Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 74

99K to 102K   out of 221.1K words

kira ya shigo mai wayar kai idanun sa yayi ya sauke kan sunan mai
kiran sai ya ga Ammin sa ce dan haka yayi saving sunan my Ammi ɗauka yayi yana mamakin ko lafiya
cikin daren nan take kiran sa.

Kafin ya ce wani abin har ta riga sa ta hanyar ce mai

"My boy ina ɗiya ta take ne wai tun ɗazu nake ta kiran layin ta but bata ɗauka kai kuma taka wayar bai
shiga sai yanzu na yi sa'a ina fatan dai bata fara barci ba"?haka ya ji tambayar daga sama sai ya yi shiru
yana tunanin me zai ce mata dan kam bata da masaniyar ba ɗaki ɗaya suke rayuwa ba shi da Bilkisu ba
hala ma ta rigada ta fara baccin tun ɗazu yanzu me zai ce da ita in ta nemi sanin ba'asin rashin haɗa ɗaki
ɗaya da basu yi ba a matsayin su na ma'aurata,idan ta yi tunanin raina ta yayi fah me zai ce da ita dan ta
fahimce sa..

Jiyo muryar ta yayi tana kiran sa

"Zaid kana ji na kuwa"?firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi cikin sarƙewar murya da ruɗu cikin zance
ya ce

"Na'am na...aa.mm Ammi..Am..mi ina jin ki"..da mamaki ta ce

"Zaid lafiyar ka kuwa"??da sauri ya tari numfashin ta ta hanyar amsa mata da

"Ehh..Ammi,lafiya ta ƙalau"??sai kuma ta yi wani hangen a matsayin ta na babba tunanin nan ne yasa ta
basar haɗe da sakin murmushin manya wanda ya fito fili har yana iya jiyo ta sai ta ce
"Oh common my boy is normal it happens guess what?i understand your state of being ba damuwa
gobe ka haɗa ni da Bilkisun ok,goodnight my boy"zata sauka a kan layi sai yayi saurin hana ta dan ya
gano abin da take nufi wanda sam baya jin Ammi ta ma san matakin auren su da ba zata yi wannan
doguwar tunanin ba.

"Ammi tsaya bara na tashe ta dan ta fara bacci"a karo na biyu da ya ma Ammin sa ƙarya na fari akan
Bilkisun ne dai ranar da ta kira sa a asibiti tana tambayar ko ya sha maganin sa ya ce a'a ta tambayi dalili
dan ta san alhakin Bilkisu ne bashi nigh medications ɗin ta but sai yayi ƙarya ta hanyar cewa itama ai
rashin lafiyar ta ne yake son tashi saboda sanyin da ake yi a garin gashi yau a karo na biyu ya kuma yi
mata ƙarya all because of Bilkisu.

"My boy ku kwanta abin ku gobe zamu yi magana".sai ya ce

"No Ammi lemme wake her dan gobe zamu tafi checkup bana jin zamu sami time mu yi waya"..sai ta ji
daɗi wato har closeness nasu yayi nisa haka hala ma ba fitan kaɗai suke yi zuwa asibiti ba maybe har
zaga gari suke yi tare sai kuma ta ji wani excitement ya shige ta ko dai yaran nan sun kai wani mataki ne
a rayuwar auren su??sai ta shiga juyi a ɗakin nata dan Dr baya kusa yana ƙasa suna zantawa da Prof ita
kaɗai ce a ɗakin.

Yin wannan tunanin ya saka ta jin kamar ta janyo su su dawo nan kusa da ita ta rungume Bilkisu and
thank her for introducing her Zaid to the real world..

Ko kafin ta sani har ya datse kiran ya tashi ya nufi ɗakin ta babu tantama ya turo ƙofar bai sauke idanun
sa akan komai ba sai a kan kyakyawar surar jikin ta da ke ɗaukar hankali dan bata da girman jiki haka
bata da ƙanƙanci sosai dan ta ƙara weight akan tiny structure ɗin ta na da.

Kasancewar rigar mai santsi ne sai ya ɗan yaye sama kaɗan exposing her navel but iya nan kaɗai ya fito
waje sai gyalen da ke yashe gefen ta a saman gadon idanun ta luf sai sharar bacci take yi tana fidda
numfashi a yadda ya kamata.

Zuba mata idanu yayi yana kallon fuskar ta da ke nan so smooth babu taɓo sai dai wanda ba za'a rasa
ba eyelashes ɗin nan zara zara kamar lema suman kan ta dama a ɗaure yake da robber band ta naɗe shi
ta yadda ba zai takura ta ba dama ba wani cikan cunkus bane da suman it is scanty and silk soft and
tender to touch dan yana da tsayi daidai misali bai fi ƙarfin jikin ta ba dan a ƙiyastin masana an gano
yawa yawan masu ƙananan jiki ko sirara sun fi albarkatun suma toh a wurin Bilkisu ma haka ne dan
suman mashaAllah cika ne kawai bai da shi amma tsayi na nunawa kuwa akwai Alhamdulilah..



He was lost in his imaginations sai ya ga ta juya ta cigaba da baccin ta hakan ne ya ankarar da shi yayi
saurin ƙarasawa gare ta ya kai hannun sa cikin son nuna darajawa gare ta a matsayin ta na ɗiya mace ya
ɗan yi tapping nata a hankali.
Bata da nauyin bacci sai ta buɗe idanun ta ta sauke su kan na sa idanun mayar da idanun tayi ta lumshe
sai ta kuma buɗe su tar sai cikin nasa ta gwalalo idon zata maimaita abin da tayi da safe sai dai bai bar ta
ya ce

"Hey calm down Ammi wanna talk to you"sai ta fara neman gyalen ta at the same time tana rufe jikin ta
da bed blanket da ke kan gadon.

Abin dariya sai ya shiga taya ta rufe jikin ta da blanket ɗin har yana ma fin ta saurin lulluɓe jikin,hakan
ya bata mamaki and she began to wonder is he this gentile dama?wow he is a nice guy.tayi exclaiming a
ran ta sannan ta ce mai

"Thanks"da little smirk ya amsa mata sannan ya yi dialing numbern Ammi,babu jimawa ta ɗaga sai ya
saka wayar a hands free ta yadda zasu jiyo ta sosai

Tana ɗagawa ta shiga yi masu ba'a

"Zaid wani irin ɗaukar alhaki ne wannan na ce maka ka bar ƴar nan ta huta da wanne zata ji gajiyar yi
maka aiki ko gajiyar aikin da kake saka ta"!??sai suka haɗa ido suna kallon juna.

Cikin su babu ƙaramin yaro kowa ya mallaki hankalin kan sa sun gano manufar Ammi sai suka juya at the
same time suka girgiza kai kamar haɗin kai.

Dariyar Ammin suka jiyo sai suka gyara zama suka shiga gaishe ta ta amsa masu tana tambayar lafiyar
su,ƴar hira suka taɓa da ita a ƙarshe ta nemi Bilkisu da ta bar inda Zaid yake dan tana son yin maganar
sirri da ita saboda ta kalli Zaid ɗin ya mata alamar zai fita da ido dan ya bata privacy na yin magana da
Ammin.

Bayan fitar sa ne hirar su da Ammi ya canza layi dan ita duk ganin ta ai Bilkisu ta zama babar mace dan
haka ta shiga yi mata manya manyan maganganu irin na cikakkun mata a wun mazajen su ciki har da
yadda zata canza shigar ta,yanayin zaman ta in suna tare,irin kallo da murmushin da zata na aiko mai in
suna tare,irin takun da zata na yi in ta gan sa ƙarshe ma mai kankat ta mata wanda a nan Bilkisu ta fara
tarin ƙarya wai ta shaƙe sai hankalin Ammin ya tashi ta shiga tambayar ta ko lafiya ta mata ƙaryar zata
sha ruwa ta shaƙe ne.

Kashe wayar tayi ta zauna shiru tana tunanin maganganun Ammi wai ita kallon hapoy couples take
masu ne da har take tunanin sun zama ɗaya?



Dafe goshin ta tayi da hannun ta biyu tana jujjuya kai dan bata mafarkin akwai ranar duniya da zai zo da
zasu haɗa shimfiɗa da Zaid sai dai in an wata duniyar amma ba a nan ba dan ba son juna suke ba kawai
umarnin iyaye suke bi..
Tana zaune a haka ta ga kiran Ammi ya shigo sai tayi salati ita sam bata son jin wannan wa'azi da
huɗuba ta Ammi basu ƙaran ta da komai sai sha'awar samin life partner da zata iya yi mai duk
shawarwarin da Ammin ke bata dan dai kam in har Zaid ne,ta san ta rasa wannan mafarkin na son
experiencing irin epics da suka shuɗe a tarihin gidan su da ahalin su baki ɗaya.

Barin wayar tayi har ya ƙaraci ƙarar sa ya mutu daga wannan bata kuma kira ba hakan ya ma Bilkisu
daɗi sai ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya..



Ganin Zaid bai dawo karbar wayar sa ba sai ta yi swiping sama ta ga bai da security lock dan haka tayi
tunanin shiga gallery ɗin sa sai dai ta ga already a gallery yake dan haka ta shiga kallon hotunan tana
zooming wasu tayi dariya wasu tayi murmushi sai ta shiga tunanin toh ko dai yana da wani abu ne game
da ita dan in ba haka ba ta san ba zai shiga kallon hotunan da suka yi tare ba.

Wani irin juyi tayi wanda yayi daidai da sallamar sa a bakin ƙofar ɗakin ta kai idon ta tayi ga ƙofar ta ce
da shi

"Wa'alaikumul salam,shigo".

Turo ƙofar yayi kan sa a ƙasa sai ya tsaya mata a kai yana mai tambayar ta

"Kun gama wayar"?ta amsa mai da cewa

"Eh mun gama gashi"ta miƙo mai wayar ya kai hannu zai karɓa kenan hannun su ya haɗe da na juna sai
electrification ya shige su at the same time suka ɗago suka zuba ma juna ido sun ɗau lokaci a haka suna
kallon juna kafin daga baya yayi namijin ƙoƙarin janye nasa idanun ya shiga yin wasu moves na rashin
gaskiya yana sosa giran sa da yatsa ɗaya yana son basarwa..

Ganin hakan ya sa ita ma ta shiga basarwa ta yi kamar bata ji baƙon yanayin da ya shige ta ba a lokacin
da hannayen su ya sarƙe tare da na juna ba.

"Sai da safe calm sleep"ya faɗa kamar yadda nurses ko doctors ke ce ma patients ɗin su in zasu kwanta
baccin dare.

Abin sai ya saka ta murmusawa kaɗan sannan ta ce

"Thanks goodnight"daga haka ya juya ya fita yana zuwa daidai bakin ƙofar ta ya dakata ya yi switching
mata light na ɗakin haɗe da kuma yi mata sai da safe ta amsa da

"Uhumm"jan ƙofar yayi sannan ya nufi nasa ɗakin ya kwanta wai dan yayi bacci amma kuma sai me?
bacci ya ce bai san haka ba, gizo idanun sa ke faman yi mai akan shigar da ya riske ta ɗazu haɗe yanayin
suffar jikin ta,juyi yayi sai ya tuno da sarƙewar hannayen su ɗazu da irin electrification da ya shige sa
ɗazu ne ya rinƙa dawo mai sai ya tsinci kan sa da son ƙara ganin fuskar ta a halin da ya gan ta ɗazu sai dai
wani hanzari ba gudu ba,not all we want we get dan haka ya sakawa zuciyar sa haƙuri da dangana dan ya
san ba zai ma iya komawa cikin ɗakin ba at this very moment.
Rufe idanun sa yayi dan dole yayi forcing kan sa baccin dole ba wai dan yayi niyar yi ba dan da fari ya
matsu yayi baccin but after what happened earlier sai ya ji baccin ya ƙauracewa idanun sa a haka a lalace
yayi spending daren sai kusan ƙarfe uku saura na dare ya sami ikon runtsawa amma ciwon kai mai
tsanani ya gama kama sa dan haka baccin wahala yayi a daren.



A chan ɗakin baby doctor ma kusan haka labarin ya kasance dan har nata tunanin ya ɗare nasa da
kusan ɗigo cas'in da biyar,sosai ta lasa saƙat sai tunanin abin da ya faru a safiyar ranar zuwa ɗazu da ya
bar ɗakon take ta faman yi,ta juya nan ta juya chan har dai ɓarawo ya sace ta ba tare da ta sani ba.



8:45am

Cikin sauri sauri ta fito dan sun makara dan ya kamata a ce suna asibitin by now but sakamakon rashin
baccin da basu yi ba da wuri a daren jiya shi ya sa suka makara wun tashi.

Zuwa tayi ƙofar ɗakin sa bata tsaya jiran izinin sa ba ta shige wuluf tana mai kiran sunan sa

"Zaid ina kake mun yi late fah zo mu tafi kar mu kai yamma"maganar take yi cikin nuna halin fara
ƙosawa san lattin ba kaɗan bane.

Yayin da ta shigo mai ɗaki kai tsaye babu excuse bare ta natsu ta san yana tsaye tuntuni yana kallon ta.

Gyaran murya yayi wanda ya saka ta ankara da shi sai kuma ta juya mai baya cikin jin kunyar sa dan he
is almost half naked daga boxers sai singlet dake jikin sa wandon da yake sakawa ma bai rigada ya ƙarasa
saka shi ba, ga blazers da zai saka haɗe da accessories ɗin sa nan kan gadon.

Shi kan sa mamakin ta ne ya kusa shagalar da shi dan ya rasa ta ya ma za'a ce ga mutum a gaban ka
amma ka ce baka gansa ba how comes?

Ganin juyawar da ta yi ne ya saka shi girgiza kai kafin ya ce da ita

"Is okey i understand..we are now even na gan ki almost naked yesterday and now...,kema kin gan ni
almost naked..is okey just sit and wait for me"..

Kamar ya mare ta haka ta ji saukar maganar na sa har cikin zuciyar ta ta ji ba daɗi dan ita ba niyar ta ba
kenan tsakani da Allah ta shigo kuran sa ba wai dan wannan dalilin ba.

Cikin ɓarin baki ta shiga yi mai bayani



"Zaid ka yarda da ni wallahi ba haka bane,shigowa nayi dan in kira ka mu tafi asibiti saboda time ya tafi
kuma ban son mu kai dare bamu dawo gida ba shi yasa na shigo maka kai tsaiye believe me ba
intentions ɗi na ba kenan wallahi"..kamar zata yi kuka haka ta ƙarasa maganar sai kuma ya ga rashin
kyautawar sa dan he was little bit hard and his words weren't respectful hakan ya sa ya ce da ita cikin
tausasa murya

"Is okey na fahimta and am sorry just wait for me ina zuwa"kamar jiran sa ya kai ƙarshen ayar maganar
sa tayi hanzarin barin ɗakin.

Shine da abin jin kunya amma ita ce da jin kunyar sa saboda yadda ta gan sa babu kaya cikakke a jikin
sa.zama tayi a parlor tana jiran fitowar sa sai kallon kan ta take yi shigar ta dai ba shigar tsiraici tayi ba
dan doguwar riga ce mai igiyar ɗaurawa simple gown ash silver colour sai gyalen da ta naɗa kan ta da shi
wanda ya kasance milk colour haka jakar da ta sagala ƴar ƙarama itama milk colour ce takalmin ta kuma
mai tsini ne kalar gyalen.

Tana zaune tana jiran sa sai yanayin da ta riske sa ya shiga dawo mata sai yawo a idanun ta abin ke
yi,gyara zama tayi tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta tana cigaba da tuno halin
da ya gan ta jiya and yau kuma reverse is the case ita ce ta gan sa almost naked.



Fitowa yayi yana mai gyara botirin blazer da ya saka,botir ɗaya ya saka ya bar ɗayar sai ya ce da ita

"Tashi mu tafi"buɗe idanun ta tayi ta sauke a kansa sai ta kasa ɗaukewa dan wani irin special kyau ya
mata da safen sak ya fito a ainihin Dr Zaid Maher ɗin sa da ta sani da chan.

Tafa hanun sa yayi yana faɗin

"Excuse me Ms Muhammad,na ce ki tashi mu tafi"cikin jin kunya ta tashi tana son riga sa fita sai dai bai
bari ba dan dawo da ita baya yayi by means of holding her hand firmly yana faɗin

"Kar ki damu in dai akan ɗazu ne feel free feel comfortable ba komai,,ya ɗan ja fasali kafin ya
cigaba..after all you are my wife so ba komai bane dan kin gan ni a halin da kika gan ni ɗazu"!!!ɗif ta ji
wuta ya ɗauke mata shin kunnuwar ta daidai suke jiyo mata maganar ko dai ƙarya ne kawai gizo
maganar ya mata??his wife?strange,,a zuciyar ta tayi maganar sai tayi saurin ɗago kai daidai shima ya
ɗago dan ganin me ya hana ta yin magana

Cak suka haɗa ido,kallon juna suka shiga yi ido cikin ido suka ƙi cire idon tsawon lokaci,sai da yayi ƙarfin
halin juya idon sa sannan itama ta sami damar juyar da nata idon har dai ya sami damar yi mata magana

"Shall we"??ta amsa mai da kai daga haka suka ɗau niyar fita..

Har zasu fita wannan receptionist ɗin ta tare su da fara'ar ta tana cewa

"Good morning Mr and Mrs Maher,you look perfect i couldn't keep my compliments to myself,i must
say that you are the best couples i have ever seen you are just too perfect for each other"ta faɗa da
sincerity sai dai walwalar fuskar Bilkisu ya daɗe da ƙauracewa fuskar ta dan matar ta wani zaƙe a dole sai
tayi impressing nasu ko wa saka ta.

Haɗe girar sama da ta ƙasa tayi ta kai hannun ta kan na Zaid haɗe da ce mai
"Mu tafi"sai ta juyo ga receptionist ɗin cikin isa da gadara ta ce

"We don't need your compliments we know that already humm so keep it to your self"daga haka ta ja
hanun sa da matuƙar haushi suka fita,suna fita ta ware kamar ba ita tayi displaying little madness ba
ɗazu ɗazu a cikin hotel ɗin,shima dai kam yana da ƙudirin tambayar ta dalilin dasawa mutani magana
son ran ta ba tare da sun mata komai ba.




Ko breakfast basu tsaya sun yi ba suka ɗauki hanyar zuwa asibitin ya so su tsaya a eatery na jiya su ci
abincin but ta dage akan sai dai in suna dawowa su yi branching nan ɗin.

Tafiyar kusan awa suka yi kafin ya sada su da asibitin,tun daga bakin asibitin ta hango wata na kallon su
sai ta kalli Zaid ɗin ta ga shi ta mai cab ma yake yi sai ta sake ran ta ta tsaya jiran sa har ya gama sannan
suka shiga ciki.

Without much waste of time suka doshi ofishin Dr wanda shi ke da alhakin kula da Zaid in zai rinƙa
zuwa checkup.

Bayan gaishe gaishe da tambayar lafiyar su suka ɗunguma zuwa ɗakin da za'a duba sa,ana kaiwa ɗakin
ta ja ta tsaya a bakin ƙofar dan ba zata iya tsyawa kallon sa ba a yayin da ake gwada accuracy na brain na
sa ba.

Murmushi ya mata dan ya gane gudun ganin checkup ɗin take itama sai ta maida mai da murmushin ta
zauna su kuma suka shige ciki.

Gudun kar ma ta jiyo hayaniyar su ya sa ta saka ear piece ta shiga danna wayar kawai sai ga kiran
Bahajjatu,ɗagawa tayi tana mai nuna ɓacin ran ta ta ce

"Babu ruwa na da ke yauwa"!!shewa Baha tayi kafin ta ce

"Excuse me Mrs Zaid Maher kar fah ki manta matar yaya na kike ba yayar tawa ba"da dariya ta ida
maganar sai

34 / 74