Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
tara saura kuma da ciwon kai ya
farka dan tun yana tsammanin har ya gaji ya kwanta dan ya san by now iyayen sa sun gano asalin abin da
ya faru but he pray that Bilkisu hasn't told Ammi about their little mighty secret oh Allah..
Tashin farko bai tsaya ba ya nufi ban ɗaki yayi wanka ya fito ya zauna yana shafa cream a jikin sa brain
nasa sai pictures ɗin ta yake kawo mai amma ya kasa gane abin da ya hanasa dakatar da ita daga tafiyar
da tayi ta baro sa,.take kuma zuciyar sa ta bashi amsa da
"Why will you exhaust your time thinking about her,ai da ƙafar ta ta fita again kafin ta fita sai da ta yi
cursing naka and she went ahead and slapped you kana mijin ta humm in ma ka cigaba da tunanin ta
kenan kana supporting violence ɗin ta just let her be for the main time in ta sauko sai kuyi settling"..
Wannan tunanin ne ya ƙarfafa masa gwiwa har ya gama shafa cream ɗin sa ya yi sauran lakuce lakucen
da zai yi sannan ya ɗauko best traditional attire nasa wato kayar mallam bahaushi,baƙar shadda ce mai
shara shara kamar boyel material,ya saka inner white singlet sannan ya saka kayan sa,hula ya ɗauko mai
adon silver colour pattern ɗin kuwa baƙa ce,agogo mai baƙar fata ya saka ta brand ɗin Gerlad genta
takalmin Salvatore Ferragamo ya saka black colour bayan ya gama shirin sa ya bi adon nasa da turaruka
masu ƙamshi a gaban mirror ya tsaya ya gyara sajen sa sai ya fito dal kamar wani ango sabon aure..
Cikin ƙarfin sa da kuzari ya baro ɗakin sa ya nufi ɗakin Ammin sa yana ɗan jin ɗar ɗar amma yana ganin
in har bai sanar da ita gaskiyar lamarin ba ba zai sami sauƙin abin da ke damin sa a ran sa ba at least ko
scolding nasa tayi ya fi ta yi ignoring nasa dan share sa da tayi ba ƙaramar damuwa bane a gare sa sam
baya son damuwa ya so a ce Bilkisu ta fahimce sa sun yi maganin damuwar su amma sam bata ba sa
sarri ba dan shi yanzu ko wuƙa zaka saka mai a wuya ba zai iya faɗin ga takamammen laifin da ya mata
ba shi ya rasa dalili behind her possession sam bai ji daɗin abin da ya faru tsakanin su ba a daren nan..
Sallama ya doka a bakin ƙofar ɗakin ya dakata yana jiran a mai iso,bata biye masa ba har sai da yayi sau
uku sannan ta ce da shi ya shigo.
Kamar munafiki haka a ɗarare ya shiga ɗakin nan ƙasa kusa da ƙafar ta ya zauna yana mai duƙar da kan
sa ƙasa dan sai ya ji kunya da nauyin Ammin ya mamaye sa da wani kalma zai yi amfani wurin yi mata
bayanin shi kan sa bai san abin da yayi yiwa Bilkisun ba but ya san ita ɗin mahaifiyar sa ne and he knows
for sure son da take mai bata yiwa siblings nasa dan haka ko ya mata bayani zata fahimce sa tayi
preferring masa solution..
Da ɗan guntun confidence ya gaida ta
"Ina kwana Ammi"fuska ba yabo ba fallasa ta amsa cikin sakin murya
"Lafiya ƙalau my boy how was your night"?mamaki ne ya kama sa me hakan ke nufi..,,Ammi bata gano
matsalar ba ko kuma har yanzu babu wanda ya sanar da ita ne,,she is nice to him ya ji mamaki...
"Lafiya Ammi"daga haka sai yayi shiru yana tunanin ta ina zai fara maganar ko ya ma zata ɗau maganar
bai sani ba.
Kusan minti ɗaya bai iya furta komai ba haka zalika itama Ammin bata ce da shi komai ba tana jiran
sa,.ganin Ammin bata mai maganar komai ba haka bata ɗauko maganar sashen shekaranjiya ba sai yayi
tunanin kawai sanar da ita...
"Ammi am sorry..am so sorry"..kallon sa tayi ta ɗan buɗe idanu tana faɗin
"Sorry?sorry for what Zaid"?Ammi ta gama ɗaure sa da jijiyar jikin sa wannan tambayar na nufin ya buɗe
baki yayi mata bayanin komai a wuce wurin
"Ammi i couldn't take care of your flower ki gafarce ni"sai kuma ya riƙo hannayen ta cikin nasa ya
camza poaition daga zaune zuwa tsugune gwiwowin sa ƙasa kamar mai nemar yafiyar ta.
Cikin jimami ta ce
"Zaid ka saka ni cikin loko ban fah gane inda zamcen ka ke nufa ba"!!duƙar da kan sa ƙasa yayi dan ya
rasa ƙarfin kallon ta kunyar ta yake ji sosai..
"Ammi Bilkisu ta yi fushi da ni...,ranar da muka dawo ba tare muka dawo ba,a chan ta baro ni ita kuma ta
dawpmo sai daga baya na dawo..., nayi tunanin zata tafi chan gidan ne shi yasa nikuma na kasa tafiya
gidan dan kunyar ki nake ji ban san yadda zaki ɗauki magana ta ba but believe me Ammi na ba zan maki
ƙarya ba ban san abin da na ma Bilkisu ba kawai fushi ta yi da ni ban san laifin da na mata ba trust me
Ammi i tried so hard ta tsaya muyi magana but she didn't listen to me"zuba mai idanu tayi tana kallon sa
kamar bata san da zaman labarin ba sai yanzu da yake sanar da ita,ƙala bata ce da shi har sai da ya kai
aya sannan ta buɗi baki kamar abin ya bata mamakin nan ta ce da shi
"My boy toh ni kuma mai ya shigo da ni cikin matrimonial affairs ɗin ku?uhum?you see..,shi dama
auren haka yake dole ana samin matsaloli dan haka is not a big deal ba wani issue bane you can solve it
yourself,ka ga tun ɗazu Abban ku ya tafi office kuma ya kamata in tafi dubo sa dan i have start missing
him already okey,let me get going"tana gama faɗar haka ta ɗau car keys dama cikin shirin fita take
shigowar sa ne ya sa bata fitan ba.
Abin da Ammi ta mai yana iya kiran sa shaguɓe dan yi mai hannun ka mai sanda ta yi sam bai zaci haka
response ɗin ta zai kasance ba sai gashi ta bar sa guiltiness ya gama da shi kenan.
Cikin zuciyar sa ya ce
"Wannan ai shine iya ruwa fidda kai" ɗin,Ammi ta gama da shi yana tunanin in ya mata bayani zata yi
reasoning da shi sai gashi ta bar sa what will he do..
"My boy bara na tafi take care ko"!!murmushin ƙarfin hali yayi daga haka ta sa kai ta fita shima sai ya
tashi cikin azama ya biyo bayan ta a yadda ya so abin ya zo mai bai zo mai a haka ba dan so yayi da Ammi
ta fahimce sa sai ya mata maganar tafiyar da yake son yi zuwa koma dan har mafarkin Asma'u yayi cikin
baccin sa na daren jiya wai tana mai kuka tana neman taimakon sa shi yasa da ya tashi a yau ya ƙudiri
aniyar tafiya Yola da sai wani satin ya so tafiya amma mafarkin da yayi da ita sai ya yanke shawarar tafiya
yau kawai in ya so sai ya kwana a chan dan yana ji a jikin sa kamar babu lafiya..
Tare suka sauko har ƙasa ta mai bye bye shi kuma ya zauna nam falon yana tunanin yadda zai ɓullowa
lamarin tsakani da Allah ji yake in har bai tafi ya ga yarinyar nan ba ba zai iya samin sukuni ba,ajiyar
zuciya ya sauke ya kirawo mai abincin su ya ce da ita ta kawo mai breakfast shi kuma ya shiga laluɓar
layin Dr Hussain dan ya san by now yana chan yana hutun sa.
Sau biyu yana kiran sa sai a karo na ƙarshe ya ɗaga cikin tsokana ya ce
"Na baby doctor ba da kanka a sare in ka koma gida ka ce da Ammi ya ɓace"dariya yake yi a yayin da
yake mai wannan tsokanar shi kuma Zaid ɗan murmusawa yayi yana kuma tuno dargar da suka yi shi da
ita a shekaranjiya tunowa yayi da yadda body structure nata yake in ba dan yanzu da ta ƙara weight ba
very tiny amma mighty,kuma tunowa yayi da daren su wanda ya rasa matsayin da zai ba wa wannan
dare cikin zuciyar sa dan har yanzu ya kasa tantance ma'anar daren nan ko da mai zai wa daren laƙabi shi
bai sani ba..
"Hey na Bilkisu"sai yayi tsirit ya dawo daga tunanin da yake yi ya ce da shi
"Good morning Hussain"amsa mai yayi da
"Morning babyn Ammi"dariya yayi kafin ya ce
"Hey kar fah ka manta na ajiye mata dan haka na fi ƙarfin a ce da ni baby"dariya sosai Dr Hussain ya mai
kafin ya ce.
"Toh na ji na Bily goga"dariya suka yi at the same time wani banzan tunani Zaid wanda ya saka sa cige
lips ɗin sa yana girgiza ka yana murmushi sai ya shafo sajen sa yana jin nishaɗin yanayin da yake ciki dan
hasashe mai tsanani yake yi duk hankalin sa ya tafi ga wannan tunanin ya manta shaf akan waya yake..
"Zaid kana nan kuwa"?ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce cikin kwanciyar hankali dan hasashen da yayi
ya saka hankakin sa kwanciya
"Guy akwai damuwa fah"sai yayi shiru hakan ya saka Dr Hussain saurin tambayar sa
"Damuwa kuma?wace irin damuwa kuma Zaid"
"Huh"ya furzar da iska daga bakin sa yana jujjuya maganar a ran sa kafin ya furta
"Menn,Bilkisu has gone mad for the past 2 days"...
Abin ba ƙaramin dariya ya ba Dr Hussain ba wai she has gone mad
"Kai fah ɗan rainin wayo ne Zaid,matar taka kake ce mawa tana hauka?anya ba tare kuke haukar ba ma
kuwa"?abin ya ba Zaid dariya dan haka ya ce
"Hussain ba fah wasa nake ba.,fushi fah sosai Bilkisu ke yi da ni kuma wallahi wallahi ban san me na
mata ba ainihin laifin da na mata ban sani ba"!sai a sannan Dr Hussain ya natsu ya ba da Zaid hankalin sa
"Wai da gaske kake kuna da matsala tsakanin ku"?sai kuma Zaid ya ga rashin dacewar hakan ko ba komai
bai kamata ya faɗi sirrin sa ga wani ba aure ya wuci gaban wasa dan haka zai barwa kansa damuwar sa in
yaso in ta sauko sai suyi settling kan su dan hakan zai fi.
"Don't border manta kawai"abin mamaki sai Dr Hussain ya ce
"No Zaid gaya min mana"girgiza kai Zaid yayi kafin ya ce.
"Am serious ka manta kawai yanzu ina kake"?girgiza kai Dr Hussain yayi yana jimamin rayuwar Zaid
mutum ya ɗaurawa kan sa izza kana tattare da matsala da damuwa amma ka ce ba zaka yi sharing da
wani ba sai kai kaɗai Allah ya shirya mai abokin nan na sa..
"Ina gida na"sai ya ce
"Wani gidan naka"cikin rashin tunanin komai ya ba sa amsa
"A nan yola"da sauri ya tashi daga jinginar da yayi da kujerar yana faɗin
"Alfarma zaka min kuma kar ka ce a'a please Hussain"sai yanzu Dr Hussain ya gano bakin zaren
Goddamn it bai so hakan ba dan har shi kan sa baya son alaƙar sa da Asma'u bare yanzu ma da abubuwa
suka kacame masu da matsalar da ta kunno kai gidan su Asma'un dan komai a kunnen sa tun daga rashin
mutuncin fyaɗe da Mudan ya mata har kawo ga labarin cikin da ke jikin ta duk yana sane hakan ne ma ya
sa yake son nesantar Zaid da ita
"Hello Hussain kana nan kuwa"??duk a dame yake
"Ehh....ehh...ina nan..errmmn..ka sani..yanzu dai ka bari anjima zamu cigaba da magana ka san yanayin
mutum mai iyali ba sai na maka bayani kaima ka san yanayin ai"shashantar da maganar yayi dan baya so
Zaid ya zurfafa cikin zance kwata kwata baya son ya ɗauko masa maganar Asma'u..
Cikin ƙosawa Zaid ɗin ya ce.
"I know that you wanna dodge me and my questions amma ka sani in baka tsaya mun yi maganar nan da
kai ba yau ba sai gobe ba zaka gan ni a yola am serious"..
Iska ya furzar daga bakin sa kafin ya ce
"Zaid you won't enjoy any thing cikin bayanin da kake so na maka dan haka kawai ka bar maganar nan
dan rashin jin sa ya fiye maka allhairi"shiru Zaid yayi kafin ya ce
"Wani abin ne ya faru da Asma'u"?wai shi Zaid ba'a iya shigar da shi ne?toh ko ma dai menene ba zai ji
komai daga gare sa ba.
Pretending yayi wai baya jin sa sosai ƙarshe ma kashe wayar yayi yayi saurin sakawa a flight mood..
Ba ƙaramin ɓaci ran Zaid yayi ba kenan wasa da intelligence nasa Dr Hussain yayi,bin kiran ya rinƙa yi
kamar marar hankali amma bai zuwa abin ya ƙona mai rai wurgar da wayar yayi saman kujera yana mai
jin ba daɗi cikin ran sa abincin da aka kawo masa ma har ya fara hucewa kallon abincin yayi ya kalli
agogo hannun sa ya ga har goma yayi sai ya ɗau slice ɗaya na toasted bread ɗin ya ɗauka ya kai bakin sa
yayi biting ya ɗau kofin ginger tea da aka haɗo mai ya kurɓa daga haka ya tashi ya nufi hanyar waje yana
kiran mai aikin ta zo ta kwashe kayan abincin..
Saurin ƙarasawa yayi zuwa wurin motar sa yana zuwa ya buɗe ya shiga ya tayar da speed ya ƙarasa
zuwa gate ɗin yana danna horn da azama mai gadin ya buɗe mai gate ɗin yana mai gaishe sa amma bai
amsa masa ba sai ɗaga mai hannu da yayi.
A tsiyace ya figi motar ya bar gidan har yayi nisa da gidan nasu kaɗan sai ya dakata yayi reverse ran sa a
ɓace ya juya kan motar ya dawo street ɗin nasu yayi horn a gate ɗin su Bilkisu sai aka buɗe gate ɗin
ƙarasa shiga cikin gidan yayi da sauri yayi parking motar ya tsaya for a while dan baya so ɓacin ran sa ya
fito sarari.
Buɗe motar yayi daidai da shigowar motar su Jamil cikin gidan dan haka tsayawa yayi har suka ƙaraso
shi da matar sa.
Ganin Zaid ɗin ya saka sa tunowa da gargaɗin da aka kashe masu akan kar su kuskura su biyewa bayanin
da ɗaya daga cikin su zasu yi su bari har a kammala meeting ɗin kafin a san abin yi,tunowa da hakan ya
sa gabaɗayan su sake fuska kamar babu komai..
Suna ƙarasowa da fara'a saman fuskar su da zuwan sa ya miƙowa Zaid hannu suka yi musabaha ita
kuma Zainab ta gaida Zaid ɗin tana mai ƙara yi masa fatan samin sauƙi ya amsa haɗe da yi mata godiya
daga haka ta riƙo hannun Jamil ɗin sama sama tana mai cewa
"Love,sai ka ƙaraso ko"?da kai ya amsa mata suka ma junan su murmushi tayi gaba ta bar su tsaye nan
suka jingina da jikin motar a nan suka kuma gaisawa properly in a formal way sai Zaid ɗin ya tambaye sa
"Hutu kake ne na ga kana gida"gyaɗa kai yayi kafin ya ce
"Yeah ina hutu ne but very sokn zan koma"gyaɗa kai yayi ya shiga tunanin ko dai ya sanar da Jamil ɗin
ne maybe ya fahimce sa.
Ai kuwa babu second thought ya fara mai maganar kamar ana buɗe mai baki ana saka mai maganar
"Jamil i know Bilkisu is your sister aa kayi haƙuri ka fahimce ni na yiwa Ammi bayani but bata fahimce ni
ba"Kallon sa yayi irin me ya faru ɗin nansai ya sunkuyar da kai ƙasa ya ce
"Bilkisu na fushi da ni kuma nayi nayi ta sanar da ni laifi na amma bata saurare ni ba kuma sosai ina son
jin damuwar ta but tayi distancing kan ta da ni ban san ya zan yi ba can you please do something about
it"??ɗago kan sa yayi sama ya saka yatsar sa ɗaya bisa bakin sa ɗaya a haɓar sa ya shiga girgiza mai kai
yana faɗin
"Nop..., i can't Zaid am so sorry...shi auren dama haka yake ana samin matsaloli daban daan but dole
ma'aurata su koyi yadda zasu rinƙa handling matsalolin su ai is normal to have wife-husband problems
zaku iya handling da kan ku"..yana faɗin haka ya sauke hannun sa ya saka a aljihun sa ya ce
"Ka ga har time ya tafi kiran Umma ne ya tsayar da mu if not da mun tafi inda zamu tafi kasan yau
juma'a weekend hangout ne we gonna dine there"!!..ɗage mai gira yayi haɗe da kashe mai ido ɗaya
yana murmushi yayi ciki abinsa..
Toh shi yanzu me families ɗin nan ke nufi ne da shi?ya wa Ammi magana tayi ignoring nasa yanzu kuma
ya wa Jamil magana shima ya share sa me suke nufi ne?
"Ai duk ita ta janyo mana had it been ta tsaya mun yi magana mun fahimci juna all these wouldn't have
happened"a zuciyar sa yayi wannan maganar.
Tunowa yayi da ya kamata ya tafi yayi booking fight na gobe dan yana son tafiya yola if possible ya
dawo a goben he just wanna see Asma'u ya kuma san state of health ɗin ta..
Ɗago kan sa yayi sai ya hango wata kamar Bilkisu,ƙara girman idanun sa yayi sai ya ga ita ɗin ce dai sai
ya shiga waving nata da hannu sarai tana kallon sa dan tashin ta kenan daga bacci ta fito nan ɗin
receiving fresh air dan har ta ce a kawo mata abincin ta nan sama ta ci dan bata ci na safen ba gashi
aunty Zee bata zo ba sai abin ya mata yawa tsabar sakawa kan ta abin ma har mafarkin sa sai da tayi
sama da biyu a one single sleep..
Haɗa ido suka yi sai ta juya ta shiga tafiya daga ƙasan ya rinƙa kiran ta amma ta mai banza shi kan sa ba
zai ce ga abin da yayi prompting nasa ya shiga biyo ta ba sai ganin kan sa yayi yana tafiya cikin sauri har
da ɗan gudu gudu.
Ko da ya shiga zuwa main parlor bai ga kowa ba dan haka yayi saman da saurin sa yana zuwa tana
banging ƙofar ɗakin amma ƙarfin su ba ɗaya ba da azama ya tura ƙofar ya buɗe ya shigo kamar an jefo sa
tana ganin haka ta juya mai baya sai ya juyo ta inda ta mayar da fuskar ta ta juya kuma shima ya juya
zata kuma juyawa ya riƙo ta da ƙarfi ya haɗa ta da jikin sa he can't believe that Bilkisu is actually losing
her mind.
Masifa zata fara yi mai kamar ba yunwar ganin sa take ba,rigar ta magana yayi cikin zafi
"Not a single word from you yau ni zan yi maganar ke kuma ki min shiru and you have to listen to
me"fincikewa ta shiga yi amma ya ƙi sakin ta zata kai bakin ta dan kuma yi mai cizo ya ce
"Kika kuskura kika cije ni zaki gane"ɗago kan ta tayi tana hararar sa shi kuma ya rinƙa kallon ta so yake
ya gano matsalar ta amma bata bar sa ya gano hakan