Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   74 / 74

219K to 221.1K   out of 221.1K words

ta farko sunan Umma za'a saka in namiji ne
kuma sunan Dr Maher za'a saka..

Sanar da ita yayi tayi murmushi tana kallon sa sai ya ɗora da cewa

"Zamu na kiran sa da khalifah"gyaɗa mai kai tayi tana mai jin daɗin hakan sai ya ɗora mata babyn a jikin
ta suka cigaba da kallon babyn suna ɗaukar hotuna kala kala..



Gyaran murya suka jiyo daga bakin ƙofar sai suka dawo daga duniyar shirmen da suke yi,wayar sa da ya
ɗaga sama da nufin kashe maau wani selfie ne yayi ƙasa da shi yana mai son saita kan sa dan mantawa
yayi a asibiti suke..



Ƙarasa shigowa tayi tana murmushi ta ce

"Congrats doctor ina taya ka murna fah"sai ya wani sunne kai ƙasa yana faɗin

"Nagode aunty Zee"ba ita kaɗai ba hatta da Bilkisu dake ta ɓoye dariyar ta tun ɗazu sai da ya fito suka
dara ita da Zee

"Yau kuma ni ce aunty Zee doctor"?sai yayi murmushi yana mai kallon Bilkisu ya mata alama da ido daga
haka ya fita ya bar masu ɗakin suka gaisa ta karɓi baby tana yabawa haɗe da saka mai albarka...



Sai dare around 8 aka sallamo su inda a nan ne kuma daru ya kaure dan Baha tayi conveying saƙon
Ammi akan nan gidan za'a kawo Bilkisu shi kuma ya dage da faɗin bai san zancen ba ai Ammin bata sanar
da shi haka ba moreover a ina ake wannan wankar azabar shi fah kar a kawo mai al'ada da bidi'a matar
sa a gidan ta zata yi wankan jego kuma ba zai lamunci wankan ruwan tafashen nan ba haka kawai a saka
mata hawan jini da zubar jini ba gaira ba dalili...



Kiran Ammi Bahajjatu tayi ta sanar da ita komai sai ta ce a bar su su tafi chan gidan Bilkisun in ya so sai a
samo mai kula da ita ta rinƙa yi mata al'adar jegon..

Da haka aka wuce gidan Bilkisu inda tana zuwa gida aka kai ta ɗakin Zaid ɗin dan ta samu ta huta sosai
shi kuma aka ja mai layi da shigar ɗakin sai da ƙwaƙwarar dalili wannan dokar Ammi ne ya amince da
hakan than a ce matar sa sam bata kusa da shi shi yana gida ita tana wata uwa duniya...



Tun da aka yi haihuwar nan Bilkisu bata wani sami hutun kirki ba dan jama'a ne ke tururuwa akai akai..
Yau kusan kwanaki biyar kenan da haihuwar ana kan shirye shiryen suna ita kuwa mai jego an mata
adon gargajiya da ƙawatarwa dan zanen ƙunshi ja aka mata a ƙafar ta da hannun ta aka mata kitso masu
ɗan girma dan kam da ƙyar aka yi kitson kasancewar tana gaba da kitso ko kusa bata son kitso,an mata
kalailaya ta ƙara fitowa shar da ita ga jikin ta ya fara dawowa dan tana samin kulawa sosai ba laifi..

Haka babyn ta yaron akwai kyawun kallo dan har ana faɗin tana da nono mai kyay yaron MashaAllah..

Angon ƙarni kuwa ba'a magana an yi family abu kaɗan sai dai in ba'a yi magana ba amma zai ce _kun
san am a family man_abin ya zame mai jiki already..

Kula iya kula yana ba matar sa duk wasu needs ɗin ta yana ƙoƙarin sauke mata su ba laifi haka zalika
yana kan nuna mata how important she is to his life..



A ranar suna aka bayyana sunan baby da inkiyar sa ranar Hajiya Zeenat da Hajiya Madina baki ƙin rufuwa
yayi barin ma Hajiya Zeenat da tun da aka yi haihuwar bata ga babyn ta ba her baby is now a mother,sai
a hoto ta gan ta dan Bilal bai rabuwa da saka ta ɗaukar mai hotunan babyn da nata kanta sometimes...

An yi suna lafiya an rabu lafiya sai fatar samin albarka da ribar ɗa..a ranar da aka yi sunan ne da dare
Bilkisu ta sami sarari ta kira Zaid a waya ya zo ta falon bayan su suka keɓe inda take tambayar sa labarin
Asma'u dan tana buƙatar nemar yarinyar ta bata haƙuri..

Nan ya bayyana mata ai tun da suka tafi ɗin nan ya saka Dr Hussain ya mata alkhairi daga gare sa ta
hannun shi Dr Hussain ɗin dan kar ta gane taimakon kuwa shine ya rinƙa assisting nata financially har ta
haihu lafiya after ta haihu kuma an kai ma Mudan ɗan sai ita a nema mata makaranta ta fara zuwa since
she have the zeal and passion in ya so a hankali tana karatun har Allah ya kawo mata mijin aure...

Yake ce mata

"Unfortunately,,ta haihu amma babyn ba rai sakamakon yawan damuwar da ta sakawa ran ta so Dr
Hussain ya mata bayanin ni na turo sa ya kuma nemi da ta amince ya saka ta a school dan rayuwar ta ya
inganta and she agreed he was able to put her through ya ma yayan ta bayanin komai and they agreed
after long argument akan abin yayi yawa so presently da nake magana da ke Asma'u ta fara zuwa school
yanzu da haka tana aji biyar dan dama tayi da fari kawai rashin natsuwa ne ya sa bata cigaba ba dan dole
yanzu aka mai da ta baya saboda ta tuno abubuwan da ta manta and she is leaving much more better
and comfortable more than the way you think"tausayin ta ne ya kama Bilkisu sai ta nuna mai inshaAllah
suna gama puerperiun nasu zai raka ta su gana da Asma'u she have to contribute positively to her life..

Hakan ya ma Zaid daɗi and he praised her for the zeal she got...



****************
Yau da gobe bai bar komai ba life was a success for Asma'u dan yanzu tana matakin ƙarshe a ajin JSS har
sun rubuta Junior WAEC ɗin su sakamako kaɗai suke jira,sosai tayi concentrating tana karatun ta dan ta
san shi kaɗai ne legacy nata da wanda zata bar wa ƴaƴan ta as for the relationship tsakanin ta da ɗan
birni babu abin da ya sauya tana mutunta sa fiye da da shi da matar sa dan sun mata alkhairi ba adadi
bata da abin cewa gare su sai addu'ar gamawa da duniya lafiya,sam bata sauraron maza a cewar ta ilimi
ta fiye mata dan ta gwada sauraron ɗa namiji amma bai bar mata tambari mai kyau a rayuwar ta ba a
kullum in ta tuno da rayuwar ta na da a ƙauye sai ta ji kamar ta tariyo lokacin ta goge duk kurakuran da
ta yi a lokacin but nevertheless yanzu ma Alhamdulillah dan bata rasa ci,sha,lafiya da sutura ba tana nan
dai tana aikin ta a gidan Hajiyar birni wato inda yayan ta yake aikin gadin sa lafiya ƙalau suke zaune babu
tsangwama bate hantara she can say that life is extremely sweet for her bata da wata danuwa sosai
yanzu....



As for Aslam kuwa ya rungumi matar sa suna zaman su lafiya yayi setting hospital ɗin kan sa yana
running kuma he has 1 kid and matar sa na da cikin na biyu shima kam bai da wata matsalar rayuwa
apart from taking care of his family..



Lukman ya sami mata ya aura 2 years back kuma har Allah ya albarkace su da albarkar aure sun sami
baby girl mai sunan Hajiya Zeenat abin sai Alhamdulillah.

Yayin da Afzal da Bilal ke da ƴaƴa bibbiyu dan kamar kusan tare matayen su ke ɗaukar ciki,su dai Ammi
da Umma kam abin gaba ya kai su a tara masu jikoki..



Hakim was able to invent the mechanical electro machine mai kula da lafiyar bugun zuciyar ɗan adam
yayi lunching machine ɗin a nan ƙasar tamu ta Nigeria kuma ya sami alkhairai da recognition ba kaɗan
ba presently ana anfani da machineries ɗin a cases na cardiac patients wannan babbar cigaba ne a gare
su shi da ahalin sa..he has a girl he wanna marry ba'a rigada an yi fixing date ba sai mu ce Allah ya sanya
alkhairi..

Babban yaya jamil kuwa matar sa ta haifi wasu twins ɗin after baby Zarah,abokantakar su shi da Dr Zaid
sai abin da yayi gaba very smooth relationship..



Hajiya Madina da Hajiya Zeenat kuwa haɗe da mazajen su rayuwa ta masu daɗi sun tara jikoki ga ƴaƴa
abin tubarkallah dama akan bar wani abin dan wani abin a yanzu kam sai su kai wata shida basu tafi
yawon buɗe idon ba dan jikoki kam basu bari a kowani sati nan suke yini wasu ma su kwana masu ƙyuya
ke bin iyayen su su koma gida so they can also say that life is comfortable with them...
***********

Gudu yake ana bin sa da wandon makarantar,haka kamar tayi kuka ta ɓata fuska ta shiga kiran sunan sa

"Khalifah ka rufa min asiri kar mamin ka ta fito ta ga baka shirya ta tsige ni"sai ya saka mata dariya yana
gudu sau uku suna rounding parlorn ya ƙi tsayawa sai chan ga wata serious heavily pregnant woman na
saukowa cikin shigar doguwar riga da gyale ta yi rolling a kan ta,flat shoe ne a ƙafar ta dan ƙafar baya
amsar takalmin gayu sakamakon kumbyrin da yayi na masu nauyin ciki..

Tana kallon su har yaron ya haɗa ido da ita yana faɗin

"Mami kin ga Lauretta tana cewa in kika fito zaki tsige ta ko,,mami menene tsigewa"?yaron ba dai
wayon tambaya ba komai ya gani sai ya tambaya ita kam bata iya mai dan ji da kan ta take sai dai in
Abban sa na gida ya biye mai

"Khalifah ban sani ba ke kuma Lauretta zam dawo maki ne"sai ta kaurara murya tana faɗin

"And you,,,koma ka tsaya a ƙarasa shirya ka tun kan rai na ya ɓaci da kai"salin alim yaron ya kai kan sa
aka saka mai kayan makarantar sa sannan aka ɗora mai da wata ƙaramar lab coat,pink paediatrics
stethoscope aka saka mai round his neck aka sagala mai eye glasses kamar medicated amma ba
medicated bane..

Sak yaron ya fito a siffar doctor sai mahaifiyar nasa ta zo kusa da shi ta duƙa da kyar ta manna mai kiss a
goshi tana faɗin

"That's my boy let's go Abba is waiting outside"daga haka suka fito tare da shi suka doshi wata red
tinted car da ke faman ƙyalli,..

Buɗe ƙofar aka yi daga ciki ta zauna ta ɓangaren da aka buɗe ɗin sai aka fito aka zaga aka buɗe fannin
baya aka saka boy ɗin daga haka aka tayar da motar suka bar gidan..

"My girl amma dai wannan cikin ƴan biyu za'a sulluɓo mana ko kin ga tsakanin cikin nan da haihuwar
khalifah is exactly 4 years"hararar sa tayi tana faɗin

"Hero in ka ishe ni da zancen twins ɗin nan ina iya barin ku ku tafi foundation ɗin nan ku kaɗai ka ga ba
zaku sami abin teasing ba ai"ƙumshe dariyar sa yayi dan wannan cikin nata ba kamar na fari ba saurin
masifa ne da ita ga saurin fushi ko a office yake in ta kira sa bai ɗaga ba ta rinƙa faɗa kenan gashi shi
kaɗai ke running hospitals ɗin dan Afzal kam ya ce bai ga ta zama a nan ba Canada ya koma shi da matar
sa toh taimakon sa Hakim ne in yana da time amma duk ayyukan shi ke handling nasu sannan yayi
handling masifar ta da ita kan ta.



Daga baya yaron ya ce

"Abba haihuwa Mami zata yi"juyowa tayi ta ce.
"Ba'a sani ba"ai ko uba da ɗan suka saka mata dariya sai ta ɓata fuska alamar ran ta ya ɓaci cikin sauri ya
ce

"Am so sorry Dr Hajiya Bilkisu Muhammad Zaid ki gafarce ni ni da ɗa na bamu ƙarawa"kwafa tayi daga
haka suka cigaba da tafiya har suka zo inda zasu zo ɗin inda ya kasance wani NGO foundation ne da
Bilkisu ta saka Zaid buɗewa saboda a rinƙa taimakawa mutani tun daga kan Asma'u she learnt to
become more helpful and kind to people..

Wurin cike yake da yara kala kala sun saka kayayyaki na different fields
lawyers,nurses,doctors,pilots,Engineers,Police,soldiers duk kowa da presentation ɗin da zai yi shi yasa
Maher junior wato khalifah ya saka na field ɗin iyayen sa dan that is what he wanna become in future..

Sun yi presentation ɗin su lafiya an bada gifts da awards Bilkisu da mijin ta haɗe da ɗan ta suka kamo
hanyar gida already ta gaji tausa take buƙata kafin tayi bacci dan cikin nan na bata ciwon kai..



Toh gashi nan dai ciki ya girma haihuwa yau ko gobe ko me za'a haifa wannan Allah ne masani....




*Alhamdulillah MashaAllah*



*_Allah nagode maka da ka nuna min ƙarshen wannan littafi mai taken IYA RUWA FIDDA KAI (The Love
Saga)lafiya kamar yadda ka nuna min farawar sa lafiya ya Allah ka gafarce ni kurakuran da ke ciki ka sa an
amfana da abin da ke cikin sa na alkhairi*_



*_Ni Siyama ibraheem nake maku fatan alkhairi sai mun haɗu a wani karon cikin sabon littafi na mai
taken

BAMBANCIN ƘASA!!! InshaAllah but is not coming any moment soon amma zan ce da ku kar ku bari a
bar ku a layin baya dan kuwa zai zo ne da salo na daban siga mai birgewa,till then,na barku lafiya.._*



*_S,Ibraheem_*

74 / 74