Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ɗin..
Gyara mata kwanciyar yayi yana tambayar ta
"Kin ji abin da doctor ya ce ɗazu"?ɗan shiru ta mai kafin ta ce
"Wanne kenan"?daɗa rungume ta yayi yana faɗin
"Wanda ya saka min ƙa'idojin nan kin tuna"?sai yanzu ta gane inda maganar sa ta dosa sai ta yi kamar
bata gane ba ta ce
"Uhmm what about that"??sai ya mata kallon mamaki kafin yayi scoff yana faɗin
"You must be kidding me"!!sai ta kuma haɗe fuska irin bata gane ɗin nan ba sai ta ce
"Am serious ban fahimce ka ba hero"ai da sauri ya ɗaga ya zauna yana mai zaunar da ita kallon tsantsar
mamaki yake bin ta da shi
"Babes you mean,,,baki tuna rule da Dr ya saka min ba"?fuskar ta tab da alhini ta girgiza kai tana faɗin
"A'a ban tuna ba"!!riƙo kafaɗun ta yayi yana faɗin
"He asked me not to be committed to you wai har sai na ji sauƙi can you believe him"??dariyar bazata
ne ya kufce mata ai kuwa ta shiga yin dariya shi kuma ya rinƙa kallon ta wato sarai ta gane amma tayi
pretending wai bata gane ba lallai zai nuna mata shi ɗin namiji ne dan sai ya gwada mata ƙarfi a daren
yau ba sai gobe ba ko da kuwa in ya gama zai yi collapsing ne ya amince duk dan kar ta raina sa..
Tana dariyar ne ta rinƙa yunƙurin yin magana amma dariyar ya mata yawa dan haka aai da ta tsagaita
sannan ta ce
"Hero you are a hero a real hero that i won't oppose amma in ka saka ma patient ɗin ka sharuɗa ina
kana tsaurara mai ne dan kar a samu akasi?toh me zai sa kai aka ce da kai kar ka yi certain things amma
kake son tsallake sharuɗan likita uhum"??sai ya haɗe rai ya ɗage gira ɗaya sama yana faɗin
"Da bakin ki kike wannan maganar ko"?sai ta kuma fashewa da dariya tana faɗin
"Hero bana son mu kuma komawa asibiti da zumar kwanciyar rashin lafiya in har asibitin ya zama dole
zamu koma then akan wani dalilin ne saboda kai zaka karɓi delivery ɗin nan inshaAllah"sai ya mai da
idon sa saman cikin ta ko kafin ta sani har ya ɗora hannun sa saman cikin yana faɗin
"My girl this is the product of our love right"?girgiza mai kai tayi sai suka murmusa ya mayar da
hankalin sa ga cikin ta yana shafawa shi da ya ce bacci zai yi sai ya ɓige da hira da unborn baby ita kuma
tana taya sa wani lokacin kuma sai ta mai dariya..
Baccin da ba'a yi ba kenan har sai da ƙarfe takwas na dare ya buga dan shiririta suka rinƙa yi tun lokacin
har daren nan..
Kwata kwata bai nuna mata manufar sa ba akan ta haka zalika bai bari ta san takun sa ba coz yana ta
acting gentile kuma fah zazzaɓi ne ke fizgar sa amma tsabar son nuna mata shi ɗin likita ne wanda ya san
abin da ya dace da shi ba sai wani ya sanar da shi ba kuma yana son proving mata shi ɗin ba lusari bane
da za'a ce dan baya da lafiya shikenan ba zai iya yin komai da matar sa ba ai wannan tunanin shi
balaraben likitan ne wanda ya san ko shine aka saka mai wannan sharaɗin ba bi zai yi ba...
Lafiya ƙalau suka kwanta har da goodnight wishes da kisses suka yi addu'a bacci aka kashe light aka
shige cikin comforter cikin kwanciyar hankali ta kanannaɗe mai a jiki tunanin ta ai ya san illar tsallake
zancen likita dan haka ko kusa bata kawo a ran ta cewa zai yi wani abu da ita ba because she knows he is
gentile and man enough ba sai an tsaya sa'insa da shi ba,..shima sai ya daɗa rungume ta irin Allah ya
tashe mu lafiyar nan tun tana sauraron sa tana jin motsin sa har ta ji ya daina alamar bacci ya ɗauke sa
sai ta ɗago ta gan sa kamar dai baccin ne ya ɗauke sa sai ta kai lips ɗin ta dai dai lips ɗin sa ta manna
bakin ta saman nasa bakin ta sauke mai slight kiss tana faɗin
"I love you my hero and i missed you a lot.,,goodnight"ta ƙarasa faɗa tana mai kai mai wani kiss ɗin
gefen cheeks ɗin sa sannan ta koma ta mayar da kan ta gefen ƙirjin sa ta kwanta..
Yana jin ta natsu ya buɗe idanun sa yana murmushi lallai wato itama kewar sa take amma tsabar jan aji
ta rinƙa kawo mai sharuɗan da likita ya saka.
"hmm ashe dai a hannu take"ya faɗi hakan a ran sa yana murmushin jin daɗin kama ta red handed tana
faɗin yadda take kewar sa.., he have the whole tonight he is a happy man..
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*43*
*_Vibes_*
"Baby kina ji na"?ya tambaye ta yana mai leƙo fuskar ta,chan ciki ciki ta amsa mai da
"Uhmm ina jin ka hero"!!murmushi yayi jin muryar ta cike da magagin bacci dan ba wani jimawa tayi da
kwanciyar ba kenan har yanzu baccin nan na bin ta bai rabu da ita ba..
"Tashi mana mu yi hira"!!sama sama ta ji sa sai ta ce
"Hira wani iri kuma hero"?duk bacci ne ke fizgar ta..
Murmushi ya kuma yi ya ce
"Mata da miji har wata kalar hira suke yi da ya wuce na buƙatar juna a irin wannan lokacin"?a cikin
magagin baccin nata ta yi caraf ta tashi a birkice tana mai mutsitsiƙa idanu sai ta ba sa dariya sakamakon
firgigit ɗin da tayi ta tashi zaune..
"What?why the sudden confusion"??kamar bai gane halin da ta shiga ba sai ya wani basar ita kuma
al'ajabin abin ne ya ishe ta sai ta buɗe baki cikin jimami ta ce da shi
"Hero me kuma haka wace irin magana ce haka"??ɗage mata gira yayi yana mata kallon kyar har dai ta
kawo hannun ta ta riƙo nasa hannun
"Hero yi bacci ka ji,saboda abin da kake son aikatawa bai dace da lafiyar ka ba right now ka bari har ka
kuma warwarewa okey"??ta lankwasar da wuya sai yayi wani dariya yana kallom ta..
Ya saka ta a duhu har ta rasa me zata ce da shi sai ta cigaba da kallon sa har ya tsagaita dariyar nasa ya
kalle ta yana mai kai hannun sa saman bakin sa
"My girl ɗazu ɗazu fah kika gama shafe ni kina romancing ɗi na kina faɗin kin ji kewa ta kina kan jin
kewar ma har yanzu duk kin gama tattaɓa ni kin saka ni cikin halin da kike ciki sannan yanzu dan zan
taimaka in taya ki quenching thirst ɗin ki shine kike wani noƙewa kike son ƙaryata zamcen da na zo maki
da shi?haka kike dama baby"!???..
"What"?ta faɗi a bayyane sai ya ɗage kafaɗar sa alamun oho sai ta shiga girgiza kai tana mai son
kwanciya dan zancen nasa kamar wasar yara yake a kunnuwar ta..
"In kika kwanta zaki ja ma kanki"!!cak ta dakata haɗe da ɗagowa tana kallon sa fuskar ta babu alamun
wasa ta ce
"Zaid baka da lafiya,kana buƙatar kuzarin jikin ka ko so kake ka cigaba da zuwa asibiti a ko da yaushe
kullum muna hanyar asibiti duk dan saboda kai haka kake so?uhum?me ya sa baka son fahimta ne wai?
in ka ƙara haƙuri kamar yanzu ne dan baka huta da ni ba Zaid hakan ba yana nufin baka isa bane,,a'a
yana nufin kai ma ka damu da lafiyar ka kana son samin sauƙi..amma kawai dan kana son kayi proving
min kai ɗin jarumi ne da har zaka tafi kowani length just to show me sam baya birge ni bana son
hakan,na fi son ka natsu mu taru mu samar maka da lafiyar ka ingantacciya har ka wake in ya so duk
wani abin da zai faru sai ya biyo baya ta hakan ai zamu fi mayar da hankali mu yi komai cikin lumana da
jin dadi hade da kwanciyar hankali zai fi armashi Zaid baka tunanin haka"??shiru yayi yana sauraron ta ya
san gaskiya take faɗi dan sam bai wani jin kuzari amma so yake ya isar mata dan kar ta mai kallon lusari
marar jarumta..
Ɗago ƙwayar idanun sa yayi ya zuba cikin nata sai ta kai hannun ta kumatun sa tana shafawa ta ce
"Trust me hero,kai ɗin jarumi ne ni zan faɗi haka can you believe it,?rounds huɗu muke yi a single night
kuma baka gajiya hasalima ni ce mai nuna gajiya ta ni ce marar jarumtar ba kai ba Hero dan haka ka ƙara
haƙuri kamar yanzu ne highest ba zamu ƙare honeymoon ɗin nan ba tare da mun yi resuming duty ɗin
mu ba sanin kan ka ne hakan ai ko"?fuskar sa kamar wani ƙaramin yaro haka kamar zai yi kuka ya ce
"Amma ni so na ke in isar maki babes,bana so ki zauna cikin thirst ɗi na alhalin ba rasa wanda zai yi
quenching maki kika yi ba i don't wanna let you all alone shi yasa na ke son fitar da ke daga ƙishirwar da
kike ciki"murmushi tayi tana mamakin hali irin na Zaid ita kam Allah ya haɗa ta da miji
"Na sani hero shi yasa nake kiran ka da hero dan kai ɗin hero ne babu wanda ya isa ya nuna maka
jarumta ta ko ina miji na na yarda da dalilin ka amma mu ƙara haƙuri duk mai wucewa ne wataran sai
labari hmm"??gyaɗa mata kai yayi yana mai bin ta da kallon sha'awar ta dake damin sa sai dai kamar
yadda ta faɗi ne lafiyar sa na gaba da komai a gare su su duka dan haka lallaɓa sa tayi yayi bacci ita kuma
ta tsura mai ido tana kallon sa tana kallon erection ɗin sa sai ta girgiza kai dama mutumin da yake ji da
ƙarfi da bajinta ba ko wani lokaci yake iya jure rashin abu mafi muhimmamci a rayuwar sa ba...
Miƙewa tayi ta sauko ta nufi hanyar toilet tayi alwala ta fito ta fara sallar nafila,zama tayi tana tasbihi
har shabiyu da rabi ya gota sai tayi estimating time kasancewa awowi biyu ne tsakanin Dubai da Nigeria
sai ta yi concluding kiran Umman ta dan yanzu su suke kaiwa 10pm saboda shawarar ta take nema cikin
gaggawa dangane da zancen da Zaid ya mata akan Asma'u dan ita sam abin bai kwanta mata a ran ta ba
wai su nemo ainihin bakin zaren ta fi ganin a share zancen kawai shi zai fiye masu dan ita ba wai son
kuma haɗa ido da yarinyar nan take ba...
Tashi tayi ta ɗauki wayar ta dake saman side drawer ta dawo saman sallayar ta zauna tayi dialing
numbern Umman nata ta tsaya jiran ayi picking,ba jimawa aka ɗaga wayar sai ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Umma ina yini"!!cikin ɗaurewar kai Hajiya Zeenat ta ce
"Lafiya ƙalau Bilkisu lafiya cikin tsakar daren nan kika kira ni"??ajiyar zuciya ta kuma saukewa kafin ta ce
"Lafiya Umma amma ba lau ba"!!tashi tayi daga kwancen da take tana faɗin
"Me kuma ya faru Bilkisu ba dai jikin Zaid ɗin bane"?girgiza kai tayi kamar tana gaban ta kafin ta ce
"A'a Umma ba shi bane"sight na relieve Hajiya Zeenat ta sauke sannan ta ce
"Toh ina jin ki menene"??jujjuya maganar take a ran ta ta faɗa ne ko kuma tayi shiru ne saboda a wani
fuskar abin yana mata kamar sirrin su ne ita da mijin ta bai kamata ta bayyana ba sannan ta wani fuskar
tana ganin ya kamata ta faɗawa mahaifiyar ta dan wannan zancen ba wanda zata iya sanar da Bahajjatu
bane kasancewar ta ƙanwa ga mijin ta dan in a matsayin aminiya zata faɗa mata maganar toh ba laifi
amma tana matsayin ƙanwar Zaid bata jin abin zai dace maybe ma Bahan ta rinƙa kallon yayan nata da
wani irin ido ita kuma ba kasafai ta fiye son ana raina mata miji ba dan haka sai kawai ta yanke shawarar
sanar da mahaifiyar ta kawai at least zata iya bata shawarwari more than Baha..
"Bilkisu ina jin ki dare fah yayi bacci zan yi kika hana ni yi"!!shiru tayi kafin ta buɗe baki ta fara yi mata
bayani
"Umma kin ga Zaid ne,,,har yanzu fah bai rabu da zanven wannan Asma'u of a girl ɗin nan ba,sai cewa
yayi ma wai mu tafi mu samo asalin zancen har fah ya fara ganin laifi na wai bana fahimta ce min yayi
baya jin yarinyar na da laifi akan allegations da nayi laying mata is like yana goyon bayan ta ne ko
menene ban gane mai ba ni kuma gaskiya Umma hankali na sam bai kwanta da wannan shawarar nasa
ba kwata kwata bana son sake haɗa ido da yarinyar nan i don't know why kawai bana son ta ne bata
kwanta min a rai ba kuma Zaid sai nanata min kalmar in ba dan ita ba da baya existing yanzu da haka
does that mean that ni baya recognizing nawa ƙoƙarin da nake mai dan ganin ya samu lafiyar sa ya dawo
dai dai yadda yake a baya?Umma ni na gaji da halayyar Zaid babu abin da yake min da bana so illah abu
ɗaya shine kiran sunan wannan yarinya da yake yi ba wannan kaɗai ba har kare ta da yake yi ba son sa
nake ba ni na gaji ma da jin zancen ta ɗazu ya ke ƙara tambaya ta akan amsar da tambayar da ya min
gameda maganar yarinyar da ya kawo min i have to take his moment duk dan kar ya kuma yin maganar
saboda ban da tangible response ma tambayar nasa shi ya sa na ce zan sanar da ke Umma in kina da
alternative please engage me in it dan Zaid yana pushing ɗi na so hard akan zancen Asma'u of a girl ɗin
nan"!!!duk ran ta ya gama ɓaci yayin da take maganar ita kuma Hajiya Zeenat bata yi interrupting mata
maganar ta ba har ta dire..
Idan akwai abu da zata cire cikin zancen Bilkisu toh abubuwa guda biyu kacal jiga jigai zata iya cirewa
cikin zancen nata wato kishi da rashin fahimta dole ta fitar da ita daga cikin wannan duhun tunanin da
zargin dan kishi dai irin na Bilkisu bata taɓa ganin sa ba ko a baya da tayi irin tata kishin akan gaskiyar ta
tayi ta ba akan zargi da rashin fahimta ba..
"Bilkisu kina ji na"?amsa mata tayi jiki a sanyaye
"Eh ina ji Umma"
"Da kyau toh,,ki saurare ni ki kuma fahimce ni da kyau dan abin da zan sanar da ke ƙila ba zai maki daɗi
ba amma dole ni ɗin ce zan sanar da ke..,Bilkisu kina fama da matsananci kishi mai duhun gaske sam
babu haske cikin kishin ki wanda shi ya janyo maki rashin fahimtar mijin ki kwata kwata kin kasa gane
abin da ke gaban ki sakamakon baƙar kishin sa da kika ɗorawa kan ki Bilkisu,ban ce kar ki ji ko kar kiyi
kishin sa ba amma ana sara ana duba bakin gatari shi fah Zaid namiji ne mijin mace ɗai ɗai har huɗu
kenan bayan ke yana da ikon ƙara wasu har uku dan ya cike gidan sa,baki da hurumin taso sa gaba kina
nuna mai aon ra'ayin ki akan dole shi zai hau ya zauna duk dan kar ya ɓata maki rai...,kija sane yarinyar
nan da za'a bar sa auren ta zai yi dan shaƙuwar da ta shiga tsakanin su a baya bugu da ƙari yana mata
kallon yarinyar da ta taimake sa saboda wannan dalili kawai Zaid na iya auren ta kuma babu tambayar
hakan dan so dama yakan faro ne da tausayi toh a naki case ɗin sai kika tausaya masa fiye da yadda shi
yake tausaya maki wanda ya saka ki zurfafawa da yawa cikin son sa da ƙaunar sa har ma kike kishin sa
fiye da yadda mutum zai iya misaltawa kwata kwata baki ganin abin da ya dace da wanda bai dace ba
iyakar wanda hankalin ki ya kwanta da shi shikenan shi zaki yi which is totally wrong,,namiji ne fah Zaid a
ganin ki kin isa hana sa ƙaro mata ne?ko gani kike son da yake maki zai rinjayi faranta ran sa?namiji ba
zai taɓa sakewa da ke ba muddin kika zaɓi ki rinƙa canza hanya da shi ta yadda in ya kawo maki magana
sai ki nuna cewa baki tare da shi duk saboda wani dalili chan na ki toh kuwa in kika nuna mai haka dole
ya fara janye jikin sa da ke daga haka sai ku nesanci juna abubuwa su ta faruwa a tsakanin ku amma baki
sani ba rashin fahimta ta shigo tsakanin ku duk sakamakon laifin mutum ɗaya amma in kika nuna mai
kina tare da shi ko da kuwa hakan bai maki ba ba ƙaramar ƙima zai ƙara maki a idanun sa ba dan zai rinƙa
counting on you zai ga yana da strength bai da wani fargaba saɓanin ture sa da ingiza sa shi da damuwar
sa kawai dan baki yi na'am da shawarar sa ba...wannan kishin da kike ganin sa Bilkisu nayi fah,na yi shi a
lokacin da yake da riba ba yanzu ba da in kika yi wuya zaki sha dan mazan zamanin nan ba'a nuna masu
baƙar kishi tuni suna jin kan su suna ji da kuɗi da ganin zamanin su ne sai su sauya ki,,.. Babu abin da ya fi
ƙarfin addu'a i was very prayerful da ƙarfin addu'a Allah ya yaye min kusan 85% cikin kashi ɗari na kishin
da nake fama da shi..na daɗe ina maki addu'ar nan taAllah ya sa kar ki yo gado na ta fannin kishi sai dai
ban san me ya sa ba sai gashi kishin ki har yana son ɗare nawa kishin,
Ɗazu da kike narrating min matsalar ki sai na gano wani abu is like you are lacking in your prayer
point,baki da ƙaƙƙarfar prayer point Bilkisu dan da a ce kin san falala da ƙarfin addu'a da kin damƙe sa
sosai dan shi kaɗai ne zai magance maki wannan tsantsar baƙar kishin ta ki da ya saka ki kasa fahimtar
mijin ki..
Bilkisu falalar addu'a mai girma ce dan ni zan faɗi hakan kafin ni akwai mutani da yawa da zasu bayyana
maki falalar addu'a kafin su akwai amintattu,Mursalai da addu'a haɗe da falalar ta suke magance masu
damuwar su kamar Annabi Ibrahim addu'a yayi Allah ya ƙetarar da shi daga sharrin mutanen sa da kuma
wutar da suka saka shi ciki,haka annabi Yunus shima yawan