Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
motar
ya shiga cikin gidan yayi tambayar ta aka ce mai ta fita hamdala yayi ya koma cikin motar shi ya ja zuwa
cikin gidan su ya shirya shima ya fita.
Sai dare families ɗin biyu suka dawo gida inda suka sha faɗa da ƴaƴan nasu musamman Hajiya Madina
da ta takurawa Zaid ɗin a ranar haka yayi ta faɗa kamar zai yi me ita dai shiru ta mai har ya gama sannan
ta ce
"Zaid ka daina shigar min ido fah da yawa ba fah hanaka auren nan na yi ba ga abokin ka nan Jamil da
mata har ma da ƴar ƴar shekaru biyu da rabi kai baka yi ba ban hanaka jin daɗin ka ba sannan a ce kai
ban takura ka ba amma kai kana son amputating min farincikin rayuwa ta ba zan ɗauka ba yauwwa"tana
gamawa ta kalli Dr Maher ta ce mai
"Only talk to your boy"ta yi wucewar ta a dole an ɓata mata rai,bayan wucewar ta mahaifin ya kalle shi
cikin taarguwa kafin ya ce
"Zaid we are sorry ka san halin Ammin ta ka"kallon tsaf ya ma mahaifin na sa dan ya san har da laifin sa
a yawan yawon nasu dan haka ya zauna kusa da shi ya ce
"Abba toh wai dole sai kun fita yawon nan ne zaku nunawa duniya cewa kuna son junan ku"? ya girgiza
kai
"Toh me yasa ba zaku rage ba at least not always koh da once in a month ne"ya kuma girgiza mai kai
kamar wanda ya ɗau shawarar ta sa shi so yake ma ya rabu da shi ya wuce ya rarrashi heart ɗin sa lallai
yaro man kaza su da suke planning tafiya ƙasar London dan buɗe ido zai wani kawo masu tsarin su rage
yawon buɗe idanu hmm Zaid bai san me ake kira da soyayya da ƙauna ba anyway he didn't blame him
bai san daɗin su ba shi yasa,
Da haka suka rabu kowa ya wuce shi Dr Maher ya tafi rarrashin Hajiya Madina shi kuma Zaid ya koma
ciki yana mamakin rayuwar mahaifin sa wai a ce mutum da girman sa amma mace ke juya shi kamar
ƙaramin yaro a ce mahaifin at his early 60's amma mahaifiyar su sai yadda ta yi da shi sannam in aka yi
magana su ce soyayya ce to he with the word soyayya meye gamon shi da kalmar,shi ba zai yi tolerating
wannan shirmen a gidan sa ba.haka ya kwanta yana mamakin halayar iyayen su na both houses ɗin.
_Monday morning_
8:50am
Sauri saurin shiga office ta ke dan ɗauko important files ɗin da ta bari tun friday she was in a hurry so
bata lura ba kwata kwata ta take shi da takalmin ta,ja da baya tayi tana jin damuwa gashi ita kuma ba
zata iya ce mai yi haƙuri ba dan haka ta tsaya shima ya tsaya yana kallon ta ga shi dukkan su suna da
uzirin da ke gaban su amma izza ta hana su motsa fatar bakin su dan haka suka cigaba da tsayuwar har
sai da Dr Aslam ya zo giftawa ya tsinkayo su wani kishi ne ya taso mai wanda yayi sanadiyar chanza
hanyar tafiyar shi zuwa direction ɗin su ya iso su yana kallon su afar dan son jin me suke cewa amma har
shafewar mintuna biyu bai ji sun ce komai ba dan haka ya yanke hukuncin tunkarar su dan ganin irin
kallon da suke aikawa juna a tunanin shi kallon so ne bai san wuta ne ke ruruwa a cikin kallon ba,
Da zuwar shi ya yanke kallon ta hanyar kiran sunan ta
"Beelove good morning how was your night"?jin muryar shi ya sa ta sami kafar barin wurin ta ƙara gaba
abin ta ta bar su a wurin yayin da shi kuma Dr Zaid ɗin ya bankawa Dr Aslam harara yana cewa
"Wawa yarinya ƴar ƙanƙanuwa na juya ka kana abu kamar wanda bai da tunani mtsw"ya yi tsaki kafin ya
bar wurin shi kuma ya raka shi da harara yana cewa
"Eh na ji ɗin haka kawai in bari ka sami lafiyayyiyar yarinya haka ɓagas inaa ba zai yiwu ba"shima ya
wuce abin sa.
Throughout ranar a hide and seek suka yi ta Bahajjatu was supposed to return back yesterday amma ta
ɗaga har sai yau dan haka da wuri baby doctor ta yi closing komai nata dan ta tafi tarbar aminiyar tata,..
A airport ɗin da ta ke jiran isowar ta ne ta hangi Dr Zaid ɗin yi tayi kamar bata san da zuwar shi ba
yadda shima ya basar kamar bai gan ta ba haka suka yi zaman jira har jirgin su ya sauko aka gama
firfitowa daga baya ta fito itama da yayan ta ta fara tozali dan haka ta yi saurin ɗaga mai hannu har dai
ya hango ta shima suka sakarwa junan su murmushi har suka iso dab da juna ya bata side hug yana
tambayar ta ya hanya
"Very hectic journey yaya na gaji sosai"ya ɗan murmusa kafin ya ce
"Then you need to rest"ta ce
"Yeah sure"suka cigaba da takawa har suka zo zasu shiga motar sa sai ta hango aminiyar tata tana kallon
su da sauri ta ƙarasa wun ta ta na
"Ohhh my God Beelove dama kin zo ne ban gan ki ba"hararar ta tayi ta ce
"Ban sani ba"ta rungume ta tana ce mata
"Ya hanyar"?
"Babes babu daɗi tafiyar yau na gaji da yawa"
Kallon ta tayi tana cewa
"Anya ko dai fever ne ke son kama ki"jan jikin ta yi ta ce
"Zaki fara kenan da zarar mutum yace nan na zafi sai kun yi analysis" ɗan dara suka yi kafin ta ce
"Mu je ma a motar ki zamu tafi"juyawa tayi ta ce da yayan ta
"Yaya na mu haɗu a gida zamu biyo ka"ɗaga mata kai kawai yayi ba dan ya so ba da haka suka wuce
shima ya biyo su a baya.
Ta so barin har sai sun isa gida kafin ta sanar da ita maganar da ta ke ta jiran ta ta dawo ta sanar da ita
amma abin na damin ta dan haka ta fayyace mata saidai rashin nuna kulawar ta ya sa Bilkisu ƙara
tsarguwa da tafiyar har dai ta ajiye ta a gida ta ce mata anjima zata dawo suka rabu.
Da tunani fal a ran ta smta kwana tafiyar will be friday kuma ita she is not just comfortable with the
outreach kuma mahaifin ta bai son fahimta babu ma wanda ke son fahimtar..
*****************
A daren da yake washegari ne tafiyar ta tafi asibiti dan ɗauko wasu abubuwan da ke da muhimmanci a
tafiyar tata ta fito tana kallon office door ɗin shi a buɗe kamar ta shiga ta tunkare shi da maganar dalilin
shi na son tafiya tare da ita outreach ɗin sai dai girman kan tsiya ya hana haka ta rinƙa kallon ƙofar har
ya fito ya ja ya rufe zai tafi kenan ya hango ta tsaye da kayan a hanun ta tana kallon shi.babu alamun
damuwa a tattare da shi dan shi matsuwa ma yayi ya je ya ga sanyin idaniyar sa he use to take soyayya a
matsayin abin da bai da wani ƙima though yana da wacce yake son yin rayuwar shi da ita sai ya ke
mutunta kalmar son har da dai ba chan sosai ba amma ya san dai yana son ta but ba irin blind love da
iyayen su ke ma juna ba he cursed that type of love.
nufota yayi yana tsare ta da ido ita kuma ta kasa cire idanun ta daga nashi har ya ƙaraso ya tsaya yayi
folding hannayen sa ya ce
"Are you prepared"?
Ɗan shiru ta yi kafin ta ce da shi
"Why?me yasa ka min haka a wun mahaifi na bayan ka san ba zan iya ƙin amsa duk umarnin sa ba why
did you do that to me"? Murmushin ƙasaita yayi ya ce.
"Hmm baby doctor kenan ba dai har kin fara tsorata da outreach ɗin na mu ba"? ɗan rausayar da idanu
ta yi cikin takaici ta ce
"Ni dai tambayar ka na yi me yasa ka min hakan"? saka hannun sa yayi a waist ɗin sa ya rage tsayin sa ya
ce
*_"iya ruwa fidda kai_*
yana kaiwa nan yayi gaba abin shi ita kuma ta bi shi da kallo har ya ɓacewa ganin ta kamar zata yi kuka
haka itama ta bi bayan shi ta wuce zuwa gida tana tunanin yadda zaman su inuwa ɗaya zai kasance a
ƙauyen...........
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*4*
A ranar kasa rintsawa ta yi sakamakon zullumi da fargaban ko me zai wakana washegari kiran Bahajjatu
ta yi a waya bata ɗauka ba an saka mata number busy kuma kira ta yi har sai da ta ɗauka
"Haba Beelove wani irin fitina ne da daddaren nan kin kira kin ga am busy kin kuma kira na saka ki a on
hold wai menene"?
Gauron numfashi ta sauke kafin ta ce
"Baha ina tsoron tafiyar nan"ɗan shiru suka yi kafin ta ce da ita
"Me ya sa zaki ji tsoro Beelove bayan kin saba zuwa outreach ɗin nan ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba toh
nervousness ɗin na meye"?
"Ban sani ba Baha amma ina da atrong feelings akan cewa babu alkhairi a outreach ɗin nan i don't know
maybe is because of your brother am not just comfortable Baha"!! ta ida kamar zata yi kuka dan haka
Bahajjatu n ta ɗan saurara mata kafin ta ce
"Beelove calm down please you are being over reactive na ke ganin kamar ki yi magana da yaya Zaid
kafin goben saboda ki sami relief ko me kika ce"?Bahajjatu is always putting a bilnd eyes ma duka
abubuwan da ke wakana a tsakanin su haka take da halin ban san kuna da misunderstanding ba which
hurts baby doctor ba kaɗan ba..
"Alright fine tunda haka kika ce nagode good night take care".. Tana kaiwa nan ta datse kiransau uku
Bahajjatu na kiran ta ta ƙi ɗagawa dan ta san ta mata sallamar da ɓacin rai shi yasa ta rinƙa calling back
amma ta ƙi ɗagawa haka ta haƙura ta tura mata saƙon safe journey akan washegari zasu yi goodbye
proper ignoring message ɗin ta yi ta tashi ta saka slippers ɗin ta ta nufi ɗakin Bilal wanda ke ta faman
rarrashin apple ɗin sa dan ta ƙi magana da shi laifin Bilkisu ya shafe shi,bata wani tsaya buga kofar ba da
yin sallama ta turo ƙofar luckily yana buɗe,
Da sauri ya leƙo daga cikin comforter ɗin dan bai yi tsammanin ganin kowa ba..haɗa ido suka yi ya ga
yanayin ta ya chanza sai ya bama Bahajjatu haƙuri akan zai kira anjima ya katse wayar yayin da ita kuma
ta ƙarasa shigowa ɗakin tana taku a hankali kasa haƙura yayi har sai da ya tambaye ta me ke damin ta.
zama ta yi a saman hannun kujerar ɗakin tana ƙoƙarin danne hawayen ta
"Apple me ke damin ki har kike ƙoƙarin zubar da hawayen ki"? ai kuwa sai ga hawaye sun gangaro ta yi
saurin goge su
"SubhanaAllah apple wai menene"?
Juyar da kan ta gefe tayi ta ce
"Bilal bana jin akwai alkhairi a tafiyar nan da za'a yi amma babu wanda ya fahimce ni nayi nayi in
fahimtar da Abba amma baigane ba ya yarda da Zaid Maher sama da misali umma ma ba'a magana dan
bata son jin laifin sa Bahajjatu ma bouncing ɗi na take yi saboda yayan ta ne tauraron ta bata ganin illar
abubuwan da yake aikatawa kai kuma tun farin maganar nan na sanar da kai yadda nake ji amma baka
taya ni jimami ba toh duka waɗanda na amince da su basu yarda da ni ba wa kuma zai yarda da ni"? ta
ƙarashe tana sakin silent cry wanda ya karya zuciyar ɗanuwan nata har shima ya ga rashin kyautawar sa
out of all peoplr he should understand sama da kowa but bai bata wannan chance ɗin ba ya biye ma
halin ta na sanyi ya ƙi fahimtar damuwar ta.
"Bilkisu am so sorry please forgive me ban san abin ya dame ki da yawa har haka ba ni duk a tunani na
maybe kun sami masalaha ne a tsakanin ku but believe me apple wallahi wallahi ban san har yanzu
akwai matsala a tsakanin ku ba but since it turns out to be this way ki zo mu je wun Abba a san na yi dan
shi kan shi ba zai yarda ki tafi outreach ɗin da hankalin ki bai kwanta da shi,lets go"! ya miƙe tsaya yana
ƙoƙarin jan hannun ta su tafi dan abin ya ƙona mai rai.
Dakatar da shi tayi ta hanyar dawo da shi ya zauna ta fuskance shi ta ce
"Bilal duk duniya ban da wanda nake da burin farantawa kamar Abba,zuwa sanar da shi wannan
maganar kamar janyo mai ɓacin rai ne wanda hakan na iya janyo masu saɓani tsakanin su da daddy
Maher wanda duka iyayen namu ba za su so ba dan haka ka bar maganar kawai i accept defeat zan tafi
tare da shi muyi outreach ɗin mu dawo kuma inshaAllah zan rufe idanuna kuma in rufe kunnuwa ta ga
duk wasu abubuwan da zai min a garin har mu dawo ban san dalilin shi na ƙi na ba but ko ma dai
menene ba zan taɓa ɓatawa mahaifi na rai ba"ta ida tana share hawayen da ke tsilalowa daga idanun ta
wanda ya kuma karyar da zuciyar ɗan uwan nata.
"But apple are you comfortable with the decision you just made"?? Kallon shi ta yi tana jinjuna kai
"Alright,just always remember that am with you ko ina kusa ko bana kusa da ke huh"? jinjina kai tayi
tana jin sanyi a ran ta ɗan uwa ɗan uwa ne dan tun da maganar ta taso bata taɓa jin sauƙi da sanyi haɗe
da kwarin gwiwa ba sai yau da ta fitar da abin da ke ɗawainiya da ita a ran ta.
"Thank you apple"comforting smile ya mata ya raka ta har ƙofar ɗakin ta suka yi sweet dreams har sai
da ta rufe ƙofar ya koma ɗakin shi ya kwanta koh Bahajjatun bai kira ba da kyar yayi bacci yana tsoron
tafiyar twin sis ɗin ta sa.
A nata ɓangaren ma haka ne dan ta sami courage ba laifi a haka ta harhaɗa abubuwan da zata buƙata a
trip ɗin ta gama ta kwanta bacci with less worries...
*************
Tun 9am suka gama packaging kayayyakin tafiyar ta su wanda Hajiya Zeenat ta haɗa mata kayan cime
cime kala daban daban dangin su dambun nama alƙubus cupcakes plantain chips dried smoked fish da
dai sauran kayan fast food da ba zai wahal da ita wun dafawa ba.
Bayan breakfast suka ranƙaya gabaki ɗaya har da yaya Lukman suka raka ta dan zuwa airport inda a nan
suka haɗe da su Zaid suka ƙarasa har airport ɗin dan by air zasu yi tafiyar saboda sauƙaƙa gajiyar hanya.
Sosai Hajiya Zeenat ta nuna jin kewar ta ga ɗiyar tata haka Hajiya Madina ma duk ta damu saboda
pneumonia ɗin ta shi yasa ta jadadda ma Zaid akan ya tabbatar ya kula da baby doctor though bata
sanar da shi cewar tana da pneumonia ba but ta ja mai kunnen ya rinƙa kula da ita sosai ya amsa mata
da cewar inshaAllah..
Bilal kamar kar ya rabu da ƴaruwar sa haka ya rinƙa ji.wata ƴar drama aka yi a airport ɗin dan wani koke
koke iyaye matan ke yi yayin da iyaye mazan ke rarrashin su abin sai ya zama abin dariya ga ƴaƴayen
nasu Lukman da ke kallon su ya kasa haƙura ya ce
"Alright drama over a tafi gida haka nan"hararar wasa Hajiya Zeenat ta aika mai da shi suka kuma yin
dariya da haka suka shige jirgin ya ɗaga zuwa ƙasar Adamawan Yola su kuma iyayen suka koma gida.
Tun da suka shiga jirgin nan babu wanda ya kalli juna a cikin su kowa harkar gabar sa yake yi har jirgin
yayi landing safely suka shiga taxi zuwa inda zasu tafi uhum bai shiga tsakanin su ba shi da ya san wuri
shi ya rinƙa kwatance har suka yi tafiyar kusa 2¼ hours kafin su kai ciki cikin yankin _koma_ inda aka
masu masauki a gidan mai gari tuni labari ya zaga gari bokan turai ya zo tare da wata wacce ake
tsammanin itama bokar turai ce ai kuwa aka fara tururuwar zuwa ganin su dama shi ɗan gari ne ita ce
sabuwar zuwa dan haka suka rinƙa zullumin ko likitar ce ita ko dai ƴar rakiya ce ita dan haka suka rinƙa
tambayar samarin garin wanda suma jira suke washegari yayi su ji cikalen labari daga bokan turai sun so
yin takakkiya su tafi har gidan mai garin dan jin rahoto amma mai gari ya hana ya ce a bar su su huta har
gobe dan haka suka haƙura.
Matan mai gari suka karɓe su hannu bibiyu tun ma ita baby doctor wacce ta kasance mace ta ji daɗin
tarbar da suka mata har da dai basu da wani ƙarfi amma sun yi ƙoƙarin su abinci kala kala daidai ƙarfin su
shi da ya zama ɗan gida ya ma manta da wata wai Bilkisu dan samarin gidan mai gari sun ja sa da hira
kuma yanayin sauƙin kan sa ya sa suke son sa har suke mai kirarin bature ya ƙi halin turawa dan su sun
san ƴan birni na da ƙyanƙyami da tsantsene akan ɗan kauye amma ta fannin bokan turain nasu ba haka
bane.hira sosai suka sha har aka kawo mai abinci suka ci suna hira har lokacin sallah yayi suka tafi suka yi
daga nan ma ɗan zaga gari suka ui har sai bayan sallar isha'i suka koma gida inda a nan mai garin ya ce a
bar shi ya huta haka nan dan haka suka bar shi akan gobe zasu dawo.
A gefen ta kuma haka dai suka so sakewa da ita amma ganin kamar bata saba da hayaniya ba yasa suka
rabu da ita sun fi dangana hakan da gajiya akan gobe zasu yi hira itama hakan ya fi mata dan so take ta
huta gyara mata wurin kwanciya aka yi a ɗaya ɗakin matar mai gari wacce ita ce ta fi su wayewa dan ita
ce ƴar gaban goshin mai gari kasancewar ta amarya kuma ɗiyar mai kuɗin garin so komai nata tsaf tsaf
yake watannin ta 8 kawai da aure bata kuma da ciki bare ɗa ko ƴa.lafiyayyen gadon ta da ya sha gyara da
zanin gado mai kyau ga blanket mai