Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
har yanzu bata gane cewa son
Zaid ne da kishin sa ya mata dabaibayi haɗe da kane kane a zuciya ba dan alamu sun nuna ƙarara cewa
mugun kishin Zaid ne ke barazana da zuciyar aminiyar tata.
Kallon ta tayi ta ce
"Beelove ba kya ganin kina wahalar da zuciyar ki da yawa akan zancen zuciyar ki"?ɗagowa tayi haɗe da
share hawayen ta da bayan hannun ta sai ta ce
"Baha ban sani ba,wallahi ban sani ba ni kaina ba son wannan halin da nake ciki nake ba sam ban san
yadda zan yi ba"!!da cracking voice ta ida maganar wanda ya saka Bahajjatu girgiza kai kawai dan ta san
ko shekara zata yi tana mata bayanin feelings da take da shi towards her brother ba ganewa zata yi dan
haka ta ɗan yi tapping shoulder ɗin ta tana mai cewa
"Beelove zan bar ki ki gano abin da ke damin ki a zuciyar ki wanda ke faman wahal da ke"kallon juna
suka yi kafin Bahajjatu ta fita daga ɗakin tana alhinin irin wannan soyayya a da gani take ita da Bilal are
the best couples but she has been proven wrong saboda yadda ta ga so da kishin yayan ta a idanuwan
Bilkisu abin ba'a cewa komai amma ita sai ta ga kamar son da takewa yayan nata yana so ya mata yawa
dan haka wun Ammi ta wuce straight dan shafa mata labarin komai.
**********
_NIGERIA_
_1:00am_
Kwance Hajiya Zeenat take tana ta juya juye ta matsu washegari yayi ta ga ɗiyar ta dan tun da suka
dawo bata yi magana da ita ba most of the time tana bacci take kira shi yasa da Dr Muhammad ya sanar
da ita cewa tunda komai ya tafi masu yadda ya dace ba sai sun kai one week ɗin ba ma just 4 days suka
yi already kayan gyaran da Bahajjatu ta ce a karɓo mata ta aiki Bilal ɗin ya amso mata ita kanta ta gama
haɗe haɗen ta da zata gyara ɗiyar tata dan an gama fixing ɗauren auren biki ne dai ba za'a yi kasancewar
halin da ake ciki ba na wani shagali ko nishaɗi bane,a cikin kwanaki huɗu da suka wuce Dr Aslam yayi
nasarar shawo kan iyayen sa akan batun su tafi nema mai auren Bilkisun a cewar sa suna son juna kawai
halin ƙyaliyar ta ne ya sa bata iya expressing son ta but suna son junan su iyayen sa sai da suka kuma
tambayar sa ko ya tabbatar tana mai so irin wanda yake mata ya ce eh shi yasa suka shirya da abokan
baban nasa biyu making them three suka tafi har gidan Dr Muhammad Sulaiman dan nemawa ɗan su
auren ɗiyar sa babu sanarwa babu komai hakan ma harzuƙa Hajiya Zeenat yayi har ta so magana sai prof
ya hana ta ya ce shi zai yi handling nasu dan haka ƙyale ba dan ran ta ya so ba.
bayan gaisuwa ta mutunci da girmamawa prof ya tambaye su ko me ke tafe da su a nan amimin
mahaifin Aslam ya mai bayanin abin da ya kawo su sai dai kash rashin sa'a amsar da ya basu ne ya sa
suka kasa furta wani abin sai dai suka yi musabaha haɗe da godiya kafin su koma gida ai kuwa Aslam ya
haɗu da fushin mahaifin sa ranar dan sai da ya ja mai kunne dan baya son irin hakan ya faru but ɗan sa
ya janyo mai ko da Dr Aslam ya nemi sanin ko wanene mijin da aka ce an yiwa Bilkisu sai mahaifin ya
sanar da shi wai ɗan gidan aminin mahaifin Bilkisun ne sunan sa Zaid sai ya ji gaban sa ya faɗi ran sa ya
ɓaci dama wannan naƙasasshen har da halin da yake ciki sai ya mai shigar sauri ne wai,abin ba ƙaramin
girgiza shi yayi ba dan haka ya rinƙa ƙiran layin ta amma bata ɗagawa ƙarshe ma message ta tura mai
tana mai kashe mai warning akan ya fita harkar ta takaici ne ya ishe shi but bai haƙura ba ya san shi da
Bilkisu are made for each other he saw it countless times in his dreams kuma an ce ai dreams can
sometimes become reality shi yasa bai cire tsammani ba.
A kwanakin ne kuma Dr Hussaini ya kawowa iyayen Bilkisu ziyara haɗe da tambayar su jikin marasa
lafiya suka sanar da shi halin da ake ciki har ma da dalilin su na dawowan dan amsar mai magani godiya
suka mai da nuna kulawar sa kafin daga ƙarshe Hajiya Zeenat ta matsu ta tambaye sa ko ya san wani
abin akan yaron da ya ma ƴaƴan su wannan abin sai ya ɗan murmusa kawai kafin ya ce da su
"Umma ai an wuce wurin tuntuni"!sai abin ya ɗaure masu kai dan ba su fahimci an wuce wurin ba sai
prof ya tambaye sa dan ƙarin bayani
"Dr bamu fahimce ka ba me kake nufi da an wuce wurin"?sai ya sauke ajiyar zuciya haɗe da fara labarta
masu abin da ya faru
"Wato bayan na dawo da su nan gida na kuma zuwa visiting na su after 2 days sai Bahajjatu ta tsare ni
ta tambaye ni ko ina da masaniya akan abin da ya faru da yayan ta sai na sanar da ita komai da na sani ta
min godiya muka rabu,bayan kamar kwanaki huɗu da haɗuwar mu da Bahajjatu sai yayan ta Hakim ya
kawo min ziyara ta musamman a inda ya ce da ni in basa cikakken tarihin yaron da ya ma ɗanuwan sa
wannan abin a iya tsawon rayuwa ta a ƙauyen koma ban yaɓa jin labarin tsagirin yaro kamar Mudan ba
dan haka na sanar da shi komai sai na ga kamar ran sa ya ɓaci amma nayi calming nasa dan na san halin
sa na zuciya a yadda muka rabu ya nuna min komai ya wuce ya kuma sanar da ni da zarar sun farfaɗo zai
ɗaga ƙara ya shigar da hukuma cikin lamarin lafiya ƙalau muka rabu bai kuma nema na ba ban kuma ƙara
jin wani abu ba a ƙauyen mai muni dangane da Mudan,kwatsam bayan tafiyar ku germany da kwanaki
na sami kira daga wun mai garin koma wanda a gidan sa su Zaid suka zauna lokacin da suka tafi outreach
shi ke sanar da ni wai akwai wasu yara biyu da suka tafi garin suka bi su har gida suka masu alheri daga
ƙarshe suka nemi da a kai su gidan su Mudan a lokacin basu yi revealing identity ɗin su ba sai aka haɗa
su da babban ɗan mai garin ya kai su har gidan su Mudan a nan ɗin ma alherin suka masu ba tare da sun
sanar da su ɗin ko waye su ba sai suka nemi sanin inda shi Mudan ɗin yake akan wai sun zo ne daga birni
dan taimaka mai da jari saboda ya daina halin da yake yi na rashin ji a cewar su ma daga hukumar yaƙi
da zaman banza suke daga cikin garin Adamawa ai kuwa jin wannan sai mahaifiyar Mudan ta masu
kwatancen inda yake zama wanda yake chan bayan gari cikin daji da taimakon babban ɗan mai gari suka
yi tracing Mudan sun yi sa'a dan shi kaɗai suka samu a wurin yana shan barasa duk sauran yaran sa basu
nan dan haka suka sallami ɗan mai gari haɗe da yi mai godiya har da kyauta ya tafi yana farinciki dan har
yayi niyar kirawo samarin ƙauyen akan su zo ga masu yaƙi da zaman banza nan sun zo,sai da suka
tabbatar ya tafi sannan Hakim ya cire suit ɗin sa ya bama Bahajjatu ta riƙe mai ya naɗe hannun rigar sa
ya shiga jibgar Mudan ba ji ba gani each punch da yake kai mai gani yake kamar heaviness da ke ran sa
bai raguwa dan sosai ya rinƙa kai mai punches bai bar sa ba sai da ya mai dukan da ya san dole ne ma ya
kwanta jinyar sati ko bai kai wata ba da ya gama ya saka hannun sa a aljuhun sa ya fiddo da allurar kashe
zafin gaɓa ya zuƙe kwalbar gabaɗayan sa ya danna ma Mudan a daidai cinyar sa inda ma bai kamata ba
bayan ya mai ya kuma zuƙe wata kwalbar ya danna mai a ɗaya cinyar sa daga haka ya hankaɗa sa ya ja
hannun Bahajjatu suka bar wurin a nan suka bar Mudan suka yi tafiyar su,toh according to mai gari wai
da suke dawowa ne suka biya ta gidan sa suka sanar da shi cewa wai ai da suka tafi neman Mudan ɗin
bayan sun gan sa sai tsagerun ƙauyen suka kawo masu hari da kyar suka gudu dan haka su zasu tafi
tunda ba'a son taimakon su,sai mai gari ya ce da ni wai yayi yayi su tsaya ya kirawo masu na garin
ƙauyen amma suka ce a'a su tafiya zasu yi a nan yake sanar da su labarin su Zaid wai suma da kyar suka
sha da shi tsagerin da suka tafi taimaka wato Mudan su dai kawai sallamar su suka yi suka tafi ko ta kan
ita Asma'un basu bi ba a cewar su zasu kai mata ziyara ta musamman bayan kwana biyu dan sanin dalilin
ta na saka hannu a ta'addancin da aka yiwa ɗanuwan su"numfasawa yayi ya cigaba
"Duk wannan ƙarin bayanin daga bakin Hakim na same su dan sai da na kira sa na tambaye sa shin ko su
suka aikata hakan sai ya tabbatar min da cewa eh sune kuma muddin yayan sa bai farfaɗo ba toh sai ya
koma ya kasara Mudan dan yayan sa ba zai yi jinyar wahala shi kaɗai ba nikuma calming nasa kawai nayi
dan dama mutanin garin na neman mai saita yaton ba'a samu ba not until when Hakim and Baha went
there and deal with him,toh kun fah ji Hakim dai da goyon bayan sister ɗin su Bahajjatu sun ɗau fansar
abin da aka yiwa yayan su ina ga ai ko a haka ma aka bar shi an kasara mai rayuwa dan a halin yanzu
yana nan a gida an ma rasa ta yaya za'a fara da treatment ɗin sa duk jama'an ƙauyen murna suke yi yana
gida ana gargajiya amma saboda ƙarfin allurai da Hakim ya mai ya sa ya sami temporal lost of function
wanda sai a hankali zai warware but before then ya ji jiki gashi a buge yake bare ya ce ya gane waɗanda
suka mai dukan dan haka shiru iyayen sa suka yi dan sun san sakayyar mutanin da ya cutar ne ya biyo
sa".yana kaiwa nan yayi shiru ajiyar zuciya suka sauke su sun rasa me zasu yi murna ne kokuma akasin
haka dan Hajiya Zeenat ta ɗau burin hukunta yaron sai dai yanzu ta sami sauƙi da relief tunɗa an ɗau
masu fansa shi kuma prof godiya ya ma Dr Hussaini haɗe da miƙa mai hannu suka yi musabaha sannan
suka rabu.
Al'amarin ya ba Dr Muhammad mamaki zuciyar Hakim ya kai har haka dama toh dole ne ma ya mai
faɗa dan da a ce yaron ya rasa ran sa fa ai sai laifin su ya danne wanda yaron ne yayi masu.
Ran Hajiya Zeenat fes dan jin an rama masu abin da yaron yayi wa ƴaƴan su har ɓarin jiki take yi
washegari yayi su koma germany dan ta labarta ma Hajiya Madina gwanintar da ɗan su yayi,.
A washegarin da wuri Bilal ya raka su airport a inda ta bar mai saƙo zuwa ga babban yayan su wato
Jamil akan ya sanar da ƴanuwan su cewa nan da sati za'a yi ɗaurin auren Zaid da Bilkisu saboda Jamil ɗin
baya nan ya sami tafiyar gaggawa,bayan jirgin su ya tashi ne Bilal ya kira apple ɗin sa ya sanar da ita
aminiyar ta fah zata zama matar brother In-law nan da sati guda kamar ta yi hauka dan murna dan haka
ta ce da shi zata bashi goron wannan albishirin da ya mata matuƙar sun haɗu.
***********
Already Hajiya Madina ta gama jin bayani daga wun Baha akan tattaunawar su da Bilkisu itama ta zage
akan ba ma Bilkisun shawarwarin zaman aure har da nasihohin haƙurin zaman gidan miji,dama bayan
48hours da ta ɗibarwa Bilkisun ta sami ƙwarin gwiwar sanar da ita cewa ta amince zata auri Zaid hakan
ba ƙaramin farincikin ya saka Hajiya Madina ba shi yasa ta ja ta a jiki ta shiga yi mata nasihohi because
that is all she have for her at that moment duk wasu maganar gyara kuma sai bayan sun dawo gida dan
she is absolutely sure cewa babu wani abin da zai shiga tsakanin ta da Zaid that she can guarantee shi
yasa ta dage da koya mata abubuwan mata matan ma masu aure waɗanda suka amsa sunan su ota dai
jin Ammin take yi ba wai ta gama yarda Zaid zai so ta bane ko da ya farfaɗo and yet bata gama
concluding ba a zuciyar ta son sa take kokuma tausayin sa take..
Lafiya ƙalau suka dawo ƙasar germany a inda suka nufi apartment ɗin su abin da ya zamewa Dr Maher
da Hajiya Madina kamar almara dan basu yi tsammani ba a nan prof ke sanar da su ai abin da ya kai su
ne dama ya zo masu da sauƙi.
Bayan wasu lokuta sun huta sai Hajiya Zeenat ta matsawa prof akan ita fah lallai lallai sai sun gana da
aminiyar ta dan abin na tsungulin ta ya ya iya da ita haka ya bar ta ta tafi asibitin wanda da ganin ta
Bilkisu ta faɗa jikin ta kamar zata yi kuka ta shiga complaining wai tun da suka tafi bata kira ta ba sai ta
mata bayani haɗe da ɗaga ta daga jikin ta tana mai ce mata zata dawo anjima bari ta gana da momma
ɗin ta girgiza mata kai tayi sannan Hajiya Zeenat ta fita ta nufi ɗakin Zaid inda ta san zata ga Hajiya
Madina ai kuwa sun yi murna a karo na biyu wanda Hajiya Zeenat ta kasa haƙura har sai da ta feɗe mata
daga biri har wutsiya duk a cikin labarin babu wanda ya fi burge ta sama da fansar da Hakim ya ɗaukar
masu daga shi sai maganar maganin Zaid ɗin wanda ya saka Hajiya Madina zubda ƙwallar farinciki after a
long while ɗan ta zai farka kuma,hira suka yi sosai a nan Hajiya Zeenat ke sanar da ita ai ta kawowa
Bilkisu kayan gyara na musamman sai abin ya bama Hajiya Madina dariya ta ce
"In ban da abin ki Hajiya Zeenat ina shi Zaid ɗin ya gama samin lafiya har da zai nemi matar sa kar fa ki
manta ko ya farfaɗo bai gama samin lafiya ba"sai itama Hajiya Zeenat ɗin ta dara haɗe da cewa
"Hajiya Madina kenan ai yanzu zamani ya zo ma yaran nan da abubuwa daban daban ɗan nan kar kiyi
mamakin in ya farka ayan kwanaki kaɗan ya fara nemar matar sa dan fah shi ɗin namiji ne wanda bai
san daɗin mace ba the moment ya ga sun keɓe da yarinyar nan ya kuma san cewa matar sa ce a jin ki zai
yi ignoring nata ne?ai sai dai bayan ya aikata mai gabaɗayan a maida shi kan gadon asibiti kin ga kenan is
inevitable we can't tell"shewa suka yi suna mamakin yaran zamanin nan.
A ranar kuwa aka fara bankawa Bilkisu kayan gyara a same day aka fara treating Zaid da maganin da aka
kawo daga Nigeria but basu bari asibitin ta sani ba dan suna iya hanawa su kuwa so suke ɗan su ya farka.
Askin da ta damu a yi masa kuwa aka ƙi yi aka ce sai ta aure shi sannan ita ta mai dan tsabagen damuwa
har Umman ta ta ma magamar askin bata sani ba because wani abu wai kunya kamar ƙaurace mata yake
yi in zata yi maganar Zaid.
A nan Nigeria ana ta preparation na ɗaurin auren Zaid da Bilkisu a nan germany kuwa ana jiran
farfaɗowar Zaid dan ana 4th day kenan da aka fara mai treatment tukunna prof bai sami kan sa ba dan
haka bai sanar da Dr Maher abin da su Hakim suka aikata ba kuma bai ma nemi Hakim ɗin ba iyakan abin
da suke jira shine farfaɗowar Zaid wanda a tsarin treatment ɗin suna saka ran kafin satin ya ƙare zai
farfaɗo wanda kuma ya rage saura kwanaki biyu a ɗaura auren sa da Bilkisu ita kanta bata san me take ji
dangane da auren ba daɗi ne kokuma tausayin kanta dan daga Ammi,Umma da Baha duk sai zuzuta
mata maganar auren suke yi wai dan ta ji sauƙi da daɗi a zuciyar ta.
ranar da ya kasance ranar da su Dr Maher da Dr Muhammad zasu koma Nigeria dan washegarin ranar
za'a ɗaura auren ƴaƴan su,a ranar bayan tafiyar su Bilkisu ta kasa sukuni ta rasa me ke mata daɗi gashi
tana son ganin Zaid ɗin amma ta rasa yadda zata yi bata gan sa ba sai cikin dare ta sulale ta nufi ɗakin ta
zauna tana kallon sa ta rasa me zata yi farinciki ko akasin haka dariyar murna ko akasin haka yanzu fah
auren ta za'a ɗaura da shi what if he wakes up and said baya son ta ya zata yi?sai ta kuma mayar da dara
daran idanun ta kan kyakyawar fuskar sa ta kasa furta komai ta kasa tantance feelings da take da shi ma
Zaid,ƙura mai ido tayi tana kallon sa what is she feeling?the feelings is different is she actually in love
with Zaid?sai ta ƙara girman idanun ta ta hanyar buɗe su sosai ta furta a zahiri
"Am i in love with Zaid Maher"?....
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*18*
*_promise_*
Abin mamaki me ke damin ta ne wai haka,ta yiwa kanta tambayar sannan ta ba ma kanta amsa "what
else if not love"!!hakan ya sa ta shiga murmusawa ita kaɗai ba tare da ta san tana hakan ba mayar da
idanun ta tayi zuwa kan suman kan sa da yayi yawa fiye da da sai ta ji kamar ta masife Hakim da ke kula
da shi akan menene ba zai gyara mai fuska da kai ba gashi nan suman kan sa da na fuskar sa sun wuce
misali ai hakan sai ya ƙara mai rashin lafiya,
Zancen zuci take ta yi ita kaɗai daga bisani ta miƙe ta tofa mai addu'a sannan ta fara tafiya dan komawa
ɗakin ta tana tafe tana juyowa tana kallon sa har dai ta kai bakin ƙofar kamar kar ta fita ta zuba mai
idanun nan nata