Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
haɗe jikin sa wu ɗaya at the same time yana karantar add'uar
tsari da kariya bai farkan ba haka bai daina yin add'uar ba har sai da hotunan mummunar ranar takau
daga baccin sa sannan ya cigaba da yin baccin duk ya gama haɗa zufa gashi ya rufe kan sa da blanket
kuma ba ƙaramin zufa yake yi ba..
Juyawar ta ke da wuya taji ƙarar wayar ta sai ta fara laluɓo wayar har da ta kai hannun ta kan wayar ba
tare da ta duba sunan ba ta ɗauka haɗe da karawa a kunnen ta ta kwanto ta gefen da ta ɗauko wayar
idanun ta rufe da ragowar magagin bacci cikin muryar ta ta ce
"Hellooo"..haka ta ja kalmar wanda ya saka Umma kallon aminiyar ta Hajiya Madina sai suka ɗan yi
murmushi dan dama sai da Ammi ta hana ta kiran ta ce da ita maybe fah basu tashi ba amma Umma ta
ce ita kam tana jin yin waya da su..
Jin ba'a ce komai ba sai ta kuma maimaita kalmar
"Hello"sai a wannan karon ne aka amsa
"Goodmorning Mrs Zaid Maher"muryar da ta ji ne haɗe da sunan da aka kura ta da shi ga kuma
ƙamshin da ta ji su suka haɗu suka saka ta warewa da kyau ta tashi a birkice tana zazzaro idanu waje
cikin rikiɗewa ai a sittin ta ce
"Umma please can i call you back in the next 15minutes"??tayi tambayar gaban ta na faɗi sai Umma ta
ce mata
"Yeah...sure...why not...just..just take your time okey baby bye"wani irin ajiyar zuciya ta sauke idanun
ta na daɗa buɗuwa da kyau kan ta na sara mata kamar ta kwana biyu tana rashin lafiya.
Dafe kanta tayi ta zauna kam gadon tana son tuno abin da ya faru jiya..
Iya abin da take iya tunawa shine jiya sun yi sai da safe ita da Zaid kuma distance dake tsakanin su da
ɗan tazara tana kwance ne shi kuma daga bakin ƙifar ya sallame ta but how come take jin ƙamshin
turaren sa a saman gadon ta gashi nan dai babu alamun mutum ya shigo dan gadon is neat babu wani
canji daga yadda yake..
Ganin zata wahal da kan ta garin nemo amsar da bata san inda zata samo shi ba ya sa ta tashi ta nufi
hanyar bayi dan gyara kanta.
Wanka tayi ta gyara jikin ta sannan ta fito ta buɗe closet na kayan ta duk ta ma rasa abin sakawa sai
kawai ta ɗau wata bum short da one single hand shimi ta saka ko bra bata saka ba da ta gama saka
kayan sai ta ɗauko wata doguwar riga mai hula orange colour blended with red touches ta saka ya kuwa
sauko mata har ƙasa sai ta nemi room slippers ta saka kasancewar babi inda zasu tafi ranar dan next
checkup nasa sai washegari zaman gida zasu yi a yau..
Turare kala kala ta feshe jikin ta da shi sanna ta ɗau wayar ta tayi dialing digits na Umman ta,tana tafe
da wayar a hannun ta har ta iso falon ta nemi wuri ta zauna haɗe da ɗauko remote ta ƙunna tv,tana
ƙunna tv Umma na ɗaga wayar sai ta riga ta yin magana ta hanyar ce mata
"Umma na ina kwana"dariyar manya Hajiya Zeenat tayi kafin ta ce
"Bilkisu kenan shikenan cikin waɗanda zaki manta har da ni a ciki baby?,,ki ce kawai in kama baby Zara
dan ina ganin in kuka yi naku ƴaƴan hana su zuwa wun mu zaku yi tunda gashi tun yanzu kun manta
mu"murmushi tayi kaɗan kafin ta ce
"Umma ni na isa,,wallahi ba haka bane Umma kin ga jiya gabaɗaya ban yi baccin daɗi ba rashin lafiya duk
ya saka ni gaba dama kwanannan kawai managing kai na nake yi dan bana so Zaid ya zama demoralize
saboda ni but am really sick please Umma ki min haƙuri inshaAllah hakan ba zai kuma faruwa ba kin ji"?
tun da ta fara wannan maganar babu gaɓar da ya taɓa Umma sai inda Bilkisu ke faɗin"jiya bata yi baccin
daɗi ba kuma ganaɗaya satin managing kan ta take yi" what does that implies?
Cikin jan wani irin ƙara Umma ta ce
"Baby you pregnant"tari Bilkisu ta shiga yi har tana wani shiɗewa tsabar mamakin abin da Umma ta faɗi
kuma ya zo mata ne kai tsaye daga sama.
Sorry Umman ta shiga yi mata sai Bilkisun ta tari numfashin ta ta hanyar ce mata
"Umma is not what you think,,ban da lafiya ne saboda monthly cycle ɗi na was about coming ne and
jiya da na ce maki ban yi baccin daɗi ba,cramps nake ta experiencing a bacci na shi nake nufi ba abin da
kike tunani bane"sai kuma anmashuwar fuskokin su ya kau Hajiya Zeenat ta kalli Hajiya Madina suka
girgiza kai su duk tunanin su ko sun kusa zama grannies ne especially Ammi da yanzu ta ɗora buri akan
babban ɗan ta Zaid tana bala'in son samin jika daga gare sa time is flying any moment za'a wayi gari
babu su and she can't help her self but say it out to her friend wato Hajiya Zeenat and she made her a
promise that inshaAllah ba zasu bar duniyar ba ba tare da sun ga jikokin su ba waɗannan kalamai kaɗai
ke kwantar mata da hankali..
"Kina nufin har yanzu baki fara jin alamomin masu ciki ba baby"?da mamaki ta ce
"Strange Umma,,why are you asking me such question"??kamar jirar ta Umman take ta ce
"Saboda na matsu in sami jika why are you people delaying it"??ya salam su kam Allah ya albarkace su
da iyaye sai ta ce
"Umma in dai har irin tambayar da zaki na yi min kenan toh i wi stop picking your calls i promise
you"babu alamar wasa a muryar ta sai suka kuma kallon juna suka girgiza kai sai Hajiya Zeenat ta ce
"Fine na daina kuma ba zan sake ba but ina dai fata baby ba planning kuke yi b?dan Allah kar ku bi
hanyar yaran zamanin nan masu cewa sai sun gama enjoying honeymoon kafin suyi conceiving please
kar ku mana haka mu muna buƙatar jikoki as soon as possible"shiru Bilkisun tayi tana sauraron
mahaifiyar tata cikin rashin sanin abin da zata ce da ita dan abin nasu ya fara takura mata 2 days back
Ammi ta yi nata part ɗin and now,,her mom is portraying her own pattern..
"Oh ya Allah Umma,dan Allah ki daina ke da Ammi have to stop all these things you are doing,seriously
kuna takura ni i can't please,,,sai anjima i will call you when the need arises"ɗiff ta kashe wayar ta ajiye
saman kujerar haɗe da kwantar da kanta saman pillow dake bayan kujerar,shiru tayi tana tunani..
She was lost in her thinking har ya fito bata lura ba tana kan tunanin abubuwan da ke faruwa da ita a
ƴan kwanakin nan ga matsananncin son Zaid da ke juya ta ga asassawar iyayen su da wanne zata ji..
Ya kai minti ɗaya tsaye kan ta bata sani ba shi kuma a nasa tunanin gani yake kamar she is still in pains
shi yasa take zaune haka..
Zama yayi a same chair da take zaune ya kai hannu ya taɓa gefen wuyar ta sai ta buɗe idanun ta a ɗan
birkice sai ta ga shine hakan ya janyo mata baƙuwar yanayi tun ma bai tambaye ta ba kenan ina ga in ya
tambayi health ɗin ta.
"Good morning"da ɗan murmushi ta ce
"Morning"sai ya kuma tambayar ta yana mai kawo hannub sa kusa da goshin ta
"How was your night"?imagine Zaid is a good pretender kamar ba ɗakin ya kwana ba sai ta bashi amsa
da
"Alhamdulilah"ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
"Your health"??sai a nan ta haɗa ido da shi dan shima abin da yake so kenan,so yake ya haɗa ido da ita
ko zai sami wani amsa cikin idanun nata dan shi ya rasa gane abin da ke damin lafiyar tunamin sa.
Cikin sanyin murya da ke tattare da tsantsar so da ƙaunar sa ta ce
"Alhamdulilah nagode"sai suka yi shiru suna kallon juna kafin daga bisani ya tambaye ta
"Waya...da wa kike waya..na daɗe a nan baki sani ba"cire idanun ta tayi daga nasa tana gyara zaman
rigar ta sannan ta bashi amsar tambayar sa cikin unexpected response
"Hmmm i see,,me kuma ya sa kake son sanin ko da wa nake magana"?wani irin kallo ya mata mai nuna
tsantsar mamakin sa da irin amsar da ta basa har ma da tambaya a ƙarshe.
Bai so amsa mata ba but wani sashe na zuciyar sa na ingiza sa akan dole ya amsa mata dan haka ya ce
"Babu,kawai gani nayi hankalin ki ya koma kan wayar gabaɗaya"!!ƴar murmushi tayi sannan ta rausayar
da kai gefe kafin ta ce
"Da Umma na yi wayar"sai ya gyaɗa kai yana mai kai hannun sa kan teburin da ke mafi kusa da
ita,landline ya kira ya masu ordern breakfast har ya ajiye sai kuma ya juya ya kalle ta cikin kulawa ya ce
"Sorry ban tambaye ki abin da kike so ba na bayar da ordee,what would you like"??kallon sa tayi kafin
ta miƙe tana tafiya a hankali zuwa ɗakin ta ta ce da shi
"Abin da zaka ci shi zan ci ko ka manta a ƙarƙashin ka nake"??ta juyo ta mai kallon da ya saka jikin sa
sakewa,kasala ce ta sauko mai a bazata ba zato ba tsammani ya ji kawai ita yake son kallo sai dai kafin
yayi wani yunƙuri har tayi shigewar ta ciki.
"Damn it...Zaid common man up man up..."ya furzar da iska mai ɗauke da ɗumi daga bakin sa dan
hucin iskar alama ce ta yamayin da zuciyar sa ke ciki but why all these me ya sa haka me ya kawo haka
he thinks he should visit a doctor seriously..
Da dariya ta ƙarasa shigewar ta ɗakin dan ta san ta ƙunna sa dan dolen sa ma ya ji a jikin sa saboda ta
san yanayin maganar da ta mai sai ya ji wani abin all she need is for him to realise and keep her in his
head kuma ba zata iya yin hakan ita kaɗai ba dole sai da sanin sa da kuma yardar sa..
Kwantawa tayi bisa kan gadon ta tana jin wani sassanyar annashuwa na shigar ta from no where,juyi
tayi tana tuno wasu moments da suka yi tare da shi most especially jiya da ya nuna damuwar sa gare
ta,tunowa tayi da lokacin da ya ruɗe a jiyan yana ta tambayar ta ko me ke damin ta sai ta tsinci kan ta da
yiwa kanta dariya lallai ta shiga sabuwar duniyar da bata san da akwai shi ba a duniyar nan the feelings is
extraordinary abin ya mata nauyi da yawa tana buƙatar mai taya ta riƙon abin da take ji a zuciyar ta..
Tana duniyar tunanin ta ne ta ji an turo ƙofar ɗakin kamar ba'a son turowa hakan ya tabbatar mata da
Zaid ne dan shi kaɗai ke tare da ita a gidan.
Tashi tayi daga kwanciyar riginginen da tayi tana mai kallon sa da murmushin son da take mai shi ko
shagala yayi yana kallon ta yana jin wani abu na fizgar sa sai dai yayi ƙoƙarin controlling kan sa dan yana
ganin kamar yana overreacting da yawa.
Gyaran murya yayi game da riƙe ƙofar ɗakin yana mai sauke mata idanun sa cikin wani salo hakan kuwa
yayi tasiri a kan ta dan kallon yayi affecting nata sosai sai dai itama tayi controlling kanta dan so take ta
gama tabbatarwa ko shima yana jin abin da take ji ko ita kaɗai ke jin abin..
"an kawo mana breakfast zaki yi joining ɗi na ne a parlor ko in kawo maki nan"?cikin salon jan ra'ayin sa
ta ce
"Hmm Zaid kenan..,ai duk inda kake nan nake duk inda ka zaɓar min nan zan zauna"
Ya ilahi,me yarinyar nan ke son yi mai ne haka shin?sam yakan kasa ganewa kan sa in har tana kusa da
shi shi dai ya san abu ɗaya ne tak wanda ya san ko a baccin sa zai iya shaidar sa sai ya sami mai warware
mai..
Kallon kallo suka shiga musayar yi da juna kafin ya ce da ita
"Toh ki zo mu tafi parlor in yaso sai mu kalli theater show"tashi tayi da fara'ar ta ta ce
"Hakan ma yayi"!!ta rigasa fita falon shi kuma yana biye da ita a baya yana saƙe saƙe..
Shi ya ɗauko plates biyu da spoons ya zo ya juye masu abincin cikin different plates ɗin sannan ya
zuzzuba masu chill drink a tumbler,tana bin sa da kallo har ya kammala tana kallon sa bata ce da shi ƙala
ba sai da ya kammala duka ya ɗago ba yabo ba fallasa ya ce
"Bismillah"!!...wani irin kallon kashe jiki ta mai dan ƙanƙance idanun ta tayi tana mai kallon ƴan
boko,shi kuma ya kasa furta komai sai bin ta da ido da yake yi kan sa duk ya ƙulle ya rasa dalilin ta na
nuna mai wannan attitude ɗin.
Bai gama tunanin nasa ba ya ji muryar ta kamar mai jin baccin tana faɗin.
"Bismillah??toh bismillah"ta faɗa cikin halin ko in kula haɗe da ɗaukar spoon da side table knife tana
kallon sa dan kamar statue ya koma a zaunen yana mamakin ta sam bai san ta shahara har haka ba sai
yanzu.
Alama ta mai da ido irin ina jiran ka ɗin nan dan kuwa babu alamar wasa a fuskar ta kenan bata ji daɗin
yadda ya mata tayin abincin ba.
Kallon ta yake kyar dan dai ya fara shiga duhu da ɗabi'un da tayi adopting tana displaying mai.
Saka cokalin yayi cikin plate ya fara ɗibawa zai kai bakin sa sai ya ƙaƙare ya kasa sakawa ya tsaya kallon
ta sakamakon ganin nata cokalin cikin plate ɗin abincin sa hankali kwance ta ɗibo sai ta dakata bata saka
a bakin ta ba ta aika mai da wani kallon kashe jiki sannan cikin taushin murya ta ce
"Bismillah"ai bai san lokacin da ya fara tari repeatedly babu tsagaitawa ba sai ta ɗan nuna alamun
damuwa a kan fuskar ta sannan ta tashi cikin kula ta ɗauko mai ruwan sha dan organic drink ɗin na iya
increasing mai rate na tarin bit water will be more suitable for him.
Bashu ruwan tayi a baki ya ɗan yi sipping sannan ya ɗaga kan sa yana kallon ta,haɗa ido suka yi ta mai
sannu da idon haɗe da gyaɗa mai kai irin it is well ɗin nan sai kawai ya sauke idon sa haɗe da furta
"Nagode"sai ta ce mai
"Ba komai ai aiki na ne"da murmushin ta ta faɗi hakan sannan ta dawo ta zauna ta ɗebi abincin ta kawo
bakin sa haɗe da ce mai
"Haaa"sai ya kalle ta a kasale bai buɗe bakin ba har sai da ta mai alama da kai sannan ya buɗe bakin
yana mai yin bismillah,saka mai cokalin abincin tayi a baki ya karɓa sai ta cire ta kuma ɗebo wani ta ƙara
bashi ya karɓa,a taƙaice dai ita ta ciyar da shi har ya ƙoshi sannan ta ɗau nata plate ɗin ta saka same
spoon da ta bashi abincin da shi ta ɗauka zata tashi dan komawa ɗakin ta cin abincin.
Yana ganin haka kuwa ya kawo hannun sa ya riƙe nata hannun da take da nufin ɗaukar tumbler,dakatar
da ita yayi yana mai cewa
"Zauna mana ina kuma zaki tafi"??sai ta ji gaban ta ya ɗan faɗi dan riƙon da ya kawo mata ya shige ta
ba kaɗan ba.
Haɗa ido suka yi sai ta kawar da nata idon kamar marar gaskiya ta ce
"Dinner zan yi having"!!still yana kallon ta ya ce
"Wayo dai zaki min,kin gama bani na ci sannan ke ki ce guduwa zaki yi ki ci alone dan kar in ga menene"?
dariyar mamakin sa tayi sannan ta ce
"Ban gane ba?abinci zan tafi in ci,,ina son shan magani kai ma ya kamata ka sha night medicine
naka"sarai ya gane so take tayi dodging tambayar da ya mata dan haka shima sai yayi claiming ai bai ma
san inda maganar tata ta dosa ba yayi pretending dan dolen ta ta dawo ta zauna ta ɗau cokalin zata fara
ciyar da kanta sai ya riga ta riƙo cokalin,ta zuba mai idanun ta bata ce komai ba sai ta ga yana ƙoƙarin
fara feeding nata abin ya ɗaure mata kai but bata dai ce komai ba.
Sai da ya ɗibo iya bakin ta sannan ya ce da ita
"Haaa"kamar dai yada ta mai sai abin ya saka ta darawa wato shi ba'a mai bai rama ba..
Share ta yayi dan shi dai duk abin da yake yi ji yake kamar ingiza sa ake yi yayi su dole dan haka baya jin
wani damuwa ko da ta mai dariya in dai zai sami sauƙin damuwar da yake damin sa he is okey..
Buɗe bakin tayi ya saka mata,a ƙalla sai da ta yi rabin plate ɗin nan sannan ta shiga girgiza mai kai
alamun ta ƙoshi sai ya tambaye ta
"Are you sure"?ta kuma girgiza mai kai sai ya miƙo mata drink ta sha haɗe da karɓa daga hannun sa tana
ce mai
"Thank you"ya ɗan murmusa sannan ya tashi ya kwashe kayan dama tana da niyar taya sa kwashen
kayan amma ya ce ta bari ita da ba lafiya sai ta yi zaman ta haɗe da ƙunna plasma ta kamo tashar da ya
kamo ranar da suka kalli theater da dare.
Zama tayi haɗe da crossing ƙafafun ta tana ɗan kaɗa su a hankali ta natsu tana kallon yadda ake feɗe
wata mace ana son cire mata fibroid mayomas,ta zurfafa a kallon har ya fito bata sani ba sai da ya zauna
yana mai faɗin
"Interesting"sai a nam ta kalle sa tana mai yin murmushi haɗe da gyaɗa mai kai,daga haka suka mayar
da hankalin su kan kallon har aka gama sai dai ana gab da ƙarasa ɗinke feɗan suka shiga yiwa kan su
tambayoyi a course of tambayar ne suka shiga arguing da juna har ma da abin ya masu sugar suka koma
yin raffle draw sai da aka kammala show ɗin sannan suka natsu sai suka koma yiwa kan su dariyar
shirmen da suka rinƙa yi,gaskiya ta ji daɗi abin nan dan ko ba komai yana copping da internal response
nasa ta ji daɗi ba kaɗan ba..
*3 hours later*
Bayan sallar azahar ya shirya cikin ƙananan kayan shan iska ya duba ta a ɗakin ta dan yana son su ɗan
zaga hotel ɗin tare since they have no where to go..
Ganin ta yayi kwance babu doguwar rigar sai ƙananan kayan da ta saka a ciki,bacci take sosai hankali
kwance sai ya mata kallon ƙurilla tun daga ƙasar ƙafar ta