Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
mai da ita shi ya sa yana idar da
sallar ya nufo gida lokacin har gari ya fara wayewa haske ya fara bayyana sai ya ɗan ƙara saurin sa ya iso
gida,gaisuwar su da mai gadin sama sama ne burin sa ya isa ciki ya tayar da ita dan lokacin sallah na
tafiya kuma ya san har in ba tayar da ita aka yi ba ba tashin zata yi dan bacci mai nauyi ne ke ɗaukar ta..
Kamar ya sani,yana shiga ɗakin tana gyara kwanciyar ta dan cigaba da baccin sai da ya bar ta ta sami
mintuna biyu a haka sannan ya zo har saman gadon ƙafar sa ɗaya dogare da gadon ta ƙasa ɗaya kuma ya
ɗora bisa kan gadon ya duƙar da kan sa ƙasa kaɗan ya yaye blanket ɗin ta wuyan ta ya kai lips ɗin sa ya
manna a wuyan ta ba kiss ya mata ba amma ya ɗau lokaci da lips ɗin sa a nan tun tana share abin har ta
ji ba ta iyawa dan dole ta buɗe idanun ta ta juya zuwa direction ɗin sa cikin kula ya kalle ta ya ce
"Lokacin sallah yayi baby tashi ki yi"!!shiru tayi na wasu seconds kafin ta fara yunƙurin tashi jikin ta duk
ciwo yake mata dan baccin da take yi ba na daɗi bane kawai dai ba yadda zata yi dan duk lokacin da ta
kwanta baccin dolen a takure take yin sa sai ta tashi duk jikin ta ya rinƙa mata ciwo tana jin zafi but tana
da niyar zuwa asibiti a duba ta dan ita ta kasa yiwa kanta diagnosis mai ma'ana at first ta yi tsammanin
tunanin Zaid ne da ta sakaea kan ta sai ta rage tunanin amma still babu wani canji sai ta canza diagnosis
ta ce maybe zaman wuri ɗaya ne dan in ba wani aiki ne ya taso da za'a kira ta yi ba shima da ta kammala
take komawa gida,bata yin komai but still abin sai ya girme mata fiye da tunanin ta dan haka ta yanke
shawarar zuwa ganin wani likita maybe zata sami lafiya..
Tana dire ƙafar ta ɗaya ƙasa yayi saurin zagowa ya riƙo ta yana ce mata
"Easy...slowly"!duk hankalin sa ya koma kan ta sai taka tsantsan yake yi da ita abin sai ya saka ta
wondering me yake ta damuwa da ita har haka,ta san dai ba sauraron sa tayi ba but why all the caring
stuffs..
Hannun ta cikin nasa ya ɗaga ta ta tashi da ƙafafun ta sai ta zame hannun ta ta wuce ciki ta yi brush
haɗe da yin alwala tun kafin ta fito har ya ɗauko mata hijabin sallah ya shimfide mata sallaya ita kawai
yake jira.
Wow is this guy for real!?tambayar da ta wa kanta kenan ganin yana ta abubuwa so gentile ta manta
shi ɗin haka yake dama chan yanayi ne da rashin fahimta ya sa ta kasa gane hakan sai yanzu da aure ya
haɗa su ƙarƙashin inuwa ɗaya..
Tana hawa kan sallayar ta yi kamar zata tsugunna ta ɗau hijabin sai ya riga ta ya ɗauko ya miƙo mata ta
karɓa tana mamakin sa sai dai bata iya cewa komai ba.
Tada sallar tayi shi kuma ya ɗan kishingiɗa yana kallon ta har ta idar da sallar tayi addu'ar da zata yi
idanun sa na kan ta tana gama addu'ar kawai ta kwanta nan ta cigaba da baccin ta dama ba isar ta baccin
yayi ba gajiya ne ya saka ta farkawa.
A ɗan hanzarce ya tashi ya ƙura mata ido me ke damin ta ne wai haka?baya jin tsetse fly na yawo a
gidan bare yayi tunanin baccin ta na da nasaba da cizon sa toh anya kuwa lafiyar ta ƙalau...
Tasowa yayi ya zo inda take kwancen ya tattare mata hijabin ya gyara ta yadda zai rufe ta da kyau shi
kuma ya ɗan raɓa ya kwanta a gefen ta yana kallon ta sai sharar bacci take yi.,hannun sa ya sagala da
nata hannun yayi creating interlock ymda yatsun su ya kuma matso da fuskar sa kusa da nata ya kwantar
da kyau ta yadda duk wani abin da zai yi zata jiyo sa itama haka..baccin ne dai ya kuma ɗauke su.
_8am_
Sai yanzu suka farka daga baccin daga ita har shi sai da jikin su ya gaya masu kwanciya a ƙasa bayan
sanyi ga ƙarfi da rashin taushi dan ma da darduma kenan,ganin sa kwance kusa da ita sai ya kuma bata
mamaki ta kasa gane shin gaske ne ko faking yake yi..
Ita ta riga sa tashi tana miƙa shi kuma daga kwancen ya ƙare mata kallo ba komai miƙar ta ke haddasa
masa ba illah sha'awar ta amma ba halin manifesting dan sai tayi tsammanin dama dan hakan ne ya ke
mata abubuwa yake kuma bata kula..
Tana sauke hannayen ta hamma ya biyo baya sai yayi saurin ce mata
"Hungry"!?gyaɗa mai kai tayi sai yayi saurin tashi yana faɗin
"Ina zuwa ki bani 15minutes okey don't go anywhere"!!da kai ta amsa mai yana gama faɗin haka ya
tashi yayi waje ita kuma ta tashi daga saman sallayar tayi cikin toilet dan yin wanka sai dai babu wasu
abin buƙatar ta dan haka sponge ɗaya da ta hango da shi tayi wankan ko cikin bathtub ɗin bata yi gigin
shiga ba dan ta san tana shiga bacci ne zai ɗauke ta.
Cikin kwanciyar hankali tayi wankar ta ta saka rigar wankar sa dan ya fi ƙarfin ta lulluɓe kan ta tayi da
towel ɗin sa ta fito kan ta tsaye bata yi tunanin ganin sa cikin ɗakin ba sai dai what shocked her shine
tana turo ƙofar ɗakin ta gan sa tsaye babu riga sai boxer da yake sanye da shi,tun daga ƙasa ta fara
kallon sa tana kallon ƙafafun sa da ke ɗauke da suma kwance har wani gazar gazar suke yi wanda ta ji
tsigar jikin ta ya tashi at once,kaɗan kaɗan ta rinƙa kallon sa har ta kawo jikin sa ta rinƙa kallon bare
chest ɗin sa da ke a ɗan buɗe ta kalli right and left side na ribs ɗin sa ta ga ABS packs ɗin sa sai ta tsaya
tunanin ita ce ta ɗauki nauyin sa a daren rannan?she can't believe it ta san in aka bar ta da shi a rightful
senses ɗin ta toh lallai zata mai kuka wataƙil har da shessheƙa dan shi ɗin ba na wasa bane..
Yana kallon ta tana ƙare mai kallo yana bin ta da ido har ta gama ta sauke idanun ta ƙasa ta shiga
nemawa kan ta hanyar tafiya bai yi gardama ba ya ja gefe ya bata hanya,raɓawa tayi ta gefen sa ta wuce
sa shi kuma ya shige toilet ɗin dan yin wanka..
Da wani irin full force ta zauna bisa gadon tana maganganu da iya gaskiyar ta
"Toh kuma menene na cire kayan jikin sa alhalin ya san ina ciki kuma ma ni ba ce mai nayi ina buƙatar
kallon jikin sa ba in ina son kallon jiki ne ga nawa jikin ba sai in kalla ba mtsw"ta ja tsaki sannan ta hau
dube duben inda zata ga cream dan ga dukkan alama nan ɗin ba ɗakin ta bane nasa ne saboda babu
kayan gyara irin na mata,.
Hango cream ɗin tayi saman abin shafe shafe sai ta kai hannun ta ta ɗauka ta matso ta shafa a ƙafar ta
tana shafawa tana tuno jikin sa da ta gani ba kaya wani bin tayi tsaki wani bin ta girgiza kai..
Shafe jikin ta tayi da cream ɗin sannan ta koma ta zauna tana jiran fitowar sa dan ya kai ta inda zata
sami kayan sakawa,.
Abin dariya tana kwantawa kawai sai bacci wannan abu ya ba Zaid mamaki ba kaɗan ba dan yana ta
kiran ta akan ta kawo mai towel amma bai ji amsbi ba sai ya keƙi da kansa only to see her
sleeping,ƙarasa fitowa yayi ya duba ya ga towel ɗin gefen gadon a ƙasa ɗagawa yayi ya ɗaura sannan ya
goge jikin sa da ƙaramin towel da ke hannun sa,..
Shirya kan sa yayi cikin kaftan grey colour ya fito da ƙwarjinin sa fili matsalar ɗaya ce rashin gyaran
fuskar da bai yi ba kuma shi ba wannan ne damuwar sa ba damuwar sa shine Bilkisu ta cigaba da zama
da shi kar ta ce gida zata tafi dan tana faɗin hakan zasu ɓata because he won't let her go home..
A yau ɗin ma abincin da ya saka a haɗa masu ɗakin ya shigo da shi ya ajiye bisa wata madaidaiciyar
table dake ɗakin sai ya fita ya koma ɗakin ta ya binciko mata wata native,atamfa ce mai zanen tsuntsu
an mata ɗinkin doguwar riga hannun ta dogo amma an tsaga daga bakin hannun har zuwa tsakiya jikin
rigar kuwa a riƙe yake wato straight gown wuyan rigar kuma ta ɗan sauka ƙasa kaɗan off shoulder kalar
mai fuhu ce sai ya haɗo mata da mayafi mai kalar zanen tsuntsun ya haɗo mata da kayan kwalliya da
accessories da zata haɗa da kayan..
Jan ƙofar yayi ya rufe ya dawo nan ɗakin ya gan ta still baccin take yi sai yayi murmushi kawai ya wuce
ta ya ajiye kayan sannan ya shiga tayar da ita
"Hey....sleeping beauty..,wake up"yana gama faɗin hakan kamar an tsungule ta ta buɗe idanun ta dan
dama baccin ba nisa yayi da ita ba.
Cikin miƙa ta tashi tana hamma sai ya ƙura mata idanu so yake ya duba wani abu a jikin ta dan bai yarda
da yawan baccin nan da take faman yi ba tun jiya har yau a ƙalla sau uku kenan tayi bacci a yau ɗin nan
cikin safiyar nan what could possibly be the reason..
Zuba masa ido tayi tana girgiza kai irin me kuma ɗin nan.,a ɗan firgice ya ce
"Your clothe...,gashi nan ki saka in mun karya zamu fita ina so ki raka ni wani wuri ne please"abin da ta
lura da shi shine yawan amfani da kalmar _Please_da yake yi kamar wanda yake ƙarƙashin ta yana
nemar amincewar ta,bata ce mai komai ba ta saka hannu ta karɓi kayan sai kuma ta kasa tashi tana jiran
ya matsa shi kuma da yake ɗan duniya ne sai yayi ignoring irin bai gane ma'anar zaman ta har lokacin
ba,abin ya harzuƙa ta so tayi ta hukunta sa by not talking to him for 72hours dan ta tabbatar ko da gaske
ya yarda da auren su kokuma pretending yake yi amma yadda yayi kunnen kurma sai ya saka ta haɗe
girar sama da ta ƙasa dan kar ma ya fara tunanin raina ta
"Ina buƙatar sirri"!!..sai ya shiga jujjuyawa yana kallon gefen sa wai so yake ya ga baren da yake ɗakin
apart from the two of them,tsayar da fuskar sa yayi a daidai nata fuskar sai ya saka silly face ya shiga
kaɗa mata kai yana faɗin
"Sirri"???kallon sa tayi ta gyaɗa kai sai ya ce
"Amma ai babu stranger a nan daga ni sai ke...wani sirri kuma kike nufi"??sarai ta san ya gano abin da
take nufi amma dan shi ɗin ɗan rainin tunani ne sai ya sakankance yana nuna shi bai gane me take nufi
ba..
Kyaɓe fuska tayi ta saka fuskar cat tana faɗin
"Ni dai ka fitar min dan sarai ka fahimce ni ka san me nake nufi"!!shagwaɓe muryar ta tayi sai ya riƙe
dariyar sa ya ce
"You are funny,,sirri??where??here??just the two of us and you still need privacy or what"??ɓata fuska
tayi tana shirin yin kuka ta ce
"Ni dai ka rabu da ni i never intended talking to you but you made me did it"ta ƙarasa tana mai juyar da
kan ta gefe sai ya tsinci kansa cikin yanayin son raha da tsokanar ta dan haka ya wani matso kusa da
kunnen ta yayi ƙasa da murya kamar mai jin bacci ya ce
"Na fah san komai,,na taɓa nan,na taɓa nan,na yi wasa da nan,kuma kema kin ji daɗin hakan,har ce min
kike _Zaid taɓa nan,Zaid taɓa min nan_ kika rinƙa nuna min inda zan taɓa tun bana so har kika saka ni yi
shine kuma yanzu zaki ce kina buƙatar sirri?me ya rage ban gani ba ban kuma sani ba?huhh"?tun da ya
fara maganganun sa ji tayi kamar an tsoma ta cikin Electric Convulsive machine an kuma saka vibrating
speed ɗin as high as 200/300,zirr zirr ta rinƙa ji madaɗin ta ji haushin maganar nasa sai tayi ending up
falling for him again,bata tashi jin haushin sa ba sai inda ya ce tana ce mai ya taɓa nan ya taɓa nan,ita
yaushe aka yi hakan da ita..
A zuciye ta ɗauko mini trow pillow dake saman gadon ta mare shi da shi haɗe da jefa mai,..
Burin sa ya cika ya saka ta hawa kan hanyar da yake son saka ta dan haka da dariyar sa cikin son cigaba
da tsokanar ta ya ce
"Common baby doctor,ai ba ƙarya na yi ba a hakan ma fah ban sanar da ke ire iren noises da kika rinƙa yi
ba kenan"ya buɗe baki dan cigaba da magana sai ya ji saukar hannun ta saman bakin sa tana mai girgiza
mai kai da fuskar yayi haƙuri yayi shiru sai ya tsaya ya ƙura mata ido yana jin wani abu game da ita,ya
shagala da kallon halittar ta yana yaba kyakyawar fuskar ta da ƙwayar idanun ta da yake roƙon Allah ya
sa ƴaƴan sa su yi gadon sa dan ba kaɗan ba yake admiring eye balls ɗin ta,da ta ga yayi shiru yana bin ta
da kallo sai ta ji ta tsargu har ta kasa cigaba da kallon sa ta cire hannun ta daga bakin sa cikin sauri ta
juya mai baya tana faɗin
"Am sorry"!!. synchronously ya tako har daidai space dake tsakanin ta da shi ya cike space ɗin ya kai
hannun sa yayi grabbing waist ɗin ta yayi wrapping hannun sa biyu daga waist ɗin ta zuwa ta gaba lower
abdominal region ɗin ta ya janyo ta baya ta haɗe da jikin sa sai suka lumshe ido at the same time suka
sauke ajiyar zuciya,gaban ta ne ya shiga yin gudun tsere kamar gudu tayi,saka fuskar sa yayi ta gefen
wuyan ta ya sauke haɓar sa daidai clavicle bone ɗin ta ya shiga brushing slowly yana lumlumshe ido,taya
sa sauke ajiyar zuciyar tayi wanda suka ɗau mintuna biyu suna a haka sai shine ya tambaye ta cikin
sanyin murya
"Don't you like and enjoy this moment"!?shiru ta mai tana jin touch ɗin nasa na shigar ta ga nishin da
yake yi daidai kunnen ta kawai rasa inda zata saka kan ta tayi sai ta kawo hannun ta ta ɗora saman nasa
hannun tana son cire hannun amma ya ƙi barin ta ta cire..
Ƙyale sa tayi tana jiran ganin iya gudun ruwan sa dan abin yana mata daɗi kawai fushin da take yi da shi
ne ya sa take shasshare sa da duk wani abin da yake mata..
Ita shiru shi shiru a tsayen da take har ta fara jin wani jiri jiri domin kuwa bacci ne ke son yin awon gaba
da ita amma ta kasa sanar da shi ta mai shiru tana jiran ganin ko zai daina ko ba zai bar ta ta saka kayan
ba.
Kamar wasa kuwa tun tana iya hana kan ta har ta kasa ba haƙura bacci ya fara ɗaukar ta dama idanun sa
a lumshe suke yana sauraron numfashin ta sai ya ji kamar numfashin ya fara canzawa saurin buɗe
idanun sa yayi ya leƙo fuskar ta sai ya ga abin mamaki "wai bacci tayi kuma"??ya ma kansa tambayar sai
yayi saurin juyo ta ta ɗan buɗe idanun ta tana son daidaita su amma ta kasa dan haka luu tayi ta faɗa a
jikin sa bacci ya shiga next stage ta cigaba da sheƙa baccin ta..
Over 60 seconds yana rungume da ita tana baccin kuma bata motsa ba izuwa yanzu kam abin ya fara
razana sa ya fara jin tsoro dan lafiyayyen mutum baya bacci haka kowani lokaci,ko dai bata da lafiya ne
take ɓoye mai..
Yin ƙasa da fuskar sa yayi yana kallon ta sai ya ga ba baccin kaɗai take ba har da riƙo rigar sa tayi tana
sauke numfashi a tsanake kamar ta daɗe bata yi baccin ba sai yanzu..
"What the heck,,why did she sleeps so fast"?ya tambayi kansa dama so yayi in ta shirya sai ya kai ta
asibiti a duba ta hala wata matsalar ce da ita amma basu damu ba..
A hankali ya nufi kan gadon da ita yana lallaɓa ta kar ta tashi,suna zuwa gadon ya kwantar da ita haɗe da
ɗaga ƙafafun ta ya ɗora bisa gadon yana mai kallon ta,zama yayi yana kallon ta kamar wata sabuwar
halitta abin na ɗaure masa kai ta yaya mutum zai rinƙa sharara bacci haka sannan in ya farka babu wata
alamar rashin lafiya tattare da shi,..
Riƙo hannun ta yayi cikin nasa yana ƙare mata kallo she is damn beautiful,innocent and so flawless me
yasa bai taɓa lura ba a baya sai yanzu da ta nesanta kan ta da shi ya daina ganin ta..
Baccin mintuna goma tayi yana monitoring nata time na cika ya hau susa mata tafin hannun ta yana yi
yana kiran ta
"Bilkisu,baby,..wake up..kin ji"!??kamar a mafarki ta ji muryar sa yana kiran ta sai ta ɗan buɗe idanun ta
ta sauke cikin nasa idanun,ɗage mata gira ɗaya yayi yana faɗin
"Let's eat abincin zai yi sanyi"!!nayar da idanun tayi ta lumshe sannan ta buɗe zata kuma rufe idon ya
tashi a 360 yana faɗin
"Not again baby not anymore tashi kar ki fara baccin nan kuma"!!kamar zata fashe da kuka haka ta tashi
dole ba dan ta so ba taya ta saukowa daga gadon yayi yana mai nuna mata inda zata zauna dan cin
abincin..
Zama tayi tana fushi tana faman kumbure kumbure kamar an mata laifi,shi dai ido yake bin ta da shi
dan abin nata gaba yake yi bacci fiye da ƙima ba alama ce mai kyau ba..
Yana zama ta ce da shi
"Ina abincin"!?saurin serving nata yayi yana mai yi mata Bismillah,janyo plate ɗin tayi gaban ta ta shiga
cin abincin tana jin baccin na fizge ta daga sama so take tayi ta kammala da abincin nan ta kwanta,yayin
da take cin nata abincin shi kuma yana kallon ta,kwata kwata bai fi rabin kashin abincin da aka zuba
mata ba ta ci ta ce ta ƙoshi zai yi magana ta ce
"Enough please i wanna sleep na ci abinci ai toh me kuma ya rage"??ta mai tambayar tana mai ƙure sa
da idanun ta sai ya hau girgiza mata kai.
Tashi tayi tana maganganu ƙasa ƙasa tayi kan gadon ta kwanta,still rigar wankan ne a jikin ta bata sauya
ba.
Bin ta da ido yayi yana nazartar ta har