Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
kin san mai jinya ba ta kwalliya yake ba"daga
haka ta fita cikin farinciki da jin daɗi ta bar hospital premises ta ɗau cab zuwa hotel apartment ɗin
su.bayan fitar ta Bilkisu ta zauna zaman jiran ta amma sai ta ga kamar da gayya Bahajjatun ta ƙi dawowa
on time haka ta rinƙa kai kawo a ɗakin ta gaji kawai sai ta fita tana saka ƙafar ta a wahe ta ci karo da mai
bata magani da fara'ar ta ta ce
"Good morning ma'am you look beautiful"a dame ta ce
"Morning Thanks for the complement"sai ta kalle ta alamun mu tafi amma sai ta ce
"No not now i need to clear something i will be back in a jiffy"zata kuma yi mata magana ta wuce ta
cikin sauri bata tdaya ko ina ba sai ɗakin Zaid sarai fah ta ga Hajiya Madina a ɗakin amma bata san abin
da yasa ta kasa jin ɗar ba ta tura ƙofar haɗe da yin sallama ta shiga.amsa mata Ammin tayi suka gaisa ta
tambaye ta ko ta sha maganin ta sai ta ce a'a sai anjima
"Baby amma kin san kina wasa da lafiyar ki koh?jiya a nan kika kwana dan kin ga babu kowa da zai hana
ki futa ko?me yasa ba kya jin magana ne wai baby ba fah haka kike ba da"ƙasa tayi da kanta sai ta ce
"Sorry Ammi zan daina"
"Hmm Bilkisu kenan toh na ji amma wannan kwaliyar fah?ta mecece"?sai ta ji kunya ta kama ta me zata
ce da ita
"Anyway in Zaid kika zo dubawa yi sauri ki duba shi dan ki tafi ki sha maganin ki kar lokaci ya wuce dan
very soon ma Abban ku zasu zo bana so su zo su ganki ba a ɗakin ki ba hmm"??amsa mata tayi sai ta
tashi ta bar masu ɗakin dan dama jiya tana daga ɗaya ɗakin da masu kula da marasa lafiya suke ta ga
shigowar Bilkisun girgiza kai kawai tayi sai ta kyale ta dan ta san babu wani abin da zai faru saboda shi
marar lafiyar kamar marar rai yake dan haka ba wani damuwar da ta ji sai ta ƙyale su afterall dama tana
son closeness nasu ya ƙaru ninkin ba ninkin ita abin armashi yake mata..
Ɗaga ƙafar ta tayi ta fara tafiya sai ta ga kamar idanun ta na nuna mata wani abu daga gefen comforter
da aka rufe Zaid da shi sai ta tsaya tana examining but bata kuma ganin abin ba tana ɗaga ƙafar ta ta
kuma ganin kamar movement daga cikin comforer ɗin sai ta ƙara girman idanun ta tana mamaki dan
movement ɗin yanzu ya fi na ɗazu rufe baki tayi da hannun ta dan saura kaɗan ta fasa ihu sakamakon
abin da ta gani...
*_"S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*_I LUV U ALL HAPPY WEEKEND 💋_*
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*THIS PAGE IS ALL URS FAUZIYA SHU'AIBU KAMBA MRS KT AMINIYAR ƘWARAI 😊*
*16*
Sauri tayi ta ƙarasa zuwa gadon jikin ta na mazari idanun ta na ƙaiƙayi zuciyar ta na kwaɓon ta a'ah fah
halan sakamakon zullumin da take yi da saka abin a ran ta shi yasa deception ya riske ta dan dai ta
amince da mafarke mafarken da take yi but unluckily enough for her tana zuwa hannun ya daina motsi
zama tayi daɓas a kan kujerar da ke kusa da side drawer sai ga hawaye na tsere a kan kyakyawar angelic
innocent face ɗin ta babu kwalliya a fuskar amma is naturally glowing saboda irin hutun da yake samu
haɗe da kula,kai hannun ta tayi kan comforter ɗin ta yaye gefen da ta ga kamar yana motsi ta ƙurawa
hannun ido sai kallon hannun take yi kamar ta mai magana ta ce ya motsa kusan 5 minutes tana kallon
hannun ko zai motsa amma bai motsa ba sai ta cigaba da kuka mai cin rai kukan tsakanin ta da Allah take
yin sa dan har shesheƙa take yi kasa furta komai tayi sai kukan dan shi kaɗai ne mafita a gare ta ta ɗau
lokaci tana kukan daga bisani ta miƙe ta gyara mai comforter ta juya ta fita ta koma ɗakin ta breakfast ta
taɓa kaɗan ta yi saƙo ta telegram dake ɗakin dan a kawo mata morning drug na ta because 6am
medication ya wuce sai dai na 6pm jim kaɗan sai ga nurse ta shigo suka gaisa ta miƙa mata medication
ɗin ta sha sannan ta fita ita kuma ta kwanta cikin wani hali tun tana iya fidda hawaye har dai bacci mai
nauyi ya ɗauke ta..
Da Bahajjatu ta dawo ta iske ta tana bacci sai tayi mamaki kuma da ganin baccin an san ba na daɗin rai
bane na wahala ne dan ga shatin hawaye nan a kan fuskar ta kuma breathing pattern na ta ya chanza ba
kamar mai bacci cikin kwanciyar hankali ba sai ta tausayawa aminiyar tata duk a tunanin ta tsaban
tausayin ɗanuwan ta ne ya sa ta kasa sukuni sai ta zauna ta zuba mata idanu tana kallon ta shigowar
Hajiya Zeenat ne ya sa ta miƙe da sauri ta ce
"Umma yanzu ta sami baccin dan jiya a wahale ta yi baccin ba mai daɗi ta yi ba please kar a tashe ta"ta
saka fuskar tausayi sai ta bawa Umman dariyar ta ce
"Toh Allah ya baku haƙuri dama dubiya na zo yi kafin mu tafi dan jiya Abban ku ke sanar da ni wai in
shirya zamu tafi Nigeria mu dawo nan da sati ɗaya kuma late notification ya bani shi yasa na zo sallamar
ku but an kora ni shikenan ni na tafi"tayi maganar tana mai dariyar Bahajjatu da ta haƙiƙance akan ita
dai kar a tayar mata da aminiya.
Dakatar da ita tayi ta hanyar ce mata
"Umma please in kun tafi akwai wata yarinya a kusa da da boutique ɗi na da ke kusa da parks and
garden suna da babban manicure da pedicure na gargajiya suna ƙoƙari please umma ki ce ni da kai na na
ce ta haɗo min items da ake haɗawa a gyara jiki irin dai wanda take min ta haɗo da steps da ake bi dan
haɗa su da amfani da su wai na ce first grade manicure treatments nake so ba 3rd grade da suke yiwa
mutani ba saboda ina ta trying line nata amma baya shiga kuma private line ɗi na bana son kiran ta da
shi please Umma ki aiki Bilal ya amso min dan in na ce ya amso min da kai na ba zai tafi ba kuma ina
buƙatar su ne"girgiza kai kawai Umma tayi dan bata gano cewa Bilkisu ake son yiwa gyaran ba sai ta ce
"Toh le Baha in ban da abinki kina nan Bilal na chan wa zaki yiwa gyaran jiki"??sai a nan ta jo kunya dan
haka ta ce
"Laa Umma wallahi ma kaina zan yi ba shi ba..please Umma kar ki bari Ammi ta sani if not sai ta fara
faɗan bata yarda ba please"murmushi Hajiya Zeenat tayi dan yaran na su Allah ne ya taya su rainon su
bisa tsaftattaciyar tarbiya dan a zamanin yanzu yaran da ke jin kan su waɗanda shekarun su ma bai kai
na su Bahajjatun ba muddin suka ga suna aikin kan su basu da wata matsala toh kuwa ganin kan su suke
kamar sarakai iyayen nasu ma a hoto suke kallon su but su sai Allah ya kare masu nasu ƴaƴan gasu dai
gabaɗayan su aiki suke yi but har yanzu fear da aka yi installing masu tun yarintar su tana nan bata fita
ba dan haka basu iya yin abu kai tsaye daga matan har mazan har da ma dai su iyayen sun kasance masu
son hutu masu yawon buɗe ido ƙasa daban daban most of the time suna barin yaran ba tare da masu
tsaro ko duba su ba saboda sun yarda da tarbiyar da suka basu sun kuma san ba zasu yi abin da zai janyo
masu matsala ba.
Bayan ta gama tunanin rayuwar su sai ta kalli Bahajjatu ta ce
"Alright shi da kan sa zai karɓo miki maybe ma ya kawo da kan sa dan na san dai shi za'a wa kwalliyar
kuma ba zai kyautu a ce an yi abu dan shi ba sannan bai gani ba"sai tayi dariya itakuma ta murmusa kafin
ta ce
"A'a fah Umma ni ba ni zan yi gyaran ba ajiyewa kawai zan yi zuwa wani lokacin"ta faɗa tana mai juyar
da fuskar ta sai Umma ta yi dariya ta ce
"Kan ku ake ji yaran nan muma mun yi wannan har ma wanda ta fi naku za ma ku dawo kan hanya
ne"daga haka ta fita abin ta ta nufi hanyar ɗakin Zaid dan ganawa da Hajiya Madina sabida basu sami
damar yin magana ba a daren jiya sakamakon tsalawa da dare yayi kuma a lokacin prof ke sanar da ita
batun tafiyar wanda ta ga bai kyautu ba ta kira ta a daren kai tsaye shi yasa ta bari har yau dan ta mata
bayanin abin da zai mayar da su gidan
On reaching there ta hango ta zaune tana danna wayar ta kamar dai abu mai muhimmanci take yi a
wayar sai ta yi sallama ɗagowa tayi ta amsa mata sallamar haɗe da cewa
"Hajiya har kun uso da wurwuri haka"?ta faɗa tana mai ajiye wayar a gefe.amsa mata ta yi tana mai
zaunawa ta ce
"Eh har fah mun iso Hajiya,mun tashi lafiya"amsa mata tayi suka tambayi junan su how their night went
bayan hakan ne Hajiya Zeenat ta sanar da ita cewa komawa Nigeria zasu yi ta kuma sanar da ita dalilin
komawar su but bata gaya mata har da dalilin maganin Zaid da zasu karɓo ba ya sa zasu tafin
"Toh da ƙarfe nawa jirgin naku zai tashi"?tambayar da Hajiya Madina ta mata kenan sai ta numfasa kafin
ta ce
"Ya ce jirgin ƙarfe tara na safen nan zamu bi shi yasa ma na yi saurin zuwa ina ganin ya sanar da Dr ai"
"Eh toh ba shakka maybe sun yi maganar but tafiya da wurwuri haka short notice Allah dai ya kai ku
lafiya,kuma kika ce 1week kawai zaku yi"?amsa mata Hajiya Zeenat tayi ta ce
"Eh,ni kaina na rasa me yasa ya kasa sanar da ni tun da wuri sai tsakiyar dare nima ban shiryawa tafiyar
ba but kin san halin prof komai sharp sharp ne"sai suka ɗan dara dan gaskiya prof duk da tsufar sa na
tsayin shekaru dan a wasu yankin mutum mai shekarun sa ba su iya yin abubuwan da yake yi but shi
sakamakon agility na sa da tun yana ganiyar shekarun sa ya kasance a jinin jikin sa sai abin ya bisa har
tsufar sa ko a asibitocin sa in har aka kawo wasu cases da su yaran yake basu wahala wato young doctors
da ke aiki a nan,shi ake kira shi ke iya handling hakan ya sa sunan sa bai bar yaɗa asibitoci ba dan
banbancin su da Dr Maher shi ne shi prof komai na ƙarfi ne wanda Bilkisu ta kwaso shi a wannan fannin
dan itama haka take komai na ƙarfi ne bata damu wai she is tiny ba all she knows shi ne in har ta saka
hannun ta a jikin mutum da sunan surgery ko treatment bata ɗagawa sai an sami sakamakon da ya
gamsar da ita while a fannin Dr Maher kuma komai nashi cikin sanyi da lumana yake yi dan shi gani yake
lokacin aikin ƙarfi ya wuce a wurin sa dan haka yake barin young doctors na taking over a asibitin sa
iyakar sa ya basu shawarwari masu amfani shi gani yake yanzu ƙarfin sa lies only in his wife's wish kuma
shine yawace yawacen da suke yi wanda shi kuma Dr Zaid ya ɗauko sa a fannin lumana sai dai shi bai da
sanyin jiki when it comes to work he is very active..
Ɗan hira suka taɓa suna cikin hiran ne wayar Hajiya Zeenat ya ɗau ruri,cirowa tayi daga jakar ta ta duba
sai ta ga mai kiran murmushi tayi ta kara a kunnen ta ta ce
"Gani nan zuwa prof kaii ni Allah nagode ma"ta kashe wayar tana tashi tsaye Hajiya Madina ma tashin
tayi tana dariya ta ce
"Ba dai har ya gama ba"
"Hmm ya gaman kenan shi fah prof akwai asassawa wallahi musamman in ya ga ina ɗaga mai
ƙafa"dariya suka yi suka tafa sannan Hajiya Madina ta fara fita ita kuma Hajiya Zeenat ta nufi gadon Zaid
ta kalle shi kafin ta ce
"InshaAllah zaka farfaɗo Zaid cikin hukuncin ubangiji"addu'ar da ta mai kenan ta fita.
A daidai bakin ƙofar ɗakin suka yi kiciɓis da prof yana magana da Dr Maher jiran su suka yi har suka
kammala wanda a nan suka yi bankwanan sai sun dawo dan babu wanda zai kula da Zaid in suka ce
rakiyar su zasu yi.
Cab ne ya kai su har airport bayan ƴan wasu mintuna jirgin ya tashi addu'a suka yi daga haka suka shiga
tattaunawa akan batun abin da zai kai su Nigeria wanda muhimmin abin shine maganin Zaid da zasu
karɓo,wanda already sun yi wa Dr Ruzu bayanin komai kuma yayi fixing masu appointment wanda shine
dalilin dawowar su cikin gaggawa ba tare da sun shirya ba dalili na biyu shine extensive injury da wani
yayi sustaining wanda daga Dr Afzal har sauran doctors sun kasa sanin yanda zasu yi suturing for almost
a month ana fama da shi da an ɗinke nan sai chan ya kunce da an ɗinke nan chan ya kunce wanda daga
baya dai barin sa aka yi dan an gano cewa cutar Human immunodeficiency virus ne da shi(HIV) saura
kaɗan ma ya shiga Aids dama duk mutum mai wannan cuta in har ciwo ya ji kokuma aka ce aiki za'a mai
toh akan sami matsaloli irin haka sai ayi ta ɗinke ɗinke amma ya rinƙa kwancewa a rasa dalili(Toh dalilin
shine jinin jikin su ya rigada ya lalace da ƙwayar cutar wanda a taƙaice dai jinin sa ba mai ƙarfi bane
kuma duk inda mutum ke ciwo jini yana ɗaya daga abubuwa da ke taimakawa healing process a nan sai
aka sami akasi jinin ya zama marar inganci madaɗin ƙwayoyin sinadarai da ke jinin da ke taimakawa dan
ciwon ya warke ya rufu ba tare da an sami matsalar invasion of foreign bodies ba sai ya kasa aiwatar da
aikin nan instead sai ciwon da ake ƙoƙarin warkarwa ya rinƙa faɗaɗa yana buɗewa saboda jinin da ke
taimakawa wun circulating a area of injury is infectious and non sterile daga haka sai a rinƙa cewa
mutum na da ƙan jiki,kokuma a ce ai gado yayi dan duk ayarin gidan su haka suke in sun sami matsalar
da ya yi necessitating surgery toh ko an yi ba'a dacewa daga haka maganar so called "our village people"
will come to play a nan za'a fara suspecting ana blaming ancestors da cewa they cast a strong powerful
curse a family na wani ko na wance gashi nan ɗa ko jikar wani ya sami hatsari an ui ɗinki sau ba adadi
amma abin bai yi ba in ba mutanin su ba wa zai janyo wannan rashin dacen blah blah blah sai a ƙarshe in
akwai mai zurfin tunani sai ya ce ko dai gwada jinin sa za'a yi dan a ga meye musabbabin ƙin zaman aikin
da ake mai toh sai a nan ne za'a gano wai yana da cutar sai kuma zagi da hantara ya dawo kan sa a fara
jeopardising nasa a community forgetting that mutum na iya contacting cutar ta hanyoyi daban daban).
They arrived safely and Bilal was the one that picked them daga airport yana ta zumuɗin jin ko Zaid ya
farka ne amma bad answer ɗin nan ya samu wato not yet sai mood ɗin sa ya chanza a nan ya tambayi
lafiyar twinien sa har gida bai bar su sun yi sukuni ba sai da motar ta tsaya suka fito suka yi cikin gida
inda gabaɗayan family ɗin ke jiran dawowar su daga jamil da matar sa haɗe da baby zarah,Lukman da
sauran ma'aikatan gidan farinciki ne ya luluɓe su ganin familyn na su all present except baby doctor da
ke chan ƙasar samin lafiya.
Welcome pleasantries aka yi exchanging daga nan baby zarah ta nufo grannyn ta ɗaga ta tayi tana mata
wasa har dai ta haura da ita sama tana mata tsiyar kar ta ƙwace mata mijin ta dan idanun nan irin na
Bilkisu ta kwaso dara dara,dariya kawai jama'ar falon ke ta yi har shima prof ɗin.
A ranar dai sai chan wuraren 10pm suka kwanta inda su Jamil da matar sa suka koma gida yarinya ta
tafi wun iyayen ta ta ƙi ita kuwa Hajiya Zeenat ta ce ai sai ta yi dan ba ta kwana mata a gida salon mijin ta
ya ve yana so an yi rarrashin amma ta ƙi ji da bori da botsarewa aka danƙwafar da ita aka saka ta baccin
dole da haka suka koma gida dan Hajiya Zeenat ta sanar da su in dai yini ne guda ta yarda ƴaƴan su su yi
mata amma kwana baza ta lamunci haka ba ta raini iyaye ta raini ƴaƴan su ba zai saɓu ba..
Basu kwanta ba sai da Hajiya Zeenat ta shirya mai komai na washegari dan Dr Ruzu zai fara visiting kafin
ya tafi asibitin wanda ya kai su har ƙarfe 12 na dare sai a lokacin suka kwanta,washegari da wurwuri ya
shirya shi kaɗai yayi tafiyar sa zuwa HRR&T dan tun 7am ya bar gida bai kai ba sai 8am a hakan ma dan
ya saka speed a tafiyar kenan saboda yayi ya gama ya wuce asibitin dan ganin in case ɗin nasu ne in
kuma na referring ne sai a yi providing referral means dan abin na worsening each day.
Yayi nasarar zuwa har ma ya gana da shi ya kuma mai bayanin dalla dalla Alhamdulilah ya bashi
magungunan game da prescription da yadda za'a yi administering komai ya mai bayani suka yi settling da
girmamawa suka rabu and yhe very good and sweet paer of it Dr Ruzu ya sanar da shi cewa matuƙar aka
fara mai medication yadda yayi prescribing in less than a week yana iya farfaɗowa abin nan ba ƙaramar
daɗi ta yiwa prof ba dan har kasa ɓoyewa yayi sai da ya kira Hajiya Zeenat ya labarta mata komai ai ko
har guɗa tayi dan murna mata ba'a rabasu da budi'a sai da ya tsawatar mata akan godiya zatawa
ubangiji da ya ɓullo masu da waraka a sauƙaƙe ba guɗa ba sai a nan ta ta