar jin daɗi dan da shi ta sabarwa prof babu inda ta rage shi hakan yasa ta rinƙa janyo
surikar tata a jiki tana koya mata techniques ɗin har dai itama ta hau kan karatun dan zee ba baya ba
itama dan kuwa bata son sunan kishiya ganin hakan ya sa Hajiya Zeenat daɗa dulmiya ta tsundum cikin
rafin ƙwato ƴancin ta a wun mijin ta ta yadda babu ma inda zai juyi ya ji un ba zee ba toh kowace mace
mujiya ce agare sa ta yi nasarar yin hakan dan a halin da ake ciki kam bayan kasancewar sa soldier baya
d lokacin kan sa sosai toh mace ma in ba matar sa ba bashi da tabbacin cewa akwai wacce zai iya kallo ya
kira da matar sa....
"Bilal zo ka raka ni gidan Ammin ku"cewar Hajiya Zeenat da ta ke ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.miƙewa
yayi daga kan sofa da yake kwance kamar marar lafiya ya ce
"Toh mu je umma"daga haka suka fito daga gidan since their houses is adjacent to each other sai basu
wani yi doguwar tafiya ba suka iso gidan su Hajiya Madina.ko da suka shigan ba su ci karo da kowa ba a
tsakar gidan saboda yanayin rayuwar da ta juyawa jama'ar gidan straight babu dogon juye juye suka
shiga main apartment ɗin Hajiya Madina inda a nan ma bata sauya zani ba dan babu kowa a parlorn ce
mai tayi ya jira ta ita kuma ta shiga cikin ɗakin Hajiya Madina da ke chan sama.
Sallama tayi ta ji shiru ta kuma yi ta ji shiru sai ta tura ƙofar ta shiga bata gan ta ba ta kuma doka
sallama still ba response sai ta ɗan jiraye ta na wasu lokutan bata ji motsin ta ba hakan ya sa ta nufi
sashen ban ɗakin ta ɗan tura kaɗan aiko sai tayi arba da Hajiya Madina kwance ƙasar tiles ɗin banɗakin
Kamar dai a sume da sauri ta ƙarasa ciki ta shiga kiran sunan ta tana jijjiga ta
"Madina....Madina ki tashi me kija yiwa kan ki,Madina ya zaki yiwa ƴaƴan mu haka in baki da ƙarfin yi
masu addu'ar samin lafiya wa zai masu Madina ki tashi dan girman Allah"..
Abin duniya duk ya ishe ta ga damuwar ƴaƴan su ga Hajiya Madina da