Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
su ba dan haka ta daɗa ɗaga murya ta
ce
"Right"? a firgice ya ce
"Ye...ee...sss yeeee.... sss"sai ya kuma cewa
"Yes yes"abin sai ya bata mamaki toh dama ina hankalin shi ya tafi tana nan tana mai yaƙin sanyin
idaniyar sa shi kuma yana wani tunanin dan haka ta ce da shi
"Are you okey"?saurin girgiza mata kai yayi kafin ya miƙe tsaye ya ce da ita
"Let's get going is getting late"da mamaki ta tashi tsaye ta ce da shi
"Me kuma ya faru ba mu fah gama abin da ya kawo mu ɗin ba kuma kake cewa mu tafi"!!!
"I said let's go"ya ida cikin nuna halin ya fara gajiya da conversation ɗin.
Ƙala ba ta ce da shi ba ta ce da mahaifiyar Asma'u
"Toh mama za mu tafi zuwa goben ma ta na iya fara zuwa karatun in ya so shi likitan sai ya rinƙa rako ta
gida ba ki da matsala da wannan"murmushin gamsuwa ta yi kafin ta ce
"Nagode Allah ya maku albarka ya kare mana ku wannan irin ƙoƙari da kuka min kuka mana a wannan
ƙauye na mi Allah ne kaɗai zai baku lada shi kaɗai zai biya ku"ɗan taƙaitaccen murmushi baby doctor ta
yi ta ce
"Mun gode mama bara mu tafi dare na yi"
"Toh Allah ya kuyaye hanya ga shi nan ta ƙi fitowa tabbatacciyan wai kunya take ji"ɗan darawa ta yi ta
ce
"Hmm mama bara mu tafi"daga haka suka yi sallama shi dai bai ce komai ba har suka yi nisa kafin baby
doctor ta dakata ta ce
"Wait"sai shima ya tsaya ya kalle ta bai ce komai ba
gyara tsayuwa ta yi ta fuskance shi ta ce
"Wai tunanin abin da aka sanar da kai kake yi"?shiru yayi bai ce komai ba sai ta ce
"Toh ai ba abin mamaki ba ne dan ka ji cewa ta na da saurayi you shouldn't be surprise"ta cigaba da
tafiyar ta sai ya ce da ita cikin sanyin murya
"Dama kin san da labarin ne"?dakatawa ta yi tana jin wani iri kafin ta ce
"Yes i know"!!sai ya ji mamaki kafin ya ce
"Tun yaushe"?kasa bashi amsa ta yi dan ya fara bata tausayi dan kuwa ya zurma a son yarinyar da yawa
though is something else not pure love but kamar yana wahala..
"tun ranar da na fara ganin ta a wurin outreach ɗin nan"!! daga haka ta yi shiru tana sauraron sa sai dai
bai ce komai ba ya cigaba da tafiya itama bin sa ta yi a bayan...
*******************
Bayan dawowar su gida sun yi abin da ta dace na yau da kullum wato koyar da karatun da take ma yaran
da iyayen su ta basu assignment ɗin su as usual ta kwanta saman ɗaya kujerar falon yayin da zulfa'u ke
zaune a ƙasa tana gyara zogale na dambun da take son yi washegari da rana kasancewar ita ce da girki
jifa jifa suna hira
Lokaci zuwa lokaci takan tuna scenario ɗin ɗazu sai ta yi dariya ita kaɗai countless time zulfa'u na
tambayar ta amma sai ta ce babu komai karshe dai shiga toilet ɗin zulfa'u ta yi ta danna wa Bahajjatu
kira ringing biyu ta ɗaga.
"Assalamu alaikum baƙin ƙauyen koma"dariya suka saka kafin ta amsa da
"Wa'alaikumul salam matar mu". Dariyar suka ƙara sakawa dan duk lokacin da zata yi shu'umancin ta
toh da shirme suka fara gaisuwar.
"Halan me ya faru ne na ga har goman dare ta yi amma kika danna min kira"
"Ke dai bari wata labari na kawo maki"gyara kwanciya Bahajjatu ta yi ta ce
"Haba da gaske?toh faɗa min ina jin ki"sai da baby doctor ta dara kafin ta ce
"Halan Baha wai wacece budurwar yayan ki"? Da mamaki ta ce
"Budurwar yaya na?wanne a ciki"?
Cikin gatse ta ce
"Bilal"! Doguwar tsaƙi Baha ta ja ta ce
"Ban son wulaƙancin Beelove wani yayan na wa kike nufi"?
Itama tsaƙin ta yi ta ce
"Toh shikenan in kin shirya jin ko wanene sai ki kira ni"cikin hanzari ta dakatar da ita ta ce
"Tsaya tsaya tsaya,kaii Beelove wai menene na wani ɗaukar zafi?babban yaya kike nufi"? Scoff ta yi ta ce
"Toh in ba shi ba dama tare da wa nake"?
"Goodness toh yi haƙuri,babban yaya ai bai da budurwa sai ko in a chan ya samo mana new sister in-
law".
Abin dariya sosai ya ba ma Bilkisu sai ta ce
"Ai ko ya samo maku sabuwar sister in-law apple"ta ida tana me kecewa da dariya
Shiru Bahajjatu ta yi kafin ta ce
"Jokes apart Beelove da gaske yaya ya samo budurwa"?
"Hmm Baha kenan na taɓa kawo maki hirar wannan izgilallen yayan na ki in ban da yau"?
Ta ce"a'a".
"Toh wallahi am serious ya samo wata yarinya kyakyawa mai kyawun kallo sai dai ba natsuwa"!
Miƙewa ta yi daga kan gadon ta diro ƙasa ta ce
"Mene?budurwa a ƙauyen nan?impossible"?
"Hmm Baha kenan wallahi da gaske na ke"a nan ta kwashe duk abin da ya ke ta faruwa tun zuwan su
har ma da tarihin yarinyar ta sanar da ita me Baha zata yi in banda Allah ya raba mana jaha,sai nanata
shi take yi kamar ba za ta daina ba
"Allah ya tsare uhuhm shi kuma yaya haka ya ke son tozarta mu ya daɗe bai yi aure ba sannan ya ce
wannan zai ɗauko?toh ba gidan Dr Maher ba sai dai a chan ƙauyen"?
"Ha'an toh what if in Allah yayi matar sa ce fah?what can you do"? Da sauri ta ce da ita
"Tofar da yawu tun kafin abin ya zama gaske"suka dara kafin daga bisani ta sallame ta ta kira umman ta
a waya.
Ba ta ɗauka ba sai ta kashe sannan ta kuma kiran ta
"Assalamu alaikum umma"
"Wa'alaikumul salam baby ya kike ya garin"?
"Lafiya ƙalau umma ya na ku"? Sai ta yi shiru alamun tana jin nauyin ta sai ta ɗan yi murmushi kafin ta
ce
"Common umma am serious ya London ɗin"? A nan ta sani relieve sai ta ce
"Lafiya lau baby ungo ku gaisa da Ammin ku"ta miƙawa Hajiya Madina wayar cikin raha ta ce
"Baƙin Yola ya kuke"?itama da fara'a ta ce
"Lafiya ƙalau Ammi"
"Ina my boy ya ke ban ji kun kira tare ba"
"Ammi yana ɗakin shi maybe yayi barci nima barcin zan yi"
"Noo i need to speak with him akwai muhimman magana da nake son yi da shi please call him".shiru ta
yi ta rasa ta yaya zata fara kiran shi zuwa ɗakin mace kuma har cikin privacy ɗin ta sai ta ce
"Ammi i can't"!!
Cikin damuwa ta ce
"But why baby?koh ya ɓata miki rai ne"she was sounding emotional already dan haka cikin sauri ta ce
"No Ammi"a nan ta sanar da ita dalili sai ta ce
"Alright na fahimta yanzu dai zan sanar da ke saƙobn in kun haɗu sai ki sanar da shi"
"Okey Ammi"
"Kina ji na,in kun haɗu ki ce da shi na ce amanar nan da na bari mai kar yayi wasa da ni ya riƙe da kyau
dan in ya bari na san yayi wasa da amanar toh har abada amanar ta suɓuce mai kenan kuma ba da wasa
nake ba".
Cikin ɗimuwa da zancen dan she was very serious while saying it sai ta ce
"Ammi why me?me yasa ni zan yi conveying mai wannan saƙon"?
dariyar manya ta yi ta ce
"Bilkisu ki sanar da shi jakan dan le kaɗai gare ni a garin da zan iya aika zuwa wun My boy ba tare da na
sami matsala ba dan haka ki sanar da shi shi zai gane me nake nufi"daga haka ta ce
"Alright Ammi zan faɗa mai ki gaida mana su Abba"
"Za su ji baby and don't forget to take care of yourself humm"
"Yes Ammi i will"
Suka yi sallama ta kashe wayar tana mamakin wannan saƙo da aka bata,
Fitowa ta yi ta ga zulfa'u ta daɗe da yin barci dan haka itama ta kwanta ta yi addu'ar barci ta rufe jiki sai
barci..
A fannin su Asma'u kuwa ashe laɓe ta yi ma su Dr Zaid Maher tana sauraron duk wasu kalaman su tana
jijjiga kai suna tafiya ta fito tsakar gidan da ɗaurin ƙirji ta saka kuka tana ta ja kamar jiniya mahaifiyar ta
dai shiru ta mata tana kallon ta tana jiran ta gama darun ta ta kuma assasa mata nata ƙudirin dan haka
ta gama birgiman ta tana surutan ta.
"Kee Asma'u ji ni nan wallahi wallahi kin ji na rantse maki babu makawa babu kaffara sai kin fara
halartar karatun nan na rantse maki ba ki isa ki take doka ta ba ni na haife ki ba ke ba..
Daga nan tayi shigewar ta ta bar ta tsaye nan tana ta birgima..
**************
Washegari wanda ya kasance asabar wuraren ƙarfe 9 na safe suka shirya zasu tafi wurin outreach sun yi
sallama da jama'an gidan sun fito suka shiga taxi a ciki ta fara sanar da shi saƙon mahaifiyar sa kallon ta
yayi sai ya mata shiru kawai itama sai bata kuma cewa komai ba har suka iso..
Da zuwan su babu ɓata lokaci suka fara da masu rashin lafiya suna ba su magungunan har dai ƙarfe 2 ya
kai suka rufe session ɗin ranar suka dawo gida.
Abin mamaki sai ga Asma'u da mahaifiyar ta sun zo wai an kawo ta koyon karatu dan haka babu
tsangwama bare hantara baby doctor ta yi welcoming ɗin ta faram faram.
Mahaifiyar ta ta tafi ta bar ta ita kuma ta zauna nesa da yaran,ba'a takura mata ba ana karatun hankalin
ta na wani wajen sai da aka gama sannan baby doctor ta ja ta gefe ta fara mata nasiha..
"Asma'u kina ganin wani za ki cutar in kika ƙi mayar da hankalin ki a karatun nan?babu fah wanda za ki
zalunta sama da kanki,sarai kin san da a ce mu ma irin halin ki muke yi toh ba mu isa mu zo nan muna
karantar da mutanin garin ku akan abin da zai taimake su ba babu yadda za'a yi mu zo nan mu tsaya har
a saurare mu kin ga duk hakan ilimin mu ne ya janyo mana hakan ke ma ba za ki so ganin kan ki haka ba
Asma'u"? A yanayin yadda ta yi maganar sai ya sa Asma'u ta ji jikin ta yayi sanyi dama chan tana da
hankalin ta kawai dai rashin samin kyakyawar foundation ne ya sa ta bi ta taɓarɓare.
"Ina so mana amma kun ga Mudan baya so dan ya ce ƴan birnin nan cutar da mutani suke yi kuma
karatun boko ai dan a sami abin dogaro ne kuma ya ce shi zai tsare min komai ba sai na yi wani kartun
zamani ba na je na koyo nasaranci shi ya sa ban yarda da son karatun ba tun farko"!
tirkashi lallai wannan Mudan ɗin azzalumi ne wato shi bai yi itama kar ta yi Allah ya raba mu da
mugunta,cewar baby doctor a zuciyar ta
"Amma ke kina son yin karatun"? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce
"Ai ko ina so Mudan baya so kuma in kuka tafi ai shikenan ba cigaba zan yi ba kin ga ai bai da wani
amfani"ta yi shiru daga yadda ta yi maganar mutum zai gane cewa tana da zeal ɗin yin karatun amma
hindrance na Mudan ya sa ta ke withdrawing..
"Hmm Asma'u kenan ai sai dai in baki ba da haɗin kai ba amma muddin kika amince ni na maki alƙawarin
saka ki a makaramtar birni chan cikin Yola ki yi karatu mai zurfi har inda ran ki ke so dan kema ki zo nan
ki faɗakar da mutani su ƙaru wannan alƙawari ne daga gare ni kin yarda"?? Kamar bazata ce komai ba sai
ta ce
"Na yarda amma ina tsoron Mudan kar ya cutar da ku"ɗan dariya baby doctor ta yi kafin ta ce
"In dai Mudan ne babu abin da ya isa ya mana sai dai in Allah ya tsara hakan zai faru kar ki ji komai
kawai ki bamu haɗin kai"!!
Girgiza mata kai tayi kafin ta ce
"toh na yarda zan yi karatun"daɗi ne ya kama Bilkisu dan haka ta ce
"Yauwa ƴar gidan Mudan toh yadda za'a yi ki rinƙ zuwa kafin lokacin sai in koyar da ke in kuma lokacin
koyarwar ya kai sai mu yi tare ko ba haka ba"?girgiza kai ta yi tana murmush.
Ita dai bata sanar da ita cewa Dr Zaid na son ta ba dan kar ta yi amfani da wannan ta ƙi yin karatun ko
ma ta fara jin wani iri kuma in har suka bari Mudan ɗin ya san cewa Dr Zaid na son ta toh lallai za'a yi ƴar
ƙaramar yaƙi su kuwa ba abin da ya kawo su ba kenan..
Dan haka tsara komai suka yi tun a ranar har dai aka fara karatun rumui rumui kafin 6:30pm suka dakata
a inda baby doctor ta tafi kiran Dr Zaid dan shi bai ma san cewa an kawo Asma'un ba,da ya fito ya gan ta
sai ya ce
"Ya aka yi ba dai kuma aiko ki aka yi ba"? Sai ta ɗan murmusa dan ta ga changes a tattare da shi sosai
zuwan su nan ɗin a da ba su ga maciji da juna har ji suke kamar su kashe juna dan haushi but now just a
week + wai har suna iya tsayuwa su yi doguwar maganar fahimtar juna sai ta ce
"A'a ba aike na aka yi ba dama sanyin idaniyar ka ce ta zo muka yi karatu i tried and convince her kuma
ta amince"she explained everything to him murna yayi at least koh ba komai ta nan zai raba ta da
wannan Mudan ɗin sai ya sakarwa Bilkisu murmushin da ya saka ta ɗauke wuta dan bai saba ba bai
kuma taɓa yi mata ba hasali ma ba su jituwa so duk wata murmushin da zai mata na ƙeta ne ba na
tsakani da Allah ba amma yau saboda Asma'u har yayi murmushin gaskuya da gaskiya hmm lallai yana
son yarinyar koh da ma mix feelings ne gare shi a kan yarinyar ba pure love ba he still feel something
special for herdan haka itama murmushin ta mai ta ce
"Ga ta chan sai ka raka ta gida".
Godiya ya mata by saying
"Thanks"daga haka ya wuce ta tana ysaye tana mamakin halayar sa ta burgaggen mutum yanzu sanyi
anjima zafi girgiza kai tayi ta wuce abin ta.
Koh da ta zo zata shiga daga cikin sashen zulfa'u sai ta gan su suna tafiya he felt something strange sai
dai ta bar wa kanta ta shige ciki,.
Abincin daren ta ta ci ta yi alwala ta yi sallah zama ta yi ta karanta Qur'anin ta a wayar ta daga nan ta
tayar da sallar isha'i ta yi azkar kafin ta ɗora da shafa'i da wutri ta yi doguwar addu'oin ta kafin ta kwanta
sai juyi ta ke yi ta kasa barcin duba time ta yi ta ga past 9pm sai ta fito waje ta tsaya a tsakar gidan tana
jiran jin dawowar shi dan bai dawo ba ga abincin sa nan ba'a kai masa ba zulfa'u kuma ta wuce turakar
mai gidan ta a haka ta cigaba da tsayuwa har dai 9:30pm kafin ta ga shigowar sa zai wuce ta kira shi cikin
sanyin murya ta ce
"Sai yanzu kake dawowa a cikin daren nan bayan ka san yanayin garin nan"!! Dakatawa yayi ya juyo a
hankali suka haɗa ido sai ya ga damuwa a cikin idanun ta he became confused takawa yayi zuwa kusa da
ita ya tsaya yana nazarin ta na wasu lokuta before he otter a word.
"Are you disturbed"? Shiru ta yi kafin ta ce
"Am not am just concern"ganaɗayan su shiru suka yi kafin daga bisani ya ce da ita
"Go to bed tomorrow is a new day akwai ayyuka da yawa a kan mu goodnight"daga haka ya wuce ta ita
kuma ta tsaya a wurin tana tunanin abin da ta yi is she scared of Mudan that his violence might affect
Zaid?koh dai wani abin ne na daban? Babu mai bata amsa dan haka sai ta wuce zuwa ɗakin ta kwanta
but still barci bai ɗauka ta ba sai around 12 na dare bata ma san lokacin da barcin ya ɗauke ta ba..
*************
_two weeks later_
Suna last week ɗin su a garin suka fita outreach ɗin su ranar monday a inda suke kuma jaddada masu
cewa ranar asabar zasu koma basu ji daɗi ba mutanin garin dan sun saba ga shi zuwa lokacin mutanin
ƙauyen sun waye da karatun boko da na islama da baby doctor ke koya masu dan har magana suka yi da
Dr Zaid akan why not a yi enrolling yaran a makarantun government sharing suka yi da iyayen yaran
iyayen suka yarda a fannin islama kuma a ka nemo malamai da zasu na koyar da su sun dai sami haske
sosai a wannan outreach ɗin da aka kawo masu,matar da ta sami annular detachment of the uterus an
kai ta city hospital an mata surgery da kyar aka yi replacing uterus ɗin aka bata necessary care har ta
warke kafin a yi discharging ɗin ta gabaɗaya family ɗin matar sun godewa su Dr Zaid da wannan taimako
da suka masu.
A fannin Asma'u da Mudan kuwa abu ya fara ɓaci dan in ya zo hira ko yawon zaga garin shi sai ya ji an ce
mai bata nan bincike iya bincike yayi but he couldn't find anything dan haka ya sa aka fara saka mata
idon lokacin da take dawowa da lokada take fita tsayin kwanaki uku sannan ya sami labarin ai bokan
turai ne ya ja ra'ayin ta ta fara karatun zamani da na addini hakan ba ƙaramin ƙunna shi yayi ba sai ya
ƙudiri sai ya mai lahani ko yanzu koh anjima ita kuma Asma'un ya daina zuwar mata yana jiran ranar da
zai lahanta shu yayi a gaban ta ta gani dan ta dawo hayyacin ta a haka yake yana kuma jiran perfect
timing..
****************
Tun da suka tafi ƙauyen nan baby doctor bata taɓa yarda ta fita after 6 ba saboda garin akwai sanyi ba
laifi ita kuma tana son kiyaye kan ta har su koma gida lafiya but tsautsayi sai ya sa yammar litinin ɗin last
week ɗin su Dr Zaid ya ce da ita wai ta shirya su shuga cikin gari it was 5pm already sai dai bata jin zata
musanta mai dan zuwa lokacin she began to realize that she respect him an so she can't go against his
wish ko da kuwa bata da niyar yin hakan bata san dalilin yin hakan ba ita kanta dan shw just develop
wani irin dislike ma Asma'u whenever she sees them together with Zaid ko me ya sa Allah ne masani.
Cikin riga da wando ta ɗora after dress a kai mai botir ta yafa ƙaramar gyale ta fito ta same