Author : Siyama Ibraheem Category : African Stories & Novels
*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_
👄 °°° °°°👄
°°
°
*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀
_{the love saga}_
*#Hot love*
*#Romance*
*#allegation*
*#Epic*
*# Arrogance*
*#Pains*
*#Regrets*
*#Obscure and more*
*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
_This page is for u Faltex Farhana can't love u less dear_
_Bismillahir rahmanir rahim_
*1*
"One... two...three.. start"
"Again
"One...two...three.. place"!!!
"Goddamn it again"!
"One.. two.. three.. place"
"Take it easy baby"
Cikin hanzari Circulating nurse ɗin da ke tsaye tana ta zazzaro idanu outside sterile surgery field ɗin ta
buɗe baki tana cewa
"Breathing pattern diminishing"
Daɗa himma nurse anaesthetic ɗin ta yi tana ƙoƙarin reestablishing numfashin patient ɗin wanda ke
kwance kamar marar rai yayin da take iya ƙoƙarin ta sauran theater team ɗin na ƙoƙarin resuscitating
patient ɗin ta hanyar bayar da chest compression at a higher rate of 4:1 sai dai still patient ɗin didn't
pick up ƙara rikicewa suka yi a inda ɗaya daga cikin su ta juya ta ce
"Increase the speed to 220"gwalo idanu suka yi suna mamaki amma bata ko bi ta kan su ba ta ce a ƙara
instead a ƙara zuwa 220 da ta ce sai aka kai 190 wani irin wawan tsawa ta dakawa anaesthetic ɗin
"Are you out of the team will you increase the damn speed" muryar ta was a little bit pieced off da
alamun anger but atill hakan bai hana cool cracking voice ɗin ta bayyana ba tun kafin ta ɗora da wani
kalmar tuni anaesthetic ɗin ta ƙara spead ɗin har ya so ya wuce misali sai da aka mata alamar ta rage
yayi yawa jiki na kyarma ta rage tana sauke ajiyan zuciya wani na korar wani.
"One...two...three..place"ta manna electrode ɗin a bare chest ɗin patient ɗin ya zaburo ya koma a nan
heart beat ɗin ya fara motsawa yana regularizing wanda hakan ya nuna a jikin monitoring machine
device ɗin da ke theater suite ɗin,bata daddara ba haka ta cigaba da placimg electrical electrode ɗin nan
duk sauran team members ɗin sun sadaukar akan the patient is passing already dan haka a ganin su
wahal da kanta kawai take.
Ɗagowa tayi ta kalle su ta ga alamun lost a fuskokin su wani irin harara ta banko masu kamar zata
duddulo kwayan idanun waje dama ga su nan tubarkallah jiki na rawa suka fara gwaje gwaje yayin da
wasu ke gwada blood pressure wasu ke gwada temperature wasu ke auscultating ita kaɗai ke faman
resuscitating ɗin babu irin wanda bata yi ba CCM,Mouth to nose,air bag,ƙarshe mouth to mouth
resuscitation ta yanke hukuncin yi kallon ɗaya daga cikin team members ɗin tayi ta mai alamu da ido
wanda da gani assistant ɗin ta ne ya gane me take nufi ya so ja amma yanayin kallon da take mai ya sa
yayi saurin fiddo sterilized gauze ɗin da ke cikin galipot rufe da murfin shi yayi saurin yin amfani da
forceps ɗin da ke kan instrument table ɗin yayi amfani da ɗaya forceps ɗin ya warware ya yi place gauze
ɗin a daidai bakin patient ɗin yana gamawa ta ɗauke numfashin ta ta nufi daidai bakin patient ɗin bayan
ta sa an yi mata ƙasa da face mask ɗin da ta saka babu wata wata ta saita bakin ta akan na patient ɗin ta
sakar mai da numfashin da ta ƙumsa jan numfashi yayi ta kuma breathing in-out ta ɗauke numfashi ta
kuma saita bakin ta daidai na patient ɗin ta busa mai iskar bakin ta sai ga shi patient ɗin ya numfasa da
ƙarfi tuni sauran suka cigaba da aikin suturing da suke yi gudun kar a sami invasion of infection a cikin
incide cut ɗin haka ta cigaba da bada mouth-mouth resuscitation ɗin nan har sai da circulating nurse ɗin
ta ce
"Perfectly done"a sannan suka sauke ajiyar zuciya especially ita dan wata nannauyar ajiyar zuciya ta
sauke na samin nasara 5¼ hours ana abu ɗaya duk an fitar da ran samin nasara dan kuwa ba su taɓa yin
complicated surgery irin wannan ba first step approach ɗin was successful amma second approach ɗin
ya zo masu da inevitable complication wanda babu wanda zai ga patient ɗin ya ce zai rayu dan duk signs
of dying patient has been exhibited by the patient dama tun kafin a fara patient ɗin has gave up already
sai dai good rapport da ke tsakanin theater team ɗin da patient ɗin ya sa ya sami ƙwarin gwiwar cewa zai
fito da ran shi after surgery ɗin..
Akwai wani particular theater team member ɗin da tun da aka fara surgery ɗin yake tsaye ƙeƙam kamar
an dasa wani live statue ƙwaƙwaran juyin nan bai yi ba movements ɗin shi was restricted iya wall
mounted white latrine da ke haska ko ina a cikin surgical suite ɗin bai ƙara gaba ba haka bai koma baya
ba yayi folding hannayen shi cikin shigar complete surgery attire ɗin shi wato dark green surgical gown
da hular shi iri ɗaya hannun shi cikin elbow surgical glove ƙafar shi sanye da surgical suite flexible booth
wanda ya rufe mai ƙafar shi tun daga tafukan ƙafar sa har zuwa dab da gwiwar sa yayin da sauran
theater team ɗin suka saka boot ɗin yakai masu har gwiwa shi a iya gwiwar ta tsaya mai dan tsananin
tsayin shi fuskar shi ɗauke da operating google ya haɗe fuskar nan tamau kamar wani wanda bai san
abin da ake kira da murmushin fuska ba duk waɗannan tashi faɗin da ta rinƙa yi yana kallon ta cikin
tsananin izza da dakiyar zuciya ƙala bai ce da su ba har suka kammala suturing ɗin suka yi cleaning
patient ɗin aka gwada temperature,pulse,respiration da blood pressure ɗin shi sannan aka saka shi a
wheel table couch aka yi wheeling ɗin shi zuwa post operative room.
Scrub nurse ce ta ƙarasa gyara wurin surgery ɗin yayin da circulating nurse ta shigo ta fara praising ɗin
su sun amsa mata except surgeon ɗin da ta mata banza ta wuce zuwa tap ɗin surgery room ɗin ta fara
cire elbow hand glove ɗin ganin haka ya sa ta yi shiru ta ƙarasa zuwa cikin part ɗin surgeon preparation
room ɗin ta yi saurin unbuttoning mata surgical gown ɗin tana yi tana son mata sannu amma ganin babu
fuska ya sa ta mazge ta ja bakin ta tayi gumm but dole ne ma ta mata sannun nan dan duk sauran
doctors ɗin sun cire hannun su a case ɗin except su theater team ɗin da suka yi performing recent
surgery ɗin cikin izza ta goge hannun ta ta cire face mask ɗin,ya salam wata kyakyawar slim innocent
creature ta bayyana wacce fuskarta ya kasance doguwa dai dai ƙima ɗauke da dara daran idanuwa masu
ɗauke da breathtaking light blue eyeballs yayin da fararen eye sclera ɗin ta suka zagaye attracting
eyeballs ɗin ta making them to appear so angelic and uniquely perfect hancin nan karan shi tun daga
marabar frontal bone ɗin ta har zuwa gab da upper lip ɗin ta inda a nan ya dakata bakin nan daidai
fuskar ta so cute ɗauke yake da lip bam marar shining daga fuskar ta kawai mutum zai gane cewa ilahirin
jikin ta haske ne tass dan kuwa fuskar nan babu taɓo ko kaɗan ga alamun hutu nan da ya bayyana a
fuskar dan the face is looking so smooth and rough free babu spot ko ɗaya kamar a taɓa jini ya fito ko da
ta cire hular kanta dan saka ƙaramar headwear da ke gefen ta well parked neatly appeared dark curly
hair ne ya bayyana wanda shi bai kasance a cike ba daidai dai bai yi kaɗan da yawa ba haka bai yi kaɗan
ba parking ɗin an bi shi ne da pony style wanda ya sauko har gefen kafaɗar ta baƙi ƙirin ne babu abin
kushewa ko da aka gama cire mata gown ɗin ma glowing skin ɗin ta ne ya bayyana mai ɗaukar ido da
hankalin mai kallo,scrub wear ne a jikin ta navy blue riga da wando ta cire surgery boot ɗin ko da ta cire
surgical boot ɗin sai ta fito doguwar ta samɓal very slim kamar wacce bata cin abinci dan ba wani jiki ne
da ita ba sai tsayi da doguwar fuska mai ɗaukar hankali,saka flat surgery shoe tayi wanda yayi covering
mata ƙafar ta gabaɗaya da ganin ta ka ga mace marar damuwa a rayuwar ta, ta fito tana ɗaɗaure fuska
babu wasa ko kaɗan a fuskar ta ta fito tana mai cewa
"Let's meet at the conference room in the next 15minutes"daga haka ta cigaba da tafiya bata kuma
furta komai ba takun ta biyar a na shida da zai sada ta da transparent tinted glass full operating room
door ɗin ta ji saukar muryar shi a kunnen ta cikin gadara da nuna isa na shi ɗin wani ne ya ce mata
"You are a loser and you will always be a loser ki rubuta ki ajiye"za ka rantse ba magana ya gaya mata ba
dan duk ƙwazbar ka ƙarya ne ka ce ka ji sautin muryar sa bare ka ce ga abin da ya gaya mata dan he
made his voice to be as lower as anything ta yadda daga ita sai shi zasu iya jin maganar.
Kallon tsana ta aika mai da shi ta harare shi harara irin na takaici kamar idanun zasu faɗo ƙasa ta buga
tsaki ta tura ƙofar ta fita kamar zata tashi sama dan haushi..
Bayan fitar ta daga theater suit ɗin sauran team members ɗin suka fara shiga taitayin su dan sun san yau
sun takalo fitinar baby doctor haka suka rinƙa undressing theater wear ɗin suka wanke hannayen su
suka fito a nan suke lura da shi shaf sun sha'afa yana ciki dama chan basu da wata kyakyawar jituwa
tsakanin shi da baby doctor a duk ranar da aka ce ita ke da surgery toh fa zai zo amma stitches wannan
ba zai taya ta da shi ba haka ita ma in dai shine on call kuma yana da surgery toh zata halarci wurin sai
dai kuma babu ruwan ta da shi sai dai su rinƙa muzurai wanda shi kuma wawan doctor da ke son ta ya
tsani ya ga suna kallon juna a yanzu ma hakan ta kasance dan bayan an gama za'a fita daga theater room
ɗin ya dakata yana kallon shi ya ce
"Ɗazu me kake gayawa baby na na ga ran ta a ɓace ta bar wurin nan"? Cikin fushi yayi maganar yayin da
shi kuma ya mai kallon tsanake kafin ya ce da shi
"Well doc,ka ga shiga hurumin da ba naka ba bai dace da kai ba a matsayin ka na wanda yayi rayuwar
turai i guess it will be safe for you if you learn how to mind your business in you little world"kaiwa nan
ya bar wall ɗin ya shiga cire kayan jikin sa shikuma kamar yayi hauka dan takaici ya tsani ya ga ana raina
ma babyn shi ɗazu a wun surgery ɗin nan duk ganin ƙoƙari da himmar da take yi yasa shima ya sami
ƙwarin gwiwa amma da fari ya yi losing hope gabaki ɗaya.
Juyawa yayi ya kalle shi kafin ya ce
"Kuma ka dai ji abin da ta ce mu haɗu a conference room"banza ya mai dan shi fa ya tsani takura kwata
kwata a rayuwar sa dan haka amsa ɗaya ya bashi wanda ya san duk daƙiƙancin sa dole ya rabu da shi
"Wasu dai haka suke daƙiƙai ana ƙin su suna nacewa"daga haka ya sa kai ya fice
Kenan shi ne daƙiƙin wato shi ke ɗawainiya da son baby doctor amma ita bata damu da shi b?toh ai
babu komai ko da zagin shi zata na yi ba laifi bane duk a cikin soyayya ne moreover yadda yake ganin
doctor ZM ke da shegen siffar ɗaukar hankalin nan ya sa shima ya fara zuwa gym duk dan ya buɗe ya
haɗa abs ɗin karfi da yaji koh zai kai kamar shi dan a tunanin shi ta hakan kaɗai zai iya ɗauke hankalin
baby doctor ɗin shi alhalin ya san ba ta kanshi take ba amma shegen kishin tsiya ya sa yake son haɗa kan
shi da doctor ZM thinking that he can beat him after all shima ai ɗan masu kuɗi ne in ma kyau ne toh
dakaɗan doctor ZM ɗin ya fishi amma shi ya ma fushi hasken fata kyau kaɗai zai nuna mai da well
developed body structure ɗin da yake da shi da ɗan banzan muscles kamar basamude dan shi haka yake
kiran shi da basamude he just hate him so much kawai bai da yadda zai yi da shi ne da ya sa an nesanta
su da baby doctor ɗin sa..
Bayan kamar mintuna 15 suka hallara a conference room ɗin gaba ɗayan theater team ɗin.
Juyawa tayi ta kalli ko ina bata gan shi ba dama ta san ba zuwa zai yi ba dan haka ta fara zazzaga masu
kwandon bala'i ta inda take shiga ba ta nan take fita ba sannan ta hana su furta kalma ko ɗaya lallai sun
janyowa kan su ruwan dafa kansu da kansu dan masifar yau tafi ta kullum gata nan dai ƴar tsirit babu
wani jikin da mutum zai gani ya ce zai tsorata amma fuskar nan da ke ɗaure tamau a kulliyaumi ya sa dan
dole a rankwafa a daraja ta dan bata son raini duk wata mu'ammala ta mutunci concerning her work
tana kiyaye shi bata shiga sabgar da ba tata ba haka itama ta tsani a shiga sabgar ta in ba ita ta gayyace
ka ba shi yasa ba su jituwa da doctor ZM saboda kowa na da principles da policy kamar sarkin kansa da
suna da hali ma da sun saka an raba masu wun aikin saidai iyayen su sun hana dan haka a dole kawai
suke aiki tare ba dan ransu na son hakan ba.
"Baby ga ruwa ki sha na ga ran ki ya ɓaci da yawa"ya miƙa mata glass tumbler wani irin kallon
wulaƙancin da ta aika mai da shi haɗe da buga tsaƙi ya sa sauran durƙusar da kawunan su suna mai
dariya ƙasa ƙasa dama sun san za'a yi haka on normal basis ma da ba'a taɓa baby doctor ba ya aka ƙare
bare yau da aka taɓo ta shi kan sa rashin kamun kai ke damin sa if not ya dage dole sai ta saurare shi ita
kuwa yadda take ji da izza da kan ta bata da lokacin sauraron samari duk wani kyau da izzan ka baka kai
matsayin ta sakaya maka saboda waɗannan qualities ɗin ba,sau nawa sauran male doctors ke kawo
mata gayyatar son su amma tsagaben yarfata su da take yi kamar ba mutani masu ƙima ba yasa kowa ya
ja girman shi ya fita harkar ta duk wata mu'ammala da zai shiga tsakanin su baya wuce na aikin subayan
wannan babu ruwan su.shi shi kaɗai ya nace dan haka shi ɗin ne ya zama garbage bin ɗin ta madaɗin ya
kiyaye ta sai ya ƙi ya amince da karbar duk wata wulaƙancin da ta ke mai shi yasa a duk sanda ta mai
hakan mutani kan mai dariyar wautar sa saidai shi ko a jikin sa dan shi bai ganin laifin baby doctor ɗin
shi.
"Me kuke ma dariya"?ya faɗa yana zazzaro masu idanu kamar wani damisa,dan haka suka yi shiru suna
mai danne dariyar su amma da sun sami sarari lallai zasu sheƙe da dariyar shiriritar sa.
Kallon shi tayi cikin jin haushin shashancin sa ta ce
"Daga yau sai yau in ka kuma kira na da sunan baby a yayin da ake abu mai muhimmanci duk abin da na
maka kai ka ja wa kanka wawa kawai"ta zabga mai tsaki instead yayi fushi sai ya bige da murmushi yana
washe baki
"Yes baby"wani hararar ta zabga mai sai yayi saurin rufe bakin shi ya ce
"Sorry baby doctor na daina"a nan ta mai kallon wofi ta cigaba da masifar tana ƙin haɗa kan da aka yi a
theater suit har da alƙawarin dakatar da su zuwa ranar da suka koyi rashin yin panicking a middle of
surgery haƙuri sosai aka shiga ba ta ta ƙyale su kwatsam sai suka ji buɗewar ƙofar conference room ɗin
gabaɗaya juyawa suka yi dan ganin wanene ya shigo a makare sai dai ganin wanda ya shigon ya sa suka
miƙe baki ɗayan su suna gaida shi cikin girmamawa da gani dai shi ɗin babba ne wanda ya cancanci ban
girman da aka mai,murmushi ne fal fuskar shi ya ce da su su zauna suka zazzauna.
A kiyasti dai mutumin ba zai wuce 60years ba fari ne da shi tass kasancewar sa tsoho wanda shekaru
suka fara ɗan ja masa bai nuna a jikin sa ba dan jin daɗi da hutu sun runfe hakan sai ma wani yarinta da
ke nunawa a jikin nasa dan in aka gan sa za'a yi tsammanin ɗan kimanin shekara 49-50 ne sam 60years
ɗin bai yi fitting ɗin shi ba in ba wai faɗa yayi ba to a ɗan 50years za'a na kallon shi,kyakyawan dattijo ne
wanda ya kasance cikakken dan boko da sanin ilimin zamantakewar ɗan adam dogo ne shi sosai kuma
tsufar shi da tsayin shi basu saka shi rakwafawa ko kaɗan ba yana nan a tsaye cur abin shi idan mutum
ya kalle shi ya kuma kalli baby doctor ɗin nan toh babu tantama koh second thought za'a iya concluding
cewa jini guda ke running through vein ɗin su dan kamannin ya ɓaci da yawa kama ce ta sosai wanda
za'a ce wannan mahaifi ne ita kuma ɗiya ce bambancin ɗaya ne shi fuskar shi da rahama ita kuma masifa
ce fal a kan fuskar ta.
Bayan ya zauna ta gaida shi
"Good day dad"amsa mata yayi da murmushi dan ya ji rahoton scene ɗin da ya gudana a surgical suit
kuma ya san mai kwatar surgical team a hannun ta yau sai ikon lillahi ko kuma shi shi yasa yayi takakkiya
ya zo har conference room ɗin
"Baby doctor me aka miki ne yau na ji muryar ki har waje da fatan dai ba failure aka samu a process of
surgery ɗin ba"?wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin calming kan ta dan ta san duk
bambamin ta she can't include her father in it sai dai ta sauke shi akan su.
"Dad talk to them because am tired of warning them to stop panicking whenever a surgery is going on
amma yau ɗin nan sun wuce limit ɗin sa dan haka duk hukuncin da na masu no one among them should
question my act"kaiewa nan ta zauna tana sauke numfashi.
Murmushi yayi irin na manya kafin ya kalle su cikin sakin fuska ya ce da su
"And me kuke cewa a duk lokacin da kuka yiwa boss ɗin ku laifi"? Cikin chorus suka