Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 74

3K to 6K   out of 221.1K words

ce



"We are sorry forgive us"jinjina kai yayi cikin gamsuwa ya kalle ta ya ce



"Baby doctor kin ji abin da suka ce"? girgiza kai ta yi ta haɗe girar sama da ta ƙasa



"Good what did you do as the chief head then"? Bata so furtawa ba amma haka ta daure ta furta

"Let it be"cikin jin daɗin ɗiyar ta shi ta ji maganar shi ya ce

"Allah ya maki albarka"ya juya gare su ya ce dasu

"You guys can go amma kar ku bari hakan ya sake faruwa again ina dr ZM"? Suka rasa abin cewa yayin
da ita kuma ta ɗan yi leaning da kujerar da take zaune jira kawai take su fita ta saka mai kukan gajiya da
tayi da aiki tare da su ita ya haƙura ya tura ta ɗayan asibitin sa ta yi aikin ta a chan in ya so sai shi dr ZM
ɗin da na nace mai ya bar shi a nan.jin yayi tambayar shi yasa ta daɗa mayar da hankali dan jin amsar da
zasu bayar sai dai kafin su ba da amsar ya riga su ta hanyar cewa



"Am here sir"cikin mamaki suka juya auna kallon shi ita kanta buɗe lumsassun idanuwar ta tayi ta zuba
su a kan shi shima kallon seconds ya mata ya ɗauke fuskar sa ya mayar kan wannan dattijon wanda ya
faɗaɗa murmushin sa ya tambaye shi



"Where were you ban gan ka cikin conference room ɗin ba tun da na zo"kallon sauran yayi sun gane me
yake nufi dan haka suka fita ya tura ƙofar ya zauna kusa da shi ya ce



"Dad ban sami damar halartar meeting ɗin ba ne sakamakon emergency call da aka min a skylight yanzu
na dawo"mamakin ƙaryar da ya zabga take yi mutumin da yake asibitin nan tun ma kafin a fara meeting
ɗin zai ce wai ya wani tafi skylight lallai wasu lokutan al'amurar shi na bata mamaki gashi dai namiji a
tsaye amma some times yakan bata mamakin kare kansa da yakan yi in ya aikata ba daidai ba gashi
mahaifin ta baya ganin laifin sa
Murmushi ya mai kafin ya ce"Zaid Allah ya maka albarka irin ayyukan da kake yi da ɗawainiyar da kake yi
between this three hospitals ban da komai na cewa gare ka sai albarka da maka fatar alkhairi indeed my
friend has trained and raised a kind hearted son ina fata wataran alaƙar mu ta ƙara ƙarfi fiye da
haka"haɗa ido suka yi shi da ita wai me yasa addu'ar iyayen su bata wuce wannan ne?basarwa suka yi
kamar babu komai yayin da shi kuma ya amsa mai da

"Amin dad"daga haka ya juya ya kalle ta ya ce



"Baby ya maganar outreach ɗin da zaku tafi a garin Adamawa have you finish your preparation"?

Ya ilahi wai me Abban ta ke nufi ne da batun wannan outreach ɗin a ce gabaɗaya asibitin an rasa
waɗannda zasu tafi outreach sai su yau da ita da wasu ne abin zai zo da sauƙe amma ita da shi how?ina
ba zata yarda ba,ɗagowar ta kenan dan sanar da shi cewar itafah ta fasa amma kuma sai ya rigata
magana



"Dad ta gama tun last week muka gama komai da yadda abin zai gudana within 3week ɗin baka da
damuwa in dai ta nan ne"ya ida yana mai sakar mata da murmushin mugunta dan ya rantse sai ta tafi
outreach ɗin nan ko tana ra'ayi ko bata ra'ayi kuma ya san ya gama ɗaure ta da jijiuoyin jikin ta dan bata
iya jan magana muddin yana wurin dan izza da jiji da kan ta ya sa bata son yawaita magana a gaban sa
dan haka shiru ta yi tana kallon ikon Allah



"MashaAllah Alhamdulilah toh ai ina ganin babu wata magana kuma tunda kun gama komai about your
accommodation kuma komai has been settled jiran ku kawai ake"ɗagowa yayi ya kalle shi cikin
girmamawa ya ce



"But dad ai har accommodation ɗin has been taken care of by me in ba zaka damu ba nake ganin tunda
ni na kawo shawarar ai ni ke da alhakin kula da lafiyar ta dan haka na yi booking mata accommodation
already sai dai in ita ce ta ce bai mata ba"taɓdijam wai me ya maida ta ne a gaban mahaifin ta ya ke
shararo mata zance cikin zance bayan ya san ba zata iya ja da maganar Abban ta ba amma ya mata
shigar sauri?kamar ta fashe dan haushi



"Ikon Allah wannan yaro da ƙoƙari ka ke ai babu wani abin da zai saka ta ƙin girmama alkhairin da ka
mata dan haka babu komai with you my baby is safe na sani so nan da 10days zaku tafi outreach ɗin
Allah ya maku albarka ya raya mana ku"da amin suka amsa shi kuma ya miƙe ya fita yana cewa
"Baby mu haɗu a gida in kin huta akwai maganar da zamu yi ok"?

"Yes dad sai na dawo"murmushi yayi ya fita abin shi,yana fita ta daɗa haɗe fuskar nan tayi kicin kicin da
fuskar ta yi kamar bata san da zamar sa ba sai da ya gyara murya shima ya haɗe fuskar sa



"Idan kin gama shirin naki just let your foolish boyfriend know about it"yana kaiwa nan ya miƙe ya fita
ya bar ta cikin tunani ta yaya ma zasu zauna inuwa ɗaya da shi shi jin kai itama jin kai hmm abin da
kamar wuya.



Ko da ta chanza kayan ta zuwa fashionista black joude arabian gown ɗin ta sai kyawun ta ya daɗa
bayyana ta fito a siririyar doguwar ta yarintar ta ya fito sarari sosai doguwar heel ce a ƙafar ta sai jakar
da ke hannun ta ɗaya hannun ta riƙe da maƙullin motarta ta fito ta nufi car park ta buɗe motar ƙirar
toyota corolla XL ta saka jakar a kujerar zaman banza ta dawo ta buɗe ɗaya side ɗin zata shiga kenan ta
hango shi shima zai shige cikin tasa motar harara suka bankawa juna kowa ya shige motar sa suka fita
yana gaba tana baya har suka isa inda zasu tsaya a inda shi ya shige ɗaya gate mai kallon inda ta shigw
kenan makwafta ne su kamar zasu tayar da anguwar da horn ɗin da suka saka cikin sauri kamar haɗin
baki aka zo aka buɗe masu gate ɗin a fusace suka shige ciki aka mayar aka rufe.



Shigar ta falon kenan ta tarar da su suna abin da suka saba yi ita dai Allah ya bata kyautar iyaye a ko da
yaushe kamar wasu yara suke yanzu ma dai umman ta ce cikin shigar fitted gown an sha kwaliya an zubo
suman nan har gadon baya she is just looking perfect kamar wata wacce bata manyanta ba yayin da
Abban ta ke cikin shigar ƙananan kaya kamar ba shi yazo hospital ɗazu ba cikin shigar manya duk sai
suka koma mata wasu teenagers



"Prof na gaya maka baby ba zata tafi wannan outreach ɗin ba muddin ba tare da company ɗin wani ba i
can't risk that"tana maganar ne tana wani mammatsewa yayin da shi kuma cikin son impressing ɗin ta
ya ce



"Haba no heart she is not going alone tare da zaid zasu tafi that is in kin amince amma in bai maki ba sai
a yafe tafiyar"kamar wani wanda yake bauta mata haka yayi maganar ga mamakin sa sai ta saka dariyar
manya ta ce

"Common are you serious"? Cikin jin daɗi yayi impressing ɗin ta ya ce

"Yes of course"ta rungume shi tana cewa
"Na amince zaid is a good boy zai kular min da baby na"daɗi ya ji sosai inda ganin abin na su ba mai
ƙarewa ba ne ya sa ta gyara murya wanda hakan ya dawo da su daga jubilation ɗin da suke yi da sauri
suka gyara zama murmushi ta masu ta ce



"Good evening love birds"hararar wasa mahaifiyar tata ta mata ta ce

"Baby me yasa kike da son yi mana shishigi ne wai kin dawo instead ki tafi apartment ɗin ki sai kuma kika
tsaya kallon mu gashi kin hana mu ƙarasa hirar mu ko prof"? Ta ƙarasa tana kallon direction ɗin shi inda
yayi saurin girgiza mata kai.



Dariya kawai ta masu ta wuce tana jin daɗin ganin farincikin iyayen ta ko da kuwa sun ɓata mata rai ne
da zarar ta birkice masu zasu sauko su fara rarrashin as if ita kadai ce ƴa a gidan tana alfahari da su duk
da ma dai Abban ta na yi wa umman ta total obedience kamar wani wanda bai girma ba ita kuma
umman ta na ruling gidan according to her desire sai dai ta san duk a cikin soyayya ce dan da babu
soyayya duk hakan ba zai faru ba.karasa haurawa tayi tana fatan wataran in ta shirya neman abokin
rayuwa ta sami kamar Abban ta dan a tarihin gidan su irin rayuwar da ya gabana kenan she just pray that
the epic will repeat it self a kan ta...



Shima da shigar sa kenan ya tarar da iyayen shi zaune bakin swimming pool an sha ƙananan kaya ana
zuba soyayya ko ba'a faɗa ba a nasu fannin dai kusan abin da ke faruwa a gidan su bany doctor ke
faruwa a nan dan mahaifiyar shi ce ke faman bayar da command akan abin da za'a kawo masu in suka
tambayi mahaifin sai ya ce duk abin da ta zaɓa ya mai alhalin bai da niya amma dan gudun ɓacin ran ta
sai ya basar girgiza kai yayi ya nufo su ya tsaya masu a kai kamar soldier sai da mahaifiyar ta sa ta juyo ta
lura da dawowar shi cikin sauri ta miƙe tsaye tana cewa



"My boy yaushe ka shigo ban sani ba me za'a kawo maka kafin ka yi wanka"? Instead ya bata amsa sai
ya haɗe rai kamar bai iya dariya ba ya ce



"Ammi sau nawa nake hana ki ke da Abba yin irin waɗannan shigar?ban ce maku in zaku yi ku bari sai ba
mu nan a gidan ba"? Ya ida maganar cikin sanyin murya

Cire hannun ta tayi daga kan kyakyawar fuskar sa wanda yake nan exactly irin nata ta juya ga mahaifin
sa ta ce
"Only ka ma ɗanka magana yana mana shishigi a rayuwar mu da yawa in bai son ganin soyayyar mu me
zai hana shi zuwa ya samo tasa matar ta yadda ba zai rinƙa ganin namu soyayyar ba"ta ida tana batsewa
a dole ya ɓata mata rai cikin hanzari ya miƙe tsaye dan cika mata umarnin ta ya ce



"Haba zaid ya zaka na saka Ammin ka da ni a gaba kamar kai ka haife mu tare fah ka gan mu ta yaya
kake son raba abin da Allah ya haɗa?toh kar ka sake ka jini ko"? Ya gama maganar yana mai signal irin
yayi haƙurin nan murmusawa yayi dan yasan Ammin sa ce ruler ɗin gidan dan haka Abban sa has no say
sai abin da ta ce well duk a cikin soyayya ce ya faɗa a ran shi yayin da ya juya ya fara tafiya ya tsinƙayo
muryar ta tana cewa

"Ni wai only yaushe yaron nan ka ce zai yi tafiya ne"?



"In the next 10days kuma tare dababy doctor zasu tafi ai yayi ko"? Cikin murna ta ce



"Kana nufin da ɗiya ta zasu yi tafiyar"? Cikin murna ya ce

"Eh tare zasu tafi"

"Ohh Allah ya kai su lafiya i have to call hajiya Zeenat dan mu raba wannan farinciki tare miƙo min waya
ta"ya miƙa mata yana farinciki shima yace

"I have to call prof mu raba farincikin mu"hararar wasa ta mai ta ce

"Whatever ni damuwa ta ma yaron nan ya tafi ya bar mu mu sake"



Murmushi kawai yayi ya wuce zuwa ciki dan iyayen shi are always behaving so childish bai san yadda zai
yi da su ba.........




_Toh ya kuka ji takun farkon?mu cigaba ne ko dai mu dakata? yawan amsoshin ku da sharhunan ku su
zasu bada cikakkiyar amsoshin ku da amincewar ku_



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim
#vote

#comment

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*




*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*2*



Dr Zaid Maher Mahmud shine cikakken sunan sa ɗa ne ga Dr Maher Mahmud retired Dr mammalakin
asibitoci biyu da ɗan sa ke running wato Dr Zaid,ya kasance babban ɗa ne ga Dr Maher Mahmud wanda
ya ke da ƙanne uku Afzal wanda ya ke aiki a Canada da wani babban asibiti a inda mahaifin sa ya matsa
akan sai ya dawo nan ƙasar Nigeria amma ya ƙi a cewar sa tunda yayan sa na kula da asibitocin sa na nan
no need ya dawo haka ya ƙyale shi kasancewar mahaifiyar su ta saka bakin a bar shi har sai yayi deciding,

Hakim shine ɗa na uku wanda ya ke kan yin masters ɗin sa a science and technology a ƙasar Qatar sai
autar su Bahajjatu wacce ita ce sa'ar baby doctor kuma babbar aminiyar baby doctor tun yarinta
kasancewar tare suka taso har rana ita yau amintakar su na nan tana running babban fashion company
na kan ta wanda mahaifin ta ya buɗe mata.



Gidan su ya kasance strict free home very simple and unique home babu takura da hantara na kasa na
girmama na gaba da shi akwai ginanniyar ƙauna da shaƙuwa a gidan tsakanin su ilimin addini da na
zamani daidai gwargwado akwai fahimta mai ƙarfi a tsakanin iyaye da ƴaƴan na su.



Dr Zaid da ya zama babban ɗa a gidan ya lashe gurbin babban yaya a gidan kuma babban ɗa very simple
and jovial brother and a son bai haɗa ƙaunar kid sis ɗin sa da na kowa dan haka ma duk mai neman wani
abu a wun shi a cikin ƴanuwan na ta ke bi ta wurin ta dan ita ce ƴar gwal ɗin sa since she is the only girl a
gidan she is just 24years amma a hakan a wun shi a ƴar 5years yake ɗaukar ta ta yadda yake zuba mata
sharuɗɗan irin saurayin da zata saurara a haka kuma ta ke bi dan duk hutu da arziƙin ki muddin ka zo
mata da abin da baya cikin sharuɗɗan yayan nata toh ta haƙura da kai kenan sai dai ka nemi wata dan
yadda yayan nata ke ji da ita haka ma ita kanta..



abu ɗaya ne ya kasa hana ta shine amintakar su da baby doctor dan kuwa ya buga ya buga har fushi yayi
da ita sai dai haka ya haƙura ya bar ta dan ƙarshe shi ya koma rarrashin ta as strong head ɗin ta in ya
motsa baya jin lallami shi kuma bai iya ɗaukar fushin da take yi da shi he just doesn't know how amma
jinin shi ne kawai bai haɗu da na baby doctor ba dan tun yarintar su yake ganin taurin zuciya irin na ta
kwata kwata when it comes to him ba ta da sauƙi ko kaɗan bata raga mai in ya ce 'a' sai ta mayar mai
since they are all neighbours kusan a gidan su take yini dan mahaifiyar su Hajiya Madina na bala'in
ƙaunar ta saboda ƙaƙƙarfar friendship relationship da ke tsakanin ta da mahaifiyar baby doctor wato
Hajiya Zeenat,ganin hakan ya sa ya ke raga mata but in da ta shi ne yarinyar ta daina kusanci da ahalin
shi but unluckily for him hatta mahaifin shi na ji da ita being his best friend only girl child ga ƙannen shi
na son ta saboda hazaƙar ta da ilimin ta tunda both houses ɗin gidan boko ne sai relationship ɗin su ya yi
ƙarfi daɗin ƙarawa irin career ɗin iyayen su suke yi sai abin ya burge iyayen har ma suke fatan wataran
ala'ƙar su ta karfafa ta fi haka fatan su kenan amma ga su waɗanda ake ɗorawa hope ɗin ba haka ba ne
dan a kulliyaumi idan zasu haɗu da juna toh babu alkhairi is either a rabu da juna ana dasa ma juna
magana ko kuma a rabu ana aikawa juna mugayen kallo,



Dr Zaid ya kasance mutum ne shi mai son girma da kamun kai hakan ya samo asali ne sakamakon zurfin
karatun da yayi a ƙasar balarabe wato Dubai dan sanin mutunci da ƙimar ɗan adam ya ƙare a ƙasar
larabawa sai dai ɗaiɗaiku da ba za'a rasa ba masu ɓata ƙas, rayuwar sa a chan ya sa ya yi adopting
halayyar su dan fah shi bai cika son raini ba bare shishigi a al'amurar mutani over 12years yana ƙasar dan
ko da ya kammala karatun sa da su ya fara aiki until his momma mounted pressure on him kafin ya dawo
ƙasar shi ko da ta ga abin na son repeating kanshi akan Afzal sai bata wani damu ba since her boy is close
to her kuma shi Afzal ɗin ya nuna mata bai da niyar dawowa yanzu shi yasa ta sa mahaifin su ya bar shi
kawai tunda bai ra'ayi.



Kwata kwata bai wuce 33years ba very young gentile and hard working guy dan shi ke handling
hospitals ɗin iyayen na shi da na mahaifin shi da na aminin mahaifin nashi wato Dr Muhammad Sulaiman
dan duk ƴaƴan shi babu wanda ya karanci medical line ganin haka ga shekaru na ja ya sa Dr Maher
Mahmud bashi shawarar ɗora Zaid akan wanda za kular mai da asibitocin sa har kafin baby doctor ta
kammala karatun ta ya ko ji daɗin shawarar dan haka ya tuntuɓe shi da maganar akan in babu takura sai
dai ya ji daɗin amsar da ya bashi na ce mai da yayi ai shima ɗan shi ne dan haka duk yadda ya ga ya dace
a wun shi ba matsalar komai tun daga lokacin ya cigaba da kular mai da asibitocin sa +na mahaifin sa it
wasn't that easy for him gashi ɗan uwan shi yaƙi dawowa sai lokacin da baby doctor ta dawo sannan
abubuwan suka mai sauƙi but still wannan baƙar tambarin ƙin da ke tsakanin su ya sa instead of them to
be close and work hand in hand with each other sai suka kuma tsanar juna because shi yana nuna mata
ya rigata zuwa system ɗin muddin girman kan ta ba zai saka ta saukowa ta nemi assistance ɗin sa ba toh
kuwa sai dai ta rinƙa yin abubuwan ta ita kaɗai dan shi ba zai taɓa saka hannun sa a abubuwan ta ba
hakan ba ƙaramin ci mata rai yake yi ba ganin ita da asibitin mahaifin ta amma ana mata iko da mulki
gashi mahaifin nata bai shirya ganin abin da ke cikin duhu ba mahaifiyar ta kuwa bata son jin negative
side ɗin Dr Zaid sanar da ita abin da ke faruwa is a total waste of time.



Bilkisu Muhammad Sulaiman shine ainihin sunan ta wanda aka fi

2 / 74