Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 74

36K to 39K   out of 221.1K words

dawo parlor da wayar ta a hannu tana duba time..



Da kyar ya sami rickshaw ya tsare ya mai kwatancen inda zai tafi tiryan tiryan ya kai sa y biya shi kuɗin
shi ya fita ya shiga cikin gidan inda ya ga jama'a cirki cirko a tsakar gidan da sauri ya tambaye su inda Dr
Zaid yake nuna mai ɗakin sa suka yi bai tsaya ɓata lokaci ba ya shiga ɗakin ya gan shi kwance kamar
marar rai shi kan sa ba dan likita bane wanda aka kira akan ya bada taimako ba toh baya jin zai iya
taɓuka wani abin dan with the physical eye examination da ya ma Dr Zaid ɗin baya jin zai iya concluding
cewa Dr Zaid is still existing but he have to put himself ya samo mafita dan haka fita yayi ya tambayi car
key ɗin aka miƙa mai ya ce a saka baby doctor a motan kafin su fito da Dr Zaid hakan aka yi dan har
lokacin bata farfaɗo ba sai aka saka ta a front seat shi kuma da muktar suka ƙoƙarta suka fito da shi aka
buɗe back door suka saka shi ya rufe ya shiga gaban motar kafin ya tayar da motar ya ce da su

"Ku harhaɗa masu kayan su zan dawo in kwashe dan muna zuwa asibitin zan bar su in tafi tare masu
jirgi dole su bar garin nan a yau ɗin nan"!..ya ja motar yayi gaba dan shi tun farko bai yi supporting Dr
Zaid ɗin ba akan kawo outreach ɗin nan ba dan ya sanar da shi ƙauyen akwai haɗari sosai ta yadda
mutum ba zai taɓa tsammani ba gashi nan yanzu sun faɗa a tarkon ƴan iskan gari dan yana da tabbacin
ƴan iskan garin ne suka masu haka saidai shaf ya manta ya tambayi wanda ya masu wannan abin
nevertheless in ya koma karɓo kayan su zai tambaya dan babu abin da zai mayar da su dajin nan sai dai a
history dan ko su da ke ƙauyen akwai tazara sosai tsakanin gidan su da na mai gari.
Yana jan motar yana ta tunane tunane sai ya ga wayar Zaid ɗin na blinking ya kai duban shi sai ya ga an
saka

'Lil bro Luk' bai san ko wanene ba sai ya ɗaga wayar ya kara a kunne

"Assalamu alaikum"yayi sallama sai aka amsa mai

"Wa'alaikumul salam please ina yaya Zaid"?aka yi tambayar still bai gane mai maganar ba sai ya ce

"He is safe yanzu ma asibiti zamu tafi ni abokin aikin sa ne sunana Hussain yanzu ake sanar da ni abin da
ya faru kuma nima ina gida mun zo hutu shi yasa na yi hanzarin tafiya ɗauko su yanzu zamu tafi city
hospital ɗin Yola daga nan zan tafi booking masu flight dan bana so su kwana a garin nan"



Ajiyar zuciya Lukman yayi daga ɗaya ɓangaren kafin ya ce

"Mun gode sosai ɗan uwa dama fligt ɗin anjima zamu bi mu zo ɗaukan su daga nan mu dawo gida nut
since kai kana nan ina ga sai dai mu yi booking masu jirgin Germany dan na san a yadda aka ce an yi
attacking ɗin shi ɗin nan Ammi ba za ta yarda a yi treating ɗin shi a nan ƙasar ba ga kid sis ɗin mu duk an
ce itama bata farfaɗo ba ina ga tafiyar su chan zai fi".



"Eh toh kai sai ku fara processing masu visa ni kuma zan yi na nan dan abin ya mana sauri"ɓoye mai
gaskiyar lamarin yayi dan da zuwan shi ya ɗag kan Zaid ɗin sai ya ga wurin yayi swelling alamun akwai
internal bleeding profuse bleeding ma ba kaɗan ba hakan na nufin duk inda aka kai aka komo ba zai
farfaɗo nan kusa ba that is in an yi nasarar saving life ɗin shi,sanar da family member ɗin Dr Zaid ɗin da
ya kira ba zai taimaka ba instead discouraging zai janyo sai yayi shiru kawai ya bari akan in sun isa chan
asibitin a basu taimakon gaggawan da za'a iya kafin ya gama processing komai that means har shi kan sa
da matar sa have to leave that same night..



Bayan kamar mintuna arba'in suka iso cikin wani asibitin gari though ba shi ne babban hospital a town
ɗin ba amma shine nearby hospital dan haka shiga yayi ya nemi taimakon ma'aikatan aka zo aka ɗauke
su aka yi ciki da su zasu fara yi mai surutan police report ya nuna masu licence ɗin sa na Dr ya kuma
sanar da su in basu yi sun taimake sa ba yana iya rasa ran sa kuma alhaki a hannun su sannan zasu amshi
sammaci daga kotu dan iyayen shi ba zasu bar asibitin ba jin haka suka fara ƙoƙarin su da ya ga sun fara
sai ya sako masu labarin abin da ya kawo su ƙauyen da irin taimkon da suka bayar sai hakan ya saka su
ƙara himma suka cigaba da aikin taimakon gaggawa daga nan ya sanar da su yana zuwa ya fita ya wuce
ya shiga motar sa dare ne dan 10 yayi a lokacin gudu sosai yake ta shararawa har ya isa inda yake son
tafiyan bai ji da sauƙi ba dan da ƙyar ya samo visa ɗin mutani huɗu ta POS aka yi komai ya kamo hanya
ya dawo gidan mai gari dan kwashe kayayyakin su a nan ya tambayi wanda yayi wannan ta'asar suka
sanar da shi sai ya girgiza kai kawai ya wuce suna tambayar sa jikin su sai ya ce shima bai sani ba dan
haushi ne ke cin sa sosai ya daɗe yana jin labarin wannan tsagerin Mudan ɗin toh kuwa tunda ya taɓo
ɗan gwal zai yi da ya sanin rashin sa'ar sa a duniya dan ya san yadda mahaifiyar Zaid ke ji da shi ɗin nan
sam ba zata taɓa ɗaukar wannan shashancin ba sai ta sa an hukunta mata yaron.

Daga nan gidan shi ya wuce inda tausayin matar ta sa ya kama shi dan idanun ta duk a kumbure suke
alamun dai kuka tayi bayan tafiyar sa ai kuwa tana ganin ya shigo ta miƙe da sauri ta rungume shi ta
sakar mai kuka a yanayin da yake ciki shi kan shi kukan ne sauƙin zuciyar sa amma bai bari yayi ba sai ya
rarrashe ta ya ja ta zuwa bedroom ɗin su ya zaunar da ita ya ɗauko mata hijabin ta ya saka mata ya
ɗauko masu jakar tafiya ya shiga shirya masu kayan su cikin sauri ita dai bin shi da ido take yi dan ta kasa
tambayar sa me hakan ke nufi har dai ya gama ya janyo jakar zuwa gaban ta ya riƙo hannun ta ya miƙar
da ita tsaye ya ce da ita

"Sweetheart am so sorry zamu koma gida my friend is in serious pains da asibitin garin nan ba zasu iya
da shi ba in kuma muka yi delaying toh muna iya rasa sa"jin haka sai ta waro idanun ta waje sai ga
hawaye saurin share mata yayi ya ce

"Is okey Allah zai bashi lafiya"daga haka ya rungumo ta ta gefe suka fito gyara parking ɗin motar yayi
suka fito a ciki ya rufe masu gate ɗin suka fara tafiya..



**********

Sauke wayar yayi daga kunnen sa ya ce

"Big bro akwai wanda ma yayi aikin da zamu tafi yi a chan"sai ya ɗago ya kalle shi yana jiran jin ƙarin
bayani. Zama yayi ya sanar da shi komai sai ya miƙe tsaye ya ce da shi



"Ba matsala ka zauna a gida saboda bana so Bilal ya sani kar hankalin sa ya tashi ni zan tafi in fara
processing masu tafiyar"amsa mai yayi kafin su rabu ya wuce gida a inda nan ma ya tarar da matar sa
duk hankali tashe ga Zarah ta ƙi barci sai rigima take yi ko da ya shigo sanar da ita yayi abin da ke nan ya
kuma ce mata ta kwantar da hankalin ta shi zai tafi dan ya fara processing masu visa dan ya san ko su
Abba sun dawo abin da za'a yi kenan instead of delaying is better ya fara kafin su dawo ɗin dan su ma
suna hanyar dawowa.

Kuka sosai ta yi dan gabaɗayan su wato Dr Zaid ɗin da Bilkisun nata ne shi abokin mijin ta ita kuma
ƙanwar ta ƙanwar mijin ta.lallaɓata dai yayi akan ta rarrashi Zarah ta yi barci kuma kar ta tsaya jiran sa su
kwanta jin shi kawai ta yi amma ba iya kwanciyar zata yi ba ga yarinya ta dage sai Baban ta ya ɗauke ta
shi kuma duk hankalin sa baya jikin sa dan ya rasa me ke mai daɗi a hakan ma ba'a faɗa masu ainihin
labarin ba kenan ina ga sun ji root ɗin batun..
A daren nab ya tafi yayi booking masu flight ɗin washegari ya dawo guda very late gabaɗaya family ɗin
Dr Maher Mahmud ba'a sanar da su abin da ke faruwa ba except Afzal da ya san labarin pneumonic
crises ɗin baby doctor a jiya shima ban da wannan bai san komai ba ko Hakim da yayi waya da yayan
nashi bai san komai ba apart from that.babban yaya ne ya hana a sanar da family ɗin Dr Zaid abin da ke
faruwa har sai in sun dawo gidan wato jamil...



****************



Da isar su bai tsaya wata wata ba ya ce da matar sa ta jira sa yana zuwa haka ta zauna a motar cikin
fargabar ko sun farfaɗo ko basu farfaɗo ba da ya shiga dai duk labarin jiya ne dan kuwa kawai first aid
treatment suka yi rendering amma babu wanda ya farfaɗo a cikin su a cewar su ma shi Dr Zaid ɗin da aka
samu aka ɗan ɗauko hanyar saita numfashin sa sam abin ya rikice masu dan suna da ƙarancin likitoci so
the available doctors around su suka yi iya ƙoƙarin su...



Bai tsaya jin wani dogon turancin su ba ya ce su saka su a ambulnce car ɗin su aka taimaka aka saka su
yayi masu transferring kuɗin su suka fito sanar da security ɗin yayi akan zai yi parking motar sa a nan ya
kwana zai dawo bayan kwanaki uku ya ɗauka,fitowa matar sa tayi suka shiga cikin ambulance car ɗin
yayi driving ɗin su zuwa airport cikin gaggawa suka fitar da su suka shigar cikin jirgin babu ɓata lokaci
jirgin ya gama cika da travellers daga haka suka lula...



°°°°°°°°°°°°°°°°°°



Sai 7:50pm jirgin su Dr Maher yayi landing dan suna hanya suka dakata saboda yanayin whether ruwa
na iya farawa babu notification basu cigaba da tafiya ba har dai da ruwan ya tsaya ko ina ya zama stable.

Already jamil ya isa airport ɗin tare da Lukman sun tafi ɗauko iyayen na su already jirgin su baby doctor
ya iso tun safe har an ɗora su a intensive care ana jiran dawowar iyayen dan su gana kafin a tafi da su
germany ɗin.



Rungume Abba Lukman yayi yana ƙoƙarin danne damuwar sa dan tun daren jiyan nan kawai sha'ani aka
yi toh tsinkewar lamarin shine yau da suka iso ganin condition ɗin su sai ya sakar mai da jiki ya kasa
taɓuka komai dan ƙulle kan sa yayi a ɗaki ya yi kuka ba kaɗan ba mai rarrashin ma jamil bai iya ba dan
duk ya shiga ruɗu ganin aminin sa cikin halin life and death ga baby sis ɗin sa cikin temporal lost of
consciousness abin bai zo mai a sauƙaƙe ba,ƙwararrun doctors aka kawo gidan a nan aka gano ainihin
abin da ke damin sa da abin da ke faruwa a kan sa dan already akwai wuraren da suka sami damage a
kan na sa ita kuma baby doctor ta shiga temporal comma ne sakamakon shock ɗin da ta shiga as result
of violence ɗin da ta yi witnessing wanda ake saka ran zata iya farfaɗowa any moment from then dan
haka na ta da sauƙi amma shi na shi ne sai an kai shi higher facility wanda ke da ƙwararrun likitocin
kwakwalwa da zasu iya ɗora Dr Zaid ɗin a kan kula mai tsanani ita kuma ko a gida za'a iya cigaba da bata
kula sai dai babban yayan ta ya ce a'a bai amince ba tare za'a kai su a basu kula mai kyau toh tun lokacin
ne basu sami kan su ba tun da Bilal ya dawo daga ziyarar da ya kai office kasancewar ranar lahadi ne ba
aiki sai ya tafi rage aikin monday ko da ya dawo gidan sai ya ga mitoci ba iyaka duk a tunanin sa iyayen
su ne suka dawo sai ya ji mamaki dan ya san holiday ɗin na su bai ƙare ba toh me ya faru?

Haka dai ya ƙarasa ciki sai ya ga ana zazzaune jigum kamar ana zaman makoki sai ya ruɗe ya shiga
tambayar me ke faruwa ga matar yayan sa a gida aunty zee itama cikin wani yanayin take sai ya dumfari
yayan sa jamil ya fara tambayar sa ba'asi.rungume shi kawai ya iya yi yana petting bayan shi dan tausayin
sa yake ji apple ɗin sa na cikin halin ƙila wa ƙala daɗa dulmiyawa shi yayan na shi yayi dan haka ya ɗago
ya ce da shi

"Big bro me ke faruwa ne wai na ga kamar gidan ba'a cikin walwala"!!.

"Bilal it's your apple"!! Ai sai ya ji kamar ba a jikin sa ya ke ba apple?what about apple?me ya same ta?a
ruɗe ya kalli yayan na sa ya ce

"What about apple?me ya same ta"?



Riƙe sa Lukman yayi ya ce

"Calm down kid bro calm down"fincikewa yayi ya ce

"How can i calm down yay Luk?how?it's about apple"!!ya ida yana mai zazzaro wa yayan na sa idanu
kamar zai dake sa ba laifi Bilal akwai zuciya sai dai ba kasafai yake yi ba sai in tura ta kai bango dan haka
babban yayan dai shine ya riƙo sa ya yi supporting ɗin sa zuwa ɗakin baby doctor.



Komawa da baya yayi ya jingina da bango yana kallon twin sister ɗin sa kwanaki biyun nan sam baya jin
daɗin jikin sa kawai shiru yake yi bai sani ba but yana ta having strong feelings very strange feelings
marasa kyau da bai san dalili ba could it be this?why his apple?sai ga Bilal na kuka kamar ƙaramin yaro a
hakan bai ga brother in-law ɗin sa ba kenan.

Rungume shi yayyen na sa suka yi suna rarrashin sa kasa tambayar ba'asi yayi sai kuka.



Da ƙyar ya natsu ya sarara da kukan da yake yi a nan yayyen shi suka sami attention ɗin sa suka sanar da
shi abin da ya faru kasa motsawa yayi haka ya cigaba da zama a wurin..
A ɓangaren su Bahajjatu kuwa tashin ta da safe ta yi mugun gani dan around 9 na safe ta tashi sai ta yi
tozali da yayan ta Hakim yana ta shesheƙa duk tunanin ta ya tafi akan iyayen su ne wani abin ya same su
shaf bata yi zaton yayan ta ne ba dan ta san lokacin tafiyar su bai yi ba kuma a jiya misalin uku da rabi na
yamma suka yi waya da Bilkisu dan haka sam bata saka a ran ta cewa har sun dawo ba.



Abin da ya firgitata shine lokacin da ta yi arba da yayan ta rai a hannun Allah sam baya numfashi kamar
yadda ya kamata sai ta zube a wurin ta shiga zabga kuka kamar wacce ta rasa iyayen ta her brother
Hakim have to take her out of the roon saboda irin loud cry da take yi she couldn't take ot out of her
head wai yayan ta ne da gaske ke kwance kamar ba mutum mai rai a jikin sa ba..



Kiran Bilal ne ya shigo wayar ta ko da ta gani sai ta kasa ɗauka dan haka ya cigaba da kira har dai ta
ɗauka ta fashe mai da kuka mai taɓa zuciya gabaɗaya babu mai rarrashin wani dan daga gidan Dr
Muhammad Sulaiman har nan gidan Dr Maher Mahmud kowa na cikin halin kusan grief na abin al'ajabin
da ya same shi.



Har daren nan suna a haka until when Lukman ya sanar da yayan sa akan su tafi airport ɗauko iyaten su
dan by then jirgin su na iya landing shine suka taho airport ɗin..



Ɗaga shi daga jikin sa yayi yana tambayar sa inda yaran suke cikin sakewar jiki suka sanar da su a nan
suka ranƙaya suka tafi gida dama Dr Hussain ne ya ke kula da Dr Zaid ɗin yayin da aka gama bashi
immediate care ɗin da ya kamata matar sa na guda dan tun da suka iso bai tafi gida ba matar sa cr ta tafi
gidan kuma sau uku tana zuwa duban su kafin daren su tafi tare da shi akan anjima zai dawo in za'a tafi
da su Dr Zaid....



Da suka iso gida lamarin ba'a cewa komai dan Hajiya Madina kasa furta komai tayi ta yi shiru duk tsoron
duniya ya gama cika ta ta rasa ta ina zata fara an yi nasarar tsayar da external bleeding ɗin toh internal
bleeding ɗin fah?internal damages ɗin da aka yi wa internal structures ɗin kuma fah?who could possible
do this to their children?da waɗannan tambayoyi a ran ta ta cigaba da zaman kallon ɗan ta wanda kaf
wurin ba wanda bai ji tausayin ta ba sai marar imani..



Possible communication Dr Muhammad Sulaiman ya rinƙa yi har dai ya sami current hint akan cewa
babban likitan da ya kamata ya ga Dr Zaid ɗin baya nan ya yi tafiya kuma ba dawowar nan kusa ba sai
bayan sati biyu dan haka an basu hanyoyin da zasu bi dan kula da marasa lafiyan har lokacin da Dr ɗin zai
dawo dan kai shi wani ƙasar baya tsarin su they believe more akan german Dr ɗin dan ya san aikin sa
sosai shi yasa suka amince zasu cigaba da kula da shi a gidan har Dr ɗin ya dawo..

Komai da ya ke gudana a gidan na jin daɗin rayuwa ya tsaya masu cak ga Bilkisu sai dai ta farfaɗo na
mintuna kaɗan ta koma na ta ma da sauƙi akan na Dr Zaid da tun da aka ɗauko shi in banda allurai da
ake ɗura mai sai body care da ake mai sam baya sanin ana mai ɗin dan yanda aka ɗauko shi haka yake
har tsayin two weeks ɗin nan...



***********************



Bahajjatu ce zaune tana kallon Bilkisu kamar ta kira ta ta amsa sai dai ba halin yin hakan,hawayen da ya
gangaro mata ta goge dan bata san ranar gogewar baƙin cikin nan na su ba ga chan yayan ta kwance nan
babbar aminiyar ta twin sister ɗin saurayin ta na kwance bata san dama da hagunn ta ba sai dai a juya
ta..

Tana tunanin nata sai ta ga an fara fita da kayan su alamun tafiyar dai za'a yi

13 / 74