Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
Bilkisu ta ce
"Lalalalaaa,,Baha kin gama raina ni,,wato ni ba yayar ki bace right??ohh na gane,toh bara in gayawa
yayan naki maybe shi zai raba gardamar"ta faɗa kamar da gaske zata yi hakan.
Da sauri Baha ta ce
"Kee Beelove kar ki haɗa ni faɗa da yaya na na janye furuci na"sai suka saka dariya baki ɗayan su sai
Bilkisu ta chanza murya ta koma serious
"Amma Baha kin san baki da kirki?tun yaushe rabon da ki kira ni ko message ba kya turo min haka
rayuwa take?ashe dama akwai ranar da zata zo da har zaki iya kwana ki tashi ba tare da kin nemi sanin
lafiya ta ba?tun fah baki yi auren ba kenan amma kina distancing kanki da ni"?sai Bahan ta yi shiru dan
ta san bata kyauta ba she is her only friend wacce take iya sharing damuwar ta da but sai gashi wai
kusan sati biyu da ɗoriya ta kasa neman ta but ita so tayi ta bar su su mori rayuwar auren su dan hakan
ne zai sa su sami fahimtar juna sosai ita da yayan ta Zaid saboda kaf iyayen su sun hana su kiran su sun
ce a bar su su sake dan ta nan zasu fi yin kusa da juna shi yasa bata kira ta ba.
"Am sorry Beelove wallahi ba haka bane"sai ta mata bayanin dalilin ta hakan ya ba ma Bilkisu mamaki
wai su gani suke kamar zaman masoya suke yi kenan hmm
"Toh amma har da haka Baha kin san a yanzu na fi buƙatar ki dan ina neman shawarwari daga wun
friend but you abandoned me"!!sai tausayin Bilkisun ya kama Baha but she apologized and promised
never to let it happened again.
Haka suka taɓa hirar su har Baha ke tseguntawa Bilkisu saka bikin yayan ta da aka yi wato Afzal ta ce
Ammi ta rantse ta ce ko ya fito da mata ko ta mai auren dole shi yasa ya kawo ƙanwar Zainab matar
babban yayan su Bilkisu Jamil wanda takurawar Hajiya Madina ne ya sa ya ce ta zaɓo mai matar kawai
ita kuwa ta ce Hajiya Zeenat ta tuntuɓi mata gidan su Zainab ko suna da budurwar yarinya da ba'a mata
miji ba ai kuwa aka samu.
safiya ita ce ke bin matar Jamil kuma yarinyar ba laifi ko ta ko ina ta yi ba mishkila kuma an yi sa'a bata
da wani she is single sai abin ya zo daidai hakan ma ya sa aka saka bikin na su nan da watanni huɗu wai
dan su fahimci juna dan son komawa canada yake kuma Ammi ta kasa ta tsare akan sai da mata zai
koma by then ta san Zaid ya warke sosai ta yadda zai iya ɗaukar responsibilities ɗin asibitocin tare da
taimakon Bilkisun.
Wannan gulma da Baha ta ma Bilkisu ya mata daɗi matuƙa har ta ma manta da wai fushi take da ita.
Har aka gama dube duben da za'a mai bata sani ba sai da suka fito tare da likitan sannan ta cire ear
piece ɗin ta tashi tsaye a ɗan ruɗe tana tambayar sa
"Are you okey....are you alright?da fatan dai baka ji wani pains sosai ba"?duk ta ruɗe sai ya janyo ta
kusa da jikin sa ya ce cikin sassauta murya ƙasa
"Am good...humm!!babu komai am fit"sai a nan ta sauke ajiyar zuciya tana mai kallon gefen doctor
tana mai ce mai
"I hope there is no serious problem doc"?sai ya gyaɗa mata kai da murmushi kwance kan fuskar sa ta
kuma ce mai
"Thank you so much"ya amsa mata sannan ya bata wata white plain paper mai ɗauke da sunayen drugs
da za'a siya mai dan ya dakatar da waɗanda ake ba sa ya ɗora sa a kan wasu ƙwaya uku kacal kuma duka
sau ɗaya ale sha a rana.
Godiya ta musamman ta mai sannan suka bar asibitin bayan ya masu fixing next appointment day after
tomorrow.
Nearby pharmacy suka tsaya suka sayi magungunan,daga nan suka tafi eatery ɗin jiya dole lunch suka ci
kawai at that same privacy part wato wun _*vvip*_ lafiya ƙalau suka ci suka gama wanda daga nan suka
kama hanyar tafiya gida dan doctor ya ce ya kamata ya huta kafin ƙarfe biyar na yamma yayi.
Suna dawowa bayan sun gabatar da sallar zuhur ya zauna a falon ya ɗau remote zai ƙunna tv ta wufce
remote ɗin sai ya ɗago ya kalle ta da mamaki ita kuma ta saka murmushi ta ce
"Just obeying the doctor's orders"!!sai yayi murmushi kawai ya kwanta saman kujerar ya rufe idon sa
kamar mai jin baccin hakan ya sa ta ɗan tsaya ta yi observing nasa ta ga kamar da gaske baccin yake yi
sai ta wuce ciki tana leƙo sa dan wanka take son yi kafin ya farka.
Tana shiga ɗakin ya buɗe idon sa ɗaya ya ga ta wuce sai ya girgiza kan sa yana murmushi ganin tana son
mai da sa kamar wani ɗan ta,fiddo wayar sa yayi ya shiga kallon hotunan su na jiya yana ta kallo bai sami
ba har ta turo ƙofar sai da ta rufe sannan ya ankara a ruɗe yaayar da wayar ta gefen sa ya mayar da idon
sa ya rufe ruf kamar yadda ta bar sa taimakon sa ɗaya bata kama sa ba.
Kamar mai bincike ta gama kallon sa sannan ta matso kusa da shi ta ƙura mai ido sai ta ga baccin yake yi
da gaske dan haka ta koma ɗakin sa ta ɗauko mai blanket ta dawo ta rufe shi sannan tayi shigewar ta
ciki.
Abin dariya amma ba damar yi dan abin shi dariya ya bashi har da lulluɓe sa gani take bacci yayi..,sai ya
yi dariyar sa a cikin sa ya ƙara jan duvet ɗin har fuskar sa ya ɗau wayar sa yana dannawa yana murmushi
shi kaɗai...
_*S,Ibraheem*_
Follow@siyamaibrahim
_*⚜BWA*_
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*24*
*_Bond_*
Wanka take amma ƙwaƙwalwar ta na dawo mata da abin da ya faru tun jiya har kawo yau sai ta shiga yin
murmushi ita kaɗai kamar ana tickling nata in tayi murmushin sai ta kalli kanta a mirror tana mamakin
irin abubuwan da ke gabata tsakanin ta da Dr Zaid bata taɓa kawowa ba ko a mafarkin ta bata tunanin in
aka ce ita da Zaid zasu zauna inuwa ɗaya zata gasgata sai gashi daga ita har shi ɗin babu wamda ya yi
jayayya da ra'ayin iyayen sa haka babu wanda ya ja da hukuncin ubangijin sa.
Wankan da ya kamata ta yi sa cikin mintuna ƙalilan sai gashi ta kai mintuna goma sha bata kammala ba
sai shiririta da shirme take faman yi daga ta yi tunanin lokacin da yake kallonta sai tayi tunanin lokacin
da yake kai mata seducing touches in tayi wannan tunanin har wani lumshe idanun ta take.
Ko da ta kammala wankan zama tayi a kan tub na wankan tana tunani wanda wannan tunanin ya
zurfafa mata duk ilahurin hankalin ta,tunani take akan abu ɗaya wanda take ganin in har ta bari ta
amince da hakan toh abu biyu ne ko dai tayi gamo na alkhairi mai matuƙar garɗi da burgewa ko kuma ta
tafka babbar kuskuren da ba zata iya goge sa ba a cikin kundin shafunan rayuwar ta wanda bata fatan
hakan ya faru da maƙiyin ta bare ita kan ta.
Tambayar kan ta ta shiga yi tana ba ma kanta amsa dan tana son sanin menene mafitar rayuwar a nan
gaba in har tayi accepting defeat daga zuciyar ta dan ita kan ta ta san ta kai mataki,matakin da bata jin
kiran wani mahaluƙi zai iya dakatar da ita dan hanyar da ta ɗauko hanya ce miƙaƙƙiya mai tsananin tsayi
da ita kanta bata san ranar da zata ga ƙarshen ta ba amma tana fata akan tafiyar da ta ke yi bisa hanyar
ya zamo mata tafiya mai alkhairi wanda zai zamo kamar ƙarin fitila ne a rayuwar ta ba mutuwar haskwn
da take tafuyar tare da ba sannan tana fatar tafiyar ya kai ta matakin da zai sada ta da madagora dan in
har ita kaɗai ke tafiyar a wannan shararriyar sharahararriyar hanya toh tabbas ta ɗauko dala babu
gammu..
"Bilkisu kina ji a jikin ki kamar abin da zaki bar zuciyar ki da jigilan yi zai iya ɗaukar nauyin ta?kina ganin
ba zaki cutar da rayuwar ta nan gaba ba in har kika bi shawarar zuciyar ki ba?har ya kai matakin da zaki
gasgata tunanin ki ba tare da kin ƙarasa yin gwajin ki ba?anya ba babbar asara kike shirin tafkawa
rayuwar ki ba kuwa?what if you welcome his love whole hearted and then he ends up breaking and
tearing your heart apart?what if he still have that girl in his heart?what if he remembers her and decide
to throw her away in a garbage bin?tuno wannan abin ne ya saka ta miƙewa a 360 tana zazzaro idanu
waje tsabar masifaffen kishi ta hau cewa
"Tir...tir..tir...Allah ya kiyaye Zaid haɗa hanya da wannan yarinyar maƙiyayr mu,,,i reject this
thought,,haba,inaa...babu abin da zai yi da ita"..posting tayi tana panting tana son calming kanta sai
furzar da iska take yi tana sauke ajiyar zuciya sai numfashi ke faman tsere a tsakankanin kowani second
da take shaƙar iskar dake shiga cikin alveoli nata..
"Bilkisu ki natsu ki bi zuciyar ki,Zaid ya zama naki har abada har abada dan ko babu komai aure ya haɗa
ku wanda kike fatar ta ɗore har abada,ba laifi in ki amshi abin da kike ji game da shi a zuciyar ki da hannu
bibbiyu,,stop the unnecessary hide and seek stop relating your misery to your perfection,no it was
meant to happened baki da laifi kuma dan kin yi kishin sa ba abin kunya bane,mijin ki ne fah,ke zaki bada
ƙofar da har wata zata buɗe ta shigo rayuwar ku,ke ke da maƙullin zuciyar Zaid dan haka in kin rufe kin
adana a keɓaɓɓen wuri babu wacce zata iya zuwa ta ɗauka har ta buɗe kai tsaye ta shige ba tare da
shakka ko fargaba ba"..
Shiru tayi ta dakata tana kallon kanta a madubi sai ta ji kamar akwai wani abin dake taso mata daga ciki
cikin zuciyar ta wanda har yake son fasa tsakankanin ƙirjin ta saurin kai hannun ta wurin tayi ta dafe tana
sauke ajiyar zuciya.
Kusan awa tayi a bathroom tana yanta da warwara,bata fito ba sai da ta gama concluding kuma ta
amince da final decision da ta yankewa kanta..
Bath throb ne a jikin ta a haka ta fito daga bayin tana gyara ɗaurin igiyar rigar hankalin ta yayi nisa so
take ta ɗau wayar ta ta shiga google dan samin gamsashiyar amsar da take nema dan abin kunya ne ta
tambayi Bahajjatu wannan abin is gonna be too childish of her..
Ko da ta shiga falon bata lura da hasken dake fitowa daga cikin blanket da ta rufe Zaid da shi ba kawai
wayar ta ta ɗauka ta yi saurin ƙunna data ta shiga google ta yi typing abin da take nema.
Ba jimawa ya fito mata da amsoshi har da hotuna abin ya bata mamaki.,,tun da ta zauna a kujerar bata
tashi ba sai da ta ji kiran sallar wayar ta na ƙasar madina da tayi setting kasancewar bai da yawan
musulmai sai tsitrarai.
Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana mai kai idanun ta gare sa da zuwa lokacin baccin gaske ya ɗauke
sa sakamakon daɗewar da tayi zaune a wurin tun yana tsimayen ta har bacci ya ɗauke sa.
Share hawayen da ya silalo mata tayi tana kallon sa in complete shock dan bata san abin da ke
ɗawainiya da ita for all these while sunan sa _*Love*_ ba,dama haka abin yaje ko dai ita nata ne ya zo
mata a haka da wahalarwa?sai ta ji duniyar ya mata ba daɗi komai ma bai mata daɗi wannan wace irin
rayuwa ce haka so zai mata tana zaman zaman ta?ya rasa lokacim da zai kama ta sai lokacin da suka fara
samin fahimtar juna lokacin da suka fara fahimtar juna?ta yaya ma so zai mata haka alhalin ya san
wanda yake kaiwa harin sam bai san da zaman sa ba??share hawaye ta kuma yi tana kallon sa sai hakan
bai mata ba har sai da ta tashi ta nufi kujerar ta zauna a hankali tana son hana kukan ta fitowa fili dan
kar ta tashe sa ya farka ya ga tana kuka..
A hankali kamar mai jin tsoro ta shiga yaye mai blanket ɗin idon ta kyar a kan innocent gentile face ɗin
sa da ke nan so calm and good looking.
A hankali ta kai hanun ta dake shaking kan fuskar sa,,hannun ta na kaiwa kan fuskar sa ta lumshe
idanun ta sai ga hawaye na silalo mata dan ba komai take tunani ba illah kanta da take tausayawa dan
Zaid....bata gabar sa ita ta sani taimakon ta ɗaya ne Allah bai bashi izinin tambayar ta Asma'u ba dan ta
san da zarar ya san halin da take ciki shikenan tata ta ƙare sai dai ta haƙura dan ita ta ɗorawa kanta
lalurar da ta san ba zai kawo mata hanya mai ɓillewa ba..
Har bakwai saura tana kallon sa tana hawayen tausayin kanta haka shima tausayi yake bata dan ta san
in har ya gano Asma'u ta taimakawa Mudan har yayi achieving kai su ƙasa toh zai zama so shattered
kuma he will be heart broken ko zai iya ɗaukar wannan abin?Allah ne masani..
Share hawayen tayi a karo marar adadi sannan ta yi calming kanta ta ja iska sannan ta furzar kusan sau
uku tana breathing exercise kafin ta mai wani kallo wanda ke tafe da tsantsar tsananin so mai zafi zafi
dan hucin son na kan huro mata yana huro mata zafin sa wanda ke ratsa jikin ta har ya fara melting mata
jinin jikin ta.
Ita wannan ne kuma ƙaddarar ta a rayuwa ya zata yi da irin zazzafar son sa da ya shige ta ya ɓula ƙowani
gaɓa a jikin ta??jan hanci tayi sannan ta hau kiran sunan sa tana yi tana gyara muryar ta dan ya fara rawa
kuka ke son kwace mata but she didn't allow it..
Sau biyu tayi tapping nasa sannan ya juyo da corny looking face nasa ya sauke kan nata already falon is
spread with light sai hasken ya so tona asirin halin da take ciki but ganin zai gane sai ta sunkuyar da
kanta ƙasa sam ta manta banu kaya a jikin ta sai rigar wanka.
Shiru shiru ta ji bai ce komai ba haka bai yi attempting tashi ko moving ba sai tayi zaton ko baccin ne bai
ishe sa ba ya koma dan haka ta ɗago dan kuma tada shi sai dai abin mamakin shine tangaras ta gan sa a
kwance ya kafe ta da idon sa yana mata kallon ƙurilla sai ta rasa abin faɗa dan haka ta bi inda yake kallon
da ido sai ta ga ƙirjin ta ya kafe da ido ɗan buɗaɗɗen wurin da yayi exposing ƙirjin ta sakamakon rashin
haɗewar rigar wu guda saboda kamar falmarar riga yake haɗawa ake yi a ɗaure toh nan space ɗin yake
kallo kamar his life is laid on it sai dai the most surprising and amazing things is that she didnt react,bata
yi wani silly reaction ko response ba illah maida idon ta kan sa da tayi tana mai cewa
"Lokacin sallah ne yayi ka tashi kar ka makara"a yanayin maganar ta one can see the misery she is in
presently ga alamun karaya daga muryar ta.
Kallon ta ya shiga yi cikun ɗaurewar kai yana mamakin rashin responding ko reacting ma kallon da ya
mata.
Tashi yayi daga kwancen ya ɗan zauna haɗe da haɗa hannayen sa biyu yayi cupping fuskar sa yayi
zugum kafin daga baya kuma ya tashi yana mai ce da ita
"Thanks"ta mai murmushi haɗe da saukar da idon ta ƙasa dan bata son haɗa ido da shi kallon sa kaɗai na
increasing venom da je yawo a jikin ta wanda ya sami kafar shiga ne sakamakon son sa da yayi poising
ɗin ta because his love at this moment have no difference with a poison dan ya shige ta ba a lokacin da
ta shirya ba ba da sanin ta ba ya shige ta so she consider his love as a poisoning element that convert
and react to her chemical electrodes that moves and perform their functions by each passing second
and she have no justification to this love she have for him indeed this is *the love saga....*
Tana kallon sa yayi shigewar sa ita kuma ta zauna a wurin tana tausayawa rayuwar ta ko ya zata
kasance in har ta gama tabbatarwa da ita kaɗai ke shawagi cikin son sa amma ban da shi..
Da yake tana fashin sallah ɗazu da ta shiga wanka ta ga ta fara staining pant ɗin ta sai ta gane monthly
period nata ne ya zo hakan ne ma ya sakata zama ba tare da ta saka kaya ba dan ko ta saka ɓaci zasu yi
kuma wahala take sha ba lallai bane ta iya wanke su ko a gidan Umman ta ke mata wankin in ta fara but
now she is married kuma ba so take Zaid ya san halin da take ciki ba because they are still different basu
zama abu ɗaya ba..
Tashi tayi ta nufi table da landlune ke ajiye,so take tayi making order na dinner ɗin su,har ta kai hannu
ta ɗauka sai ta ga ya leƙo daga shi sai towel da yayi tying around his waist jikin sa jiƙe da ruwa ga kumfa
nan a wasu sassan jikin sa kamar ya sani har ya fara soaping kansa sai ya fito dan bai so su ci abincin
hotel ɗin he wanna give her a special treatment for taking care of him.
"Don't bother calling,a waje zamu ci abincin dare humm"!!ya ida yana mai assuring nata da idanun sa sai
ta ɗan murmusa sannan ta mayar da wayar ta ajiye shi kuma ya koma ciki dan ƙarasa wankan sa..
Zama tayi duk jikin ta ya saki ga matsalar menstrual cramps ga damuwar abin da tayi discovering just a
while ago,shiru tayi ta daɗe a hakan sannan daga bisani ta tashi ta shige nata ɗakin tayi freshening kanta
haɗe da saka kaya ta ɗan yi kwalliya kaɗan ta dawo falon ta zauna tana jiran sa.
Abin na ɗaure mata kai wai dama haka shi _*so*_ yake ko dai tata ne ta zo mata da wannan sigar?
tukunna ma ita kaɗai ke wannan abin da ita kaɗai ke jin wannan abin