Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
kyau ga ƙamshi na tashi a ɗakin,kwantawa ta yi tana tunanin gida
dan tun da ta zo babu network a garin shi yasa bata sami damar yin waya da ƴanuwan ta hakan ya dame
ta sosai gashi shi ɗin da ya kawo ta garin bai ma damu ya san halin da take ciki ba which hurt her a lot
but bata cire rai ba akan gobe zata kuma ƙoƙarin ganawa da ƴanuwan ta...
*************
Basu tashe ta ba sai wuraren ƙarfe 6 na safe godiyar ta ma ba sallah take yi ba dan haka tashin farko ta
ankara da cewa gidan nan akwai ƙarancin ilimin addini dan haka shima yana cikin aikin da zata yi a garin
ba ma a gidan ba kawai,
Komawa tayi ta kwanta bayan ta sanar da su cewa fashin sallah take yi ai kuwa tun lokacin da ta koma
basu tashe ta ba sai da ta tashi dan ƙashin kan ta which is 1:45pm ta ji mamaki ba kaɗan ba su kuma
haka suke rayuwar su.
Ita amaryar mai garin wato zulfa'u ita ce ta kai mata ruwan wanka a toilet ɗin ta na ɗakin wanda ya sha
gyara ba laifi yana ƙamshi dan dama zulfa'u ba laifi wun gyara da ajiye ƙamshi a sashen ta,wankan ta
shiga ta yi ta fito ɗaure da towel a ƙirji tana goge fuskar ta cikin sakin fuska ta karasa wun zulfa'u ta ce
mata
"Ina yini"amsa mata tayi ta na ce mata
"Likiciya ya baƙunta"?murmusawa tayi dan jin sunan da ta kira ta da shi wai _likiciya_
"Alhamdulilah kuma sai kika bar ni ina ta barci madaɗin ki tayar da ni in taya ki aiki"hangame baki tayi
kafin ta saka dariya tana cewa
"Likiciya rufa min asiri ina ni ina saka ƴan birni aiki likiciya?a'a wallahi ni jira ma nake ki ci abinci ki koma
barcin dan gajiyar hanyar kamar bata sake ki ba likiciya"ɗan darawa ta yi ta ce
"Ki kira ni da Bilkisu sunana kenan ba likiciya ba "shiru tayi kafin ta ce
"Toh ai ba zan iya kiran sunan ba ne tun jiya na san sunan amma ya min nauyin kira shi yasa nake kiran
ki da likiciya"da mamaki ta dakata da shafa man da take yi ta ce
"Me yasa ba zaki iya kiran sunana ba"?ta ce
"Sunan mahaifiya ta gare ki likiciya"ɗan darawa ta yi ita fah wannan sabuwar suna nata na bata dariya
"Kin san me"?ta ce a'a sai kin faɗa
"Ki kira ni da wani sunan ba likiciya ba"ɗan shiru ta yi tayi sukui alamun tunani kafin tace
"Ni kuwa jiya bokan turai ya faɗa mana ɗayar sunan ki amma da yake sunan dai kamar ta ƴan nasara ne
ban riƙe ba ni ko me ma ya ce sunan naki"??ta cigaba da nazari
Tsaf ta san da baby doctor ya yi introducing ɗin ta shi yasa suka kasa riƙe sunan wannan wace irin
wulaƙancin ne kuma shi bai neme ta ba hmm a haka ta shirya cikin atamfa wanda ya mata ɗas a jiki har
ya sa zulfa'u kasa ɓoye maganar ta tace
"Kaii amma kin yi kyau dama kuma kuna saka atamfa har haka likiciya"? Ohh matar nan ba zata kashe ta
da kayan dariya ba a iya zaman su daga jiya zuwa yau ta lura matar akwai son jan mutum a jiki kuma duk
tafi wayewa a cikin matan maybe dan itace amarya shi yasa
"Ai muma kamar kowa muke duk abin da kuke yi muna yin shi muma"sai ta saka dariya ta ce
"Kai amma na ji daɗi da ni duk kallon da nakewa ƴan birni basu da kirki kuma basu saka ire iren
kayayyakin mu ashe ba haka bane" daga haka ta kawo mata abinci cikin tray babba ga kunun fulani da ya
sha kindirmo ga sugar a ɗan ƙaramin kwano mai murfi ga alale mai rai da lafiya a food warmer ga
soyayyun kaji nan an masu pepper chicken sai ƙamshi suke yi ga plate nan da spoon haɗe da ruwan
wanke hannu komai dai MashaAllah
Zama tayi a dardumar da aka shimfiɗe mata ta zuzzuba ta fara ci tana kaɗa kai alamun girkin ya mata
daɗi ta ɗago ta ce
"Amma wa yayi girkin nan hala"?dariya ta yi ta ce
"Ni ce na yi ya miki daɗi"? Jijjiga kai tayi tace
"Ya min sosai gaskiya zaki koya min"daɗi ne ya kama ta tace
"Ai ko zan koya miki kala kala"rage murya tayi ta ce
"Kin san kuwa saboda iya girki na ta sa mai gidan mu ya fi so na?duk sauran tsohuwar hannu gare su
basu iya girkin zamani ba in kuma aka ce badu yarda ba su ƙi yarda"dariya maganar ya bata dan haka ta
dara ta ce
"Yayi kyau toh ai zaki koya min dai ni"ta ce sosai ma
"Yauwa toh bari in yi in gama"
"Toh likiciya"darawa tayi dan sunan dariya yake bata daga haka suka cigaba da hira kaɗan kaɗan har ta
gama lokacin har 2 ya wuce a nan ne kuma matan gidan suka rinƙa zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya
kowa na son samin shiga a wurin ta ita abin ma mamaki yake bata kishi muraran babu ɓoyo sai dai ayi ta
dariyar fatar baki
Bayan fitar su ta tafi wun mai gari suka gaggaisa ya mata ya hanya suka ɗan taɓa hira sai duddubawa
take dan ganin ta inda zai fito amma bata hange sa ba kuma babu wanda ya sanar da ita inda yake dan
haka bayan sun koma ciki suna tsaka da hirar su ita da zulfa'u aka shigo kiran ta wai ta zo su tafi
Ta zo su tafi ina kuma?ta ma kanta tambayar dan haka ta ce da zulfa'u tana zuwa ta fita
Ɗan duba shi tayi kafin ta hango shi cikin half jumfa da hula baƙaƙe kallon seconds ta mai kafin ta fara
takawa zuwa wurin shi ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta ce
"Gani"sai da ya ƙare mata kallon ƙuril har ta fara tsarguwa kafin ya ce
"Ba cewa nayi ki zo empty handed ba cewa nayi ki zo mu tafi hakan na nufin ki zo da kayanki mu tafi
ainihin masaukin mu"! Kallon shi ta yi ta ce
"Akwai wani masaukin da ya fi wannan ne"?ɗan jan aji yayi kafin ya ce
"Yeah cikin ƙauyen zamu tafi inda a nan zamu gabatar da outreach ɗin nan kawai somintaɓi ne ai kin
fahimta"? Ya wani sha mur wannan abin da mamaki yake cikin ƙauye kuma?jin kai irin nata ya sa bata
kuma mai tambaya ba ta juya ta koma cikin gidan cikin wani yanayi ganin haka ya sa zulfa'u tambayar ta
ko lafiya bata ɓoye mata komai ba ta sanar da ita ai kuwa ta ce bsta san da zancen ba babu inda zata tafi
da haka ta wuce zuwa wun mai garin bayan mintuna ta dawo ta ce da ita
"Ai an gama mai gari ya ce babu inda zaki tafi tunda kin ce nan ya miki kuma shima bokan turan ai nan
ya kamata ya zama masaukin sa ba chan da yake son ku tafi ba"wani sanyi ta ji at least ba zai kai ta
ƙauyen da ya fi wannan typical ba dan haka ta share zancen nasa ta cigaba da sabgogin ta har dare bata
kuma ji daga gare sa ba bata kuma damu ba.
A ƙaida ranar monday zasu fara gabatar da outreach ɗin wanda zai ɗauki steps uku ne a cikin sati ukun
da zasu yi,satin farko zasu binciko su zaƙulo matsalolin mutanin garin dan su yi creating rapport da
mutanin garin a sati na biyu kuma zasu gabatar da outreach ɗin sai satin ƙarshe kuma zasu ƙara koyar da
su abubuwa dangane da lafiyar su.
Bata sami network ba ma a ranar haka ta kwanta washegari da ya kasance litinin kuma ranar zasu fara
wanda zai yi taking place ne a wani primary school ɗin ƙauyen tun safe ta gama shiryawar ta ta zauna
zaman jiran sa ya zo su tafi bai aika a kirawo ta ba sai da ƙarfe tara na safe ya buga sannan ya aika a
korawo ta,sallama suka yi da ƴan gidan ta fita cikin shigar mutunci doguwar riga maroon da gyalen ta ta
yafa ta ɗau ƙaramar jaka inda ta saka wayar ta da pens ɗin ta tana jiran sa babu daɗewa aka aika kiran ta
har ƙofar gida zulfa'u ta rako ta suka yi sallama
"Goodmorning"tace da shi ya ji mamaki dan haka ya tsaya kallon ta kafin ya ce
"Morning"daga haka suka kama hanya babu uhm babu umumh haka suka cigaba da takawa har suka iso
inda zasu sami abin hawa suka shiga ya masu kwatancen inda zasu sauka ba wata doguwar tafiya suka yi
ba suka iso inda zaau sauka dama mai gari ya aika a sanar da su cewa ga bokayen turai nan tafe su haɗu
a inda suka saba haɗuwa dan haka a cike suka tarar da wurin.
A hankali suka taka zuwa gare su sai hayaniya ake ta yi dan ganin mace tare da tsohuwar fuskar da suka
saba gani murna sosai matan suka yi dan akwai matsaloli da dama da suke son a magance masu amma
rashin ƴar uwar su mace yasa ba su son sanar da Dr Zaid Maher gashi su ba wani ƙarfi ne da su ba bare
su rinƙa zuwa asibitin cikin gari wahala suke sha sosai dan sai sun yi dakon mazajen ke samin abin
masarufi matan kuma sune sai da kayan gida dangin su waran fulani, barkono, kindirmo da dai sauran su
dan haka kullum akan sana'ar abin da zasu rufawa kansu asiri suke dan haka cuta na cin su amma da ya
fara sai dai a yi na gida ya lafa da zarar ya tashi a kuma banka concoction a lafar da rashin lafiyar,ƴaƴan
su babu makarantar boko ba wai dan basu da burin saka ƴaƴan ba sai dan basu da hali toh mutanin da
lafiya ma bai gimshe su ba ina wani karatun boko ga matsalolin mata da ke ɗawainiya da matan yankin
amma babu wasu ƙwararru sai na gargajiya
Toh a wata tafiyar da Dr Zaid Maher yayi ne zuwa garin Adamawan ɗaurin auren wani abokin aikin su
wanda ya zaƙulo matar sa daga cikin garin dan ko da yake ba su labarin inda ya samo ta mamaki suka ji
ba kaɗan ba sai da ya masu bayanin kirki da dattako irin na ƴan garin wanda shi ɗin ganau ne ba jiyau ba
shi yasa ya ga match ɗin sa a nan she was just 16 years da ya aure ta ya ce da su zai saka ta a makaranta
a kan rainon shi zata taso wanda hakan ya ja ra'ayin Dr Zaid har ya yi takakkiya zuwa garin _koma_ a nan
ko ya shaida dan tun daga gidan mai gari ya ga kara da martabawa har dai ya ci karo da sanyin idaniyar
sa kamar yadda ya laƙaba mata dan haɗuwar su ta farko kare shi ta yi daga ƴan iskan gari da suka kawo
mai hari a hanyar sa ta komawa masaukin sa kasancewar ta budurwar mudan ɗan gayu sai suka rabu da
shi da ta ce masu tare suke kuma duk wanda yake cikin ƙauyen _koma_ ya san labarin ta da mudan
kuma kowa ya san mudan babu kirki dan akan budurwar sa yana iya shukawa mutum rashin mutunci
duk kusancin ku kuwa,
Tun daga lokacin ya tambayi gidan su ta mai kwatance har dai ya kai mata ziyara kafin ya bar garin
wanda sai da ya bar garin ya fara zargin kamar a kwai shaƙuwa mai girma a tsakanin su sai dai bai yi
concluding ba outreach ɗin shi huɗu a garin kuma ko wanne a gidan su ake masa masauki wanda hakan
ya kuma janyo kusanci tsakanin shi da sanyin idaniyar sa sai dai still bai sanar da ita abin da yake ji game
da ita ba though bai gama yarda ba kuma bai jin giyar son na fixgar sa ko me yasa ohon mai,toh a
wannan tafiyar ne ya yanke hukuncin gaya mata not knowing she have a man da take mugu mugun so
da ji da shi.
Toh ko a tafiyar da ya so su yi a daren jiya da baby doctor gidan su sanyin idaniyar sa ya so su tafi dan
hankalin shi ya fi kwabciya a chan amma kuma alfarma da mai gari ya nema a wun shi a daren jiyan ya sa
ya ji wani iri ya amince akan zasu zauna a nan but da sharaɗin zai rinƙa tafiya chan gefen da ya fi wayo.
ko da ya koma ɗakin sa ya fi dangana laifin da baby doctor ya yi fushin ita ce ta hana sa zuwa gidan da ya
saba zuwa but babu komai ita ta jiyo dan shi chan zai rinƙa wuni in ta gan ta zaume ita kaɗai ta yi bayani
ai,sai ka ce wani abin ya ke mata dama chan..
"Sannun ku da zuwa bokayen turai muna maku barka lale lalen ku"da murna suka masu sannu da zuwa
suma suka gaida su inda suka natsu dan jin da me suka zo
"Ni sunana Dr Bilkisu Muhammad kuma ni ce sabuwar fuskar da ta zo tare da likitan ku da kuka saba
zuwa ni maɗin likita ce zan mayar da hankali da kuma aiki na a fannin mata shi kuma zai yi fannin maza
da fatan zaku bada haɗin kai"?jin daɗin su ya kasa ɓoyuwa har sai da suka nuna dan kamar haske ne ya
bayyana a birnin rayuwar su ganin likita mace.
"InshaAllah likita zamu baki haɗin kanmu"first impression last long dan haka ta yi murnar haɗin kan da
suka bata dan haka ta kalle shi ta ce mai
"Ina ga mun yi creating rapport mai ƙarfi so we can commence"murmushin fatan baki ya mata ganin
jama'a sai ya ce
"Yes we can"
Daga haka suka fara shirye shiryen gabatar da abin da ya kawo su from no where suka ji an ce
"Wai farawa za'a yi ban da ni"? Juyawa suka yi daga shi har ita sai ta hango wata ƴar yarinya ƙarama dan
ba zata wuce 14years ba fara kyakyawa kamar am zana ta doguwa ƴar mai jiki da ita tana tafe tana
taunar chewing gum tana tafe kamar wacce bata san tsarin tafiya ba cikin rashin kunya da fitsara ta tako
har inda suke ta buɗe baki tana jujuya idanu
"Wai toh ba dan na zo ba shikenan babu wanda zai aika a kirawo ni"!? ta faɗa cikin izza kamar wata
sarki,gabaɗaya mutabin wurin shiru suka yi suna kallon ta dan in da sabo toh sun saba da halayar nata
na rashin girmama na gaba da ita gashi ba'a isa a mata faɗa ba da a mata faɗa gwara a yi shiru a zuba
mata idanu dan bata da kunya ko kaɗan
"Wacece ke kuma me yasa tun lokacin da aka zo ke ɗin baki zo ba alhalin tun jiya aka sanar daga fadar
mai gari"cewar Bilkisu cikin ɓacin rai dan babu sallama babu gaisuwa kawai fatam fatam faransa kamfani
ba oda
Instead ta bata amsa sai ta ja tsaƙi ta na cewa
"Hmm bokan turai ko?toh ki je ki tambaya a baki gamsashiyar labarin ko ni ɗin wacece hatta da
ƙaramin yaro ya san da labari na dan haka ni ban da lokacin baki labari na yauwa"daga haka ta juya tana
tattauna chewing gum ɗin ta tana sarrafa shi yana bada ƙarar ƙas ƙas ƙas..
Duk mamakin yarinyar ya gama cika baby doctor dan haka ta juya ga Dr Zaid dan tambayar ko ita ɗin
wacece tunda shine tsohon zuwa dole ya san ta
"Who is she"? Cikin ko in kula ya ce...........,,,,,,
*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim
#vote
#comment
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*5*
"Sunan ta Asma'u kuma ƴar nan yankin ce again bai kamata ki tsare ta kina mata ihu ba kawai dan ta zo
ƙarƙashin ki neman abu a gare ki ba"daga haka yayi shiru yarinyar ta kada baki ta ce
"Ɗan birni baka faɗa mata ɗayar sunan ba"sai ta juya ga Bilkisu ta kalle ta cikin fitsara ta ce
"Ma'ulle"inkiya ta kenan kuma bana ɗaukar raini ban ma san abin da ya sa na kyale ki kika gasa min
magana har haka ba ba tare da na nuna miki ko ni ɗin waye ba"ta juya kai tana rakaɗi
Tsyawa kallon ta tayi cike da alhinin wannan fitsararriyar yarinya marar tarbiya ta juya ta kalle shi ta ce
da shi
"What ever her name is ba business ɗi na bane dan bata gaba na iya abin da na sani ba zan ɗauki rashin
kunya daga wun ƴar ƙanƙanuwar yarinya ba kai da ka san ta sai ka nuna mata muhimmancin zuwa na
dan bata isa in zauna orienting ɗin ta ba"a zafafe ta karasa maganar wanda hakan ya bashi mamaki
dama ta na da masifa har haka?shi kam bai taɓa gani ba sai dai ji a hospital a ce ta masife su a asibitin
but shi bai taɓa witnessing ba
"Me ya sa ba zaki iya mata magana da kanki ba alhalin kin san ke ce da laifi"ƴar ƙaramar scoff tayi ta ce
"Are you for real"? Ɗage mata gira ɗaya yayi daga haka ta mai banza ta cigaba da abin da take da niyar
yi
"Ku yi haƙuri fah kun san a wuri dole mutum ya haɗu da masu tarbiya da marasa shi in kuma mutum ya
haɗu da marasa sanin ina ke masu ciwo dole ya daidaita su domin samin kyakyawar sakamako a wun aiki
ko ba haka bane"?cikon chorus suka amsa da
"Haka ne likita"ta yi murmushin gamsuwa ta ce da su
"Toh yanzu dai zamu fara abin da ya kamata saboda yanayi na gari tunda ruwa ake yi yanzu gashi akwai
ayyukan gida da za'a yi in an bar nan dan haka ba tare da ɓata lokaci ba zaku gaya min sunayen ku ne da
shekarun ku haka ma da ayyukan da kuke yi"murna suka yi sosai dan she tried as much as possible ta
wurin bringing kan ta so low wanda ya saka su jin kamar ta saka kan ta a shoe ɗin su ne dan haka babu
ɓata lokaci suka fara gabatar da kan su ɗaya bayan ɗaya yayin da ita kuma yarinyar mai suna Asma'u ta
haɗe rai tana ta faman kumbure kumbure yayin da shi kuma ya ke ta bata haƙuri,sam ta manta da su a
wurin ma kwata kwata sai da aka yi rabi da introduction ɗin ta fara duba shi,chan wani bakin bishiya ta
hango su zaune abin ya firgitata dan haka ta juya ga ɗaya daga cikin matan da suka yi introducing kan ta
ta ce mata
"Wai ni kuwa baba waccan yarinyar wacece ita"?ajiyar zuciya ta sauke ta ce cikin