Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
it but i have to...we wish you all
safe trip back home and thank you all for coming we really appreciate your gifts will be handed over to
you in a jiffy before you leave,thank you"...
Surutu wurin ya kaure da but bai dame ta ba dan ta san hakan ne kaɗai zata yi ta rufe bakin masu
cecekucen wmtaron..
Zata wuce kenan sai ga Bahajjatu ta nufo ta cikin zafi zafi ta ce
"Ammi why did you apologize to them repeatedly baki san abin da suka rinƙa cewa bane and yet you
went on apologizing to these ingrates"kallon ta Hajiya Madina tayi ta ce
"Duk wasu complains a yi shi anjima not now we have to find your friend and her husband"sai ta ce
"Ammi ai su yaya Luk da Bilal sun tafi nemo su"kallom ta tayi cikin mamaki ta ce
"How did they come to know about it sai ta labarta mata sai a nan hankalin ta ya daɗa tashi ta shiga
tunanin maganganun Hajiya Zeenat na ɗazu..
Duba Hajiya Zeenat ta shiga yi but bata gan ta ba sannan ta kira wayar ta but ba'a ɗauka ba sai ta shiga
kiran layin Dr Maher but shima bai ɗauka ba hankalin ta ne ya kuma tashi daga bisani ta ce da Bahajjatu
ta zo su tafi airport ɗin.
Cikin azama suka bar gidan suka ɗauki hanyar tafiya airport hankali tashe,kasancewa Baha ce ke driving
sai ta saka motar a speed sosai dan haka kusan lokaci guda suka sauka a airport ɗin da motar su
Bilal,already su prof sun iso tuntuni an kuma tabbatar masu da jirgin germany ya sauko tun bayan awowi
2-3 da suka wuce dan haka su Bilal na ganin su suka masu tambaya prof ne ya sanar da su a lokacin da
yake bayanin su Hajiya Zeenat na ji sai hankalin ta ya tashi fiye da ƙima dama tana ta ji a jikin ta babu
lafiya dan haka ta nemi wurin zama a wurin ta zauna jikim ta duk yayi sanyi barin ta suka yi dan sun san
abin ya ishe ta sosai da ƙyar dai Hajiya Madina ta lallaɓa ta ta tashi suka shiga motar mazajen su suka
nufi hanyar komawa gida dan gabaɗaya ba a hayyacin ta take ba tunanin ta ya zurfafa tsoron ta kar dai
sace su aka yi addu'oi take ta yi cikin zuciyar ta..
Barin su airport ɗin ke da wuya Afzal ya zo dan samin ƙarin bayani sai dai same answer da aka ba iyayen
su shi aka ba shi hankali tashe ya baro airport ɗin ya kamo hanyar gida yana nazarin inda zasu kasance
alhalin sun san ana gida ana jiran su...
_1 hour after_
Duk babu mai ƙwarin gwiwa a cikin su haka dai suka ciki dan tun a motar Dr Maher yake ta kiraye
kirayen jami'n tsaro ya damƙa masu case ɗin bayan ya masu bayanin komai,bayan sun firfito daga motar
dan a bakin gate ma motocin suka ja burki yayin da motar su Bilal yayi ciki,parking yayi ya fito Lukman
ma fitowa yayi suka tsatsaya suna jiran shigowar iyayen nasu har dai suka kammala tattaunawar da zasu
yi suka shigo chan ɓangaren su Hajiya Madina ma sun shige cikin gidan su da yarjejeniyar zasu koma
police station bayan sun canza kayan su..
Bilal ne a gaba yayin da Lukman ke biye da shi a baya sai su Hajiya Zeenat da Prof dan kasa taɓuka
komai ta yi sai da ya tallafo ta duk bata a hayyacin ta haka dai suka ƙarasa ciki tunanin su ta ina zasu fara
neman ƴaƴan nasu daga abin farinciki sai a ƙare da damuwa haka...
Ɗakin su ya kai ta tana shiga ta hau rusa mai kuka kamar an aiko mata da mummunar abu marar daɗin
ji duk ta bi ta ɗagawa prof hankali ya rasa da wanne zai ji da rashin ɗiyar sa haɗe da rashin ɗan sa ɗan
aminin sa ko da rigimar Hajiya Zeenat sam ya kasa sukuni kan sa yayi zafi but dole ya rarrashe ta konzai
sami ragim wani zafin.
Zama yayi kusa da ita haɗe da kwanto da kan ta saman kafaɗar sa ya shiga rarrashin ta yana bata
assurance ɗin inshaAllah zasu ga ƴaƴan su babu abin da zai same su,jin sa kawai take amma ta saka abin
a ran ta ba kaɗan ba..
Yana cikin rarrashin ta ne suka ji muryar Bilal yana faman ƙwala masu kira
"Umma.....Umma ina kuke.."!!!gaban ta ne ya faɗi dan yadda ta ji yana kwada masu kira babu inda
hankalin ta ya tafi sai wani mugun abu ne ya faru tana jin ya kuma kiran ta ta tashi daga jikin sa tana jan
hanci murya a disashe ta ce
"Bilal gani nan shigo mana me ya faru kake kira na haka"!!?sai ya ce
"Umma come out please ba abin a shigo bane"sai ta ji rass kan ta ya amsa
Shikenan an sace masu yara,,haka ta rinƙa ayyanawa a ran ta har ma ta koma ta zauna ta kasa fitan sai
shi prof ne ya fito yana tambayar me ya faru a nan Bilal ya riƙo hannun sa yayi hanyar ɗakin Bilkisu.
Suna zuwa ya ga ɗakin buɗe ga su Jamil nan da matar sa har ma da nannyn baby Zarah duk sun yi cirko
cirko gefen ɗakin kuma Lukman ne tsaye yana waya da alama dai da Abban su Dr Maher yake wayar dan
a ƙarshe ya ce
'Eh Abba gata nan tana bacci'
Jan sa cikin ɗakin Bilal yayi yana ce mai
"Abba ka gan ta nan,,ka ga Bilkisu bata ɓace ba basu ɓace ba"..abin mamaki abin al'ajabi
Me zai gani haka?dama yaran nan ba ɓacewa suka yi ba kuma ba sace su aka yi ba?toh me ya faru har
haka da ta zo nan gidan?me ya sa ita kaɗai ce a nan ɗin kuma har bacci take yi comfortably..
Takowa yayi har gadon ya taɓa goshin ta ya ji lafiya ƙalau babu alamun rashin lafiya bare fever..but why
what happened why is she here and not with her husband kafin nan ma ina shi Zaid ɗin yake?..
Ɗaga kan sa yayi ya kalli Bilal haɗe da ce mai
"Bilal tafi ka kirawo Umman ku"ya amsa da toh sannan ya fita ya nufi sashen Umman sa yana zuwa ya
tura ƙofar ɗakin haɗe da sallama.
A razane ta ɗago ta kalle sa hankali tashe ta ce
"Bilal an lahanta mana su ko"?sai ya girgiza mata kai ya ce
"Abba ya ce ki zo let's go Umma stop all these talks"sai ta mai shiru ta tashi jiki a sanyaye ta bi bayan sa
suka nufi sashen Bilkisu sai abin ya ɗaure mata kai me kuma zasu yi a sashen Bilkisu..
Tiryan tiryan suka iso sai ya matsa ya bata hanya ta shige shi kuma ya bi bayan ta..
Ko da ta shiga ɗakin bata lura da Bilkisun ba hankalin ta na kan ƴaƴan ta da ke cike a ɗakin sai ta gama
sadauƙarwa akan abin da take hasashe ne ya faru dan haka ta kalli prof ta ce
"Me ya faru"?sai ya girgiza kai ya nuna mata gadon da fuskar sa sai ta bi direction ɗin tana son ganin ko
menene.
Daɗa girman idanun ta tayi yayin da tayi arba da Bilkisu dake kwance tana sharar bacci ai tun kafin su
ƙifta ido ta nufi kan gadon babu wata wata ta shiga girgiza ta tana kiran sunan ta
"Bilkisu...baby...baby tashi...tashi"!!duk kallon ta ake yi tausayin ta ne ya kama prof uwa da ɗa kenan.
Tana kiran sunan ta a karo na uku kenan sai ta ɗan buɗe idanun ta sai ta mayar ta rufe tsawon seconds
uku sannan ta kuma buɗe idon ta sauke kan Umman ta a hankali ta shiga bin jama'an ɗakin da ido har ta
sauke kan Abban ta da ke shirin matsowa kusa da ita ganin ta farka..
Kafin Hajiya Zeenat tayi magana wayar prof yayi ringing dubawa yayi ya ga mai kiran sai ya ga Dr Maher
ne ɗagawa yayi ya kara a kunnen sa basu ji me aka ce da shi ba but sun ji yana hamdala daga bisani ya
datse kiran sai suka maido da duban su kan sa
"An ga Zaid"iya abin da ya iya furtawa kenan sai aka shiga yin hamdala ana sauke ajiyar zuciya.
Ita da ke rungume jikin Umman ta tana sauraron su jin an kira sunan Zaid har ma da wai an gan sa sai
abin ya bata mamaki dama ɓacewa yayi ake neman sa?.
Dawo da hankalin su suka yi gare ta umma ce ta jefo mata tambaya
"Baby ina kika shiga?ina kuka tafi?what happened?why are you all alone ba tare da mijin ki ba?me kike
yi a nan?what happened we have been calling your line but you weren't picking me ya faru baby?please
say something"!!duk a hargitse take mata waɗannan tambayoyi sai ta rasa abin cewa dan ita sai yanzu
take ma tuno dargar da suka kwasa jiya ita da Zaid har zuwa yanzu toh wai ɓacewa yayi ne ko me.
Jin muryar Umman ta tayi tana ce mata
"Baby kin yi shiru"sai ta ɗan ɗago kan ta daga kafaɗar Umman ta kalle ta sai ta kuma komawa ta
kwantar da kan ta tana ƙara tuno cin fuskar da Zaid ya mata a jiya how could he do that to her?..
Before she knows hawaye har ya fara gangaro mata sai ta saka hannu ta share su dai na su ido ne suna
jiran jin ƙarin bayani daga gare ta.
Kallon su ta kuma yi ta ja hanci ta ce
"Umma am alright am fine....ki daina ɗaga hankalin ki"!!sai sauran suka zazzauna ita kuma Umma ta kai
hannun ta saman kan ta tana shafawa kafin ta ce
"Baby me ya faru me ya sa baku tafi gidan ku ba kuka dawo separately"??sai ta sauke ajiyar zuciya
sannan ta ce
"Umma i can't"!!!shiru ɗakin ya ɗauka sai aka zubo mata idanu cikin tashin hankali Hajiya Zeenat ta ce.
"Baby ban fahimce ki ba you can't?what is it that you can't"??sai kawai ta saka masu kuka duk ta saka
su cikin duhu ɗago ta Umman tayi ta fara girgiza ta tana tambayar ta
"Me kika yi baby?ɓata masa rai kika yi?rashin kunya kika mai ya maki faɗa shine kike ganin baki iya
zama tare da shi"?..
Abin mamaki wai ita ma ake ba wa laifin all the good credits goes tio him shine gentile and good guy or
what?
"Yi magana mana baby"?kukan ta cigaba da yi kafin ta ce
"Umma i can't..i just can't..Zaid ba ni yake so ba...he...he..heee..."sai ta kasa ƙarasawa dan kukan da ya
ci ƙarfin sai Umma ta ce
"He what"??ko kafin jama'an ɗakin su ankara Bilkisu ta fara tsagewa Umman ta maganar Asma'u da
Zaid ya rinƙa yi mata a jiyan abin da ta ɓoye shine sirrin su amma duk rashin mutuncin da ya mata sai da
ta mayar a ƙarshe ta ce.
"I asked him to leave me alone if not i will kill him and he went ahead to come close to me"!!! ...sai ta yi
shiru a lokacin kamar ruwa ya gama cinye ƴan ɗakin sai Umma tayi ƙarfin halin tambayar ta me kuma ya
faru tana tsoron ba daiugun aiki Bilkisun ta aikatawa ɗan mutani ba..
"Da ya zo kusa da ke....me kika mai"???da tsoro cikin muryar ta tayi tambayar
Bata yi wani tunani ba ta ce
"Na mare sa na kuma ce mai yi warning nasa kar ya kuma nema ta and this morning i left all alone na
bar sa a chan"...ko da ta kawo ƙarshen zancen ta sai mutani ɗakin suka bi ta da kallon mamaki yayin da
Hajiya Zeenat ta ce da ita ta kuma maimaita abin da ta faɗa without thinking of the outcome ta
maimaita.
Bata kai ga ƙarasawa ba ta ga fuskar Umman ta ya chanza kamanni ran ta a matuƙar ɓace last thing she
can remember shine,cikin ɓacin rai da rage Umman ta ɗaga hannun ta a zuciye ganin haka ya sa ita
kuma ta rumtse idanun ta dan ta san hannun nan a kan fuskar ta zai yi landing,sosai ta rumtse idanun ta
tana jiran jin saukar marin saman fuskar ta...
*, S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
31
The blame games
Ko da suka dawo gida pretending gabaɗayan su suka yi kamar basu da masaniya akan abin da ya faru ko
hanyar ɗakin Zaid bata bi ba suka nufi ɗakin su hankali kwance ta shiga yi mai bayanin shawarar da suka
yanke akan matakin da zasu ɗauka game da matsalar ƴaƴan nasu amsa ya bata da
"Ina ganin da mun yiwa yaran nan faɗa saboda prof ya sanar da ni abin da ya faru according to baby
doctor sai na ga bai kamata mu bar su ba we should at least let them know their faults and improve ko
ya kika gani"ɗan murmushi ta mai mai gamsarwa kafin ta ce
"Dr ban hana ba kuma ban ƙi ta taka shawarar ba but ka sani fah yaran nan babu ɗan 18 years daga shi
har ita sun mallaki hankulan kan su babu fa'ida in mun ce zamu masu magana nake ganin in muka zuba
masu ido muka yi biris kamar bamu san komai ba da kansu zasu shirya dan babu daƙiƙi cikin su believe
me Dr this is the best way and a perfect way and method of punishing them both amma yi masu magana
will not solve the issue and at the same time punish them"shiru Dr Maher yayi yana sauraron ta kafin
daga bisani ya miƙe yana unbuttoning rigar sa yana faɗin
"Toh sauran family members ɗin kuma fah ya zamu yi masu bayanin shawarar da muka ɗauka"?tashi
tayi tana taya sa cire rigar nasa sai ta ce.
"Family meeting zamu yi gabaɗaya nan da chan gidan su Dr sai mu haɗu a yi bayani dan kowa ya san
abin da ake ciki ka ga ba za'a sami wani leaking grounds ba"riƙo hannun ta yayi ya ce
"Kamar da yaushe kenan kike ganin ya dace ayi meeting ɗin"?
"Eh toh,ko gobe ne da yamma dan ka san emergency ne kuma akwai abunuwan yi during the day time
but zuwa yamma an gama komai an dawo gida sai a yi cikin sukuni ko ya ka gani"gyaɗa mata kai yayi
kafin ya ce
"I will compose the message and make sure it communicate to everyone"gyaɗa kai tayi ta ce
"Nice Idea"sai ya ce
"Kenan ba zamu yi involving yaran ba kenan"harara ta danƙara mai tana girgiza kai ta ce
"Just yanzu yanzun nan you acted so smart and i was praising you yanzu kuma kana son sako shiririta
kamar ba da kai nayi maganar plan ɗin ba u don't know when you will ever become serious Dr"dariya ya
mata dan dama so yake ta sake kar abin ya cigaba da damin ta kamar yadda shi yake damin sa dan ya so
a ce ɗan sa na tare da matar sa by now he should have at least start a family amma bawa baya gujewa
ƙaddarar sa duk yadda ka so in Allah ya rigada ya tsaro maka dole kayi haƙuri ka karɓi ƙaddarar taka..
°°°°°°°°°°°°°
9am
Juyin farko da tayi kenan bisa kan gadon ta tun bayan da ta tashi tayi sallar asubahi ta
koma,sequentially ta buɗe idanun ta ta sauke saman fuskar Bahajjatu dake zaune saman sofa tana video
call da Bilal..
Wuf ta miƙe daga kwance ta ce
"Baha ke ce"?sai a sannan ta juyo da fara'a saman fuskar ta ta ce
"Beelove ni ce har kin tashi"?sai ta sallami Bilal ɗin dan ya zame masu addiction matuƙar ya isa wun aiki
sainya kira ta sun yi hirar mintuna biyar sannan su yi sallama haka itama in ta kai office ɗin ta sai ta kira
sa sun yi good luck wishes..
Cikin fara'a fuska ba yabo ba fallasa ta nufo ta tana ƙoƙarin mayar da wayarta cikin jakar hannun ta
wanda da ganin ta ka ga wacce zata tafi wurin aiki.
Da zuwan ta Bilkisun ta sauko daga kan gadon ta ta nufo Baha ɗin tana zuwa ta rungume ta sai kuka ita
kuwa Baha da ta san kwanan zancen sai ta ƙyale ta ta rinƙa risgar kukan ta dan a jiya bayan su Ammi sun
bar gidan babu Afzal a kusa ta tafi ɗakun Zaid ɗin ta gan sa cikin tashin hankali a nan ta damu ta shiga
tambayar sa sai ya kasa sanar da ita ainihin matsalar yayi shiru har ta gaji da tambayar sa ta fito sai Afzal
ɗin ne ke sanar da ita ɗan abin da ya sani sai tayi mamaki toh yau da safe ta shirya har zata wuce wurin
aiki Ammin su ta tsayar da ita ta mata bayanin abin da ya faru tsakanin yayan ta da aminiyar ta ta kuma
sanar da ita dalilin da ya sa mahaifin su yayi distributing masu family meeting message kenan..
Sai da ta yi mai isar ta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ita dai Baha ƙala bata ce da ita ba har
dai ta matsu ta ce
"Baha ba zaku tambaye ni matsala ta bane ko dan yayan ki ne baki son ganin laifin sa kema"?sai Baha ta
saka surprising face ta ce.
"You are unbelievable Beelove,yanzu dan kin yi kuka kamar baby Zarah har jira kike yi in tambaye ki
dalilin kukan ki sannan ki sako yaya na ciki?ai ko ba komai Beelove na san kukan ki na kewata da kika yi
ne wanda nima kin san na yi kewar ki sosai kukan ce bata kusa shi yasa ban yi ba kuma na san yaya na
shi ke da laifi dan jinyar sa ya sa bamu haɗu ba amma ki sani ni ba goyon bayan sa nake ba dan na fi
kowa jin kewar ki sam yaya bai kyauta ba"!!..sake baki Bilkisu tayi tana kallon bakin Baha da ke rero
waɗannan kalamai sai ta ce
"Yanzu Baha fahimtar da kika wa kuka ta kenan"cikin rashin damuwa da maganar ta ce
"Yes or don't you miss me as well"?idanun ta kyar saman fuskar ta yayin da take yi mata tambayar sai
Bilkisu ta zamo totally speechless ta kasa ce ma Baha komai.
"Toh na ga lafiyar ki Beelove ni zan tafi ayyuka sun taru min a office da yawa sai dai in na dawo zan zo
kin ji"?bata tsaya sauraron ta ba tayi gaba abin ta ita kuna Bilkisu ta shiga ruɗu yanzu Baha so take ta ce
da ita bata san ma'anar kukan ta ba ko me?me yasa bata ba maganar muhimmancin ba ko a jikin ta..
Wani