Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   47 / 74

138K to 141K   out of 221.1K words

sashin zuciyar ta ne ya bata amsa da

"Ai duk laifin Zaid ne dan shi ya sa Baha tayi ma magana ta kallon wofi because ta fi kowa sanin halin
Baha ko damuwa ta gai saman fuska ta sai tayi magana amma wai ina kuka kuka sosai but Baha ta ce da
ita ai saboda ta yi kewar ta ne,yes nayi kewar ta but damuwa ta daban"...



Kallon hanyar toilet tayi sai ta miƙe ta nufi hanyar toilet ɗin da nufin yin wanka sai dai kasa yin wankan
tayi dan bayan ta kammala cire kayan baccin ta ta tsaya da nufin saukewa kan ta shower sai ta shiga
tunanin moments ɗin su ita da Zaid,.

"Ya ilahi wai nikam ya zan yi da son Zaid?ina zaman zama na rayuwa ta cikin sauƙi kawai ya shigo min
ciki ya hargitsa sannan yana son yin tafiyar sa"..tana ƙunna shower ɗin ruwan na fara zubo mata ta tuno
da unforgettable moment ɗin nan da ya mayar da ita mace sai ta ji hawaye na son zubo mata at the
same time tsigar jikin ta ya tashi ga zazzafar son sa da ke huda gaɓoɓin jikin ta..

Wannan wanka dai ba na daɗin rai aka yi sa ba dan duk saukar ruwar dake fitowa daga cikin shower ɗin
nan sai ta tuno sa mijin ta sai yanzu kewar sa ke kuma kama ta..



Sai da tayi da gaske sannam ta kammala wankar ta fito dan kar ma ta cigaba da tunanin sa sai tayi
saurin zurma doguwar rigar ta bayan ta saka inner wears ɗin ta ta ɗau wayar ta ta sauko ƙasa tana
fargabar ganin fuskar Umman ta dan it was a narrow escape for her a jiya..



Babu kowa a parlor sai ma'aikatan gidan da ke gyare wurin da aka gama cin abinci kenan har suka yi
breakfast babu wanda ya neme ta.

"Ai duk laifin Zaid ne ban taɓa experiencing fushi daga wun iyaye na da yaya na ba sai a kan ka duk wai
ba'a ga laifin da kai kayi ba sai ni ake ta blaming".

Haka ta koma ɗakin ta ran ta na mata ba daɗi,zama tayi ta kira mai masu girki ta wayar ta ta sanar da
ita abin da take so a kawo mata.
Ajiye wayar tayi bayan ta duba time aunty Zee ta ce mata zata zo yau but har yanzu bata zo ba kuma a
halin da take ciki bata da wani da ya fahimce ta sama da ita aunty Zee ɗin dan haka take ganin ta sami
hope at least ba duka family nata bane suka juya mata baya ba..



Not too long aka kawo mata breakfast ta zauna da nufin farawa sai dai abin mamaki banda tuno fuskar
Zaid a lokutan da suke cin abinci tare babu abim da take yi ƙarshe ma da abin yayi yawa sai ta hau
hasaso sa tare da ita a yanzu ma har dai fuskar sa ya fara yi mata gizo bata ankara ba ta ji abu na bin
fuskar ta ko da ta kai hannun ta sai ta ga wai hawaye ne ke bin fuskar ta sai ta mayar da cokalin ta jingina
da gadon ta ta shiga rafka kuka ba ji ba gani tana ta maganganu marasa ma'ana

"Duk kai ka janyo mana,na gama tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance yadda zamu rinƙa gudanar
da activities ɗin mu amma ka wargaza mana duk laifin ka ne duk kai ka jawo mana wannan abin yanzu
ina wannan halin amma babu kai kusa da ni duk pains ɗin ni kaɗai nake ɗaukar sa kai babu ruwan ka
baka ma san ina yi ba and i believed you i trusted you i gave you my body,my heart and my soul i
thought you will take care of it amma i was very wrong na tafka babbar kuskuren da na daɗe ina gudun
tafka sa a rayuwar aure na,my dignity my virginity i gave it all to you thinking that you will respect me
after that but sai kayi proving min cewa kai ɗin cikakken namiji ka kira min sunan wata a daren farkonna
da kai ka rinƙa faɗin kalamai masu taushi akan ta gaba na fah,gaban ido na ina kwance a jikin ka ko
shakka ta baka ji ba baka yi respecting ɗi na ba ka raba ni da mutunci na sannan ka juya min baya me ya
sa Zaid?why??why did you choose to punish us in thus hard way?sarai ka sani na ƙi jinin jin sunan
yarinyar nan amma ka rinƙa maimaita sunan ta kamar abin bautar ka"!!!..kuka take yi tuƙuru duk idanun
ta sun kumburo sun yi ɓulu ɓulu kamar an daɗa mata girmar su ba ƙaramin raɗaɗi take ji a ran ta ba dan
ta gama mafarkin washegarin daren farkon ta zai dasa tarihi mai tsafta a zuciyar mijin ta she endured the
pains of a virgin lady wacce karon ta na farko da haɗuwa da namiji zata ji raɗaɗi ta kasa riƙe zafin har sai
ta fitar da muryar ta fili amma ita ta danne ta bar wa kanta duk dan ta saka sa yin alfahari da ita amma
ga abin da ya mata bai ma damu da abin da ya mata ba ya zage ne kawai yana maganganu akan wata
Asma'u



Tsabar baƙin ciki a nan ta kwanta har baccin azaba yayi gaba da ita wanda har cikin baccin ma banda
blaming Zaid babu abin da take yi a ganin ta duk shi ya ruguza masu rayuwar auren su da ta jima tana
tanadi.

Uwa uwa ce duk fushi faɗa da rigimar da zaku yi da ita dole ta damu da son sanin lafiyar ka,.ko a jiya
danne zuciya Umma tayi ta fita harkar Bilkisun har zuwa wayewar yau da za'a yi breakfast aka ce za'a
kirawo ta amma ta hana ta ce a bar ta yarinyar da bata iya zama da miji ba ai har iyayen ta ba iya zama
da su zata yi ba dan haka ko bayan sun watse sun tafi wuraren aikin su ya rage daga ita sai ita a gidan ta
rinƙa saƙawa tana warwarewa ƙarshe dai ta yanke hukuncin zuwa ɗakin ta dubo ta in yaso sai ta ce faɗa
ta zo yi mata dan kar ma ta ɗauka ko damuwa tayi da ita.
Zuwan ta ɗakin ke da wuya sai ta gan ta kwance a ƙasa fuskar ta duk ga alamar hawaye nan sun bushe
gefe ga abincin ta nan bata taɓa ba sai kuma ta dawo jin tausayin ta she knows that she overreacted
yesterday and today amma dole ne ta nuna mata rashin gaskiyar ta ba wai dan tana ɗiyar ta shikenan ta
rufe ido ta ce zata goyi bayan ta ba as a good mother she have to correct her daughter's misconception
akan zaman ta da mijin ta..

Hawaye ne ya cicciko idanun Umma sai ta miƙe ta bar ɗakin dan ita ta san raɗaɗin kishi saboda a fagen
kishi sam Bilkisu bata kamo ta ba amma yanayin rayuwa ya sa dole ta sassautawa kan ta sai gashi duk
addu'ar da ta rinƙa yi akan kar Allah ya sa Bilkisu ta yo gadon ta sai da ta yi nata kuma har da son taɓa
mata ƙwaƙwalwa yake dan ko a baya da ita tayi nata kishin Allah ne kawai ya taimake ta ya sa har yanzu
suke tare da Prof ba dan haka ba da ba'a ma haifi Lukman ba dan her past was a hectic one sai dai yanzu
ya zamo past kuma tana fatar Allah ya yayewa Bilkisu wannan mummunar kishi da ke ɗibar ta dan
mazan yanzu basu da tabbas ba kowa zai ɗauki shashancin ɗiya mace ba bare ma a ce tana ƙarƙashin sa
sai yadda ya ga damar yi da ita..



*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*
*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim




*_Munafukan zaune masu ci da gumin wasu Allah ya tono ma duniya asirin ku amma ku sani matuƙar
muka taso ku gaba sai duniyar ta maku raɗaɗi alƙawari ne wannan.._*



*_Sannan gare ku readers ku sani babu wani littafi da yake mallakin Brilliant Writers Association da zaku
gani a ce da ku na kuɗi ne ku yarda da hakan ba,duk wanda ya ce da ku littafin Association ɗin mu na
kuɗi ne toh ƙarya yake maku dan mu bamu littafin kuɗi be warned and stay alert coz criminals get
smarter by the day.._*



*30*



Da suka shiga cikin gidan ne Hajiya Madina ta fara jin raɗaɗin sanin inda ƴaƴan su suke sai kawai ta
danne ta barwa kanta har dai suka ƙarasa shiga ciki yayin da mai gadin nan bakin sa ya rinƙa mai muimui
yana son sanar da su amma sai ya ƙyale bai yi maganar ba.

Har suka isa bedroom ɗin su gabaɗaya bata jin kamar tana tare da Dr Maher kawai calming nata yake yi
tana sauraron ta amma sam ba shigar ta zantukan nasa ke yi ba.



Zama tayi saman gadon ta rafka tagumi tana jiran jin sakamako dan jikin ta ya fara bata wani abin marar
daɗin ji addu'a kawai take yi cikin ran ta dan bata son ta ji wai tunanin ta zai rikiɗe ya zamo gaske.

"Dr,ban san me ke shirin faruwa da mu ba but ina ji a jiki na kamar ba lafiya ba"ɗan rungumo ta yayi ya
ce

"Common darling,ki daina wannan tunanin ki kyautata zaton ki please yaran nan na nan lafiya just calm
down"!!ɗan ture sa tayi kafin ta ce
"Dr baka san me ke dami na ba baka san irin tsoron da ke shiga ta ba,ni uwa ce dole in tsorata ba zan iya
sanin sukuni ko kwanciyar hankali ba har sai na ji na kuma na san halin da suke ciki"..

Ajiyar zuciya ya sauke ya buɗe baki zai yi magana sai ya ji sallamar Afzal dan haka ya bashi izinin
shigowa,.bayan ya shigo ne ya durƙusa har ƙasa sannan ya fara magana

"Abba ina ga matsalar nan ta zo ƙarshe"..cikn sauri Hajiya Madina ta ɗago kan ta tana kallon sa a rikice ta
ce

"Me kake nufi Afzal"?sai ya ce

"Na ji daga wun mai gadi shi ya sanar da ni komai ya ce da ni tun ɗazu kusan two hours da suka wuce
yaya ya dawo gida kuma a yadda ya lura da shi kamar bai da lafiya dan haka da zuwan sa ma wai ɗakin sa
ya tafi and he..."ai tun kafin ma Afzal ya kai aya Hajiya Madina ta miƙe cikin sauri da azama ta bar ɗakin
tana mararin ganin ɗan ta da ta fi ɗaukaka son sa fiye da sauran ƴaƴan ta dan irin son da take wa Zaid ko
mahaifin sa ba zai nuna mata son Zaid ba sai dai ma ya daɗa ƙarfafa mata gwiwar son Zaid ɗin son nan
nasa da take yi ha haɗu har da kwaso ta da yayi a kamanni dan komai nata bai baro ba banbancin shine
ita mace ce shi kuma namiji sai ɗan shekaru da ya fara nunawa wanda ya zamo wata ƙaramar
banbancin..



Tafiyar ma nisa take mata dan haka ta ɗan haɗa da gudu gudu har dai ta iso ɗakin na sa ta tura ƙofar
tana fatan Allah ya sa ba mafarki tame ba da in ta buɗe ƙofar zata ga wayam.

Cikin kwanciyar hankali yake baccin sa kamar bai da damuwa dan babu wanda zai gan sa a haka yayi
tsammanin baccin dole da na wahala yake yi,kamar kar ta ɗauke idanun ta a kan sa sai ta shiga takowa
tana nufo sa har ta iso gab kusa da shi ta zauna saman gadon kamar mai tsoro,a lokacin da ta zaunan ne
su Dr Maher da Afzal suka shigo dan Hakim baya nan ya tafi rounding up na karatun sa baya gidan Baha
kuwa tsabar bala'in da ta kwaso na mutanin da ke ta surutu marasa daɗin ji a wun liyafar nan ya sa suna
shiga tayi ɗakin ta ta shige bayi dan son rage zafin abin dan haka bata da masaniyar wainar da ake
toyawa.

Kallon Afzal Hajiya Madina tayi ta ce

"Ya aka yi ka sami waɗannan bayanai daga wun mai gadi"??sai ya ce

"Ammi bayan kun shigo ne na koma dan in gyara parking har zan tafi sai Luk ya kira ni akan in yi saurin
shiryawa dan mu koma station a fara yin wasu aikin dan samo inda suka tafi sai na ce da shi kar ya damu
yanzu zan fito sai yake kuma sanar da ni ai ya kuma samin kira daga airport akan a dawo a duba dan
wani jirgin yayi landing babu jimawa toh amsar da na bashi ne ya sa mai gadin zuwa kusa da ni ya ce min
_ranka ya daɗe ai kamar ina jin baƙin jamani sun iso gida_ sai na tambaye sa dan ban fahimce sa ba sai
ya warware min abin da ya faru a kan idon sa na tambaye sa ya tabbata shi idon sa idon yaya ya ce da ni
ƙwarai dan shi ma ya shigar masa da kayan sa ciki kuma tun da ya shigan bai fito ba toh shine na mai
godiya na dawo ciki na nufi sashen yaya na duba na hango sa yana bacci shine nayi saurin zuwa sanar da
ku"!!ajiyar zuciya suka sauke su biyun saumi Dr Maher ya ce

"Allah ya maka albarka Afzal"ya amsa da

"Amin Abba"daga haka ya bashi umarni da ya kirawo chan jami'an tsaro ya sanar da su abin da ya faru
sannan ya kirawo masa Baha dan yana gudun kar wani abin take ƙullawa alhalin an gan sa ya kuma ce da
shi kafin ya yi kiraye kirayen ya fara kiran Prof ya sanar da shi..

Hakan ya aiwatar ya bar ɗakin ya aiwatar da umarnin mahaifin nasa a nan shima Prof ya sanar da shi ai
an ga Bilkisu shine ya dawo ciki ya sanar da su.murna suka yi sosai sai dai suna tunanin me ya faru da
suka dawo suka nufi gidaje daban daban.

Ita kuwa Hajiya Madina har ta fara tunanin hala kunya ce ta sa suka zaɓi dawowa nan gida basu tafi
chan gidan su ba again ƙila so suke a masu bikin auren su irin a ɗauki amarya a kai ta gidan mijin ta ɗin
nan,sai wani sashe na zuciyar ta ya ce a'a fah kika sani ko wata matsalar ce dan in ba wata matsala ba ya
za'a yi a yi ta kiran su su ƙi ɗaga waya dole akwai dalili.yin wannan tunanin ne ya sa ta maido da duban
ta ga Zaid da ke kwance kallon sa take kamar an ce da ita kwace mata shi za'a yi.

Kasa tayar da shi tayi har sai da Dr Maher ya taɓa shi sau biyu sai ya ɗan motsa kaɗan da niyar gyara
kwanciyar sa sai dai bai ida juyawar ba yayi tozali da Ammin sa da ke bin sa da kallo sai ya ɗan rumtse
idanun sa sannan ya buɗe,a hankali ya tashi daga kwancen da yake ya zauna duk suna kallon sa.

Jingina zai yi da kan gadon amma ta hana sa ta janyo sa kusa da ita tana faɗin

"Come to momma baby"rungumo sa tayi tana jin hawayen farinciki na bin kuncin ta,saurin gogewa tayi
dan kar ya gani.

Cikin ran sa tunani ya shiga yi anya Ammi ta san abin da ya aikatawa amanar da ta ba sa kuwa?toh in
ma ta sanin me yasa bata yi reacting ba har take janyo sa jiki?ko dai Bilkisu bata sanar da su abin da ya
faru bane?toh in haka ne ina ta tafi dan ya san da a ce sun haɗu tabbas ba tantama da Ammi zata yi
spotting abin da ya faru kuma dole zata tambayi Bilkisu dan jin ƙarin bayani and if Bilkisu responds toh
da ba haka zai ga Ammin ba toh me ya faru?..

muryar ta ne ya katse mai tunanin da yake yi

"Zaid...me ya faru baku zo nan gidan ku ba instead kuka dawo gida nan me ya faru halan"??shiru yayi
yana ingesting maganganun mahaifiyar ta sa and then he began to wonder Bilkisu bata tafi chan gidan
bane dama nan ta zo ko chan gidan su ko ina Ammi ta gan ta.

Ɗago kan sa yayi ya kalle ta sai ya ƙaƙalo murmushin dole dan he feel so pathetic for himself already in
har Ammi ta gano gaskiya dukan sa ne kaɗai ba zata yi ba because Ammi is a no nonsense woman she
won't spare him that he can assure
"Zaid talk to me"Dr ne ya zo kusa da ita ya dafa ta kafaɗa yana mata magana a hankali

"Darling allow him to refresh his memory kin san yanzu ya farka"ɗago kan ta tayi ta gyaɗa mai kai sai ta
dawo da duban ta ga Zaid ɗin

"Shikenan just rest for now tunda dare yayi but gobe inshaAllah first thing in the morning zaka min
bayanin abin da ya faru uhmm"??saurin amsa mata yayi sai ta tashi ta ɗan durƙuso ta manna mai good
night kiss a forehead ɗin sa ta miƙe

"Zan shiga chan gidan su Umman ku dan dubo Bilkisu just sleep calm har goben ka ji my boy"?amsa mata
yayi da kai yana jin tausayin kan sa dan har ta tafi gidan nan ya san komai zata ji and she will come back
and vent her anger on him ba zata tsaya sauraron dalilin sa ba shi wa zai fahimce sa ne wai..

Shafo gefen fuskar sa tayi tana murmushi sai da ta tambaye sa ko ya ci abinci ya amsa mata da eh kafin
su fita su bar sa.

Suna fita kuwa bacci ya ƙaurace wa idanun sa sam ya rasa me ya shafi Bilkisu a daren jiya daga magana
kawai sai ta ja mai tsatsauran layi tsakanin sa da ita yana matsayin mijin ta me ya taɓa ta ne shin a jiyan.

Haka ya rinƙa tunani kala kala dan ya san muddin Ammin sa ta dawo da cikakkiyar labarin abin da ya ma
Bilkisu sai ta kwance mai..



Bayan barin su ɗakin bata tsaya komawa cikin nata ɗakin ba ta yi hanyar fita sai Dr ya dakatar da ita ya
ce

"Baki fah canza kayan ki ba a haka zaki tafi gidan"?ɗan ɓata fuska tayi kafin ta ce

"Kai dai kam Dr akwai ka da damuwa me ya ma waɗannan kayan ana ta kai wa ke ta kaya"girgiza kai yayi
ya ce

"Toh mu tafi"daga haka suka fita tare suka shiga cikin gidan su Bilkisu suna tattaunawa akan al'amarin da
ya faru a yau ɗin...

************

Ƙarar wurgi da pillow ta ji sai ta buɗe idanun ta a hankali duk sun yi ja ja

47 / 74