Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
wannan mood swing ɗin zai fara mai sai yayi isolating kan sa
dan baya son affecting mutanin kusa da shi unlike Hakim da bai da control of his emotions and anger he
break it out bai iya ɓoyewa...
"Can we go home now"cewar Afzal
"Sure brother"ya bashi amsa daga nan suka cigaba da tafiya har suka iso gidan buɗe ƙofofin motar suka
yi suka fito Afzal ne ya fara shiga ciki kafin Hakim ya biyo sa sam fuskar sa babu walwala ko kaɗan dan
haka ma masu aikin gidan sun lura suka kama kan su amma still sai da mai girkin ta fuskanci masifar sa
dan bata gama arranging abinci a kan dinning ba..
Jiki na ɓari ta rinƙa bashi haƙuri dan ba kasafai ya ke samin saɓani da ita ba bai ma cika shiga sabgogin
su ba ya fi yi da masu tsaftace gidan.yau ganin tambotsan sun motsa ta mai uziri Afzal have to calm him
kafin yayi shiru
"But brother kana fah gani bata gama shirya maka abinci ba kusan an hour aikin me take yi in fact ta tafi
she is fired bata da amfani"tarar numfashin sa Afzal yayi ya ce
"Common Hakim ina mun gama da maganar nan tun a hanya?ban ce magana ya wuce ba?why must
you start the unnecessary blame?kana ganin hakan shine mafita a gare ka?in har ba ka fara controlling
fushin ka ba Hakim i fear you won't get a wife trust me"ya juya ya fara hawa kan benen sai ya dakata ya
juyo ya ce da shi
"And apologize to her she is old enough to be your grand momma humm"?girgiza mai kai yayi bayan ya
gama haurawa ya juya ya ba ma matar haƙuri dan kam in bata yi sa'ar granny ɗin sa ba toh zata girmi
dad ɗin sa not even his Ammi shima ya san bai kyauta ba zuciyar taaa ce sai a hankali..
Haurawa saman yayi bai tsaya ko ina ba sai ɗakin Bahajjatu da ke zaune tana amsar reports akan
boutiques ɗin ta,abunuwan da ake buƙata ake sanar da ita akan an yi placing order sai dai sakamakon
bata nan ya sa wasu suka fara zuwa dan withdrawing order ɗin sai dai an basu haƙurin nan da sati ɗaya
komai zai daidaita,abin haushi kamar ta janyo kelita da ke mayar mata da zancen ta tablet ta gaggaura
mata mari take ji sai dai ba hali technology bai kai nan ba sai ta shiga masife ta
"When?when did i hired you to start selling me?when did i ask you to beg some stupid useless
costumers for me?when did i agree to pay you for that?huh"?kamar zaki haka ta koma kelita kam ta ga
tashin hankali da bata taɓa gani ba dama ma'am na da fushi haka but bata taɓa demonstrating ba tabb
ita kam me ya kai ta gaya mata gaskiyar lamarin da ma ƙarya ta mata ko ma juya zancen msybe da bata
sha faɗar har haka ba,tana tsaka da tunanin ta ta ji abin da ya girgiza ta
"You know what?just go you are fired because i hate working with cheap creatures".. Wani irin ihu kelita
ta yi ta tablet ɗin ta fara surutai
"Jesus christ madam please spare me don't do this to me i curse the devil that want to see me in hell i
reject it madam i beg you in the name of Allah almighty don't send me away because i have no where to
go"hanzarin katse ta Bahajjatu ta yi cikin takaicin sunan Allah da ta kira a gurɓace ta ce
"Go to hell go there i guess your parents are there waiting for you right?go and meet them right away
for calling my creator name with no respect i will have to sue you to court annoying thing get lost and
make sure you evacuate that office before i return mtsw"bouncing ɗin ta tayi ta kashe tablet ɗin ta yi
wurgi da shi sai a hannun Hakim dan ya ɗab jima yana sauraron conversation ɗin su a zuciye ya zo but
ganin itama ta zuciyan sai ya ɗan sassauta na sa fushin ya ƙaraso ciki yana son sanin ainihin matsalar ta.
Bata san ya shigo ba sai da ya kira sunan ta
"Baha"!!a firgice ta juyo ta ce
"Na'am waye"?
Ɗan murmushi yayi saboda tsabagen masifa wai da duka hasken da ke haska ɗakin amma bata iya
ganin sa har sai ta tambayi ko wanene..
Zama yayi a saman couch da ke gefe kaɗan da gadon ta yayi crossing ƙafar sa ya miƙa mata tab ɗin
haɗe da cewa
"Me aka maki kike ta masifa bayan kin san na hana ki yawan saurin zuciyar nan"!sai a nan ta gane ko
wanene sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce
"Yaya Hakim can you imagine"??sai ya tsaya kallon ta ya ce
"Menene"?tsaƙi mai sauti ta yi ta miƙe tsaye cikin jin haushi ta ce
"Wai wannan banzar yarinyar mai fuskar shanu wai ita kelita ta je tana roƙan clients ɗi na akan sun ce
sun janye order da suka yi placing dan ban kawo masu akan lokaci ba?ta je tana siyar min da dignity a
wun waɗancan banzayen ƴan uwan ta masu fuskar shanaye?ni saka ta nayi?ko aikar ta na yi?hala gani
take biyan ta na yi na ɗauko ta dan ta rinƙa min iskanci da sunan customer care service provider,my
brother is unwell and yet those animals think that i have time for their useless order i have to deal with
her dan ta ma gama raina ni firing her won't satisfy me huuuh"!!ta furzar da iska daga bakin ta wanda
alama ce ta abin ya ƙuntata mata dan haka miƙa mata bottle water yayi wanda ya tsiyaya mata a glass
tumbler ya san ƙanwar ta sa ya san matsalar ta,matsalar yayan ta ne da na aminiyar ta ya sa duk kowa
take sauke mai fushin ta kuma shi bai ga laifin ta ba dan is normal a wurin sa
Amsar tumbler ɗin ta yi ta ƙwalƙwali ruwan sannan ta ajiye ta koma ta zauna ta na sauke ajiyar zuciya
kamar wacce ta yi race ɗin 50km,bin ta yayi ya zauna ya ɗan bata time dan ta dawo full senses nata,ta
ɗau lokaci kafin ta dawo hayyacin ta sai ta ce da shi
"Ina yaya Afzal ɗin"??kallon ta yayi yana jimamin sanar da ita abin da aka sanar da shi shima sai ya ce
"Yana ɗakin sa yana freshen up"sai ta girgiza kai ta gyara zama ta ce
"And them??are they alright"??tayi tambayar ne cikin tsoro shima ya sani sai ya amsa mata da
"Yeah suna cikin ƙoshin lafiya"bata yarda ba dan babu wanda zai gwada mata halin sa sai ta ce
"No yaya Hakim ban yarda ba ban yarda ba,ba kuma zan taɓa yarda ba tell me me yaya Afzal ya sanar
da kai akan su"?she is out of her conscious mindset already sai yayi amfani da hakan yayi narrating
exactly abin da Afzal ya gaya mai dan ya san ta nan kaɗai zai sami abin da yake so..
She was mad she was insane dan maganganu kala kala ta shiga yi wanda a nan yayi nasarar ingiza ta
har ta amince da buƙatar da ya zo mata da shi ita kaɗai ce zata amince da wannan buƙata ta shi amma
ba Afzal ba.
"Thank you baby sis kin gama min komai da kika amshu buƙatata no more cry no more worries from
now henceforth hum"?amsa mai tayi da kai tana share hawayen ta ce mata yayi ta tashi au tafi dinning
dan cin dinner,she wasn't hungry but saboda yayyen ta sai ta ji kamar ta ɗan sami appetite na cin
abincin.
Bin bayan sa t yi suna saukowa suna magana ƙasa ƙasa a nan ya ce da ita ta ma kelita haƙuri ta mayar
da ita bakin aikin ta dan yarinyar na mata ƙoƙari sosai jin sa kawai ta yi dan kamar ydda yake da kafiya
akan abu haka itama ke da kafiya as far as she is concern kelita is fired and that stay final in ba dan ma
shi da yake yayan ta ba ne kuma ta san halin sa ba da sai ta ce hala neman kelitan yake yi da ya nace da
batun a mai da ta bakin aikin ta,da haka suka ƙaraso dinning table inda suka yi zaman 5minutes dan jiran
Afzal kafin ya sauko yayi joining ɗin su,gaisuwa ta musamman suka yi shi da Bahajjatu ta mai sannu da
zuwa tare da tambayar sa masu jiki ya ce mata da sauƙi dan shi gudun sanar da ita gaskiyar lamarin yake
bai san she is aware of everything ba..
Serving ɗin su aka yi suka fara cin abincin peacefully ya ga har sun yi rabin plate bata ce ƙala ba suka
kusa gama cin abincin bata tanka ba sai ya fara suspecting ko dai an sanar da ita ne but me ya sa bai jiyo
hayaniyar madness ɗin ta ba daga ɗakin sa?ko dai ta gyaru ne ta daina masifar ta da ke yawo a jikin ta
ne?who knows maybe Allah ya shiryar da ita.sai ya basar shima bai ce komai ba har suka gama aka yi
clearing table zata tashi ta wuce ya kirawo ta
"Baha"!!tsayawa tayi ta ce
"Na'am yaya"!
"Zo ki zauna ina da magana da ke"komawa ta yi ta zauna kamar wace ba abin da ke damin ta sai da ya
gama nazarin ta sannan ya tambaye ta
"Wai kin kuwa san halin da yaya ke ciki shi da aminiyar ki"??jijjiga mai kai tayi tana share hawayen ta sai
mamako ya kama shi ya ce
"Wa ya faɗa maki"?ta ce
"Yaya Hakim ne"shiru yayi yana tunanin anya ba sauƙi daga Allah bane ya fara zuwar masu seeing that
yayi wa Hakim nasiha ɗazu ya ji yanzu kuma Bahajjatu ta san labarin abin da ke faruwa but yet bata yi
reacting ba?what a miracle yayi exclaiming kafin itama ya shiga yi mata nasiha ƙarshe ma haɗa su yayi ya
rinƙa yi masu nasihar dan dai ya kwantar masu da hankali daga bisani ya ce da su su je su kwanta su
huta.tashi suka yk suka sallame shi kowa yayi hanyar ɗakin sa shima ya nufi nasa ɗakin da relieve na
samin chanji a gidan na su daga wun ƙannen sa at least sun girma da zasu iya taya sa wurin taimakon
yayan su da baby doctor si yi recovering lafiya ƙalau,with this thought in his mind ya kwanta bacci dan
bai so a kira shi a fara tambayar sa dalilin sa na dawowa sai ya kaahe wayar gabaɗaya he believe Bilal
can handle everything kafin Hakim ya tafi dan shi a nasa ma in ya gama monitoring Bahajjatu ya ga eh
lallai ta yi hankali bata da zuciyar nan da ya san ta da shi sai su tafi tare da Hakim....
Kusan kwanaki biyu yana lura da ita babu abin da ya samo na ganin ido daga gare ta dan haka ya yanke
hukuncin yi mata albishir na tafiyar ta da Hakim zuwa ƙasar germany akan da dare in sun haɗu a dinner
zai sanar da ita dan da ya so su tafi tare da either Lukman or Jamil but dukkan su babu wanda ke
available sai dai in sun dawo daga tadiyar da suka yi.
It was in the morning da suka haɗu wun breakfast yana ma sauri zai tafi asibiti yake sanar da su cewa he
have a surprise for the both of them in ya dawo suka ce mai sun matsu ya sanar da su amma ya ƙi yayi
tafiyar sa.fitar sa babu daɗewa suma suka yi ficewar su..
_10:00pm_
Afzal,Hakim da Bahajjatu,zaune a parlor suna jiran jin me zai sanar da su amma yayi shiru sai chan ya ce
"Guess what"?turo baki tayi ta ce
"Whattt yaya kana ta ja mana rai"!!ɗan dariya yayi kafin ya ce
"Zaki bi Hakim ku tafi germany gobe dan komai naku is well set babu wani abu da ya rage"!!murna ne ya
kama su su duka har ta je ta rungume sa tana ce mai
"I love you yaya i love you so much thank you for allowing me to go visit them"murmushi suka mata
daga baya suka ma Afzal ɗin godiya ya ce da su su shirya tafiyar wuri za su yi,murna ne fal a ran su dan
haka cikin nishaɗi suka yi shirin su suka kwanta bacci....
*************
A chan germany kuwa da Hajiya Zeenat ta gama fushin ta sai ta haƙura ta tafi ta yi wankan ta abincin ne
dai bai shiga sosai ba dan bata jin zai sami masauki a jikin ta ɗiyar ta na kwance sama da sati biyu bata ci
komai ba ina ta ga ƙarfin cin wani abin.
Sai da prof yayi dagaske kafin ta chakwalkwala abincin ta ce ta ƙoshi ta matsar gefe.ce mai ta yi ita sallah
zata yi kafin su koma asibitin ya ce toh shima bari ya tafi dan yin sallar dan haka kiran Dr Maher yayi a
waya akan ya zo su tafi sallah,sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya fita daga ɗakin ta tayar da
sallah shi kuma ya sauko ƙasa dan jiran Dr Maher.
Da lallaɓa da encouraging words ya samu ta haƙura ta yi shiru ta daina kukan har zuwa lokacin da kiran
prof ya shiga ya sanar da ita sallah zasu tafi ta mai Allah ya kiyaye hanya bayan tafiyar sa ne ta yi sallar
itama ta zauna roƙon ubangiji da ya ba ma ƴaƴan su lafiya ya ta da kafaɗun su ba dan zunuban su
ba,sosai ta masu addu'a dan watanni uku zuwa huɗu da aka ɗebar ma ɗan ta akan adadi lokacin tashin
sa ba abu mai wuya bane a wun ubangiji...
Da ta idar ne ta nufi ɗakin su Hajiya Zeenat a inda suka zauna zaman jimamin conditions da likitan ya
zayyano masu game da farfaɗowar Zaid but sun yi realising cewa komai shall be possible da yardar
Allah.ba jimawa suka shirya dan tafiya asibitin inda tare suka fito suka tarar da taxi na jiran su ba ɓata
lokaci suka shiga ya wuce da su zuwa asibitin,ko da suka tafi sai suka tarar da Bilal ne kaɗai suka
tambaye shi inda Afzal ya tafi bai ɓoye masu komai ba ya sanar da su cewa ya koma Nigeria but ya ce
Hakim zai zo dan saboda akwai ayyuka da suka taru da yawa a hospitals ɗin iyayen su and there is no
one to take care of them sai shi kaɗai,
Abin ya ɓatawa Ammi rai har ta fara bambamin cewa aiki ya fi ƴan uwan sa muhimmanci a gare sa
kenan in ba haka ba ana wannan hali har wani aiki mutum zai je yi but Hajiya Zeenat ta yi calming nata ta
ce dole ne ya kula da wani fannin since there is no one to do it da haka dai ta yi shiru not because ta yi
niyar yin shirun sai dan kar ta janyo magana a hospital premises.
Ƙarasa shiga cikin ɗakin baby doctor suka yi inda suka ganta kwance tana bacci kamar dai yadda suka
bar ta this is 3 hours da barin su asibitin but bata tashi ba abin ya dame su sai suka koma chan gefen Zaid
dan ganin ko an sami improvement but shima still a nan gwiwowin su ya fara sagewa shi Bilal mai kukan
ne dai ya ƙarfafa masu gwiwa dan shima jiran zuwan Hakim ya ke yana son komawa gida yayi resuming
aikin sa maybe kafin sati ya wuce zai ji an ce da shi an sami improvement dan zaman sa a nan ɗin gani
yake kamar abubuwan basu cigaba..
Zaman jiran farfaɗowar baby doctor suke yi dan sun san shi kam Zaid ba tashin yanzu yanzu bane.. Cikin
hikimar ubangiji kuwa zaman su babu jimawa suka ji kira daga ofishin likita da suka tafi hints ya basu
akan yanda zasu kula da ita yanzu da ta farfaɗo dan gudun kar ta kuma collapsing kamar yanda ta yi ɗazu
godiya suka mai suka fita suna murnar ta farka..
She is awake and cool dan a zaune jingine da bed cradles suka riske ta an saka mata soft pillow ta bayan
ta tana sipping wani abu da basu san ko menene ba a tea cup rufe da murfi sai straw da take sipping da
shi wanda ya ke ta saman kofin..
Hamdala suka yi na ganin ta cikin sukuni har ma tana iya shan abu tana iya riƙewa da kan ta.ƙarasawa
ciki suka yi a nan aka shiga tambayar ta me ke damin ta ina ke mata ciwo ita dai murmushi kawai ta rinƙa
yi har suka yi shiru ta ce da su
"Am fine am absolutely fine you all can see that am good"!!ta faɗa tana masu murmushi dan hankulan
su ya kwanta sai suka faɗaɗa fara'ar kan fuskar su.tambayar su ta yi
"Ya jikin na sa"?a nan suka ɗan yi jimm sai ta kalle su haɗe da ajiye kofin ta ce
"Is okey kar ku damu zai tashi nan ba da jimawa inshaAllah"daɗi suka ji lallai tana da ƙarfin zuciya ita da
yanzu ta farfaɗo but har tana da ƙarfin reassuring nasu as a doctor,rungume ta Ammi ta yi ta ce
"Allah ya maku albarka ya kuma kare mana ku daga yau sai yau babu ku babu outreach ko da a nan
asibitin ku ne ba ku kuma yi"!a halin jimami ake amma sai da maganar ta ya saka kowa darawa kaɗan
ciki kuwa har da Bilkisun dan a nan ta fara tunanin shine fah ya natse na maganar outreach ɗin nan ita
kuma shegen girman kai ya hana ta ƙin yarda akan ba zata bi shi ba shi dan ya hukuntata ya shirya
tafiyan but at the end of the day abin sai ya juye masu he end at the receiving end ohh Allah ka bashi
lafiya,,a zuciyar ta ta yi wannan analysis ɗin..
Ranar murnar iyayen baya misaltuwa dan haka a nan ɗakin na ta suka kai har dare ta ce da su zata tafi
ganin shi suka ce a'a ta bari har washegari bata gama farfaɗowa ba dan haka ta haƙuran Bilal ne ya taya
ta hira har dare wuraren 11 sannan ya mata goodnight ya tafi dan hutawa yayin da Ammi da Hajiya
Zeenat suka kwana a nan dan a daren aka so yi mata wanka ta ƙi ta ce zata iya da kan ta har tsiya suke
mata wai in bata yarda an mata yanzu ba ma ai akwai na jego dole ma ta yarda jin su ta yi amma ko za'a
haɗa ƙasa da sama ba zata yi wannan wankan jegon miyatar da ake yi ba haka kawai ta janyowa kan ta
matsala.
Da ƙyar ta yi wankan aka saka mata rigar bacci mai kauri da hula abinci ta ce sai washegari dan ta sha
energy booster kafin su shigo haka suka ƙyale