Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   48 / 74

141K to 144K   out of 221.1K words

zir tsabar kuka da ɓacin rai a ce
ita aka daka an hana ta kuka sannan ɗan hawayen da zata fitar ma ta ji sauƙi shima an hana ta wannan ai
son kai ne shi Zaid ɗin ba'a san abin da ya mata bane da sun sani da ba zasu tasa ta gaba haka ba har
Umma na yunƙurin sauke mata mari lallai da Umma ta mare ta da tsanar da zata ƙara yi wa yarinyar nan
Allah kaɗai ya sani.

Ƙwafa ta yi ta tashi ta bar ɗakin sai a nan Zainab matar Jamil ta sami damar zuwa kusa da ita ta janyo ta
ta shiga rarrashin ta dan ciwon ɗiya mace na ɗiya mace ne Bilkisu aka wa rashin adalcin amma ita ce ke
jin takaicin abin.
Daga Bilal har Lukman babu wanda ya goyi bayan Zaid laifin sa suka gani dan ita ɗin ƴar uwar su ce
kuma su suka san wahalar da ta sha duk a dalilin halin da ya shiga sama da sati biyu bata san inda kan ta
yake ba duk saboda shi again an haɗa ta aure da shi ba wai dan suna son juna ba but ta haƙura ta zauna
da shi ta yi jinyar sa har ya warke sannan a ce ga abin da zai saka mata da shi he is too selfish to their
own thinking..



Share mata hawaye Zainab ta shiga yi zata mata magana kenan muryar mijin ta ya hana ta

"Tashi mu tafi gida"iya abin da ya ce da ita kenan sai ta ɗago da mamaki tana kallon sa baki buɗe

"Mu tafi gida kuma Abban Zarah"?amsa mata yayi straight foward

"Eh ki tashi ban son sake repeating kai na"a yanzu kam hatta da Bilkisun da yayyen ta sai da suka yi
mamakin kalaman yayan na su zata kuma yin magana ya dakatar da ita a ɗan tsawace

"Ban ce bana son in kuma repeating kai na ba?ki kyaleta tunda abin da ta zaɓarwa kan ta kenan duk
wani ɗan halak yana neman gamawa da iyayen sa lafiya ya gama da mijin sa lafiya ƙarshe ya gama da
duniya lafiya but she....,ita ce mai nemar ma kan ta fitina da rigingimu how on earth cam someone
respectful do such a stupid thing?har ta iya ɗaga hannun ta ta mari mijin ta,,a ina addinin mu da al'adar
mu ta amince akan mace ta ɗaga muryar ta sama da na mijin ta har ma tayi gigin marin sa?where?can
she spot it out?no dan haka ki zo mu tafi and let her continue with the new life she choose for herself
dan wannan abin da ta yi nunawa duniya tayi cewa bata da tarbiya but ki sani yadda kika zo gidan nan
kika ƙi tafiya gidan mijin ki toh da kan ki zaki tafi dan babu wanda zaki ma rashin hankalin ki ya tsaya biye
maki"rai a matuƙar ɓace ya ida maganar sannan ya yi waje yana mai ƙara jaddada ma matar sa akan ta
fito su tafi..



Kuka ta kuma fashewa da shi mai cin rai yanzu dan shi Zaid ɗin namiji ne ba zasu ga laifin sa ba sai ita da
take mace?meye laifin ta dan ta nuna ɓacin ran ta akan abin da ya mata?kuka take yi mai ɗauke da
damuwa haɗe da ɓacin rai,kasa tsayuwa Bilal da Lukman suka yi sai suka zo kusa da ita shi Bilal da ya fi
jin zafin abin dan ba ƙaramin ɓaci ran sa yayi ba duba da blames da aka ɗorawa twin sis ɗin sa sam ba'a
ga laifin Zaid ba har babban yayan su yana faɗin a rabu da ita is it because Zaid is his friend or what...

"Kun ji ko?kun ji dan na faɗi abin da Zaid ya min shine Umma da yaya suke fushi da ni dan basu san abin
da ya min bane"sai kuka kuma ya sarƙe ta Zainab bata da wani option sama da ta zauna ta rarrashe ta
ɗan ɗaga murya tayi ta ma nannyn Zarah magana ta ce da ita ta kai baby Zarah wun Abban ta

"Ki kai ta wun daddyn ta sannan ki ce da shi ya kai ki gida so sorry for holding you har wannan hour ɗin"

Da murmushi ta ce
"Is okey ma'am good night"daga haka ta sauko ƙasa ta sami jamil tayi conveying saƙon da aka aiko ta
tayi.girgiza kai yayi yana mamakin taurin kai irin na Zainab ya mata magana amma tayi shunning
maganar.



"Apple kar ki damu kin ji in su basu son ki mu muna son ki and no one will force you to go back to
brother In-law har sai da yardar ki"kallon sa tayi ta ce

"Bilal na yi laifi ne dan na nuna ɓacin rai na"?saurin girgiza mata kai yayi ya ce

"A'a apple baki yi laifi ba"sai ta cigaba da kukan ta yayin da Luk ya rinƙa yi mata kallon tausayi har dai ya
bar ɗakin da baya son ganin baby sis ɗin nasa cikin damuwa is better in sun bar ta ita kaɗai sai ya dawo
yayi mata rarrashi..



Zainab ce ta ce da Bilal ya tafi kawai ita zata rarrashe ta dan haka ya fita ya bar masu ɗakin but abin ya
tsaya mai a rai ba kaɗan ba..

Bayan fitar sa ne ta maido da kallon ta ga Bilkisu ta ce da ita cikin ɗaure fuska

"Bilkisu sarai na san ba iya dalilin da ya saka ki yanke wannan ɗanyar hukuncin ba kenan dole akwai
wani ƙaƙƙarfar dalili dan haka ki sanar da ni if not nima tafiya ta zan yi in bar ki"sai ta kalle ta fuskar ta
duk ya ɓaci da hawaye ta rasa ta ina zata fara fallasa abin sai dai fallasa shi ɗin shi zai fi zame mata
mafita dan yadda iyayen ta da yayan ta suka kasa fahimtar ta tana ganin in har ta ma aunty Zee bayanin
komai ita zata yi reasoning da ita.

"Aunty Zee.... Zaid ne....shi ne ya ɓata min rai...wallahi ban da niyar yin abin da nayi....har cikin zuciya ta
ban da niyar hurting na sa..but he pushed me so hard that i couldn't resist i have to tumble back"tana
kuka muryar ta na rawa ta yi maganar sai ta saka Zainab cikin duhu amma dai bata ce da ita komai ba ta
cigaba da kallon ta tana son jin ƙarshen maganar

Bayan ta ja fasali sai ta cigaba

"He....heeee..he told me that....thattt...he have feelings for that girl and he sai this to me he said it to my
face that what can i do about it..."kuka ne ya ci ƙarfin ta dan tunowa tayi da lokacin da ya ke gasa mata
maganar..cigaba tayi ta ce

"He said all these awful words to me yesterday and did you know what happened yesterday"??saurin
girgiza mata kai tayi

Share hawayen ta tayi ta shiga mayar mata da irin zaman da suka yi tare da Zaid ɗin a nan ta tona mata
sirein zuciyar ta game da son da takewa Zaid ta mata bayanin yadda tayi exploring feelings da take da shi
akan sa dalilin ta na amince mai har wani abin ya shiga tsakanin su..
Da kuka ta ƙarasa maganar sai a nan Zainab ta ga wawtar Zaid dan ko wace mace aka yiwa wannan
abin dole zata ji ba daɗi bare ita Bilkisu da Allah ya ɗorawa kishi mai tsanani sai sai dai ta lura ita kan ta
Bilkisun bata san cewa tana da tsananin kishi har haka ba gashi muguwar son Zaid ɗin ya ma Bilkisu
kamu ba kaɗan ba dan son ta ya fi nasa ba dan haka ba da duk borin da zata yi da sunan tafiya ta bar sa
zai tanƙwasa ta dan dole but he didn't.



Rungumo ta tayi tana petting nata sai da ta ga ta ɗan natsu sannan ta shiga yi mata magana cikin
lumana

"Bilkisu kin san fah shi sha'anin aure ba rayuwar wasan yara bane,abubuwa da dama kan faru cikin
zamantakewar aure amma ma'auratan na ɓoyewa suyi handling da kan su,ba su barin abin ya fito sai har
in abin ya fi ƙarfin su sai a dangana da manya a kawo su cikin lamarin,duk mace da kika gan ta gidan
mijin ta tana da matsalar ta wanda ya shafe ta ya ke kuma damin ta amma haka take saka fake face
mask da ya zame mata dole dan kare martabar gidan mijin ta gidan ta,..matsalar ku Bilkisu shine rashin
fahimta,daga ke har shi Zaid ɗin baku da kyakyawar fahimtar juna kuna da lapses da rift a tsakankanin ku
sam baku da proper understanding na juna..Bilkisu babbar matsalar ki a nan shine kina fama da yaƙin
mata wanda wasu kan kira shi da kumallon mata but a yanzu da yanayi ya juya sunan ya canza zuwa
yaƙin mata..Bilkisu kishi ne ke ɗawainiya da ke ba kaɗan ba Allah ya jarafce ki da kishi matsananci mai
zafi wanda yake controlling naki dan kishin ki ya fi ƙarfin zuciyar ki da tunani ki dan kin bari kishin ya rufe
maki ido yayi taking over almost 80% of your mindset but baki sani ba saboda you are ignorant of all
these Bilkisu..,you see,,shi namiji ba'a nuna mai ana kishin sa fiye da ƙima at least once in a blue moon
you can express your jealousy haƙƙin ki ne dan shi ɗin mijin ki ne amma ba wai kawai ki rinƙa portraying
kishin ki all day long akan namiji ba saboda kin san wani babban abin da kishin nan ke janyowa"?cigaba
da sauraron ta ta yi dan bata jin zata iya ce mata komai a halin nan da take ciki

"Bilkisu kishi na janyowa mace ƙaranta a idon ɗa namiji,yawan kishi na saka namiji rage respect ɗin da
yake da shi ma ɗiya mace,kishi na janyo maki raini a idon ɗa namiji saboda gani zai yi ai duk abin da ya ga
damar yi maki zai yi kuma ya wuce scot free dan son sa da kishin sa zai danƙwafar da ke and you know
what?mijin ki Zaid is a gentle guy if not for that wallahi wallahi kin ji na rantse maki Bilkisu,,tun a jiyan
nan ba sai yau ba da Zaid zai sako ki ki dawo gidan da iddar sa a kanki kuma ya tafi ya auro ita wannan
yarinyar da kike gani kamar bata kai standard ɗin zama matar sa ba ya gyara ta yayi educating nata ya
wayar da ita ya zauna lafiya da ita ta haifar mai ƴaƴa and there is nothing you can do about it believe me
ƴar kallo zaki dawo a rayuwar su,,,but sai ba maki hakan ba ya bar ki yana tunanin maybe in kika huce
zaki dawo daidai amma sai kika nuna mai no ke ɗin kin ƙware wun iya rashin kunya har kika saka ƙafa
kika bar sa a ƙasar germany kika yi dawowar ki a matsayin ki na wacce ke ƙarƙashin ɗa namiji mijin
ki,,...did you think that you are a saint or what?Zaid is not yet back ke kin sani kin fi kowa sanin jar yanzu
Zaid bai gama dawowa hayyacin sa ba tunanin sa on-off ne Bilkisu,kin fi kowa sanin amnesia na damin sa
wani lokacin ya yi daidai wani lokacin yayi akasin haka kuma kin san dawowar ƙwaƙwalwar sa sai a
hankali but you reacted that way in such manner da bai kamata ba why Bilkisu?da ilimin ki da wayon ki
da shekarun ki ki kasa handling mijin ki?..an you think fushin da kika yi zai janyo sa kusa da ke?me kike
tsammanin ji daga wun nasa family ɗin?kina ganin zasu goyi bayan ki su ƙi nasu ne?kina tunanin Ammi
zata ɗauke ki a matsayin yarinya mai tarbiya da hankali ne?tell me"?sai ta buɗe babin wani sabon kukan
dan ita kan ta ta san zafin rai ne ya saka ta aikata mai abubuwan da ta aikata ba wai dan ran ta na so ba
yanzu da aunty Zee ke daɗa farkar da ita daga baccin da take yi na ganin Zaid ba zai iya aurar Asma'u ba
sai ta ga ashe ita ce wawiyar da bata da wayo dan haka ta ce.

"Ni yanzu ya zan yi aunty Zee Zaid wronged me but i feel bad for punishing him i get hurt whenever i
remember what i did to him".

Ajiyar zuciya ta sauke sai ta tashi tsaye tana mai ce da ita.

"Yanzu duk ba wannan ba kina buƙatar hutu dan kin kwaso gajiya ki bari zuwa gobe in Allah ya kaimu
zan zo na musamman mu nemi mafitar abin but for now you need to rest uhmm"?girgiza mata kai tayi

"Okey goodnight"gyaɗa mata kai tayi daga haka ta fita ita kuma ta gyara zaman ta saman gadon tana
tunanin words da suka samu tsakanin ta da Dr Gabby Fernandez wato likitan germany da yayi treating
Zaid,ba komai ke ɗaga mata hankali ba sai option da ya bata a matsayin hanyar warakar Zaid ɗin kenan
dole sai an yi haka zai dawo full senses ɗin sa.

"Ya salam me Zaid ya min haka da na kasa cire sa daga zuciya ta har nake ƙara tausaya masa he doesn't
deserve my sympathy no"..tashi tayi ta shiga zirga zirga inside her within her heart ta san sam bata
kyauta wa Zaid ba saurin judging nasa da ta yi but still if he can remember his duties as a husband to her
then defiantly intentionally ya mata maganar yarinyar nan..

Wurgi tayi da quacker oat cup ɗin da ta sha ta barshi kusa da gadon ta sam ta tsani tayi tunanin
yarinyar never in her dream did she analyze that girl having an affairs with Zaid but me aunty Zee ke son
sanar da ita ne haka bu saying yana iya auran yarinyar ya wayar da ita sannan ta haifar masa ƴaƴa,

Wannan magana sai da ya harzuƙa ta ta yi wurgi da pillow dake kan gadon sannan ta shiga share
hawayen ta tana maganganu wanda da ji ka san kishi ne ke cin ta ba kaɗan ba

"Ai Zaid ba mayen mata bane ni....ni kaɗai na ishe sa yayi rayuwar sa da ni...babu inda zai kai wata
Asma'u...a tarihin gidan mu ma mu duka ai namiji mace ɗaya yake aura...i know Umma will support me if
she comes to know what was behind my outburst...Zaid zai dawo gare ni ni kaɗai na ishe sa i can fulfill
his wishes as a noble wife,i can do all he wants i can fulfill his desires i can do anything everything for
him just to make him mine alone..but how"?rasa amsa tayi dan haka ta koma ta kwanta tana tunanin
mafita dan ta san ko gigi take yi ba zata taɓa yarda Zaid ya auri wata yarinya ba bare ma yarinyar nan ƴar
ƙauyen nan da ta so yin ajalin sa she just can't stand seeing her anywhere close to Zaid..ihu ta yi na
azababben kishin da ke damin ta...



*******
Shigowar su gidan yayi daidai da fitowar Hajiya Zeenat daga ɗakin Bilkisu tare da prof,ran ta duk a ɓace
baƙin ciki take yi a ce ɗiyar da ta haifa ta kasa gane mutunci da ƙimarijin ta har ta iya ɗaga hannu ta
mare sa dan uban ta ne mai mulƙin duniya..,

Bata ankara ba ta ji muryar Hajiya Madina tana faɗin

"Ina Bilkisun take"juyawa tayi ta tsaya tana kallon ta duk kunyar ta ya gama kama Hajiya Zeenat su da
suka ƙulla alaƙa suna fatar alaƙar ta ɗore shikenan shi da yake namiji ya iya tanƙwaruwa ya zauna da ita
sai ita ce da ke mace ƙarƙashin sa take jin kan ta na hayaƙi ba zata iya juyuwa mai ba dan tana ganin
kanta a matsayi ɗaya suke shi doctor ita doctor..

"Hajiya Zeenat ina Bilkisun"?kallon ta tayi sai ta ga ashe har Dr Maher da prof sun bar wurin sun koma
ƙasa daga ita sai Hajiya Madina.

Riƙo hannun ta Hajiya Zeenat tayi tana cewa

"Zo mu tafi dan ba zaki iya ganin yarinyar nan ba"da mamaki Hajiya Madina ta ce

"Why"?ta bata amsa

"Because she is crazy she has gone mad"..cikin sarƙewar tunani Hajiya Madina ta ce

"Kamar ya she is crazy ni na so tambayar Zaid but Abban sa ya ce in bar sa ya huta har zuwa gobe and
now..you are saying that Bilkisu has gone crazy bam fahimce ki ba"!!jan hannun ta tayi suka ƙarasa shiha
ɗakin ta a nan suka zauna ta sauke ajiyar zuciya tana jimamin sanar da ita irin ɗibar albarka da ƴar ta tayi
wa ɗan ta wannan ai abin kunya ne.

Dafa kafadarta tayi ta ce

"Ina jin ki ta sanar da ke abin da ya faru ko itama ɗin shiru tayi"cikin jin zafi da dauriya ta ce

"Ina zata yi shiru marar kunyar yarinya wacce bata san inda ke mata ciwo ba kaii ni Zeenat ka haifi ɗa
baka haifi halin sa ba"by mow maganganun ta sun fara rikitar da Hajiya Madina sai ta ce

"Ki min bayani in ji ban gane inda kika dosa ba"!nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shiga warware
mata abin da Bilkisun ta faɗa masu ƙarshe ta ɗora da

"In ba rashin sanin daraja da ƙimar aure ba yanzu har a ce Bilkisu tayi ilimin ɗaga hannun ta ta mari
mijin ta dan ita ce fitsararriya marar tarbiya?dan ya mata maganar wata mace sai ta ɗau zafi ta rinƙa
dasa mai maganganu son ran ta?waye uban ta?yainyar nan bata taɓa yi min abin da ya ɓata min rai ba
kamar na yau tsabar rashin tarbiya har ta iya tsallake mijin ta ta bar sa tayi tafiyar ta daban saboda
zaman kan ta take"rai a ɓace take maganar Hajiya Madina zata yi magana kenan ta riga ta

"Yanzu yarinyar gani take kamar ni ta wulaƙanta ta tozarta ko?hala gani take mu da muke iyayen su ba
mu samin matsala ne da auren mu,toh in ba haka ba ta yaya zata zartar da wannan rashin hankalin ta ce
hukuncin da ta yi wa Zaid kenan dan ya kira sunan wata,ni ba gani na take yi ina wa Abban su wannan
rashin hankalin ba hasalima in har faɗar mu zamu yi barin cikin gari muke mu tadi wani wun dan mu ji
daɗin yin faɗar mu ƙarshe mu shirya mu dawo gida bata taɓa ganina na ɗaga hannu na na mari mahaifin
su ba toh a ina ita ta koyo wannan halin aure tun ba'a je ko ina ba har ta fara bashi ciwon kai ni fah abin
da na hango kenan tun fari ban yi na'am da auren nan ba amma kija ce zasu sasanta kan su wannan
shine sasantawar?rashin kunyar da ta mai shi zai saka sa son ta ko mutunta ta?ita ce ɗiyar zinari da zata
yiwa namiji wannan haukar sannan ya cigaba da sauraron ta?ni kam gaskiya ba zan iya ba gwara a raba
auren ta yi ta zama a gidan baƙin cikin

48 / 74