Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   7 / 74

18K to 21K   out of 221.1K words

jimami



"Kin ga waccan yarinyar"? ta girgiza mata kai sai ta cigaba

"Sunan ta dai kamar yadda bokan turai ya sanar da ke Asma'u ɗiya ce ga mamman mai rasuwa dattijon
kirki da kamala mutum mai haƙuri duk faɗin yankin nan ana daraja shi ba kaɗan ba dan bayan sarki da
mai gari sai shi halin dattako irin tasa yasa ko matsala aka samu wun shi ake zuwa dan ana mutunta shi
ba kaɗan ba..ita kaɗai ce ƴar shi mace yayyen ta biyu maza duk yaran kirki ne su ita kaɗai ce ta fito bare
babu hali dan uwar ta ta yi ƙoƙarin tarbiyartar da ita haka mahaifin ta ma yayi ƙoƙarin sa sai dai albasa
bata yi halin ruwa ba dan daɗin taɓarɓarewar tarbiyar ta wannan tsagerin saurayin nata mai suna
Mudan yaron nan babu hankali gashi dai a fuska kamili daga shi har ita sai dai babu halin arziƙi toh a
faɗin ƙauyen nan ko wani lungu da saƙo an san su dan tare suke zaga garin kuma duk wanda ya san
Mudan ya san shi da jarabar tsiya da fitina toh haka duk wanda ya taɓa Asma'u ya taɓo jaraba dan kusan
kowa tsoron sa yake ji ba kaɗan ba shi yasa ƙarfe shida na yamma na bugawa zaki ga yaran gari sun
koma gidajen su amma a lokacin Asma'u take cancaɗa kwaliya ta fita ita da Mudan su zaga garin nan sai
karfe tara na dare suke dawowa an daka har an gaji amma bata daina ba dan haka aka zuba mata idanu
kawai toh kamar dai yadda muka ji shi wannan bokan turai shine yayo dare a hanyar sa ta dawowa daga
cikin gari tsageran garin suka tare shi a hanya itakuma sun rabu da Mudan kenan zata dawo gida ta ci
karo da su a hanya ai kuwa shine ta masu kaca kaca kuma sun san ko ita ɗin wacece sai suka gudu ba
dan haka ba da sun mai kisan gilla dan ba su son harkar asibiti a cewar su duk ma'aikatan asibiti bankaɗo
sirrikan su na shaye shaye suke yi daga haka gwamnati sai ta saka masu ido har a tono asirin su a
hukunta su wanda hakan ba daɗi ke masu ba,toh kin fah ji labarin wannan botsararriyar ƴar wacce ta fi
ƙarfin jama'an gari...



Gwauron numfashi baby doctor ta saukeyayin da jama'ar wurin ke jinjina kai dan gabaɗayan su sun san
da wannan rikitacciyar yarinya mai sigar marasa kunya.
Kuma kallon su tayi sai ta shiga mamakin yadda aka yi rasa yarinyar da zai saurara duk jiji da kan nan
nasa da fa'ili iya nan ya tsaya lallai dole ta raba shi da wannan fetsararriyar yarinya dan sam bata ma da
gurbin zama cikin rayuwar su saboda bata da tsari bare tarbiyar da zata taki matakin zama cikin ahalin
su. Hmm ji ƙarfin hali irin na baby doctor.



Cigaba da aikin ta tayi a ƙarshe ta aiki wani yaro ya kirawo mata su sai da ya ja lokaci kafin ya taso ya zo



Tana gaba yana baya suna tafe suna ɗan zantawa kallon su take yi ta mayar da idanun ta kan yarinyar da
ke tafiya cikin iyayi tana mamakin rashin ji irin na yarinyar har dai suka nufo su sai ya dakata ya ce da ita



"Kin kira ni"cikin tsare gida yayi maganar itama sai ta haɗe rai ta ce

"Am done with today session sai ka zo mu ɗau evidence"bai ce ƙala ba ya ɗan rage murya ƙasa ƙasa ya
ce mata yana zuwa tana dariya ta ce mai toh haushin ta baby doctor ta ji ta ce

"Na fah gaji"dakatawa yayi ya fiddo wayar sa ya saita ya fara videoing ɗin su yana yi yana tambayar
yadda suka ji daɗin abin haka har suka gama da zasu tafi gida aka basu packs ɗin ktautar su kayan wanki
da na wanke wanke as an incentive duk dan su dawo washegari da murna haɗe da addu'oi suka tafi
gidahen su su kuma suka kama hanyar komawa gida bayan ya ɓata mata lokaci yana hira da Asma'u sun
dai rabu akan da yamma zai kawo mata ziyara da haka ta raka shi har wurin da take tsaye ta kalle ta
ƙerere ta ce

"Toh likita ni na tafi a huta gajiya lafiya"ƙala bata ce da ita ba wanda bai mata daɗi ba dan so tayi ta
tanka mata sai ta juye mata fitsara sai dai hankalin wayayye da ƙidahumi ba ɗaya ba dan haka ta ƙudiri yi
mata rashin kunya duk dan ta ƙure ta dan ta amsa mata.



A hanyar su ta komawa gida ne ya ce mata ɗazu an kira ta bata ɗauka ba an kira shi wai ina take.

Cikin hanzari ta tsaya ta fiddo wayar ta ta ga full service da sauri ta bi kiran da aka mata wanda ta riski
10 missed calls daga family ɗin ta sai na Hajiya Madina da na Bahajjatu kiran farko kiran mahaifiyar ta
tayi da ta ɗaga sai ta yi kamar ta saka kuka ta ce



"Umma ina yini ya gida ya Bilal da su Abba kin kira muna orientation ne sam ban gani ba"dariya Hajiya
Zeenat tayi daga ɗaya ɓangaren ta ce
"Ohh su baby an girma babu dai wani abin da bai maki ba ko"?girgiza kai tayi kamar tana gaban ta ta ce

"Umma komai yayi mutanin na da kirki"

"MashaAllah toh yanzu ina kuke na ji Zaid ya ce min motar ku ta sami matsala a hanyar ku ta tafiya dan
haka a taxi zaku koma gidan"cikin kaɗuwa ta ce

"Uhumm umma ina Bilal ki bashi wayar"murmushi ta yi ta ce



"Bilal na gida baby"da mamaki ta ce mata

"Ke kuma ina kike umma"ɗan sukwui tayi kafin ta ce



"Errr....mm..baby muna airport ne"!! tsit communication ɗin ya yanke kafin ta ce



"Umma ba dai wannan tafiyar zaku yi ba"? Cikin jin nauyin ɗiyar tata ta ce



"Eh baby tafiyar za mu yi kin ga ai ba mu kadai da baban ki bane har da su Hajiya Madina da Dr zamu
tafi"cikin ɗari ɗari ta ƙarasa maganar.

Kasa furta komai ta yi dan in suka cigaba da bin halin iyayen su toh tabbas wataran zasu haɗiye zuciya
dan haka ta ce mata



"Alright safe trip umma ki gaida su Abban"kitt ta kashe wayar tana ƙoƙarin kiran twin brother ɗin ta
wanda ringing biyu ya ɗaga



"Haba apple tun jiya nake ta kiran layin ki bai shiga me ya faru"sanyi ta ji a ranta kafin ta ce

"Apple garin ne babu network sai yanzu a hanyar mu ta dawowa daga wun outreach ɗin ne na lura shi
yasa na kira"



"Ohh i was very scared toh ya garin ba dai sanyi sosai ko"?murnusawa tayi ta ce

"Stop acting like my father sanin kan ka ne zan iya kula da kai na ba sai an gwada min ba"dariya yayi
kaɗan ya ce
"A'a fah apple kar ki yarda da mutanin ƙauyen nan na san su da son zuwa rafi kar dai ki rinƙa bin su
tohm"!! dariya ya bata dan haka ta ɗan dara



"Yes sir"gabaɗaya suka dara kafin daga bisani ta ce



"Bilal kana ina su umma suka kama hanyar tafiya yawon buɗe idon nan bayan na ce duk yadda zasu buga
kar ku bar su har da yaya Luk bai hana ba gashi yaya Jamil baya gari bare ya tsawatar masu why did you
allow them"?



"Hmm Bilkisu kenan ke kan ki kin san halin mutanin nan ba fah wannan ne na farko ba da suke sneaking
su gudu toh ko wannan ma bayan tafiya ta office na ji kiran sweet wai ko su umma na gida na ce mata eh
ta e basu nan na ce mata na baro su gida ta ce in kira in ji toh ko da na kira apple wallahi ce min aka yi
bin baya na suka yi da na fita suma suka fita tare da su Abban su sweet wai sun tafi airport i have no clue
akan tafiyar nan ta su forgive me"sauke numfashi ta yi kafin ta ce da shi

"Alright gobe zamu yi magana inshaAllah dan yanzu a gajiye nake"!!



"Alright apple i missed you"ɗan murmushi tayi ta ce

"Me too bye"suka yi sallama a nan ta tuna da mutum na tsaye na jiran ta.



"Ban fah gama abin da nake yi ba kana iya tafiya in na gama sai in biyo ka"ɗaga kafaɗa yayi kafin ya fara
tafiya bata ji mamaki ba dan dama bata saka ran samin security daga gare sa ba kiran layin Bahajjatu ta
yi bata ɗaga ba daga nan ta kira Hajiya Madina

"Ammi ina yini"



"Ƴa ta lafiya ƙalau ya yanayin garin kuma ya baƙunta"?

"Alhamdulilah Ammi har yanzu jirgin ku bai tashi bane"? Da mamaki ta ce



"Baby wa ya gaya maki muna airport"? Murmushi kawai ta yi ta ce
"Umma ce dama kawai kira na yi dan in yi wishing ɗin ku safe journey"sai ta ji nauyin ta amma still dan
kar jikin su yayi sanyi su ce sun fasa tafiyar sai ta ce

"Alright baby mun gode i promise to call you da zarar mun sauka da fatan dai Zaid na kula da ke kamar
yadda ya kamata"?



Abin mamaki ya bata amma sai ta ce

"Eh Ammi,toh ni zan ajiye wayar sai dai kun kira mu"!

"Ok take care dear"

"Uhum bye"ta datse kiran yayan ta Lukman ta kira bai ɗauka ba sai ya kashe ya kira ta

"Baby sis tun jiya nake neman layin ki bai shiga da fata dai komai lafiya"?



Ɗan murmushi ta yi tana ƙara son ƴanuwan ta dan irin kula da suke nuna mata

"Yaya Luk ina cikin lafiya mutanin na da kirki sosai babu network ne a inda muke shi yasa ban kira ba jiya
sai yanzu da muka baro accommodation ɗin mu ne na ga full service shi yasa na kira"



"Toh shikenan da fatan dai babu damuwa"?



"Hmm yaya Luk ni na rasa me kuka maida ni kowa sai tambaya ta yake da fatan babu komai of course
babu komai babban yaya na"



"Toh na yarda but ki kiyaye sanyi kin sa yanayin garin akwai sanyi kar ki rinƙa shan kayan sanyi fah kin ji
ko"? Darawa ta yi kafin ta ce



"Yes sirrrr"ta ja sir ɗin ta yadda abin ya zame masu abin dariya har suka daran kafin ta mai sai anjima
akan washegari zasu sake yin waya.



Daga shi sai babban yayan ta Jamil ta kira ya fi sau huɗu bai ɗaga ba ƙarshe matar sa ta kira zainab a
karo na biyu ta ɗaga tana tambayar ta
"Haba Bilkisu tun jiya hankalin yayan ki ya tashi wai baki ɗaga kiran shi ba ashe ma kwata kwata kiran ne
bai shiga ba sai fah da umma ta ce mai Zaid ai ya gaya masu babu service dan haka kar a damu da kiran
su akan in ku kuka kai inda zaku na reaching juna zaku kira tukunna fah ya sami damar yin barci har
zarah ta kasa barci dan hankulan mu a tashe yake toh yanzu ya lafiyar ku"?



Dariya sosai tayi irin tata gatar daban ce dan haka ta ce



"Aunty zee ai ko ɓata nayi sai haka baki bari mun gaisa ba kawai kika hau magana toh ina yini"itama
dariyar ta yi kafin ta ce

"Kin raina ni Bilkisu toh lafiya ƙalau ya kuke ya baƙuntar"?



"Hmm Alhamdulilah zamu ce aunty zee mutanin na da kirki gaskiya da fari i was scared amma yanzu ba
laifi na ma fara sabawa da su"

"Toh na ji daɗi da fatan ba wankan ruwan sanyi suke yi ba ko"?



"Haba aunty zee ko wankan ruwan sanyi suke yini sai in yarda in yi"?



"A'a dai wai saboda lafiyar ki ne kar fah ki rinƙa fitar yamma kin ji"?



Dariya ta yi kafin ta ce

"Na ji aunty zee zan kiyaye ina zarah"?

"Tana falo yanzu muka gama darun cin lunch"suka saka dariya daga bisani ta ce da ita



"Na kira yaya bai ɗaga ba in dai ya dawo ki sanar da shi"



"Eh ba zai ɗaga ba da yake sun tafi wata meeting akan tafiyar da zasu yi next week but zai kira ki ai"
"Noo koh ya kira ba zai samu ba dan babu network a chan ni dai zan kira shi gobe in Allah ya kaimu"



"Ohh Bilkisu wai babu service a chan ɗin"?



Darawa ta yi ta ce

"Eh babu aunty zee sai goben dan ga chan Dr Zaid na jira na zamu yi wayar gobe bye"



"Toh take care please"

"I will bye"suka ajiye wayar ta ɗaga kai ta hango shi chan tsaye bai tafin ba instead ya jingina da bishiyar
wurin yana waya ga kayan su a ƙasa grfe kaɗan da shi..



Karasawa tayi zuwa wurin shi ta ce da shi



"Na gama"daga haka ya sauke wayar suka cigaba da tafiya yana riƙe da kayan har suka iso kan titi inda
suka tari mai adaidaita ya kai su har masaukin su wanda ba wani nisa ne da shi ba daga wun outreach
ɗin da suka fito zasu shiga cikin gidan ya tsare ta ya ce mata



"Baki kira sakaran saurayin nan na ki ba halan dan ya kira ni yana umartata da in baki waya kuyi magana
dan naki a user busy yake saka mai me yasa kike son saka min ciwon kan ki"? Mamakin shi ta ji sai ta ce



"Hmm da sauƙi tunda sakarai ne yana da tarbiya da ilimin zamani ba kamar wasu da ke tafe a baibai ba
babu kwaɓo"daga haka ta yi gaba ta bar shi da mamakin ta dama ta iya magana haka bai sani ba lallai
mijin ta na da aiki toh wacce bata da kwaɓon?ba dai da Asmien sa take ba?no ai bata san labarin su ba
toh wacce bata da kwaɓon? Ya ɗaga kafaɗa ya shige cikin gidan shima sai barka da zuwa ake masu da
abinci aka fara tarbon su sai da ta yi wanka sannan ta ci abincin ta ta ƙoshi sannan aka dasa hirar abin da
ya faru a ranar sosai suka sha dariyar labarin Asma'u dan a nan zulfa'u ke kuma gaya mata ai suma sun
san da labarin yarinyar na rashin jin ta har yamma kafin ta ce da zulfa'u ita fah yau karatun islamiyya
take jin yi mamaki sosai ya kama zulfa'u ta ce da ita

"Ke koh likiciya a ina zaki yi karatun islama da ɗanyen daren nan"?murmusawa tayi ta ce
"A nan gidan zamu yi shi yanzu haɗo kawunan yaran gidan nan su zo nan shashin naki mu fara kin ga
yanzu biyar ta yi zuwa shida da rabi sai mu tashi kafin lokacin sallar magrib sai mu ɗora bayan sallar isha'i
zuwa takwas da rabi sai washegari ko ya kika gani"? Ta zuba mata idanun ta shiru ta yi tana tunanin ta
yaya za'a fara wannan sabuwar tarba wacce ƴan gidan basu saba da shi ba iyakan yara su tafi
makarantar allo tun ƙarfe biyu zuwa bakwai na yamma toh babu wani tsatsauran saka ido da suke ma
yaran bare su san ya yanayin karatun nasu yake gudana dan haka ta ce mata



"Anya likiciya wannan sabuwar aƙida za ta karɓu kuwa a gidan nan"?darawa tayi kafin ta ce



"Me zai hana kuwa zulfa'u?ke dai kawai ki tafi ki sanar da su su zo nan akwai labari"miƙewa tayi ta fita
tana fargabar Allah dai ya sa su amince su biyo ta amma abin da kamar wuya...



Bayan fitar ta sai ta yi saurin fiddo cupcakes ɗin ta ta jere su saman dardumar ɗakin ta fiddo ƙananan
goodies ɗin ta ta baje su a wurin ta ɗau wayar ta ta na latsawa kusan mintuna goma sai ga yaran sun fara
shigowa ɗai ɗai har dai suka ƙarasa shigowa daga baya iyayen yaran suka biyo su sai zulfa'u da ta tafi
kiran yaran.



Dakatawa da latsa wayar ta yi ta ce da su su zauna,suka zazzauna suna kallon kayan kwalam ɗin dama
abin da take so kenan ta janyo ra'ayin su kuma ta yi nasara dan haka ta fara da cewa



"Yara manyan gobe sannun ku da zuwa"cikin fara'a ta yi maganar suma cikin zalama suka ce

"Yauwa sannu anti"cikin turancin su da take irin wanda suka tsinta a bakin manya,

Murmusawa tayi ta ce



"Yauwwa toh yau dai ga kyauta nan na kawo maku sai dai ba zan baku ba"ta ida tana haɗe rai sai yaran
suka yunƙuro suka ce



"Me yasa ba za ki bamu ba anti"? Ta ɗan tsare gida kafin ta ce
"Kuna son kyautar kenan"? Cikim sauri suka haɗe baki wun cewa

"Eh muna so mana anti"point ɗin gyara kenan kalmar _'mana'_ da suka yi amfani da shi wannan kalmar
na rashin tarbiya ne dan haka tace



"Cewa zaku yi eh ba rh mana ba"

Sai suka yi saurin gyara maganar ta hanyar cewa

"Eh muna so aunty"sai ta sassauta fuskar ta ta ce

"Toh zan baku sai dai da sharaɗi"suka hayayyaƙo suka ce

"Menene anti"?



"Karatun islamiyya zamu yi wanda in har kuka bani haɗin kai toh inshaAllah kullum zaku rinƙa samin
kyautar da ta fi wannan ma kun yarda"cikin zumuɗi suka ce

"Eh mun amince anti"tafawa ta yi ta ce



"Yauwwa yaran anti toh ku gyara zaman ku"ta yi demonstrating masu zaman tarbiya suka kwaikwaye ta
ta fiddo Qur'an ɗin ta ta ajiye ihzu biyu ta buɗe shafin baƙi ta ce da su



"Kun san wannan"? Suka girgiza kai alamin eh ta ce

"MashaAllah toh kun iya karanta shi"? A wannan karon kaɗan ne suka amsa wanda hakan ya bara ikon
gane cewa ba su da yawa da suka san Qur'anin dan haka ta ce ma waɗanda suka iyan su fara ai kuwa ba
laifi ta sami kaɗan kaɗan daga cikin su da suka kawo alif zuwa nunun babu tangarɗa kuma yaran duka
ƴan ɗakin uwargidan mai gari ne dan haka sai uwar ta fara alfahari kenan kishin ma har da ƴaƴa ake yin
ta lallai akwai aiki dan haka ta ce da su



"Yanzu dai zamu yi karatu tun daga alif har zuwa ƙarshe bayan sallar isha'i sai a yi maimaici wanda a nan
kuma zan baku kyautar ku kun amince"? Suka amsa da eh daga haka suka fara kaɗan kaɗan har ƙarshe
suka maimaita sau uku sannan ta ce su tafi masallaci in sun dawo sai su cigaba yaran da murna suka tafi
bayan fitar su iyayen suka fara tambayar ta

"Likita mun gode fah wai dama bayan karatun siddabarun naku har na islama kuka iya"? Dariya kawai
tayi ta ce
"Ai da sannu zaku tantance hakan yanzu dai ku tafi ku yi sallah in yaran sun dawo sai mu ɗora"da toh
suka rabu yayin da zulfa'u ta rinƙa yabawa baby doctor da irin ƙoƙarin da ta yi akan Allah kadai zai bata
lada dan dama tun zuwan ta gidan ta so gyara tarbiyar amma iyayen yaran suka ƙi bada haɗin kai toh
gashi yanzu Allah ya kawo ta abin sai godiya.



Bayan sallar isha'i yaran suka dawo ta saka su maimaitawa ashe dai yaran na da brain gyara kaɗan aka

7 / 74