Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ke a sume bata yi tunanin
yayuafa mata ruwa ba sai da ta ga da gaske dai ba farfaɗowar zata yi ba dai ta yi wuf ta ɗebo ruwa ta zo
ta yayyafa mata,numfashi ta ja kafin daga bisani ta farfaɗo ta buɗe idanun ta sai kuka kamar me tana ta
surutai
"Ɗa na Zaid,Zeenat kin ga abin da suka wa ɗa na?kashe min shi suke son yi bai masu komai ba daga
taimako sai su lahanta min shi?ba fah rigima ne dashi ba bai da hayaniya ai ke shaida ce,yanzu a ce
mutum da ransa tsawon satin biyu bai san inda kan sa yake ba?yana duniyar amma gangar jikin sa ne
kawai tare da mu zuciyar sa da rayuwar sa baki ɗaya basu tattare da gangar jikin sa?me suke son yi min?
me suke nufi da ni?so suke su tona min asiri?ɗa na Zaid na mawuyacin hali Zeenat ya zan yi"?maganar ta
gabaɗaya abin tausayi.
Actually both of them are in state of heartache and serious uneasiness amma dole ɗaya ya rarrashi
ɗaya juma the strongest ne zai iya ba ma weak ɗin ƙwarin gwiwa wanda Hajiya Zeenat ce ke da ragamar
yin wannan ɗin dan haka riƙo Hajiya Madina ta yi suka fito zuwa bedroom ɗin ta suka zauna a nan ta
shiga bata magana da hope ɗin inshaAllah Zaid will make it zai farfaɗo kuma zai koma kamar yadda yake
da
"I hope and pray for that"cewar Hajiya Madina tana share hawayen ta daga haka kiran Dr Muhammad
Hajiya Zeenat ta yi dan sanin halin da ake ciki...
A chan parlorn ƙasa kuwa zaman Bilal babu jimawa sai ga giftawar Bahajjatu har ta wuce sai ta dawo da
baya ta ga eh apple ɗin ta ne sai ta dawo ta shigo falon tana takawa a hankali har ta iso gaf da shi ta
kirawo sunan sa
"Apple"!!a ɗan firgice ya ɗaho ya kalle ta sai ya sauke ajiyar zuciya yayin da ta zauna kujerar da ke
kallon na sa tana son samin natsuwa dan ta lura tashin hankalin da yake ciki yana son fin na ta
"Apple yaushe ka zo ban sani ba baka kira ni ba"ƙura mata ido yayi kafin ya ce
"Umma ce ta ce in rako ta shine muka zo"shiru ne ya ratsa wurin har dai Bahajjatun ta gaji ta yi bursting
abin da ke damin ta
"Apple am ill sick of all this shortcomings,na gaji da enduring matsalolin nan,na gaji da wannan wahalar
apple ban saba ba,har sai yaushe yaya Zaid da Bilkisu zasu farfaɗo?har yaushe zamu cigaba da zama cikin
wannan wahalar da tashin hankalin?apple am sick and tired of all these problems gashi tun da abin nan
ya faru Ammi bata fah cin abinci ɗazu da na kai mata sai na gan ta shiru nayi magana har na gaji but bata
amsa min ba a haka zamu cigaba da zama apple"?da kuka ta kai ƙarshen maganar wanda ya sanya shi jin
duk jikin shi yayi sanyi shi kan shi dan dai namiji ne if not for that tsaf da shima kukan zai yi dan only God
knows what is in his mind game da revenge ɗin da zai ɗauka akan wanda ya aikata wannan aika aikar.
Tashi yayi daga inda yake ya dawo kujerar da take ya kalle ta ya ce
"Wipe them off apple ina raye ban ga me saka ki hawaye kai tsaye ba wipe them off"saka bayan
hannun ta tayi ta shiga share hawayen saidai tana sharewa wasu na fitowa daga ƙarshe ma kasa zaman
falon tayi sai ta miƙe ta yi hanyar ɗakin ta tana jin ran ta na suya dan abin sabo ne fil a ran ta bata jin zai
kankaru har sai an bi an yi maganin wanda ya haddasa abin..
Shima barin gidan yayi ya koma gidan su sai ga Bilal na kuka kukan sosai ba na wasa ba dan abin na taɓa
mai zuciya what coukd possibly prompt culprit ɗin yin abin da yayi?lajfin me suka mai da ya aikata masu
wannan abin?ya ma suka haɗu da shi kuma me ya haɗa su har suka aikata mai hakan?all these questions
have no satisfactory answers dan haka ya cigaba da kukan shi yana ƙudirin abubuwa daban daban game
da lamarin....
**************
Da isar su motar asibitin ta kwashe su basu tsaya a ko ina ba sai asibitin inda aka shiga da su separate
rooms shi aka yi da shi sashin emergency cerebral room ita kuma aka shigar da ita unconscious and
lethargic room yayin da su Dr Maher suka tsaya a waje...
Da fari dai an saka shi ne a wani incubator ne wanda zai taimaka yayi monitoring internal organs ɗin
kama daga waɗanda suka sami hatsari da waɗanda suke facing trait an saka ne yayi monitoring ɗin sa na
tsayin kwanaki huɗu zuwa biyar ta nan ɗin zai rinƙa receiving ƙananan treatments wanda ba zai taɓa
lafiyar sa ba har dai a gano ainihin matsalar
A nata gefen kuwa ko da suka gwada farfaɗo da ita ƙin farfaɗowa tayi dan haka ana tsammanin ta sami
trauma da ya taɓa brain ɗin ta wanda yayi sanadiyar shigar ta temporal comma muddin ana so ta
farfaɗo toh sai an yi vibrating ɗin ta sosai dan haka an saka ta under electrification machine yana jijjiga
ta kaɗan kaɗan dan speed ɗin machine ɗin is as low as 35.3°c bai kai normal range speed ɗin ba bare a
ƙara shi ta yadda zai jijjigata sosai..
Feedback aka ba su Dr Muhammad aka kuma sanar da su cewa as soon as 4 days ɗin suka cika kuma an
sami abin da ake so toh za'a yi proceeding amma in akasin haka sai an kuma saka shi a wani machine ɗin
dan yi mai differential test ita ma aka masu bayanin nata da haka suka rabu daga nan suka nufi intensive
care room ɗin da aka saka shi sai dai ba'a shiga ta transparent glass door ɗin ake iya hango shi gashi nan
dai a kwance jikin kamar mai isashiyar lafiya amma duk electrodes ne ke juya jinin jikin shi su ke taimaka
mai,a halin nan kuka ne kawai iyayen basu yi ba suka mai addu'ar samin lafiya suka koma part ɗin baby
doctor itama dai kwancen take da maƙalallun electrodes a kan ta gabaɗa wayoyin saka kuzari ne a jikin
ta sai monitoring machine da ke reading state of wellness ɗin ta in yayi sama yayi kamar zai dawo ƙasa
sai yayi pumping electric current wanda yake taimakawa wurin girgiza ta.
Suna kallon first move ɗin suka juya baya dan ba wanda zai iya kallon mawuyacin halin da take ciki at
least ita tana da chances of surviving kusan 89/90% akan shi da ke da 45/50% of surviving amma a zahiri
condition ɗin ta ya fi na sa ɓaci shi complete comma yake ita temporary comma ta shiga kenan shi dama
nashi condition ɗin is worsen already but ita duk ta fi wahalan..
Zama suka yi a kujerun da ke kallon ɗakin nata suna kallon ta time to time da zarar electrode ɗin zai
bada electric current sai su sauke kan su ƙasa a haka a haka har Dr Muhammad ya ji ƙarar ƙiran matar sa
ya ɗaga wayar tare da matsawa nesa da Dr Maher dan kar ya tayar mai da hankali
"Hajiya ina Hajiya Madina"? itama matsawa tayi ta amsa mai da
"Tana ciki me ya faru ya ake ciki yanzu prof"?
Ɗan shiru yayi kafin ya warware mata komai ajiyar zuciya ta yi ta ce
"Toh prof muma muna hamyar zuwa ko nan da 3 days ko kuma 4 days dan Hajiya Madina bata cikin
hayyacin ta ɗazu da muka shigo ni da Bilal wallahi a sume na riske ta sai da na yayyafa mata ruwa kafin
ta tashi ko da ta tashin ma da maganar Zaid ɗin ta farfaɗo prof ina tsoron kar wani abin Allah ya kiyaye
ya faru ina ganin zai fi in tana ganin shi"!
"Hajiya toh me kike ganin zai fi"?shuru tayi kafin ta ce
"A ganina zuwan na mu shi ya fi but kafin nan kun sanar da Afzal kuwa"?
"A'a ba'a gaya mai ba dan bamu san a yadda zai ɗauki maganar ba"!
"Toh ku bari ni zan kira shi yanzu dan ya kwantarwa da Hajiya Madina rai in ba Zaid shi yana iya dawowa
yayi ƙoƙarin da zai yi dan ta sami sauƙin raɗaɗin da take ji a ran ta"
"Toh in kin ce hakan ba zan ja ba lemme get going sai mun yi magana gobe"
"Toh sai anjima"ajiye wayar suka yi ta koma ciki ta cigaba da rarrashin ta har sai da ta ɗan sami sauƙi
sannan ta sallame ta akan washegari zata dawo godiya sosai ta mata da kulawar ta gare ta daga ƙarahe
suka ma ƴaƴan su addu'ar samin lafiya..
Da suka fito sai bata ga Bilal ɗin ba hakan ya tabbatar mata da cewa gida ya tafi sai ta wuce zuwa gidan
da zuwan ta ɗakin Bilal ɗin ta fara shiga inda ta gan shi zaune a ƙasa hawaye duk sun bushe mai a kan
fuskar sa yana scrolling pictures ɗin su shi da twinin sa ba hawayen da ke fitowa amma da gani ka san
kukan zuci yake yi dan haka har ta tsaya a bakin ƙofar bai san ta zo ba har ta shigo ta dafa kafaɗar sa sai
a nan ya juyo a firgice ya ce
"Umma yaushe kika shigo"?yana yunƙurin ɓoye wayan bai san ta gama gani ba sai ta ɗan murmusa ta ce
"Let it be my boy na gani just pour ot out"ta faɗa ta na mai kwanto da shi kan kafaɗar ta kamar jira
yake ya shiga risgar kuka bata hana shi ba dan shi kaɗai ne solution ɗin halin da yake ciki haka ya sha
kukan shi dan ya manta cewa shi namiji ne yayi mai isar sa tana petting bayan sa har yayi shiru ya shiga
tambayar ta
"Umma apple zata warke ai ko"?sai tausayin sa ya kama ta mutumin da kullum a cikin raha da fara'a
yake amma yau guda ya zauna in ban da kuka babu abin da yake yi
"Bilal zata warke zata dawo gare mu kamar ma bata taɓa yin rashin lafiyar ba abin da nake so da kai
shine ka tafi ka yi alwala ka zo ka yi nafila ka yiwa ƴaruwar ka addu'ar samin lafiya dan a halin da take ciki
addu'ar mu kaɗai take buƙata a yanzu ba kukan mu ba dan ba zai yi mata amfani ba humm"?alama ya
mata da kai kafin ya miƙe ya nufi toilet duk bai da kuzari ya yo alwalar ya fito ta shimfiɗa mai sallaya ta
fita a lokacin da ya tayar da iƙamar sallar.
Bata tsaya ko ina ba sai part ɗin Lukman he is used to it already samin shi ta yi yana nafila dan haka ta
ja mai ƙofar ta fita ta nufi sashen su a inda ta tabbatar zata sami privacy ta zauna ta yi dialing digits ɗin
Afzal ringing uku huɗu ya ɗauka da fara'ar sa ya ce
"Assalamu alaikum umma na"kamar ta yi kuka haka ta ji sai ta daure ta amsa mai da
"Wa'alaikumul salam ɗan umma ya kuke ya canada"?
"Umma lafiya ƙalau da fatan dai an dawo gida ko"? Yayi tambayar da teasing tune sai ta ce
"Afzal ka mai da mu kakannin ku"yayi dariya ya ce
"Toh ummq in banu yi da ku ba wa zamu yi da"?
Sai ta ce
"Babu Afzal yanzu dai kana ina"? sai ya ɗan yi jim kafin ya bata amsa da
"Umma ina gida but inshaAllah ina son dawowa nan da sati guda saboda ina ji a jiki na kamar Ammi is
missing me and we have not been in touch kusan a week +"..
Jin haka sai jikin ta yayi sanyi dama tsakanin ɗa da mahaifi akwai strong bond da ke taimakawa wun
sadarwar su wanda in ɗaya na da damuwa ɗaya zai ji a jikin sa especially uwa dan haka ta natsu ta
warware mai komai sannan ta ɗora mai da dalilin kiran ta..
Iya ƙololuwar tashin hankali ya shiga bayan ya saurari abin da aka sanar da shi sai ya ce da ita
"Umma ina hanya gobe inshaAllah su kuma Allah ya basu lafiya"!
"Amin sai Allah ya kawo ka Afzal Allah ya kare ya tsare"
"Amin umma sai da safe"!!
Zama tayi tana ta tunanin yanayin rayuwa few weeks back sune a London cikin kwanciyar hankali basu
da damuwa ko matsalar komai sai gashi kwatsam suna tsaka da jin daɗin su kaddara ta sauko masu da
wannan tunanin ta daure tayi alwala ta yi sallah bata rintsa ba dan ta san tana buƙatar ibadan a wannam
gaɓa sama da kwanciyar barcin....
A gidan babban yaya Jamil tun bayan tafiyar su kid sis ɗin sa da aminin sa ya dawo gidan hankalin shi ba
a jikin shi ba duk dabarar da matar sa ta mai dan ganin ya sake ya bi su da addu'ar samin lafiya abin ya ci
tura dan kamar ingiza shi take yi akan ya cigaba da saka damuwar a ran sa sai ta zuba mai ido kawai dan
ita kanta tana cikin damuwar da tashin hankali wanda ita kaɗai ta san yadda ta ke ji.
Bai bar ɗakin da ya rufe kan sa a ciki ba sai chan tsakiyar dare ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita kwance
saman sallaya chan kan gadon ga baby Zarah tana barci sai ya ji ta bashi tausayi it takes a loyal,caring
and kind wife to behave and act exactly the way she does dan haka ya lallaɓa ya ɗaga ta dama akwai
nauyin bacci dan haka bata wani farka ba sai ma ta kuma lamo a hannun sa fita yayi da ita ya kai ta ɗakin
sa ya kwantar da ita ya koma ya ɗauko baby Zarah ya kwantar da ita next to her momma shi kuma ya je
yayi ablution ya zo ya tayar da sallah ya ɗau lokaci mai tsayi yana addu'a ma ƙanwar sa da aminin sa
daga kan sallayar ya hauro ya kwanta shima suka saka baby Zarah a tsakiya ya ja masu comforter haɗe
da kashe lamp ɗin ya tofe masu addu'ar bacci...
********************
Kimanin kwanaki uku aka ɗauka ana monitoring patients ɗin germany kafin doctor ɗin ya yanke
hukuncin kai treatment ɗin zuwa second stage wanda a gefen baby doctor dole ta yi undergoing electro
convulsive therapy ba ƙaramin rikita iyayen ta abin yayi ba dan a gida Nigeria sun gama shirin zuwa ciki
har da Afzal da Bilal ƙin barin Bahajjatu aka yi dan in ta tafi tana iya creating scene a wurin nan kuma
ƙasar turawa ne basu cika son hargitsatsen abu ba sai aka bar ta a gida,..
Suna airport labarin ya same su Hajiya Zeenat ji tayi kamar tayi kuka ne ko ta kurma ihu ne ko kuma ta
zauna ne ta rinƙa rasbihi,shawarar ƙarshe shine ta yi tasbihi dan haka ta yi shiru ta shiga yin tasbihi har
jirgin ya tashi dan bata sanar da Hajiya Madina abin da Dr Muhammad ya gaya mata ba sai ta bar wa kan
ta.
Shi kam abin ba'a cewa komai dan dai duk wasu analysis da diagnosis da likitocin suka yi basu sami
gamsashiyar outcome ba sai ma kamar condition ɗin na daɗa yin gaba dan already akwai concealed
blood da yayi bleeding tun daga ainihin main root ɗin sai abin ya zama somehow bulky har kan ya fara
expanding dan jinin na ta regurgitating ba kama hannun yaro abin da ya rikita likitocin kenan suka ga ya
kamata su yi mai gabaɗaya a wuce wurin wato dai brain surgery za'a mai dan haka nemo iyayen shi suka
yi bature bai da ɓoye ɓoye straight to the main point ya masu bayani sannan ya sanar da su life rate
percentage ɗin in aka yi surgery ɗin either 40/50 ko 50/50 ko mutuwa chances ɗin survival is low which
happens to be as low as 30%..
Tashin hankalin da ba'a saka mai rana daga Dr Maher har Dr Muhammad sumumui suka fito in banda
fargaba babu abin da ke ran su babu mai ce ma wani komai gashi likitan ya basu space ɗin yin decision
har tsawon awa ɗaya da rabi kafin a san abin yi a hakan ne suka zauna shiru babu magana har suka cinye
kusan rabin hour a haka a haka suka kuma shafe hour wanda ganin hakan ya sa doctor ɗin yayi
reasoning da su ya ƙara masu awa ashirin da huɗu amma ya gaya masu cewa suna delaying survival ɗin
ɗan su dan dama ita baby doctor a washegari za'a mata ECT ɗin shi kuma a ranar aka so yi mai sai dai
they can't go ahead with the surgery without the permission of the patient relative which have to be his
parents with their bold agreement and acceptance + signature da za'a yi stamping a yi forwarding to the
board dan a saka a babbar file ɗin brain trauma clients da zasu yi undergoing brain surgery...
Dan haka samin wannan damar suka koma lodge ɗin su gabaɗaya jikin su a sanyaye suke babu jimawa
suka ji kiran su Hajiya Madina akan sun iso tare suka tafi ɗauko su a cab suka dawo lodge ɗin inda aka
masu booking ɗayan ɗakin sai suka koma zaman su na ma'aurata wato kowa ya tare da mijin sa a two
rooms ɗin,su kuma Bilal da Afzal next room ɗin suka zauna su biyu.
Ordern abinci aka masu but kasa ci suka yi duk sun damu su ga ƴaƴan nasu sai dai a cikin situation ɗin
da ake ciki ba su fatan matayen na su su ga tashin hankalin da yaean ke ciki da ƙyar da siɗin goshi suka
yarda washegari zasu tafi asibitin amma fah babu kwanciyar hankali a tattare da su kowa na tsoron da
fargabar abin da zai gani a goben...
_2:50am_
Daidai lokacin da Dr Maher da Dr Muhammad suka fito daga ɗakunan su kenan dan samin mafitar abin
da likitan ya sanar da su ƙarfin hali kawai suke yi ba dan sun shirya ba dan haka bayan doguwar nazari da
hangen nesan da suka yi sun yi arriving a kan zasu yi signing ɗin a yi surgery ɗin su kuma su bisu da
addu'a dan matuƙar babu addu'ar toh ko ma me za'a yi ba lallai bane su yi succeeding a surgery ɗin ba
da haka suka koma suka cigaba da tunanin rayuwa...
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
As early as 7am duk sun gama shirin zuwa asibitin dan haka cab ne ya sauke su suka ranƙaya zuwa ciki
abu na farko da suka yi shine samin doctor ɗin suka amshi form ɗin kiran matayen nasu suka yi suka
nuna masu form ɗin kasa ƙarasa karantawa suka yi sai kuka dan haka su mazan ne suka yi namijin
ƙoƙarin saka hannu a papern aka yi submitting zaman jiran likitan