Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   38 / 74

111K to 114K   out of 221.1K words

tayi controlling kanta dan so take ta
gama tabbatarwa ko shima yana jin abin da take ji ko ita kaɗai ke jin abin..



"an kawo mana breakfast zaki yi joining ɗi na ne a parlor ko in kawo maki nan"?cikin salon jan ra'ayin sa
ta ce

"Hmm Zaid kenan..,ai duk inda kake nan nake duk inda ka zaɓar min nan zan zauna"

Ya ilahi,me yarinyar nan ke son yi mai ne haka shin?sam yakan kasa ganewa kan sa in har tana kusa da
shi shi dai ya san abu ɗaya ne tak wanda ya san ko a baccin sa zai iya shaidar sa sai ya sami mai warware
mai..



Kallon kallo suka shiga musayar yi da juna kafin ya ce da ita
"Toh ki zo mu tafi parlor in yaso sai mu kalli theater show"tashi tayi da fara'ar ta ta ce

"Hakan ma yayi"!!ta rigasa fita falon shi kuma yana biye da ita a baya yana saƙe saƙe..



Shi ya ɗauko plates biyu da spoons ya zo ya juye masu abincin cikin different plates ɗin sannan ya
zuzzuba masu chill drink a tumbler,tana bin sa da kallo har ya kammala tana kallon sa bata ce da shi ƙala
ba sai da ya kammala duka ya ɗago ba yabo ba fallasa ya ce

"Bismillah"!!...wani irin kallon kashe jiki ta mai dan ƙanƙance idanun ta tayi tana mai kallon ƴan
boko,shi kuma ya kasa furta komai sai bin ta da ido da yake yi kan sa duk ya ƙulle ya rasa dalilin ta na
nuna mai wannan attitude ɗin.

Bai gama tunanin nasa ba ya ji muryar ta kamar mai jin baccin tana faɗin.

"Bismillah??toh bismillah"ta faɗa cikin halin ko in kula haɗe da ɗaukar spoon da side table knife tana
kallon sa dan kamar statue ya koma a zaunen yana mamakin ta sam bai san ta shahara har haka ba sai
yanzu.

Alama ta mai da ido irin ina jiran ka ɗin nan dan kuwa babu alamar wasa a fuskar ta kenan bata ji daɗin
yadda ya mata tayin abincin ba.

Kallon ta yake kyar dan dai ya fara shiga duhu da ɗabi'un da tayi adopting tana displaying mai.

Saka cokalin yayi cikin plate ya fara ɗibawa zai kai bakin sa sai ya ƙaƙare ya kasa sakawa ya tsaya kallon
ta sakamakon ganin nata cokalin cikin plate ɗin abincin sa hankali kwance ta ɗibo sai ta dakata bata saka
a bakin ta ba ta aika mai da wani kallon kashe jiki sannan cikin taushin murya ta ce

"Bismillah"ai bai san lokacin da ya fara tari repeatedly babu tsagaitawa ba sai ta ɗan nuna alamun
damuwa a kan fuskar ta sannan ta tashi cikin kula ta ɗauko mai ruwan sha dan organic drink ɗin na iya
increasing mai rate na tarin bit water will be more suitable for him.

Bashu ruwan tayi a baki ya ɗan yi sipping sannan ya ɗaga kan sa yana kallon ta,haɗa ido suka yi ta mai
sannu da idon haɗe da gyaɗa mai kai irin it is well ɗin nan sai kawai ya sauke idon sa haɗe da furta

"Nagode"sai ta ce mai

"Ba komai ai aiki na ne"da murmushin ta ta faɗi hakan sannan ta dawo ta zauna ta ɗebi abincin ta kawo
bakin sa haɗe da ce mai

"Haaa"sai ya kalle ta a kasale bai buɗe bakin ba har sai da ta mai alama da kai sannan ya buɗe bakin
yana mai yin bismillah,saka mai cokalin abincin tayi a baki ya karɓa sai ta cire ta kuma ɗebo wani ta ƙara
bashi ya karɓa,a taƙaice dai ita ta ciyar da shi har ya ƙoshi sannan ta ɗau nata plate ɗin ta saka same
spoon da ta bashi abincin da shi ta ɗauka zata tashi dan komawa ɗakin ta cin abincin.
Yana ganin haka kuwa ya kawo hannun sa ya riƙe nata hannun da take da nufin ɗaukar tumbler,dakatar
da ita yayi yana mai cewa

"Zauna mana ina kuma zaki tafi"??sai ta ji gaban ta ya ɗan faɗi dan riƙon da ya kawo mata ya shige ta
ba kaɗan ba.

Haɗa ido suka yi sai ta kawar da nata idon kamar marar gaskiya ta ce

"Dinner zan yi having"!!still yana kallon ta ya ce

"Wayo dai zaki min,kin gama bani na ci sannan ke ki ce guduwa zaki yi ki ci alone dan kar in ga menene"?
dariyar mamakin sa tayi sannan ta ce

"Ban gane ba?abinci zan tafi in ci,,ina son shan magani kai ma ya kamata ka sha night medicine
naka"sarai ya gane so take tayi dodging tambayar da ya mata dan haka shima sai yayi claiming ai bai ma
san inda maganar tata ta dosa ba yayi pretending dan dolen ta ta dawo ta zauna ta ɗau cokalin zata fara
ciyar da kanta sai ya riga ta riƙo cokalin,ta zuba mai idanun ta bata ce komai ba sai ta ga yana ƙoƙarin
fara feeding nata abin ya ɗaure mata kai but bata dai ce komai ba.

Sai da ya ɗibo iya bakin ta sannan ya ce da ita

"Haaa"kamar dai yada ta mai sai abin ya saka ta darawa wato shi ba'a mai bai rama ba..

Share ta yayi dan shi dai duk abin da yake yi ji yake kamar ingiza sa ake yi yayi su dole dan haka baya jin
wani damuwa ko da ta mai dariya in dai zai sami sauƙin damuwar da yake damin sa he is okey..

Buɗe bakin tayi ya saka mata,a ƙalla sai da ta yi rabin plate ɗin nan sannan ta shiga girgiza mai kai
alamun ta ƙoshi sai ya tambaye ta

"Are you sure"?ta kuma girgiza mai kai sai ya miƙo mata drink ta sha haɗe da karɓa daga hannun sa tana
ce mai

"Thank you"ya ɗan murmusa sannan ya tashi ya kwashe kayan dama tana da niyar taya sa kwashen
kayan amma ya ce ta bari ita da ba lafiya sai ta yi zaman ta haɗe da ƙunna plasma ta kamo tashar da ya
kamo ranar da suka kalli theater da dare.

Zama tayi haɗe da crossing ƙafafun ta tana ɗan kaɗa su a hankali ta natsu tana kallon yadda ake feɗe
wata mace ana son cire mata fibroid mayomas,ta zurfafa a kallon har ya fito bata sani ba sai da ya zauna
yana mai faɗin

"Interesting"sai a nam ta kalle sa tana mai yin murmushi haɗe da gyaɗa mai kai,daga haka suka mayar
da hankalin su kan kallon har aka gama sai dai ana gab da ƙarasa ɗinke feɗan suka shiga yiwa kan su
tambayoyi a course of tambayar ne suka shiga arguing da juna har ma da abin ya masu sugar suka koma
yin raffle draw sai da aka kammala show ɗin sannan suka natsu sai suka koma yiwa kan su dariyar
shirmen da suka rinƙa yi,gaskiya ta ji daɗi abin nan dan ko ba komai yana copping da internal response
nasa ta ji daɗi ba kaɗan ba..
*3 hours later*



Bayan sallar azahar ya shirya cikin ƙananan kayan shan iska ya duba ta a ɗakin ta dan yana son su ɗan
zaga hotel ɗin tare since they have no where to go..

Ganin ta yayi kwance babu doguwar rigar sai ƙananan kayan da ta saka a ciki,bacci take sosai hankali
kwance sai ya mata kallon ƙurilla tun daga ƙasar ƙafar ta har ya kawo kan sumar kan ta yana kallon ta
yana admiring jikin ta sai ya ji baya son takura ta sai kawai yayi tafiyar sa shi kaɗai ya zaga ilahirin hotel
ɗin baki ɗaya yana zagawa yana tunanin ta har dai la'asar ta yi sannan ya dawo ya yi sallar sa ya kuma
komawa ɗakin ya ga still baccin take sai yayi murmushi haɗe da girgiza kan sa irin wannan bacci nata
haka ina zata kai sa..



Bayan kamar awa huɗu a tsakani lokacin har an fara shirin bacci dan sun gama cin abinci har sun yi sai
da safe sai ya ga kawai ba zai iya ba dole ya dawo ɗakin nata ya tura yana doka mata sallama daga
kwancen da take ne ta amsa mai tana mamaki dan har tayi addu'ar bacci.

Lighting ɗakin yayi sai ya hango ta kwance ta ɗan leƙo ta blanket ɗin tana kallon sa,rasa abin faɗi yayi
sai ya faƙe da cewar

"Dama zuwa nayi dan ƙara yi maki goodnight"da fara'ar ta ce

"Alright goodnight"sai ya tsinci kansa da waving nata yana murmushi itama martanin hakan ta mayar
mai,ya ja mata ƙofar haɗe da kashe hasken ɗakin.

Komawa baccin ta tayi shi kuma ko da ya isa ɗakin sa baccin kasa ɗaukar sa yayi dan haka ya rinƙa juye
juye shi bai san me ke damin sa ba sam wannan baƙon al'amari bai mai adalci ko kaɗan.

Da ƙyar da yaya baccin ya sace sa babu labari,baccin kusan baccin wahala ne dan kan sa ya kusa
bugawa tsabar takura mai da yayi da tunani marasa mafita...



*7 days later*

_*Last night in Germany*_



Misalin ƙarfe takwas da mintuna ashirin da biyar na dare tana kwance da ƙaramar nightie tana tsara
abubuwan da zata yi a washegarin in sun koma gida saboda daga Ammi har Umman ta sun gama zuzuta
mata kyawun gidan ta sun sanar da ita yadda aka tsara masu gidan very portable kuma an gyare ko ina
jiran zuwar su kawai ake yi dan har abincin da za'a masu washegarin an gama harhaɗa su a row suna
kamo hanya za'a fara dafa masu,duk sun saka mata kwaɗayin gidan nata a ran ta ga ƴan uwan ta sun
gama kwaɗaita mata jin daɗin rayuwar da zasu yi a gidan su dan gida ne mai tsarin gaske wanda yake
situated a Apo Hills birnin tarayya na ABJ..

Juyawa tayi bisa kan gadon tana ƙara tuno rayuwar da suka yi a gidan har zuwa goodnight da suka yi da
juna cikin ƴar kwanakin nan da suka zauna inuwa ɗaya.

Wato wano irin zama ne suka yi wanda ke tattare da tsantsar kulawa da daraja juna haɗe da taka
tsantsan dan gudun ɓacin ran wani a cikin su ga so da ke girgiza su a karkace for her,she is aware amma
shi kam bai ɗaukar hakan a bakin komai ya fi dangana hakan da zaman taren da suka yi wa da shi ya
janyo masu jituwa mai tsananin gaske..



Ita kaɗai ta rinƙa analysis ɗin ta sam babu wani abin da ya shiga tsakanin su tun da aka ɗaura auren har
kawo yau da yake masu daren ƙarshe a ƙasar,kuma abin bai dame ta ba dan ta san duk wani abin da zai
rikita sa ta mai kuma ta san ya ruɗe ba kaɗan ba..



Tana nan kwancen ta ji ya turo ƙofar ɗakin dama akwai haske a ɗakin dan haka ya sami direct access na
kallon ta,ƙare ma jikin ta kallo yayi sai ya ji wani abin na taso mai from nowhere sai ya haɗiye yawu haɗe
da buɗe baki da nufin gaya mata abin da ya kawo sa amma sai me?kasa magana yayi dan kayan jikin ta
have tempted and seduced him already.

Tana kallon sa gaban ta na faɗi shi kuma ya ƙi cire idanun sa daga kan ta wani mugu mugun muguwar
sha'awar junan su ne ya taso masu,strong desire ne ke ɗeban su but sun kasa aiwatar da komai sai
idanun su da ke aikin aiken da sukewa junan su mai ɗauke da saƙonni daban daban masu girman gaske..



_*S,Ibraheem*_

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°
°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI🎀*

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*25*

*_Conspicuous_*



Kamar wasa sai ga Dr Zaid ya shafe awowi sama da huɗu wanda yayi daidai da ƙarfe 1:30am na dare
yana zaune yana kallon Bilkisu,idanun sa duk sun yi ja ja zir sun ƙanƙance dan bacci yake buƙata amma
baya jin in yayi baccin nan zai wa kansa adalci duba da yadda ita ta tsaya ta dage a lokacin da shi bai da
lafiyar ta kula da shi ta tabbatar da safety haɗe da security nasa bata bar sa ba toh me zai sa shi ya bar ta
tana cikin halin nan ya je ya kwanta saboda selfishness bai jin zai iya wannan abin.

Countless times without number yana jin hausawa na faɗin kalmar *_"IYA RUWA FIDDA KAI"_* amma
bai san cikakkiyar ma'anar kalmar ba a hausance all he know shine yadda ake amfani da kalmar cikin
magana dan dasawa mutum baƙa hakan ne ma ya saka sa gayawa Bilkisun a lokacin da ta nemi sanin
dalilin zuwa da ita da zai yi yola dan yin outreach but apart from wannan bai san ma'ana gamsasshiya da
za'a iya alaƙanta kalmar da ba..
Ɗago kan sa yayi ya kalle ta tana bacci cikin doguwar rigar baccin ta da kaɗan ya rage ya kai mata ƙasa
hular baccin ma duk ya fita daga kan ta gashi nan a gefen ta kamar dai kullum tayi twisting sumar kanta
ne ta tura ciki babu robber band bare wani abin takura.

Bayan ya gama ƙare mata kallon ne ya kai hannun sa cikin salon da ba zata ji ba bare ta tashi daga
nannauyar baccin da take yi,warware mata suman yayi a hankali sannan ya shiga gyara mata cikin taka
tsantsan dan kar ta farka ta kasa komawa baccin.

Da ya gama gyara mata sumar sai ya cire hannun sa daga kan ta ya kawo ya haɗa da wanda ya riƙe
hannun ta da shi ya maida idanun sa kan ta yana kallon ta shi kam bai taɓa jin tausayin mace har haka ba
tun da yake a rayuwar sa yana iya cewa ko Bahajjatu dake ƙanwar sa har yake iƙirarin son da yake mata
na daban ne toh har ita bai jin ya taɓa yi tausaya mata kamar yadda yake tausaya Bilkisu a halin yanzu,ya
kasa tantance ɗaya abin da ke damin sa game da ita dan irin feelings da yake experiencing time to time
ba tausayawa bane kawai dole akwai wani abin na daban wanda yake buƙatar ƙarin haske akai.

Toh wai ma ya aka yi tun da chan baya bai taɓa jin irin wannan abin ba?da da suke tare a kullum da in
tayi magana yayi sai dai tayi shiru kuma akan gaskiyar ta take maganar ko da kuwa yin maganar sa na
nufin janyo mata babbar disappointment ne bata cigaba da magana sai dai ta yi shiru ko ma ta bar wurin
highest in ya ɓata mata rai da yawa sai ta aika mai da mugun kallo ta yi tsaki tayi tafiyar ta but bai taɓa
jin ɗigon tausayin ta ba sai yanzu,yanzun ma a yau a wannan halin da ya ganta.

Dole wannan tausayin ba shi kaɗai bane akwai wani al'amari behind it ba natural bane..

A karo na sau ba adaɗi ya kuma kallo ta tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,mai da idanun sa yayi ga
flower vase dake ɗakin sannan ya dawo da idanun sa gare ta sai kuma ya koma duniyar tunanin sa

A halin da ake ciki yana ganin kamar muhimmancin ta a gare sa is more fragile than the flower
vase,yana ji a jikin sa kamar akwai wani babbar al'amari that is yet to come his way sai dai kuma kamar
akwai hindrance da zai yi forming babbr rift a tsakanin sa da ita..

Jin faɗuwar gaba yayi ba tare da ya san dalilin hakan ba,kallon ta yayi sai ya ji faɗuwar gaban ya ƙaru
ninkin yadda yake ji,shiru yayi yana son dawowa daidai sai dai abin ya ci tura dan the more thought of
separation ya zo mai sai ya ji heart race nasa na ƙaruwa.

Toh shin me ma yasa yake tunanin wataran zasu iya rabuwa alhalin gasu nan tare kuma in bai manta ba
they are married so why is he thinking about separation?ko dai bai da lafiya ne bai sani ba?



A wannan karon da ya kalle ta sai ya ji yana son kwanciya next to her maybe zai sami sauƙin raɗaɗin da
yake ji a ran sa dan haka ba tare da wani doguwar tunani ba ya saki hannun ta ya tashi daga zaunen da
yake ya dawo kan gadon ya kwanta a left side adjacent to her ya juyo fuskar sa daidai nata fuskar yana
kallon ta.
Akwai wani maganaɗisun da ke ingiza sa yin abubuwa da dama da bai gama yin shawara da zuciyar sa
akan halascin su ba amma yana jin in bai yi abin ba toh kamar a takure zai kasance wannan ne dalilin sa
ma na barin ɗakin sa ya shigo nata kenan ba tare da ya tsaya yayi doguwar tunanin abin da zai yi ba
sannan yanzu da yake zaune ya tashi daga zaunen da yake ya dawo kan gadon ya kwanta next to
he,kuma ikon Allah sai ya ji faɗuwar gaban da yake experiencing ya ragu kusan kashi talatin cikin
ɗari,yana kallon nata ne yana tunanin zuci har bacci mai naiyin gaske ya ɗauke sa wanda bai san ba a
ɗakin sa yake ba dan he feel very comfortable and free a inda yake sanadiyar samin lafiyayyiyar baccin
da yayi kenan..



_5:14am_

A daidai wannan lokacin ne ya juya da nufin gyara kwanciyar sa sai kuma ya dakata daga komawa baccin
dan ya ji different scent ba kamar wanda ya saba ji ba in ya juya a ɗakin sa,a hankali ya shiga buɗe
idanun sa har ya gama buɗe su duka sai a nan ya fara tuno abin da ya faru da shi a daren jiya,dafe goshin
sa yayi yana mai lumshe idanun sa kusan mintoci kafin ya buɗe su ya juya ta ɗaya gefen sa sai ya ganta
kwance lafiya ƙalau tana kwasar baccin ta juyawa yayi ya ɗauko remote ɗin air split na ɗakin ya rage
yawan shi dan yana gudun wani abin da zai janyo mata ƙaruwar zazzaɓin da take ciki already.

Tashi yayi daga kan gadon ya nufi hanyar fita daga ɗakin,ba sallah take ba bare ya tashe ta sai kawai
yayi tafiyar sa zuwa ɗakin sa ya yi alwala ya zo yayi sallah..

Wani baƙon lamarin da ya same sa shine yadda ya taƙarƙare ya rinƙa yi mata addu'ar samin lafuya haɗe
da yi mata addu'ar tsari daga yin wani rashin lafiyar dan shi kaɗai ya san yadda ya ji a jiya da ta shiga
halin nan sam baya so ya kuma witnessing..

Sai da haske ya fara haska ɗakin nasa sannan ya tashi daga saman sallayar nasa ya dawo kan gadon sa
ya kwanta daga haka ne wani session ma baccin ya kuma yin awon gaba da shi kuma a cikin wannan
baccin nasa ne ya rinƙa mafarke mafarke marasa daɗi dan kaf abin da ya faru da shi ne a dajin nan ya
shiga dawo mai sai ya shiga karkarwa yana

38 / 74