Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
zata iya losing mind nata..
Bayani doctorn ya mata akan zasu kwantar da ita har su kammala surgery ɗin amma ta shiga girgiza
masu kai akan bata so dan tsoro take ji kar su yi mata wayo su ƙarasa mata shi ko ma su ƙi yi masa
surgery ɗin..
Tana ƙi tana turjewa aka danna mata already loaded diazepam Valium,wani irin mugun jiri ne ya ɗebe
ta ga ciwon kai da ya rinƙa fizgar ta da kaɗan kaɗan har idanun ta suka rufe gabaɗaya sannan suka shigar
da ita ɗakin hutu aka kwantar da ita,setting mata lactate ringers aka yi saboda state of sudden shock da
ta shiga kuma sun gano kamar tana ɗauke da ciki saboda an yi mata examinations kuma wasu signs ɗin
na nuna alamun ba ita kaɗai bace shi yasa suka tabbatar da safety ɗin ta..
ƙoƙarin tracing last call na wayoyin su aka yi a asibitin dan a sanar da su abin dake ƙasa,bayan an ƙunna
wayar ne sai ga saƙonni kala kala na shigowa ciki har da voice messages sai suka duba wasu suka ga duk
congratulatory messages ne wasu kuma voice messages ɗin da turanci aka yi su haɗe da yaren hausa
dan haka ta turancin suka gane ba'a jima da tabbatar da pregnancy ɗin ba sai suka yi saurin tracing last
numbern da Bilkisu tayi kira da shi luckily da Dr Gabby suka yi wayar ƙarshe dan haka kira suka yi suka yi
bayanin ko su ɗin waye kuma daga inda suke kira sai ya masu bayanin ainihin musabbabin abin da ya
faru da dalilin Bilkisu na yin abin da tayi and he told them the reasons sai suka kuma gasgata maganar ta
dan ya nuna masu cewa shine likitan da yayi treating Zaid ɗin har ma da ita kan ta lokacin da aka kai su
chan ƙasar..
Godiya suka mai suka fara shirye shiryen surgery ɗin nasa wanda zai kasance by 11pm na daren ranar
banbancin lokacin zuwan su da lokacin surgery ɗin awa guda da mintuna talatin da uku...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_2 days later_
Tana unconscious bata farka ba sam bata san inda kan ta yake ba for the past 48 hours under
seductives take z da zarar ta farka za'a kuma yi mata wani duk dan kar ta farka a firgice is better at least
in ta farkan by now an gama surgery ɗin ko tayi tambayar za'a kai ta wurin sa...
Kaɗan kaɗan ta buɗe idanun ta har ta gama buɗewa gabaɗaya sai ta sauke su kan Hajiya Zeenat da ke
zaune idanun ta jazir fuskar ta ya ɓaci da hawaye duk kamar ba ita ba...
Daɗa girman idanun ta tayi sai ta ga eh da gaske Umman ta ne dan haka ta yunƙura zata tashi sai Hajiya
Zeenat tayi saurin maida ta tana ce mata
"Kwanta baby,,kwanta please"idanun ta na ciccikowa da hawaye sai dai bata bari sun fito ba ta rinƙa
riƙe su haka ta kwantan tana jin ciwon jiki gabaɗaya bata jin daɗin jikin ta sai yi mata wani iri yake yi
gashi jiri ya saka ta a gaba...
Hajiya Zeenat ce ta saka hannun ta tana gyara mata sumar ta da suka ɗan barbaje tana jan hanci tana
faɗin
"Ya jikin naki baby"??kallon Umman nata tayi tana jin anya tana iya yin magana kuwa ko dai tayi shiru
ne...sai ta ji muryar Hajiya Zeenat tana faɗin
"Go on speak out,kina iya magana yanzu,yi maganar ki kawai"..
Gwada gyara murya tayi sai ta ji throat ɗin ta ya buɗu sai ta gwada yin magana
"Ahhh....ah"sai ta yi shiru sai Umman ta yi fara'a tana murna ta ce
"Yess yes cigaba"...da sauri ta buɗe bakin tana faɗin
"Umm..ummmm..Umma...Zaid.Zaid"sai kuka maganar ta ƙaƙare mata ta faɗa jikin mahaifiyar ta tana
rusa kuka rarrashin ta ta shiga yi dan tun zuwan su ƙasar suke ta kula da ita dan so suke su tabbatar da
bayanin da likitan ya masu akan dalilin aikata abin da ta aikatan dan gani suke maybe akwai wani dalilin
ne na daban....
Almost 15seconds tana kuka Hajiya Zeenat tana rarrashin ta daga ƙarshe ta ɗago kan ta tana faɗin
"Umma Zaid fah,,ina yake,,,ina miji na Umma i almost killed him...da hannu na Umma da hannu na na
kusa halaka miji na miji na the father of my baby Umma i want to see him"...duk a bauɗe take
maganganun dan sam ba'a hayyacin ta take ba maganar sam a hargitse yake fitowa daga bakin ta ƙarshe
dai kiran likita Hajiya Zeenat tayi tana hawaye aka zo aka mata abin da zai yiwu da maganar a bakin ta ta
rufe idanun ta bacci ya ɗauke ta...
Fita daga ɗakin Hajiya Zeenat tayi ta zauna a kujerar dake kallon ɗakin ta rinƙa risgar kuka tana share
hawayen ta dan ta rasa ainihin dalilin Bilkisu na yin hakan dan sun yi tunanin in akwai wani abin ya
kamata likitan ya sanar da su amma bai sanar da su ya ɓoye masu sannan ya sanar da Bilkisu ita kaɗai
alhalin suma ɗin families ne..
Dafa ta aka yi sai ta ɗago ta ga Hajiya Madina ce dan ita kaɗai ce ke da ƙarfin halin iya rarrashin
aminiyar tata ba wai dan abin bai shige ta ba a'a sai dan son samin kwanciyar hankalin abubuwa saboda
a ji dalilin Bilkisu na aikata hakan,,.da wata ce ta aikata ma ɗan ta hakakn ba Bilkisu ba toh lallai duk son
da take mai da iƙirarin ita ɗin matar sa ce dole sai ta saka an kame ta hukuma sun hukunta mata ita
amma wannan ɗin rainon su ne ko ba komai akwai amintaka mai ƙarfi tsakanin family ɗin su da na su
Bilkisu dole a rinƙa yi ana dubawa...
Jiya da dare suka iso sakamakon kiran gaggawar da asibitin ta masu akan su zo suyi signing aka masu
bayani sama sama tun a daren ranar da aka kawo su asibitin shi yasa su suka saka aka nemo masu ticket
ɗin dubai su biyun in yaso daga baya in suka ga yanayin jikin nasu zasu sanar da iyayen nasu maza in na
zuwa a duba su ne sai su zo in kuma da sauƙi sai a bar shi in sun farfaɗo sai su dawo nan Nigeria...
Toh a jiyan da dare aka masa aikin cikin gaggawa kuma an tabbatar masu da cewa zai farka cikin awowi
72-78 kuma ba zai daɗe kamar na farkon ba a jinya da zarar ya farka zai iya komawa baccin kwanaki biyu
sannan ya farka gabaɗaya,toh jin wannan ne ma ya sanyaya masu zukatan su dan sun tsorata gani suke
kamar wannan ɗin ma zai kasance irin na farkon nan ne...
Zama tayi kusa da ita tana rubbing hannun ta bisa kafaɗar ta
"Ya isa haka Hajiya Zeenat in kika tasa ta gaba kina kuka ta yaya ni zan sami ƙwarin gwiwar cewa zasu
farka any time soon?uhum?ki daina kin ji"?..kallon ta tayi tana girgiza kai tana faɗin
"Ba wannan ba Hajiya..,me ya sa Bilkisu zata ɗau babbar risk haka ko da gani tayi yin abin da tayi shine
daidai ai bai dace muna iyayen su suna ƙarƙashin mu duk wani wayo da dabarar su mu mun fi su mun
riga su sanin menene duniyar ya zata ɗau hukunci irin wannan a hannun ta bata da tunani ne ko me"??ta
share hawayen ta sai Hajiya Madina ta yi zugum ita kan ta abin da ta matsu ta ji kenan dan duk bayanin
da aka masu bai wani gamsar da su ba..
Rarrashin ta kawai take yi itama tana rarrashin kan ta at the same time dan encouragement da
assurance suke buƙata...
Daren nan haka suka yi shi baccin ma ƙaurace masu yayi bai zo ba saboda fargaba da zullumin ko meye
mafitar su ina kuma makomar su da na ƴaƴan su,waya kawai suka yi ma ƴan gidan akan su kwantar da
hankalin su very soon zasu farka daga Zaid ɗin har Bilkisun shi dai Bilal matsuwa yayi akan sai ya zo
amma Hajiya Zeenat ta taka mai birki akan babu inda zai taho ya natsu a gida ya bi su da addu'a if not
zata yi fushi da shi...
***************
_1 day later_
Da sanyin safiyar ranar laraba Bilkisu ta farka cikin ƙarfin jiki dan da ƙarfin ta farka ta dawo hayyacin ta
sai ta cigaba da kwanciyar tayi shiru tana sauraron abin da zuciyar ta ke karanto mata a hankali ta fara
recalling abubuwan da ya faru har kawo zuwan mahaifiyar ta da ta gan ta jiya sama sama..
Wuf ta miƙe ta yi hanyar waje kai babu ɗankwali,daga nesa da suke zaune suka hango ta cikin sauri
suka taso suka nufo ta sai suka ga duk a hargitse take saurin mai da ta ɗakin suka yi suna rarrashin ta dan
tuejewa take tana faɗin ita a bar ta ta tafi wurin mijin ta ta saka masu hauka da iya ƙarfin ta da ƙyar suka
tanƙwara ta dan cikin da ke jikin ta is still unstable yana iya ɓarewa in aka asassa mai..
Danne ta bisa gadon Hajiya Madina tayi tana faɗin
"Ki natsu mana Bilkisu ya kike abu haka kamar wacce bata san ƙaddara ba ko so kike ki ce min kin manta
jinjirin ciki ne da ke da kike wannan hayaniyar"sai a sannan hankalin ta ya ɗan dawo mata ta fara
recalling cewa ranar da aka yi masu babbar albishir da cewa ciki ne da ita sai dai same day ɗin ne ta
aikata babbar kuskuren da take regretting a rayuwar ta tun daga ranar har zuwa yau a yanzu...
"Ammi...Ammi Zaid ɗi na Zaid,na mai laifi ya gafarce ni ya yafe min ban kuma yi daga wannan shi kenan
daga wannan bai kuma experiencing wahalar rayuwar sa kuma please take me to him i..i want to see my
husband"..kuka take yi babu ji su kuma dama abin da suke son ji kenan dan haka suka zaunar da ita da
kyau fuskar Hajiya Zeenat babu wasa ta ce
"Faɗa min Bilkisu..muna jin ki yi mana bayanin dalilin kisar da kika yi niyar yiwa mijin ki are you that
heartless or what speak up"??da sauri ta ɗago kan ta tana girgiza kai tana kuka ta ce
"No Umma ba kashe shi zan yi ba wallahi ina son sa ina son sa fiye da rayuwa ta amma ba zan iya ganin
sa cikin halin da ya shiga ba a watannin da suka wuce ba i can't bear seeing him in great pains ba zan iya
ba shi yasa nayi da kai na"by now Hajiya Zeenat is already losing her patience dan haka cikin daka tsawa
ta ce
"Toh dan ubanki buɗe baki kiyi magana buɗe bakin ki ki mana bayani tun kafin rai na ya ɓaci da
ke"saurin ja da baya tayi Hajiya Madina ta ɗan ɗaga murya tana dakatar da Hajiya Zeenat akan ta rage
zafin da ta ke yi da Bilkisun su lallaɓa ta dai har su ji dalilin ta..
Tana jikin Hajiya Madina tana ɓari tana kuka mai shiga rai dan duk zafin da suke ji bai kai wanda ita take
ji ba duk tashin hankalin da suke ciki bai kai wanda ita take ciki ba...
Masifar Hajiya Zeenat zata kuma yi Hajiya Madina ta ɗaga murya tana faɗin
"Kina furta wata kalma toh gaskiya barin ɗakin nan zaki yi kin ji na gaya maki bana son fitinar nan taki
haba da wanne zata ji da masifar ki ko da halin da mijin ta ke ciki"shiru Hajiya Zeenat tayi tana faman
hararar Bilkisu..
Kallon ta Hajiya Madina tayi tana faɗin
"Yi shiru ki mana bayanin abin da ya faru kin ji"??gyaɗa kai tayi tana jan numfashi yayin da Hajiya
Madina ke rubbing bayan ta sai ɓari jikin ta ke yi kusan mintuna da yawa tana a haka har dai ta fara iya
controlling kan ta suna sauraron ta sannan ta buɗe baki ta fara yi masu bayani kamar haka
_"Ranar da Zaid ya farka har kuka tafi office ɗin doctor Gabby sakamakon kiran ku da yayi ya maku
bayanin Zaid ya farka ya kuma tabbatar maku da cewa ya farka kenan kuka amince da hakan..toh ba
duka bayanin ya maku ba ya ɓoye maku wani matsalar da zai zo ya faru da Zaid bayan wasu lokuta,ya
ɓoye maku saboda ganin halin farincikin da kuka shiga...bayan kwanaki da sanar da ku sakamakon ne na
koma office ɗin sa na mai bayanin nima relative ce na patient ɗin ya so ɓoye min gaskiyar lamarin sai dai
na nuna mai ni ɗin doctor ce yana iya sanar da ni komai,,...bayanin da ya min shine....,,Zaid zai farka ya
warke a fuska a ɗauka ya gama warkewa kenan har abada dan babu abin da zai yi da za'a mai kallon
marar lafiya ko marar hankali sai dai babbar matsalar da ke cunkushe a kan sa ya fi wanda yake ciki aka
mai magani a lokacin,,,da na nemi sanin ko menene wannan matsalar sai ya bayyana min komai kuma
gaskiyar maganar shine bayan Zaid ya wartsake da kamar watanni takwas zuwa shekara ɗaya....Zaid na
iya haukacewa sakamakon rashin tabbatar da komawar ƙwaƙwalwar sa inda ya kamata.....da na
tambayae sa hanyar kaucewa hakan sai ya sanar da ni hanya ɗaya ce matuƙar muna son samim sa cikin
yanayin mutani masu hankali,,hanyar ɗaya ce.,shine dole sanadin da ya saka sa cikin matsalar wannan
sanadin za'a bi a kuma nemo makarin hakan...kenan dole wannan Mudan ɗin da ya bige Zaid a kai shine
dai still zai kuma bige sa dan samin sauƙin sa gabaɗaya...,,a ranar da ya faɗi min haka hauka ne kaɗai ban
yi ba dan har tambayar sa nayi da in akwai wata hanyar ya sanar da ni amma ya ce min in ba wannan
hanyar ba toh sai dai mu kalle sa yayi losing mind ɗin sa dan in aka cigaba da ɗura mai magunguna da
yawa wata rana yana iya zamowa resistant to the drugs and their effects..na rasa wa zan yi sharing
matsala tare da shi tun ranar nake tsoron zuwar wannan ranar da zan yi witnessing Zaid na losing mind
ɗin sa,ban sanar da kowa ba dan bana son ɗaga maku hankali bana so ku tsorata ku rasa kwanciyar
hankalin ku tun ranar nake planning hanyar da zan taimaka mai dan ba zan taɓa barin sa ya koma
ƙauyen nan ba bana jun zan kuma yarda ya ƙara haɗa ido da Mudan bare ya kuma repeating mai abin da
aka ce sai an kuma yi,,i was hoping kafin time ɗin ya kai zan sami alternative other than wanda Dr Gabby
ya ce sai dai har ranar da incidence ɗin ya faru ban sami mafita ba,a lokacin da Dr ke sanar da mu cewa i
am 3weeks pregnant hankali na ya tashi weighing the fact that zan kai 9months ina ɗauke da cikin kafin
in haife shi kuma zan yi rainon babyn and what Dr Gabby said was 8-12months later after the first
surgery in ba'a yi abin da ya sanar da ni ba Zaid will definitely go mad,i never wished and pray to pass
through my pregnancy all alone ba tare da support ɗin Zaid ba haka zalika ban taɓa mafarkin rising
babyn mu ni kaɗai ba ba tare da Zaid ba,,a lissafe,mun kai wata ɗaya da kusan rabi which is equal to 6
and half months to expiry of cosmetic surgery da aka ma Zaid wanda in har hakan ya kasance kenan zan
yi rainon cikin nan ni kaɗai kenan ba tare da Zaid ba saboda zuwa lokacin zai fara losing mind ɗin sa,,rasa
abin yi nayi sai na kira likitan na mai bayani dan bana so in raini cikin nan ni kaɗai ba tare da miji na ba
sai ya ce min toh mafita ɗaya ne in babu wanda zai aikata abin da ya ce min toh dole ni ɗin da nake
kaucewa ni zan yi shi saboda a ceto sa daga shiga cikin halin da zai shiga nan ba da jimawa ba kokuma a
yi transporting nasa zuwa chan germany su zasu yi exorcism ɗin nikuma na ƙi amincewa da wannan
shawarar dan na san wahalar min da shi zasu yi sannan abin zai fito har ya dawo kunnen ku nikuma ba
son ku sani nake ba dan ya sanar da ni jinyar ba zai daɗe ba so i thought if i should do it all alone kafin
mu dawo gida zai farfaɗe gabaɗaya ba tare da Kun san da hakan ba shi yasa na ce mai zan yi ni da
kaina...ba tare da nayi weighing wani side effect ɗin abin ba na aikata mai hakan saboda ya farka ya
cigaba da rayuwar sa kamar kowani ɗan adam ta yadda ba zai sami fargabar faɗawa wani halin ba kp da
nan gaba ne that was my only intension Umma i never intended to kill my husband i never planned to
kill him i love him so much i can't bear seeing him going crazy that was why i did it please understand me
i beg of you"_..
Da kuka mai matuƙar ɗaga hankali ta ƙarasa maganar saboda tana da ta sanin aikata wannan hukuncin
ita kaɗai a nata tunanin sai ta ga kamar yin komai tsakanin su su biyun zai fi sirri da zuciya ɗaya ta yi
hakan dan kar hankalin families ɗin su ya tashi bata san abin will turn out to be like this ba...
Daga Hajiya Madina har Hajiya Zeenat shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su tabbas wannan abin da tayi
akwai ƙuruciya cikin sa sai dai ita gani tayi kamar shine mafi sauƙin aikatawa fiye da fallasuwar abin sai
dai kuma me ya sa Dr Gabby ya ɓoye masu ya ƙi sanar da su yau da a ce Bilkisu bata da ƙarfin imani tana
iya kai sa wurin maƙiyin sa Mudan ɗin ya kuma yi mai kokuma ta kai sa germany ɗin su mai exorcism ɗin
sai dai ita ta amince akan zata yi da kan ta tsabar son da take mai ba zata iya bari ya rasa abu mafi
muhimmamci a rayuwar sa ba lallai wannan abin hikimar ubangiji ne..
Ɗago ta Hajiya Madina tayi daga jikin ta ta kalle ta tsaf sannan ta ce
"Bamu ce kina son kashe mijin ki ba Bilkisu but kin san abin da kika aikata is risky what if the hotel
receptionist didn't come on time?me zai faru?maybe da an ɗora maki alhakin rasa rayuwar sa muddin
aka rasa ran sa,,,dan haka next time involve elders in your decision whenever you think of doing
something as big as this okey"?gyaɗa mata kai tayi tana kuka so take ta haɗa idon ta da mijin ta amma
babu halin yin hakan dan nauyin faɗin hakan take ji maybe a mata kallon muguwa mai son kashe mijin
ta...
Kasa magana Hajiya Zeenat tayi sai dai bin Bilkisun da ido dan ta rasa me zata ce da ita game da abin da
ta yi,kamar Hajiya Madina