Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 74

75K to 78K   out of 221.1K words

ta ce
"Eh Ammi ai yanzu muka gama waya da Aslam ya sanar da ni"

"Oh ya kira ki ne ashe"yadda tayi maganar sai ya saka Bilkisu ɗagowa tana kallon yanayin ko in kular da
ta saka yayin tambayar ta sai ta girgiza kai kawai.

Toh Ammi ƴar ayi a wuce wurin ne dan haka ta gyara zaman ta da kyau ta fuskanci Bilkisu ta fara
zayyano mata abin da ke tace da ita wanda ba komai bane face maganar auren su da Zaid



A firgice da tsoro tab zuciyar ta ta shiga girgiza wa Ammi kai tana faɗin

"A'ah Ammi baku san komai ba kawai abin da idanun ku ya gane maku kuka sani apart from that you all
know nothing between i and Zaid"ta ruɗe uya ruɗewa sai Hajiya Madina ta riƙo hannun ta da ɗan force
ta ce

"Bilkisu Zaid ɗa na ne kuma sai da yarda da amincewa ta zai wulaƙanta ki wanda har duniya ta naɗe ba
zan lamunci hakan ba what we see or didn't see doesn't matter abin da ya fi muhimmanci shi ne
amincewar ki akan zaki auri Zaid ki kula da shi kafin ya farfaɗo dan kema ki sami lada bibbiyu ga na aure
ga na jinyar sa da kika yi ko baki son samin wannan ni'imomi da rahama ta ubangiji ne Bilkisu"?sai ga
hawaye na bin fuskar ta dan ita gaskiya ba ta son yin rayuwar aure da mutumin da bai son ta mutumin
da laƙaba mai ita za'a yi it will appear like a big disgrace to her yadda take magarki da burin jin daɗin
rayuwar aure da mijin ta kamar dai yadda iyayen su ke yi sai a ce She end up with someone she doesn't
love someone that doesn't love her wabda basu yi courtship ba kawai daga sama yana ciwo ba ma a
cikin hayyacin sa ba a ɗaura masa auren ta inaa impossible ita dama tausayin sa lawai take ji banda
wannan babu wani abin.

Ganin kukan ba mai ƙarewa bane sai Hajiya Madina ta shiga ƙwabon ta dan ta san in tayi sanya tayi
lagwa lagwa toh ba abu mai wuya bane a wun Bilkisu ta ce bata yi kuma in hakan ya faru uta zata cutu
dan ta daɗe da yin mafarkin kasancewar su inuwa guda

"Bilkisu ji ni da kyau,kin ga Allah in kika bari tunanin zuciya barkatai suka rinjaye ki?toh wallahi babu ke
babu samin natsuwa da kwanciyar hankali har abada,haba,Zaid ɗa na ne kamar yadda kike ɗiya a gare ni
ko babu komai akwai amintaka da dangantaka tsakanin mu da iyayen ki which equally make Zaid to be
your brother,ko ba komai a matsayin ki ta doctor mai kula da kuma kare lafiya da matsalar client ɗin ta
in kika dubi Zaid da kyau zaki hango damuwar sa Bilkisu,uhmm,Zaid na buƙatar kula daga wun wanda ya
wuce ƙani ko iba ko uwan sa yana buƙatar kula ne mai zurfi daga wun sirrin sa,muharram ɗin sa,matar sa
which he have not,amma kin ga yanzu with the little closeness da nake gani a tsakanin ku da yadda kike
reacting when it comes to Zaid sai na ga a duniyar nan babu wacce ta cancanta ta kuma dace da zama da
amsa sunan matar Zaid sama da ke Bilkisu forget about his jinnkai stuff duk izzar sa sai dai in ba haɗuwa
yayi da mace wayayyiya ba kamar dai ke,matuƙar Zaid ya farfaɗo ya ji cewa kece matar sa believe me he
will appreciation our effort kuma kar ki saka a ran ki wai in ya farfaɗo ya san cewa ke matar sa ce zai
wulaƙanta ki a'a ba zai yi hakan ba dan zaɓi na ce ke kuma ko bana nan Zaid ba zai taɓa wulaƙanta abi na
ba dan haka ki kwantar da hankalin ki ki amince tun kafin ma ya farfaɗon ki fara samin ladar bautar
auten ki da ladar jinyar sa da zaki fara i can't force you zan baki time ki yi tunani but kae yayi exceeding
sama da 48hours".ta miƙe zata fita ta ce

"And don't forget to pray to Allah for guidance hmm"?da ido ta bita har ta fita daga ɗakin kafin ta sauke
idanun ta masu fidda ƙwaa ƙasa tana maganar zuci

"Lallai Ammi bata san komai ba game da su biyun,mutumin da ba son ta yake ba tun asali har ya iya
ɗaukar ta ya kaita ƙauyen nan da sunan punishment ina ga in ya san an aura mishi ita in ya farfaɗo?
kasbe ta zai yi kawai ya huta..da Ammi ke maganar bata ga macen da ta dace da zama da kuma amsa
sunan matar zaid ba sai abin ya bata dariyar baƙin ciki dan tuno da Asma'u da tayi,hmm Ammi bata san
cewa ɗan ta na cikin soyayya mai zurfi da wata ba watan ma yarinyar da ta januo mai shiga wannan
halin"..

Lokaci sosai ta ɗiba tana saƙawa akan batun a ƙarshe dai ta tsaya akan zata sanar da mahaifiyar ta
kawai dan ita kaɗaice zata san abin da fi dacewa da ita a rayuwa in ma auren Zaid ko rashin sa..



Tashi tayi ta tafi ta wanko fuskar ta ta dawo ta goge ta gyara gyalen ta ta fito saɗaf saɗaf ta kama
hanyar ɗakin Zaid wai duk dan kar Ammi ta ganta ta ɗauka ko dan ta damu da shine bare tayi concluding
abin da ke ran ta na cewa tana son zaid har ta zafafa akan maganar auren.

Wulup ta shige ɗakin yayin da Hajiya Madina da ke daga balcony na sama tana kallon ta ta saka dariyar
wautar ta imagine mai cewa a'ah ba'a san abin da ke faruwa ba tsakanin su su biyun ba kenan tana satar
hanya kamar wacce tayi sata ta taho ɗakin sa dan dai ta gansa anjima kuma she will claim ita ba haka ba
dariya kawai Hajiya Madina ke yi dan ta matsu bata ga ɗan ta ya fara gwadawa Bilkisun soyayyar sa ba
dan kuwa shakka babu matuƙar ya san ita ta yi ɗawainiya da shi tun daga ƙauyen nan har izuwa
farfaɗowar sa toh ta san siga da launin soyayyar da zai gwada mata babu makusa da irin tasu da suke yi
dan haka ta girgiza kai da ragowar murmushi a kan fuskar ta ta fara saukowa tana nazari a zuciyar ta..




*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄
°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*Explore*



*17*



At first da ta shiga ɗakin zuba mai idanu tayi sai daga baya ta zauna ta cigaba da kallon sa azimun babu
shakka so take ta fitar da wani abu daga fuskar sa sai dai hakan bai samu ba dan ɓata lokaci tayi tana
kallon sa bata san time ya tafi ba sai da ta ji gyaran murya sai tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin
da ta faɗa,.
Ammi ce ta shigo ɗakin dan tuntuni take kallon ta ta transparent glass door dake ɗakin nazarin ta take
yi shi yasa bata yi interrupting mata analysis ba har sai da ta ga kamar kan ta zai buga dan dagewa tayi
tana kallon sa tana ta wasu abubuwa masu kama da analysis.

Kunya ne ya kama ta Ammi caught her again oh no sai ta fara inda inda tun ma kafin Ammin tayi magana
wanda ya saka Ammi fitar da dariyar ta fili dan kasa riƙe sa tayi,

"Wait Bilkisu,wa ya saka ki a gaba akan sai kin yi explaining dalilin ki na shigowa ganin Zaid?i guess babu
right?common dear is a natural feeling feel free and express your feelings is not a crime rather is it a
sin,open your eyes and heart,learn to accommodate the stranger in your heart,ki daina ɓoye abin da
kike ji game da Zaid,Bilkisu da a ce ban hango wannan abin ba,da a ce ban ga tsantsar so da kike yiwa
Zaid ba wallahi tallahi ko da shi Zaid ɗin ne ke son ki amma ke baki son sa toh wallahi ba zan taɓa yarda
ya aure ki ba ko da hakan na nufin threat ne ma rayuwar sa dan haka baby,ki amince da abin da zuciyar
ki ke faɗa maki"ta ƙarasa maganar tana mai daga kafaɗun ta.

Ko uhum bata ce ba sai ta fita abin ta dan waɗannan maganganu da Ammi ta mata kamar watsa mata
garwashi tayi saboda yadda take rera kalaman ta sai suka rinƙa taso mata da tunanin Asma'u dan ita
kaɗai ta san ya take ji a ran ta a duk sanda ta tuna da Asma'u ta kuma tuna da abin da ya faru da su abin
ba ƙaramin rura mata wutar ƙiyayyar yarinyar yake ba shi wanda ya aikata abin ma bata jin haushin sa
kamar yadda take jin haushin yarinyar kuma all she can see and say shine Zaid is blindly in love with that
villager what if he regain consciousness and decided not to make her his Mrs?what if he develops love
for that strange girl and not her?what if he hates her after knowing that she is his wife and life partner?
ya salam sai ta zauna tana tunanin mafita gashi su Hajiya Zeenat basu riga sun yi landing ba bare ta kira
ta ta sanar da ita abin da ke gudana.

Throughout ranar babu wani kuzari ko walwala a tattare da ita iya tayi sallah ta ci abinci ta sha magani
sai kwanciya amma baccin ma ba zuwa yake yi ba saboda tsananin damuwa da ta sakawa kan ta duk
brain ɗin ta ya ɗau chaji ta rasa menene abin nan da ya ke mata ƙatutu a ƙirjin ta babu damar ta ji sunan
Zaid sai gaban ta ya faɗi hatta ita kanta in zata yi yunƙurin kirab sunan sa sai ta yi da gaske if nit kasa
furtawa take,toh me hakan ke nufi?wannan tambayar ta tsaya mata a rai sosai duk ta kasa shikir but she
knows that damuwar ta zai ƙare da zarar ta yi magana da Umman ta.

A haka Bahajjatu ta same ta sai ta kira sunan ta yayin da take ƙoƙarin zama

"Beelove"amsa mata tayi ta ce

"Na'am Baha"sai ta tashi ta zauna tana son gaya mata wani abin but bata san yadda zata fahimci
maganar ba but she have to say it

"Baha ni ko na ce me zai hana a yiwa Zaid gyaran fuska he is going out of his usual appearance kuma
kamar ba wanda ya shirya gyara shi haka za'a cigaba da kallon sa dan baya cikin hayyacin sa"?tsayawa
kallon ta Bahajjatu tayi dan ta bata mamaki wato har lura take da yanayin fuskar sa tsabagen so da ya
matu mahaukacin kamu but she doesn't wanna admit it sai ta ce
"Toh ke in banda abin ki beelove ai ina ga since babu wanda ya lura da hakan sai ke why not ki tafi ki
mai gyaran fuskar coz na ga yanzu ba lafiya kike nema ba dan kin ji sauƙi already sai dai ki yi jinyar marar
lafiya and i guess babu zunubi dan mata ta gyara mijin ta for her own satisfactory purpose right"??da
teasing tune ta kammala maganar wanda ya sa Bilkisu jefar ta da ƙaramar pillow da aka yi beautifying
gadon da shi,gudu tayi tana dariya ita kuma ta ɓata fuska a dole an laƙaba mata abin da bata lamunta da
shi ba sai ta ce

"Amma dai kin san ban son wannan abin ko Baha?zamu fah ɓata ta yaya zaki rinƙa kiran min matsayin da
ban kai ba a ina na zamo matar Zaid stop it please before some could hear you so annoying"!!ta ƙarasa
kamar wata ƙaramar yarinyar da ke shirin sakin kuka sai kawai Bahajjatu ta cigaba da dariyar ta kafin ta
dawo kusa da ita ta zauna ta ce

"Babes,ba fah laifi bane dan kin yarda da abin da kike ji game da yaya na,wallahi kin ji rantsuwar
musulm,yau da ace wata ce ba ke ba ta ke ƙaryata feelings ɗin ta akan yaya na toh Allah ban bin ta kanta
sai dai ma in daɗa dulmiya ta ta amince akan bata son sa but ke Bilkisu both our parents have agreed to
this wedding dan sun san alkhairi ne cike a cikin ta abin da suka hango mu bamu hango ba kuma baki san
wani abu ba,kin ga yaya na da kike gani wallahi bai da matsala bai da damuwa ko kaɗan hasalima he is a
free person very gentile and kind kawai borin fuskar sa kike gani har kike ɗaukar hakan a matsayin halin
sa ne but i will tell you a little secret about my brother"sai ta zama serious haɗe da chanza fuskar alamun
maganar da zata faɗa ɗin babba ce mai muhimmanci sai itama Bilkisun ta maida hankalin ta gabaɗaya
kan aminiyar tata dan jin me zata sanar da ita

"My brother happens to be the most quit caring and gentile out of all my brothers shi kaɗai ne mai
hanƙuri da juriyar duk wasu abubuwan da ke tasowa,bai taɓa son wata ba kuma babu macen da ta taɓa
gigin kusanto sa da sunan so ko da kuwa tana son sa ne he is committed to his duties abu ɗaya da ya
tsaya mai a rai kuma yake damun sa shine akwai wata yarinya da ya taɓa gaya min cewa yana da wani
feelings akan ta wanda bai sani ba so ne kokuma shaƙuwa ce bai sani ba amma ya san in har ya ga
yarinyar yakan ji wani abu game da ita is somehow mix bai iya tantance menene kuma ya kasa sanar da
kowa ya barwa kansa shi kaɗai sai ni da yayi min bayanin kaɗan i guess that girl is the Asma'u girl in that
village,wani abin da ya sa na ƙara yarda cewa ba son yarinyar yake ba illah shaƙuwa da tausaya mata da
yake yi shine sai da ya gargaɗe ni akan maganar kar ta wuce tsakanin mu mu biyu saboda ya san in har
Ammi ta ji toh Allah ne kawai zai taimake shi daga hannun ta dan fushi zata yi da shi and yiu know what?
ko da wasa bai taɓa yin maganar da Ammi ba kenan ba son yarinyar yake ba dan da son ta yake toh babu
wani abin da zai saka shi jin shakkar nunawa duniya ma budurwar sa har Ammi zai nuna mata but no he
is not comfortable with that decision so you see in har yaya bai san matsayin yarinyar nan a rayuwar sa
ba i don't think you should play with this opportunity for making him yours kin fah san a family ɗin mu
namiji mace ɗaya ya ke rayuwar sa da,which is equivalent to having a single life partner in kuwa ya auri
yarinyar nan shikenan ya rasa damar auren ki and our parents dream is for the two of you to get married
and leave a happy life wanda nake fatan kafin ya farka ki zamo matar sa because i don't want him to
marry that village girl dan bai san abin da yake so ba har yanzu bai san menene taste ɗin sa ba marrying
that girl will shatter all his dreams away saboda yaya na ɗan soyayya ne yana son yin rayuwar soyayya ba
kaɗan ba da matar da zai aure wanda ko da na duba sai na ga kuna a page ɗaya da juna dan kema ƴar
son soyayya ce but kin rasa da wa zaki yi rayuwar soyayyar yadda kika daɗe kina mafarki,Aslam was
never your dream guy ni na san ba kya son sa kuma in har kika zuba mai ido yana iya tura iyayen sa su
tafi gida a yi maganar auren ku because yadda yake yin abu is like irin kin amince mai ɗin nan ne dan
haka Abba might not think twice sai ya amimce though na san shima yana son auren ku da yaya na but
he won't force you in ya tambaye ki kika ce mai a'a ba ki son yaya na yana iya barin ki ki zaɓi wanda kike
so wanda a gare ni hakan babban asara ne dan i want our friendship to go beyond this so please Bilkisu
ki natsu ki duba wannan maganar da na gaya maki ki kuma yi la'akari da future ɗin ki kafin ki zaɓi life
partner ba wai kamun ƙafa nake yiwa yaya na ba a'a am here acting like a sister to you saboda na san
Umma zaki faɗawa damuwar ki but ba lallai bane ta feɗe maki komai akan rayuwar ki ba kamar yadda ni
zan sanar da ke ba just think about our conversation before you make the decision humm"?girgiza mata
kai ta yi dan bata sani ba sai yanzu da aka sanar da ita,a yanzu take jin kamar tana da wani abu a ran ta
wanda bata tsammanin zata iya sharing nasa da kowa sai mutum ɗaya who could he be?is it Zaid?did
she love him kamar yadda ake faɗa?yin wannan tunani na ƙarshe ya sa ta ɗago idanun ta ta ɗora su kan
Bahajjatu sai ta kasa furta komai illah kallon da take bin ta da shi daga bisani ta numfasa ta ce

"Nagode Baha nagode da shawarwarin da kika bani nagode da kulawar ki gare ni indeed you are a
friend and a sister to me a da na yi yunƙurin sanar da Umma danuwa ta saboda Ammi 48hours ta bani
dan yanke shawarar maganar da muka yi da ita but you coming at the appropriate time da nake cikin
buƙatar shawarar wani ya saka ni jin kai na as the most luckiest kuma inshaAllah i will follow my heart
because i was a witness akan maganar Zaid da Asma'u,ko ba komai i don't think i will allow her to marry
him koda ban aure sa ba bana jin zan iya zuba ido in kalle sa yana auren yarinyar da ta so ganin bayan sa
dan da ita aka mai wannan abin Baha ita ta nuna wa Mudan hanyar da muka bi har suka biyo mu suka
mai wannan abin sannan kina tsammani zan kyale ta ta aure sa??i can't i just can't bear to see him
leaving with that hippocrate chameleon she is a deceiver he trusted and believe in her but she went
right behind his back and stabbed him kina ganin wannan ta cancanci zama abokiyar rayuwar Zaid?ko
ba'a faɗa ba yarinyar da bata da tsarin nan za'a bar sa ya aura"?kukan da ya taso mata ne ta fito da shi
dan abin na ƙona mata rai sosai.



Rarrashin ta Bahajjatu ta ke yi a lokaci guda tana mamakin irin mummunar so da ya kama aminiyar ta
wanda yake fizgar ta ta ko ina amma ita ɗin ta ƙi yarda da hakan hasalima

26 / 74