Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Iya Ruwa Fidda Kai Complete Hausa Novel by Siyama Ibraheem

Author :  Siyama Ibraheem Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 74

90K to 93K   out of 221.1K words

desired look da ta gama ne ta dawo kan fuskar sa
tayi amfani da hand towel ta goge mai fuska sannan ta bi sajen sa ta yi amfani da brush ta rinƙa taje shi a
hankali har ta kammala sai ta ɗau face mask ta manna mai sannan ta koma kan suman kan sa ta shafa
mai wani exotic hair wash ta cuccuɗa tana gamawa ta cire mai face mask ɗin ta shafa mai cucumber
paste sama sama shi dai yana kallon ta ƙala bai ce da ita ba hakan kuma ya mata daɗi dan ta sami
ɗaukewar kashi casa'in a cikin kashi ɗari na fargabar da ta rinƙa samu kafin ta fara mai gyaran ga irin
kallon ƙur da ya rinƙa mata ɗazu sarai ta gane ko kallon menene sai dai ita kam tayi alƙawarin enduring
duk wani maganganun zafafa zuciyar da zai mata dan dole a matsayin ta na matar sa ta koyi shanye duk
wasu rigingimun da zai taho mata da su addu'ar ta ɗaya kar Allah ya bashi ilimin tambayar ta Asma'u dan
ji take kamar zuciyar ta zai buga a duk lokacin da ta tuno yarinyar abin da ya faru da su bai mata daɗi ba
ko kaɗan hakan ya sa ta ɗau tsanar duniyar nan ta ɗora shi akan Asma'u dama chan jinin su bai haɗu ba
bare yanzu da take ganin itace ummul aba'isin na janyo masu matsalar da suke ciki dan haka bata jin
zata iya yafe ma yarinyar so soon dan yanda take jin zafin abin da yarinyar tayi ko shi da ya aikata
ta'addancin bata jin zafin sa kamar yadda take jin na yarinyar..
Kusan tun da ta fara har ta ida a halin kurame suka yi gyaran fuskar sai da ta kammala ta mai kallon
tsanake ta ga ya fito a ainihin Dr Zaid Maher ɗin sa though akwai wasu tranaformational changes da ya
faru a jikin sa kamar ramar da ya ɗan yi alamomin jinya da ya nuna a fuskar sa sai gajiya da yake tattare
da shi..



Magana ta mai cikin ruwan sanyi ta ce



"Na gama duba ka gani in akwai wani wurin da kake so a ƙara gyarawa sai ka sanar da ni"!!kallon
mamaki yake mata dan maganar ta na kan yi mai yawo a ƙwaƙwalwa wai ita ɗin matar sa ce gaske ne ko
ko rainin hankali ne dan ta ga he is helpless.

Kallon sa itama take yi tana jiran jin amsar sa sai dai har ta gama ƙiyastin ta bai amsa mata ba ya ƙyake
ta kuma wannan guilty look ɗin yana nan yana bin ta da shi kasa jurewa tayi sai ta miƙe tsaye tana mai
gyara mayafin ta.

"Wanka zaka yi bari in taya ka ka shiga toilet"!!wani razanannen kallo ya bita da shi she must admit that
ta gigita da kallon saidai bata bari ya gane hakan ba ta ɓoye ta cigaba da abin da take yi

"Mu je kar ruwan yayi sanyi"!!kai hannun ta tayi ta riƙo nasa a hankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga sa with the
hope that zai taya kan sa tashi in yaga effort da take yi sai dai bai taya ta ɗin ba dan daɗa ƙara weight ɗin
sa yayi a kan gadon tayi tayi ya tashi ya ƙi sai ta ɗago ta haɗa ido da shi ta mai alama da ido akan ya
tashin mana amma yayi shunning nata sai ta gane ashe ba wai weakness ne ya sa ya kasa taimakon
kansa dan tashi ba a'a kawai ra'ayin sa me yin hakan sai ta haɗiyi wani abu da ta ji ya taso mata ta cigaba
da trying dan dai ya tashin amma ya ƙi.

Bai tashin ba ita kuma bata karaya ba ta cigaba da ƙoƙartawa dan kan shi ya tashin dan ya ga kamar ta
fara gajiya har zufa take yi,yana tashi tayi tanga tanga kamar zata faɗi sai dai ta yi saurin regaining
balance shi kan sa ya tsorata da ya ga zata faɗi sai dai da tayi regaining balance ɗin ya sami relief amma
bai nuna ba ita kuwa ko a jikin ta ta matso ta riƙe sa ta baya ɗaya hannun ta na riƙe da nasa hannun a
haka suka fara takawa har ta kai shi bakin toilet ta rasa me zata yi shin ta raka sa har ciki ne kokuwa ta
bar sa ne a bakin toilet.



Tsayuwar ya fara gundurar s sai yayi tsaki hakan ne ya fargar da ita har ta ruɗu bata sani ba ta cigaba da
tafiyan yana bin ta suna takawa ta kai sa har kan bathtub ɗin ya zauna dama komai ta tanadar mai
wanda zai baƙata ta kawo mai bath throb kusa da shi ta ajiye su sponge da bath liquids daga haka ta
kalle shi cikin tausayi ta ce

"In ka gama ka sanar da ni sai in zo mu fita"..
Wannan kallon baƙuwar ya bita da shi ita dai tayi gaba dan gani tayi kamar tunda ya farfaɗo bai da wata
ɗabi'ar da ta wuce na kallon ta dan ko sauran mutanin da ke kewaye da shi baya masu kallon da yake
mata takan rasa ma'anar kallon.



Dawowar ta ɗakin ne ta shiga gyara mai gadon sa ta canza bed linen ɗin ta share ɗakin da electric
cleaner ta biɗe waldrop ɗin sa ta shiga kallon kayan nasa dan tantance wannene zai fi masa sauƙi
sakawa,bayan dube duben da ta yi sai ta fiddo mai da Tom ford tuttle neck top ash colour ta haɗa da
black jeans,white singlet ta ɗauko,muffler ash colour ta haɗo da sai head warmer ash mai tuntu baƙi,
takalmin sneakers baƙa mai tambarin NBA da aka yi shi da ash colour gyara shoelace ɗin tayi daga yadda
aka saka shi zuwa wani iri ta yadda zai ƙayatar.mayar da waldrop ɗin tayi ta rufe ta dawo da kayan a
hannun ta a kan gadon ta zuba su daga nan side drawer ta buɗe ta duba kayan shafar sa ta fito da su ta
ajiye a saman drawer ɗin.



Zaman jiran alamar gamawar sa take yi time to time takan kalli agogon hannun ta dan ganin time in ta
haɗa duka time ɗin da yayi spending a toilet zata iya cewa ya sami kyawawan mintuna arba'in a toilet
ɗin nan wanda ta san ko da wani irin wanka ne wannan da yake yi ya ci a ce ya kammala but me yasa bai
yi alerting nata ba wata zuciyar ce ta bata amsa da cewa ta yaya zai yi alerting ɗin ki bayan ke kanki kin
san kallon da yake miki ba irin kallon ya gamsu da ke a matsayin matar sa bane sai ta yi tunanin in har
kuwa so take Zaid ya amince cewa ita ɗin matar sa ce toh dole sai ta yi mai abin da zai fahimci hakan har
ma ya gamsu da haka.



Wannan tunanin ne ya ingiza ta ta taka har zuwa bakin ƙofar toilet tana mai tambayar sa a hankali

"Zaid ka gama wankan ne"!!sai da ya ɗau lokaci sannan ya amsa da

"Uhum"kamar dai marar baki haka ya amsa mata.

Tura ƙofar tayi ta shiga kan ta a ƙasa har ta zo kusa da shi dan zaune yake a inda ta bar sa kafin ta fita
kenan bayan ya gama wankar ne ya koma ya zauna a gefen bathtub ɗin ɗaure da bath throb da ta bar
mai ƙafar sa sanye cikin slippers bath throb ɗin bai kai mai har ƙasa ba amma da kaɗan ya rage ya kai
ƙasan space ɗin da yake expose a ƙafar sa abin kallo ne dan suma ne kwance sakamakon ruwan wankan
da ya taimaka wun kwantar da suman fatar jikin sa sai glowing ƙafar ke yi.

Kai hannun ta tayi ta riƙe sa suka fito tare daga nan ta zaunar da shi a kan kujera ita kuma ta ɗauko
towel dan goge mai kai daga tsayen ta bayan sa ta riƙe towel ɗin ta shiga goge mai kan tana yi tana
massaging kaɗan kaɗan gently har ta gama sannan ta dawo ta zauna a saman gadon suna kallon juna ta
ɗauko body lotion da ta fito da su ta matsaa hannun ta ta murza tsugunawa tayi ta shiga shafa mai a
ƙafar sa ta dama ta ɗago ta kuma matsowa ta murza ta tsugun ta shafa mai a ƙafar hagu daidai inda
towel ɗin ya rufe da kaɗan wato gwiwar sa a nan take jan burki dan bazata iya shafa mai duka ba da ta
gama ta hau shafa mai a hannun sa shi kam abin na bashi mamaki ba dan komai ba sai dan farin sanin da
yayiwa yarinyar dan first class ce wun girman kai da izza amma sai gashi yau ya nuna mata attitude ta
hanyoyi daban daban duk dan ta san cewa shi fah ba yarda yayi da abin da ta gaya mai ba wai ita matar
sa ce amma bata nuna ko a fuska ba akan abin ya mata ciwo ko ya ɓata mata rai ba me yasa haka.

Jin muryar ta yayi tana ce da shi

"Na gama saura saka roll-on gashi saka"ta miƙa mai kallon roll-on ɗin yayi kafin ya kalle ta ta amsa mai
da kai akan ya karɓa ya shafa,karɓa yayi ita kuma ta shiga mayar da cream ɗin leaving a little gap da zata
mayar da roll-on ɗin in ya gama amfani da shi ko da ya gama shafawa bata jira sa ba ta karɓa haɗe da
miƙo mai fogg body spray ta ce

"Ungo ka fetsa"she behave gentile and kind it amuses him.

Karɓa yayi ya fetsa haɗe da miƙa mata ta ƙarba ta haɗa da roll-on ta mayar a drawer daga nan ta tashi
dan miƙo mai kayan sa da zai saka sai ta tuna bata ɗauko mai boxers basai ta koma ta buɗe ta hau
dubawa hangowa tayi an yi hanging nasu a wasu hangers sai ta ɗau ɗaya ta juyo da shi ta miƙo mai kan
ta a ƙasa.

Nan ma sai da ya mata kallon stranger sannan ya karɓa sai ta juya mai baya dan ya sami privacy ya saka
hankali kwance.

Da ya gama sakawa bai mata alamar ya gaman ba sai ya cigaba da saka sauran kayan ya saka inner wear
ya ɗau top ya saka ya ɗau jeans har ya fara sakawa sai ta ga kamar ya kamata a ce ya gama saka boxers
by now sai ta juyo dan miƙo mai rigar da zai saka sai dai tana juyowa idanun ta bai sauka a ko ina ba sai
kan jeans trouser da yake hannun sa ga rabi ya wuce rabin ƙafar sa sai tayi gaggawar runtse idanun ta
tana jin faɗuwar gaba oh ita me ya kai ta juyowa yana cikin halin nan har zata juya ya dakatar da ita ya
ce

"Get me a belt"!!

Da sauri ta isa gaban waldrop ɗin ta buɗe ga belts ɗin nan a gaban ta but abin mamaki shine sam bata
lura da shi ba sai da ta gama kalle kallen ta sai chan ta ga belts ɗin a gaban ta dan haka ta ɗau ɗaya daga
cikin belt ɗin ta ɗan tsaya gudun kar ta kuma yin gamdakatar da abin da ta gani ɗazu,



Ya san tsayawa tayi dan kar ta gan sa a halin da ta gansa ɗazu sai yayi gyaran murya.hakan ne ya bata
damar juyowa dan alama ce da ya gama saka kayan.

Miƙo mai tayi tana sinne kai ƙasa karɓa yayi ya shiga sakawa ita kuma tana kallon ƙasa da ya kammala
sai ta kwaso takalmin ta kawo mai kamar dai ta bar shi ya saka da kansa sai kuma ta fasa ta durƙusa ta
shiga saka mai takalmin da ta gama ta ɗaure shoelace na takalmin tana gamawa ta miƙo mai oud perf
mai ƙarfin ƙamshi ya fetsa sannan ta karɓa ta mayar muffler ta saka mai a wuyar sa ta ɗau head warmer
ta saka mai sannan itama ta gyara gyalen ta ta ɗau wayar ta da nasa ta riƙe a ɗaya hannun ta da ɗaya
hannun ta riƙe sa tunda ta ga kamar yana da ƙarfin jikin sa baya buƙatar much help haka nan tashi yayi
da taimakon ta daga haka suka shiga takowa har suka fito kamar kurame bata ce da shi a ba bai ce da ita
uffan ba da suka fito ta saka ma ɗakin security pin ya rufu sannan suka cigaba da takawan.



Ta baya suka bi suka fita daga asibitin baki ɗaya akwai wani garden mai ɗauke da park na wasanni chan
suka nufa tun daga nesa take son fara jan sa da magana sai dai hakan ya ci tura dan bayan kallon gaban
sa da yake yi baya kallon ko ina gashi fuskar kamar an mai dole.

Daurewa tayi dai ta ɗago da maganar

"Ni kam Zaid in tambaye ka mana"cikin taushin murya tayi maganar wanda ƙaryan mutum musamman
ɗa namiji ya ce an mai magana ta wannan siga bai ji shi har cikin tsokar jikin sa ba amma da yake Dr Zaid
Maher is almost back to his Dr Zaid Maher sai yayi pretending bai ji abin da ta ce ba and so she have to
ask again

"Zaid na cein tambaye ka mana"!! Sai a nan ya ce

"Uhhhnn"irin ina jin ki ɗin nan tsabar jin haushi bata san lokacin da ta ce da shi

"Damuwar ka"ba abin sai ya so bashi dariya amma ya mazge kamar dariyar bata taso mai ba saboda out
of frustration tayi maganar ba tare da ta san zai fito da sautin haushin da ta ji ba.



Sai da suka yi nisa a takawar sannan ta ji sassaucin abin haushin da ya mata har ma ta tuna da abin da
ta yi mai na demonstrating ɓacin ran ta a gaban sa.

Bata ce da shi komai ba ta ƙyale sa kamar dai yadda yayi shiru shima.

Da suka ƙarasa cikin park ɗin ne suka nemi wun zama ta bar sa a nan ita kuma ta ƙarasa zuwa ciki wun
masu saida kayan sanyi dangin su smoothies,icing,vinegar icing,ice creams,da dai sauran su ordering
vinegar icing tayi ma kanta shi kuma ta karɓo masa smoothie,master card ɗin ta ta miƙo masu suka yi
transferring haɗe da miƙo mata card ɗin ta ce da su thanks.

Daga nan wun masu siyar da kayan ciye ciye ta nufa inda akwai abubuwa da dama kamar su
cookies,spring rolls,sandwich,hot pizza,hamburger,da sauran easy chops.

Hamburger ta karbawa kanta shi kuma ta kaeɓo mai cookies though bata sani ba ko yana ci ko baya ci.

Nan ma transferring aka yi aka miƙo mata card ta juyo ta nufo inda ta bar shi tana ɗan murmushi dan
tunowa da ranar da suka haɗu a theater room yana surgery babu assistance sai anaesthetics ran nan a
haɗe ita kuma ta rantse ba zata taimaka mai ba dan bai nemi taimakon nata ba gashi babu wasu likitocin
kaf suna off ranar ma emergency surgery ne ya taso ita kuma ta zo duba patient ɗin ta sai ta ga yana
buƙatar taimako amma rashin tambayar alfarma daga gare ta ya sa ta shiga surgery room ɗin tayi zaman
ta tana kallon sa har ya gama da taimakon anaesthetic nurse yana gamawa tayi tafiyar ta shi kuma ya
rinƙa bin ta da kallon takaici.



Tana isa kusa da shi annurin fuskar ta ya kau ta zauna haɗe da miƙo mai abin da ta siyo mai karɓa yayi
ya ajiye a gefen sa sai ta juyo ta kalle sa ta kalli gefen da ya ajiye abin da ta kawo mai sai ta juyar da kai
ta ce

"Uhumm"daga haka ta fara shan ice vinegar ɗin ta tana sipping kaɗan kaɗan babu wanda ya ce komai a
cikin su shi ya zuba ma park idanu yana kallon wasannin yara dama ƴaƴan turawa da rashin ji in an ce su
bari basu bari,wani ɗa ne ke faman throwing tantrum kawai saboda an hanasa shiga cikin anaconda na
wasa da ke park ɗin, uwar tayi tayi ta rarrashe sa amma ya ƙi jin ta sai kuma uwar ta koma bashi haƙuri
madaɗin yayi shiru sai ya ƙi yin shirun ya saka mata kukan banza



Duk event ɗin nan a kan idanun Bilkisu da Zaid ake yin su,gajiya Zaid yayi da kallon rashin ta ido irin ta
ɗan sai ya miƙe a hankali ya shiga takawa har ya isa gaban su a hankali ya durƙusa ya riƙe hannun ɗan
yana kallon sa yana son sanin damuwar sa

"Hey kiddo whats up"sai yaron ya kalle sa idanun sa cike da hawayen shagwaɓa ya ce

"Momma doesn't wanna let me play with the anaconda she didn't allow me to play with the cobra all
my buddies are there play with the anaconda but momma isn't listening to me she doesn't want me to
play around i just wanna go home"..

Kwata kwata yaron ba zai wuce 5years ba a shekaru kuma daga dukkan alamu yana da tsiwa da rashin ji
sai ya murmusa ya shafa kan yaron yana cewa



"Common cobra tell me when momma says you shouldn't play and stops you from playing what does it
signifies"??sai yaron ya ƙurawa Zai ido kafin ya ce

"It signifies that something dangerous is there"cikin gamsuwa ya tari yaron ya ce

"Good cobra,that's it momma have seen something bad and that is why she didn't allow you to play
there with your friends"sai yaron ya kyaɓe fuska ya ce

"But i wanna play buddy"abin dariya one sided smile Zaid yayi sannan ya ce

"Tell me kiddo are you sure you not scared of anything"??sai yaron yayi shiru yayin da mahaifiyar ɗan
ke kallon su cikin admiration dan dai ta san wannan stranger ɗin ba ɗan ƙasar su bane but yana da kirki
gashi har ya fara gano matsalar ɗan nata da ita kanta ta kasa rarrashin sa but ga wannan yana ta jan sa
da hira shiru ta yi tana kallon su tana murmushi.
Amsar da ɗan ya bashi ne ya sa ya ji tausayin yaron

"Buddy am scared of darkness"sai ya ce da shi

"And i think the anaconda is dark what did you think"??a rikice yaron ya ce

"Yeah the anaconda is dark"sai ya ce

"And you are scared of"?? ai a mugun tsorace yaron ya ce

"Darknesssss"da gudu ya shige bayan mahaifiyar sa yana ɓoyewa tsabar tsoro sai ya shiga cewa

"I don't wanna go i hate darkness i hate anaconda"sai Zaid yayi murmushi cikin ruwan sanyi yayi
handling abin da mahaifiyar ɗan ta kasa yi wai dan ma ɗan turawa ne in ba dan haka ba da da iron hand
zai yi handling ɗin sa dan shi ya tsani rashin kunya kuma that is exactly what the boy is doing kuma uwan
na kallon sa imagine..



Miƙewa yayi ya juya zai yi tafiyar sa sai

31 / 74