Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
ta san abin da ke zuciyar aminiyar tata sai tayi karaf ta ce
"Kul Hajiya Zeenat na gama magana a bar ta haka nan ta huta ta ji da ɗaya please"sai ta yi shiru tana
kallon su,ganin Umman ta bata kuma ɗaga mata murya ba sai ta kalli Ammin ta ce
"Ammi zan tafi wun Zaid please don't say no"...abin tausayi haka Hajiya Madina ta mata alƙawarin zata
kai ta but under one condition akan sai tayi wanka ta ci abinci ta rama sallolin ta ta yi kwalliya ta amince
ba dan ran ta na so ba sai dan tana gudun rasa damar da Ammi ta bata..
Tashi Hajiya Madina tayi ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka haɗe da zuba mata bath lotions masu
sanyin ƙamshi sannan ta haɗa mata wani ruwan turare da na tsuguno sai da ta tabbatar da cewa komai
yayi daidai sannan ta fito ta ce da ita ta shiga ciki tayi wankan,.
Tashi tayi ta shige da kayan jikin ta ta rufe toilet ɗin bayan shigan ta ne Hajiya Zeenat ta buɗe baki fa
nufin yin magana amma Hajiya Madina ta hana ta ta ce magana ta wuce iya halin da take ciki ma ya ishe
ta haka nan ba sai an ƙara mata da wani damuwar ba...
Ko a toilet ɗin ban da kuka babu abin da ta ɗau lokaci tana yi kuka take na kewar mijin ta dan babu abin
da ke dawo mata sai wankan da suka yi na ƙarshe tare da shi yadda suke facali da ruwa daga cikin
bathtub ɗin har yadda ta rinƙa wasa da fuskar sa tana shafa mai foam a fuska ta shafa a girar sa sannan
ta shafa mai round his mouth wai tana mai father christmas duk waɗannan moments ke ta dawo mata
tana tuno su tana kuka,..
Bata fito da wuri ba dan sauran kayayyakin ma bata bi ta kan su ba ta fito ɗaure da towel idanun nan
sun rikiɗe sun koma jajir sun ƙara girma..
ganin ta haka sai Hajiya Madina ta ce
"Ke kin yi amfani da sauran kayan kuwa"?ko ta kan su bata bi ba dan haka ta girgiza kai sai ta harare ta
tana faɗin
"Toh koma ciki"haka kamar idol ta koma ita kuwa Hajiya Zeenat mamakin Hajiya Madina ne ya cika ta
ana ta kai tana ta kaya wato duk inda zata tafi da waɗannan kayayyakin take tafiya ikon Allah...
Tana tsaye daga bakin ƙofar tana jiran fitowar ta haka a takure tayi tayi tsugunon sannan ta ɗauraye
jikin ta da ruwan turaren da ya gama yin sanyi...
Alwala ta kuma yi sannan ta fito zata yi sallah Ammi ta hana ta akan ta fara cin abinci,a halin da take ciki
komai aka ce da ita tayi zata yi dan son gamawa da mijin ta..
Natsuwa tayi ta ci abincin a hankali har ta kammala ta yi rinsing bakin ta ta saka doguwar riga ta saka
hijabi ta hau saman sallaya ta tada sallah,..haka ta rinƙa yin sallolin har ta idar sannan ta zauna ta yi
addu'oin da zata yi ta tashi tsaye tana kallon Ammi fuskar ta gwanin tausayi sai Ammin ta miƙe suka fito
tare da Bilkisun suka nufi ɗakin Zaid ɗin da zuwan su ta ja birki ta tsaya tana faɗi mata
"Ga ɗakin nan make sure you take care of your husband properly okey"gyaɗa mata kai tayi sannan ta
shige ciki ta zauna idanun ta kan fuskar sa kan sa naɗe yake da bandage kamar dai ba wani abin da ya
same sa tana kallon sa tana tausaya masa..
Hannun su ta haɗe wuri ɗaya tayi interlocking ta yi kissing hannun tana jan hanci tana surutai kamar
zararriya kewar sa take ji tana magana tana taɓa cikin ta tana kallon fuskar sa
"Hero please wake up i missed you alot i missed your cuddle please come back to me come back to our
baby am so sorry i couldn't stay back and see you in pains please forgive me my husband my hero"tana
kuka ta rinƙa nanata kalmar ya yafe mata har dai ɓarawon bacci ya zo ya sace ta ba tare da ta shirya ma
baccin ba dan ko cikin baccin mafarkin sa take yi...
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*41*
Karaf ta tashi sakamakon jin motsin hannun sa cikin nata hannun dan a mafarkin ta ta gan sa yana mata
sallama akan ya tafi har abada kuma yana son ta fiye da yadda take tunani tana tsaka da mafarkin ne ta
ji motsin hannun sa shine ta yi wuf ra farka..
Ganin sa tayi yana juye juye a hankali daga dukkan alamu kan ne ke mai ciwo dan haka ta yi saurin raba
hannun su ta fita tayi hanyar ɗakin ta tana kiran sunan Umman ta..
Kamar daga sama Hajiya Zeenat ta ji ana kiran ta sai tayi saurin tashi tana dube dube sai ta kuma jin
sunan ta a nan ta tabbatar da cewa Bilkisu ce dan haka tayi saurin gyara hijabin ta ta fito tana duba ta..
Chan nesa ta hango ta tana tahowa a hargitse sai tayi saurin ƙarasawa inda take tana son dakatar da ita
daga ihun da take yi saboda yanayi na asibiti kar ta dami wasu..
Tana ihun tana tafe har suka haɗe da Hajiya Zeenat ta rungume ta a jikin ta tan faɗin
"Baby lafiya,,me ya faru"?jiki na ɓari tana faɗin
"Umma Zaid ne ya farka zo ki gani"...
"Ya isa haka nan na ji toh mu tafi amma calm down kina ɗaga hankalin ki da yawa kin kuma san bai dace
da state of health ɗin ki ba"shiru tayi amma jikin ta bai bar ɓari ba haka dai tana jikin Umman suka koma
ɗakin Zaid ɗin wanda zuwa lokacin har ya koma baccin sa dama tsorata da tayi da lamarin ne ya saka ta
firgita fiye da ƙima...
"Kin gani,,har ya koma bacci zo ki zauna ki daina ɗaga hankalin ki akan rashin lafiyar sa zai warke kin ji
baby"?gyaɗa mata kai kawai tayi ta koma ta zauna kusa da shi ita kuma Hajiya Zeenat ta fita ta koma
ɗakin Bilkisun duk tausayin yarinyar ya gama kama ta a ce an yi aure har yanzu ba'a sami kwanciyar
hankali da natsuwa ba sau biyu suna zaman asibiti duk a hargitse yaushe su wannan jarabawar zata zo
masu ƙarshe ne...
Tun da ta koma ɗakin ta zauna ta ƙura mai ido tana kallon sa kamar bata san sa ba,a cikin jikin ta ta san
rashin lafiya ne ƙarara ke addabar ta amma dole ta danne dan ta kula da shi,a haka har asubahi ya
gabato in ta kalle sa ta kai mai kisses a jikin sa gabaɗay ta gama sagewa da wannan irin murɗaɗɗen
al'amari masu yau lafiya ana zaune cikin jin daɗi gobe akasin haka when will all these get over....
Jin kiran sallah tayi dan haka ta miƙe ta shiga bayin ɗakin da yake ta yi alwala ta dawo ta tayar da sallah
gabaɗaya jikin ta wani iri yake mata kamar ba'a jikin ta ba rashin lafiya ne ke ɗawainiya da ita amma
haka ta daure tayi sallar ta zauna ta rinƙa yi ma mijin ta addu'ar samin lafiya haɗe da fatar iyakar wahalar
kenan...
Tana idarwa ta miƙe ta nufi gadon nasa tana kallon sa a haka bacci mai nauyi ya ɗauke ta dan
throughout daren jiya bata koma bacci ba tun da ta farka haka ba dan hankalin ta na kwance ba ta koma
baccin hannun ta cikin nasa....
A nan ɗakin ta kuwa Hajiya Zeenat da Hajiya Madina haramar komawa suke yi saboda dama abin da ya
kamata su yi sun yi kuma ya farka and they thought of leaving the children alone saboda in har Bilkisu na
ganin su tana iya zama relaxed kuma ko wace mace a gidan mijin ta dole ita zata zama komai na gidan
kamar yadda su suke yi a nasu gidajen dan haka 11am flight zasu bi su koma saboda likitan yayi
reassuring nasu akan komai zai yi daidai since he is now back to his normal state of health...
"Ni ko Hajiya Madina in tambaye ki mana"cewar Hajiya Zeenat sai ta juyo ta kalli aminiyar nata ta ce
"Ina jin ki"gyara zama tayi kafin ta ce
"Wai a ina kika samo waɗannan haɗe haɗen da kika ma yarinyar nan jiya"??murmushi Hajiya Madina
tayi kafin ta ce
"So kike ne in baki ko ko son sanin asalin sa kike"?sai itama ta mayar mata da murmushin dan ta san
halin Hajiya Madina sarai in har bata son revealing maka abu toh sai ta rufe maka baki ta yadda sai ma
ka rasa me zaka kuma yi mata tambaya a kai..
"Ko ɗaya kawai dai tambaya ne amma tunda an min hannun ka mai sanda bara nayi shiru"dariya suka yi
at the same time suka tafa sai Hajiya Zeenat ta zayyane ma Hajiya Madina abin da ya faru a daren jiya
wato firgitan da Bilkisu ta yi..
"Hmm ai ni yaran nan ma tausayin su nake wallahi kin san fah tun da aka yi auren nan kwata kwata ba
wani natsuwa suka yi ba sam yadda na so su more auren su bai yiwu ba dan basu zaga ba babu
honeymoon ga ciki ya shiga ɗan space ɗin da suka samu kuma sun zo hutawa and this is the result i feel
very bad for them is not easy gaskiya a ce kullum mijin ka bai da lafiya dan ma yarinyar na da juriya ne if
not wace macen ne zata iya da rashin lafiyar sa Allah dai ya ƙara masu lafiya"ajiyar zuciya Hajiya Zeenat
tayi tana faɗin
"Amin"daga haka suka shiga tattaunawa akan sha'anin rayuwa har dai suka komo kan zancen su Bilkisu
na rashin dawowar ta har dai Hajiya Madina ta tashi da niyar tafiya dubo su sai suka jiyo sallamar
Bilkisun haɗe da turo ƙofar ɗakin..
Karo ta yi da kayan su da suka gama haɗawa akan zasu koma sai tayi ƙasa da murya gwanin tausayi ta
ce
"Tafiya zaku yi"?riƙo t Hajiya Madina tayi tana mai jan ta har ta zaunar da ita saman gado kafin ta ce
"Tafiya zamu yi Bilkisu dan haka ki natsu mi kula da kan ki da mijin ki kin dai san yanayin da kike ciki
damuwa duk ba naki bane concentrate and take care of yourself and your baby okey"?gyaɗa mata kai
tayi tana faɗin
"Yaushe zaku dawo"?abin sai ya basu dariya su biyu har suka dara kafin Hajiya Zeenat ta ce
"Dama tare muka zo da ku?ku da kuka yo tafiyar ku ku kaɗai baku sanar da mu ba"..sai abin itama ya
bata dariya amma bata cikin yanayin dariyan dan haka sai ta murmusa kawai kan ta ƙasa ta ce
"Umma da yaushe zaku tafin"?amsa Hajiya Madina ta bata da
"11am saura ma 30minutes mu tafi airport"cikin sauri ta ɗago ta kalli Ammin kamar zata yi kuka ta ce
"Ammi amma fah bai farka ba ku bari har ya farka"sai suka kalli juna kafin daga bisani Hajiya Madina ta
ce.
"No tafiya zamu yi inshaAllah Allah na tare da ku zai farka very soon ko muna nan ko bamu nan zai
farka da izinin Allah so don't worry okey"?shiru tayi ita dai tana jin har ta fara kewar su amma bata da
bakin kuma tuhumar su akan dole sai sun tsaya...
"Kin ci breakfast ne"?girgiza kai tayi sai Hajiya Madina ta buɗe ido
"Anya Bilkisu kina kula da kan ki kuwa baki ci abinci akan wani dalili kin ga time kuwa"?sai tayi shiru
haka aka haɗa mata tea ta karɓa aka miƙo mata toasted bread da aka ajiye mata na breakfast shima ta
karɓa ba wai dan tana son cin su ba ta ɗan ci kaɗan sannan ta ajiye su gefe ai kuwa Hajiya Madina ta
taso ta gaba
"Ba dai iya abin da kike ci ki ce kin ƙoshi ba kenan Bilkisu"?sai ta kuma duƙar da kai ƙasa ai kuwa Hajiya
Madina ta rinƙa yi mata faɗa ita kuma Hajiya Zeenat na kallon Bilkisun dan dai bata da ikon magana ne
ta so ta yi maganar rashin cin abincin Bilkisun but Hajiya Madina na mata faɗa already dole ita tayi shiru
"Ammi wallahi bana marmarin shan tea ɗin ne"baki a buɗe su duka sai Hajiya Madina ta ce.
"Toh me kike marmarin ci yanzu"?tunowa tayi da mijin ta sai ta ji hawaye na son zubo mata dan shi
kaɗai ya san me ya dace da ita shi kaɗai ya san irin abincin da take son ci wanda bai wuce quacker oat ba
sai dai tana ganin in ta faɗi ra'ayin ta maybe ba zasu biye mata ba maybe su ce she is not serious
"Ammi don't worry anjima zan ci abinci masu irin wanda nake ci ne babu su a nan sai a chan masaukin
mu"gyaɗa kai suka yi kafin suka miƙe suka hau shirin tafiya..
Tsakani da Allah kamar tayi kuka haka ta rinƙa ji sai dai bata bari ya fito ba ta kwaɓi kan ta..
Tana ji tana gani suka shige cab da zai kai su airport,har sun shige Hajiya Madina ta leƙo ta yafito ta da
sauri ta matso kusa da motar ta duƙar da kan ta wani magana ta mata a kunne wanda ya saka Bilkisun
yin ƙasa da kai tana jujjuya kai gefe duk kunya ya gama lulluɓe ta..
Ɗaga masu hannu tayi tana kallon su har motar ya tashi suka wuce ita kuma ta sauke ajiyae zuciya ta
koma ciki,..
Bata bi ko ina ba sai ɗakin Zaid ɗin wanda ke kan kwasar baccin sa hankalin kwance sai ta ɗan mai
kallon sama sama kafin ta fita ta koma waje ta nufi hanyar office ɗin Dr da ya mai aikin..
Izini aka mata ta ƙarasa ciki ta zauna jiran sa dan ya tafi ganin wani patient kusan mintuna goma sai
gashi ya shigo fuskar sa ɗauke da fara'a ya gaida ta ta ansa haɗe da ƙara yi mai bayanin ko ita wacece
sannan ta mai tambayar da zata wanda tambayar akan lafiyar Zaid ne dan ta matsu ta ga ya farka haka
likitan yayi assuring nata akan any moment yana iya farkawa cikin ƙoshin lafiyar sa sai dai a hankali zai
warke wanda zai ɗau sa at most 2 weeks or 3 ta kuma tambayar sa ko in ya farkan zasu iya komawa gida
dan su rinƙa zuwa checkup kawai ba sai sun cigaba da zaman asibitin ba ya ce da ita sure muddin babu
wasu minor damuwa suna iya komawa gida da haka ta mai godiya ta miƙe ta fita ta koma ɗakin Zaid ɗin
ta tasa sa gaba da kallo kamar ta ce da shi tashi ya tashi...
Tana zaunen ta ji abin bai mata ba sai ta tashi tsam ta koma saman gadon kusa da shi ta kwanta haɗe
da ɗora kan ta saman ƙirjin sa tana mai jin kewar sa sosai hannun su sagale tana jin bugun zuciyar sa
wanda yake bugawa a hankali kamar yadda ya kamata sai ta natsu tana sauraron fitar numfashin sa...
Bata runtsa ba tana nan kwance a jikin sa har tsawon lokaci sai kuwa kamar a mafarki ta ji yana
motsawa bakin sa na motsawa kamar dai magana zai yi sai ta yi saurin tashi tana kallon sa...
A hankali ya buɗe idanun sa ya sauke su saman fuskar ta da ke saitin nasa fuskar sai ya lumshe idanun
sa ya kuma buɗewa a hankali duk tana kallon sa,jin kan sa yake ya mai nauyi da yawa kamar ba kan sa ba
sai ya rinƙa jin ɗakin na juya mai ya ɗaga hannun sa ya ɗora bisa kan sa yana mai ƙanƙamewa,ganin haka
tayi saurin dirowa ta zo ta gefen sa ta ɗora hannun ta saman nasa hannun tana mai taya sa riƙe kan..
Tsawon lokaci sai ya natsu sakamakon nin ciwon kan ya lafa mai sai ya koma ya kuma kwanciya da kyau
bisa ga yadda ɗazu ya kwanta...
Hawaye ne tab cike a idanun ta amma ta matse ta ƙi barin su su zubo ta danne su ta buɗe baki tana
tambayar sa murya a karye
"Hero,ina ke maka ciwo faɗa min"!!bin a da ido yayi yana mata wani irin kallo wanda ya hargitsa ta ya
rikirkita ta ta kasa samin natsuwa sai ta cigaba da bin sa da ido tana son jin amsar da zai bata amma bai
bata amsar ba..
Shiru shiru zai yi magana ba zai yi ba har dai ta gaji ta kai gwiwowin ta ƙasa ta fashe mai da kukan ban
tausayi tana faɗin
"Hero please talk to me silence ɗin ka na kashe ni slowly please say something ko baƙar magana zaka
gaya min go ahead and say it am all yours ka min duk abin da zaka min amma kar ka min min shiru ka
rinƙa bi na da ido"..da kuka ta ida maganar tana kallon cikin ƙwayar idanun sa tsantsar so da tausayin sa
duk sun saka ta gaba sun hana ta sukuni...
Inside him chan cikin zuciyar sa yana son yi mata magana amma ya rasa dalilin da ya hana sa furta mata
komai har ya zuba ido yana ganin hawaye na wanke mata fuska..
Juyar da kan sa gefe yayi dan baya son ganin hawayen nata suna taɓa sa a zuciyar sa sai dai bai san ta
ina zai fara ba dan maganar ma nauyin fitowa yake mai..
Ɗagowar da zata yi sai ta ga ya juyar da idanun sa gefe ai sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan
tana yi tana jijjiga gadon nasa tana maganganu marasa bearing tsabar ta ruɗe ta gama tsinkewa da
lamarin tunanin ta fushi yake da ita akan abin da ta mai.
"Hero please talk to me shirun ka azaba ce a gare ni wallahi,ni ko duka na zaka yi na amince ka tashi ka
dake ni ba zan tambaye ka dalili ba komai ka yi daidai ne"..
Komawa tayi kusa da shi ta ɗaya ɓangaren da ya juyar da fuskar sa,zuba ma juna ido suka yi suna kallon
juna shi kallon tausayin ta yake yi ita kuma kallon son sa da tausayinsa take mai hawaye kuwa kamar an
ɓalle kan famfo sai zubowa yake yi...
Ɗaga hannun sa yayi yana ɓari ya ɗora bisa hannun ta yana mai girgiza mata kai alamun tayi shiru sai ta
tsira mai ido tana kallon sa ta rasa abin faɗa..
Girgiza mata kai ya shiga yi yana mai zubda ƙwalla daga idanun sa,saurin kai hannun ta tayi gefen fuskar
sa dake fidda ƙwallar ta goge mai