Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
daga idanun jawahir tasa hannu tagoge sannan tacigaba da cewa
Saida Muhammad yadinga lalla'ba mahaifiyarsu sannan ta amince yaje chan Kaduna yayi masters d'inshi duka kud'in gadonshi ya amsa yayi amfani da su wajen karatunshi da taimakon Mahaifin wani abokinshi Salmanu da yake kaduna yasamu yagama masters d'inshi dan yana tausaya mashi sosai musamman yadda yaga yana fafucikar neman yan kud'in da yake karatun da su, da dad'i ba dad'i ahaka yagama masters d'inshi.
Bayan ya gama ne Mahaifin Salmanu yasamo masu aiki tare d'an shi a wani company da yake cikin garin Kaduna.
Murna ba a magana wajen Muhammad da mahaifiyarshi shiko Mu'azu haushi yadinga ji yana cewa ina ma amfanin irin wannan aikin ai haram kawai za'aci da zuwa yayi yakama Sana'a ita zata fisheshi shidai Muhammad bai ta6a kulashi ba.
Dakyar yasamu inna Ramatu ta amince yafara aiki a nan kaduna gidansu abokin nashi yazauna kasancewar baida amini kamarshi, albashinshi nafarko Inna Ramatu da dan uwanshi ya aiko mawa nan sukaita sa mashi albarka.
Intak'aice maka acikin shekara biyu Muhammad ya tara kud'i sosai a lokacin ne Inna Ramatu tabud'e mashi wuta akan yadawo katsina yabar kaduna shima hakan duk hadda zigin yayanshi Mu'azu dan haka yasanar ma baban nashi halin da ake ciki dayake mutum ne mai kirki nan yace kar yadamu zai nema mashi transfer yakoma katsina da aiki.
Haka ko akayi yakoma cikin garin katsina ba dan ta soba tahak'ura tace ai k'ara nan ya d'anfi kusa akan kaduna nan kuma suka tisoshi a gaba akan maganar aure nan yaimata alk'awalin insha Allahu zaiyi ammah sai ya fara gini nan ta amince da hakan, kud'in da yake samu na albashinshi biyu yake rabawa ya aika masu da rabi shikuma yayi amfani da rabi dayake mutum ne me gaskiya baifi shekara ba aka k'ara mashi matsayi a wajen aikin,
Gini babba yafara yi batare da sanin mahaifiyarshi ba cikin wata shidda yagina dank'areren gidanshi a cikin garin katsina sai bayan ya yi ginin ne yad'auko su sukazo suka gani daga nan yafara shirye shiryen aure yasamu wata bafullatana yar cikin kebbi ya aura shima lokacin sunje wani workshop ne a chan garin suka had'u da Khausar har sukayi aure bikkin da akayi shagali sosai Inna Ramatu tana son khausar sosai dan babu ruwanta ga hak'uri, shekararsu d'aya da aure yamaido su Inna Ramatu da Baba Mu'azu a gidanshi part yafitar masu da shi yace ya fi son suzauna kusa da shi lokacin Baba Mu'azu yaranshi biyu Umar shine babba sai Aliyu.
Khausar sosai take girmama mahaifiyar mijin nata da d'an uwanshi hatta matarshi khausar tana girmamata sosai, ganin haka yasa Fatima tadinga d'aukar kanta watace dan wata rana ita take bada umurnin d'in abinda za'ayi a gidan.
Muhammad ganin tunda yayanshi yadawo gidan bai aikin komai sai zaman gida duk sai yaji ba dad'i yabarshi ahaka koda dama shi yad'auke mashi nauyin komai wata rana Shima Mu'azu yaje yasamu k'anen nashi yace shi fa ya gaji da zaman gida taya zai dinga zama babu aiki kamar mace.
Jin haka yasa Muhammad yace kayi hak'uri yaya nima k'ok'arin sama maka nake dan nima banjin dad'in ganinka haka.
Mu'azu yace a'a toh hakan dai yakamata.
A cikin yan kwanakin Muhammad yabud'e mashi babban shago na kaya a kasuwa yazuba mashi komai yabashi ammah wannan abun da yayi mashi maimakon yagode sai ma yaraina yaje yasamu inna Ramatu yafad'a mata yace wai a matsayinshi na yayanshi maimakon yasama mashi aiki a company da yake aiki shine yabud'e mashi shago shi ga sarkin kasuwanci ko.
baki tarik'e tace anya kuwa Mu'azu kana da hankali yanzu duk k'ok'arin da bawan Allahn nan yakeyi akanmu baka gani kaduba fa kaga d'anka ya sakashi makaranta shi yake d'aukar nauyin karatunshi mu kanmu babu abinda muke nema murasa a gidan nan daga shi har matarshi a tsaye suke a kanmu.
Hakan baiyi ma Mu'azu dad'iba ammah babu yadda ya iya tunda mahaifiyarsu bata goyi bayanshi ba saidai yaje wajen matarshi sudinga kitstsima gulmarsu shi da ita.
_Free Page_
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/13, 20:23] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......*
_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_
*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]
*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*
_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Free Page_
*PAGE ELEVEN*
Muhammad dayake ba zaunanne bane yau baya wannan gari gobe baya wanchan gari dan haka gida yadawo kamar hannun yayanshi Mu'azu sai yadda yace hatta Khausar ita da yake gidan mijinta sai yadda akayi da ita, duk da haka bata ta'ba bud'e baki tafad'a ma mijinta ba, itadai burinta suyi zaman lafiya saboda k'arfin hali irin na Fatima habaici tadinga yada mata wai juya saidai aci ayi kashi ba haihuwa dan lokacin Khausar Shekararsu ukku da aure saidai tashige d'aki tasha kukanta tagode ma Allah.
Saida suka shekara hud'u da aure sannan Allah yabata ciki kar kuso kuga murna wajen Muhammad da mahaifiyarshi shiko Mu'azu bak'in ciki yacikashi dan baiso Khausar tasamu cikiba ya so ace shi zai gaje dukiyar d'an uwanshi, Fatima ma a fili tadinga nuna bak'in cikinta itadai khausar bata taba kulataba.
Cikin khausar na shiga wata tara tahaifi zangadediyar d'iyarta mai kama da mahaifinta sak, Muhammad kasa tsaye da zaune yayi yadinga fitar da kud'i yana siyayya abinda zai baka mamaki koda akayi haihuwar d'an uwan nashi baiyi mashi barka ba bai ma zo inda diyartake ba dan haka yad'auka dakanshi yakaimashi har part d'inshi sannan ya amshi d'iyar yakalla yamik'a mashi.
Ranar suna yarinya taci suna jawahir, Muhammad ba k'ananun kud'i yakashe ba dan kud'i sunyi kuka sosai, hakan ma ya k'ara b'ata ma Mu'azu rai har yaje yasamu k'anen nashi yai mashi magana dan mi zai dinga 'barnar kud'i haka wannan ai almubazzaranci ne, murmushi Muhammad yayi yace insha Allahu yaya zan kiyaye.
Tunda aka haifeni Umar shine me k'ok'arin zuwa yad'aukar ma Ummana ni dan tunda yak'yalka ido yaganni nashiga ranshi musamman ma tun barka da mutane suka dinga cewa ina Kama da shi kuma hakane muna yanayi sosai.
Son duniya iyayena suka d'auka suka d'aura min hatta kakata kullum sai tasa ankawo mata ni ta ganni.
Abun yana ma Mu'azu da matarshi ciwo sosai har wani lokacin yakasa boye bak'in cikinshi yaje yasamu inna Ramatu yace wai dan Muhammad yana da kud'i saisa tafi son d'iyarshi akan ya'yanshi, inna Ramatu nan zata dinga yin fad'a tace ita duka natane kar yasake irin wad'annan maganganun, dan haka saidai suyita kulle kullenshi shi da matarshi.
Lokacin da nacika shekara d'aya a duniya Abba yabiya mana umara da ni da ummana sai Inna Ramatu sannan shi mukaje a tare, yace shikuma yayanshi sai wata tafiyar sannan yaje da iyalanshi Wayyooo kar kuso kuga bak'in ciki a wajen Mu'azu dan har gaba yayi da Abbu har suka dawo daga umara yana fushi da shi duk tulin tsarabar da yayi mashi ammah hakan baisa yasafko ba saida yabiya mashi shi da matarshi sukaje sannan hankalinshi yakwanta.
Haka rayuwar gidan mu tacigaba da tafiya da dad'i ba dad'i dan shima Abbu ko bai fad'aba kasan baya jin dad'in zama da d'an uwan nashi hak'uri kawai yake da shi.
Ina da shekara biyar aka sani school lokacin Yaya Umar yana SS1 inda Yaya Aliyu kuma yana JSS2 dan dama sun girme min dan ko yaya Aliyu ya bani kusan shekaru takwas.
Gatan duniyar nan babu irin wanda ban samu wajen iyayena da kakata itako Matar Abba Mu'azu tsakanina da ita saidai hantara saboda hakane ma ban cika zuwa inda takeba daman Yaya Umar ne me d'an kulani dayake shi ba Maison hayaniya bane sosai saisa bai cika shiga shirmenaba yaya Aliyu ko kad'an kad'an ya mangareni ko yadukeni inkoma inta ma iyayena kuka saidai suyita lallashi.
Ina da shekara goma Allah yayi ma Inna Ramatu rasuwa munyi kukan rashi sosai dan tsohuwar nan ta yi yaya Umar har da suma dan duk ya fimu sabawa da ita saboda rabin rayuwarshi a wajenta yakeyinta.
Bayan rasuwarta Abba Mu'azu kullum baida aiki sai kar'bar kud'i wajen Abbu kuma baida ikon yace babu nan zai fara fad'a har sai ya bashi.
Lokacin da Yaya Umar yagama secondary school d'inshi Abbu admission yasamo mashi a chan Egypt yafita karatu.
Nayi kuka sosai da tafiyarshi dan dama dashi ne nake shiri Dan shi Yaya Aliyu tsakanina da shi sai hantara dan zan iya cewa shine yakwaso halin iyayenshi.
Arzik'i Abbu akowane lokaci k'ara bunk'asa yake dan haka ne ma yabud'e companynshi yazuba ma'aikata suna kular mashi da shi abun ya yi ma Abba Mu'azu ciwo dan shi yaso ace ya sa yakula da companyn ba wasuba.
Ana ahaka har nashiga jss 1 lokacin su Ummi da Abbu suka koma aikin hajji suka barni wajen Ummah Fatima na sha wahala sosai dan komawa nayi kamar baiwarta, hatta idan zanyi bacci saidai inkwanta k'asa duk sanyin tiles d'innan dan cewa take bana hawan mata gado, ga tsangwamar Yaya Aliyu da nakesha wani lokacin inta ji ina ma ace shine aka fitar dashi waje yayi karatu ba yaya Umar ba ammah shi a nan Abbu yabarshi yace shi yayi karatun a cikin garinsu dan baiso duk sukwashe abar gidan bakowa hakan baiyi mashi dad'iba dan ya K'wallaci Abbu sosai a ranshi akan hakan.
Wahalar da nasha a hannun bayin Allahn nan bata fad'uwa dan wata rana ko makaranta ban samun zuwa dukan da nake sha ko ba'a magana dan duk rana sai nasha dukan Umma Fatima, yadda kasan d'iyar almajira haka nakoma duk gatana ammah suka barni bana samun ko wanki.
sai daren da su Ammi zasu dawo sannan tasa aka wanke min kayana tas kuma tabarni nakwanta saman gadonta.
Koda su Ammi suka dawo sun lura da canzawar da nayi ammah basu nunaba nan suka cikasu da tsaraba babu kunya suka amshe, nice ma nake fad'a ma Ammi irin abinda aka dinga yi min saidai tace ai laifinane tasan bana jin magana koda a cikin zuciyarta ba hakaba ko kad'an bataji dad'iba kawai bata nuna bane.
Bayan shekara d'aya ranar wata laraba Abbu ya dawo daga wata tafiya da yayi a chan Dubai suna zaune a setting room d'inshi shi da Ammi suna hira nan Abba Mu'azu yashigo Indai ka ga yazo wajen Abbu Toh akwai abinda yake nema wajenshi waje yasamu yazauna nan suka gaisa, bayan sun gaisa yanemi kud'i wajen Abbu nan Abbu yaje yad'auko yabashi batare da ya musaba har ya mik'e zai tafi Abbu yace yauwa Yaya daman inaso muyi wata magana da kai.
Komawa yayi yazauna yace ina saurarenka, Ammi har ta mik'e zata basu waje Abbu yace tazauna nan takoma tazauna wasu files ne guda biyu yad'auko yace daman akan maganar gidana na goruba road da aka kammala ginawa ne.
Abba Mu'azu yana jin haka yawashe baki yace toh toh nagane wannan babban gidan mekyau kenan.
Murmushi Abbu yayi yace Eh shine nakeso kashaida na mallaka ma Khausar shi daman ita nagina mawa.
Lokaci guda fuskar Abba Mu'azu tacanza zuwa wani irin yanayi Abbu cigaba yayi da cewa sai wannan filin nawa na mallaka ma Jawahir hatta companyna komai naciki na maida da sunanta,,saurin Katseshi Abba Mu'azu yayi yace wannan wane irin zancen banza ne kakeyi watau Khausar ta shanyeka ko?
Cike da mamaki yake kallon yayannashi yace Subhanallahi yaya wannan wace irin magana ce haka kakeyi?
Cikin 6acin rai yace Eh d'in na fad'a wannan munafukar matar shanyeka tayi inba hakaba taya zaka d'auki wannan makeken gidan kamallaka mata dan gulma kamaida sunan companynka yazama na 'yar k'aramar yarinyar chan, watau ni da Ya'yana kake bak'in cikin mumoreka ko, toh ko kak'i ko kaso mune dai naka dan bamu canzuwa ammah mata ko ana canzata.
Subhanallahi Yaya wannan wace irin magana ce kakeyi?
Ammi cikin sanyin jiki tace kayi hak'uri yaya shima dawasa yakeyi maka ba gaske bane.
Wane irin kallo Abba yayi mata yace au ni kika maida yaronki da zakice wasa yakeyi min? Ke rabani da wannan munafuncin naki duk abinda kike k'ullawa minene ban saniba.
Ammi shuru tayi tare da sunkuyar da kanta k'asa tana jin ba dad'i a ranta.
Abbu da yaga abun yayan nashi ba me k'arewa bane yace yaya ammah ai hakan da nayi ba laifi bane dan na kyautata ma iyalina.
Eh ba wani abun bane Ammah wallahi bazan iya bari kamallaka mata gidan nan ba.
Kasan me hak'uri bai iya b'acin rai ba nan ran Abbu ya'baci yace saidai hak'uri yaya dan na riga da na mallaka mata ni duk abinda zanyi nafiso inyi adalci a rayuwata bakin gwalgwado kaima ina kyautata maka da iyalinka banta'ba bari kuka nemi wani abu kuka rasaba duk abinda kakeso inayi maka kuma wannan baiwar Allah bata ta'ba tankawaba toh akanme zakaji zafinta.
Jinjina kai Abba Mu'azu yayi yace Eh dole kayi min gori banga laifinkaba watau dan kana bani shine yau zakayi min gori saboda matarka shikenan nagode nima Allah yahore min kaga idan zan k'ara kallon abun hannunka yana fad'in haka yajuya yawuce yafita cikin fushi.
Ammi cike da damuwa tace Alhaji meyasa kayi haka d'an uwanka nefa ai da ka barshi ni na yafe ba sai ka bani gidan ba.
Abbu girgiza kai yayi yace ra'ayi nane Khausar kuma ba laifi bane dan na baki tunda ke matatace sannan ke shedace bakin gwalgwado ina k'ok'arin kyautata ma bawan Allahn nan ammah baya gani nidai Allah ya sani ina bakin k'ok'arina sannan idan nafasa baki gidan banyi ma kaina da ke kanki adalci ba sannan tun lokacin da aka fara ginin companyna daman dasunan na d'iyata ne, kibari kawai zai safko.
Ammi cikin sanyin jiki tace to shikenan Alhaji nagode sosai Allah ubangiji yasaka da alkhairi yak'ara bud'i.
Abbu ya amsa da Ameen.
Ummah Fatima tana tsakar gida Abba yashigo part d'insu cikin b'acin rai yawuce yanufi room d'inshi saurin binshi tayi taje tasameshi a tsaye yana zagaye d'akin tsayawa itama tayi tace Alhaji Lafiya?
Cize le6e yayi yace Fatima ina fa lafiya yau ni Muhammad yaci ma mutunci akan matarshi.
Da mamaki take kallonshi tace wane irin cin mutunci muhammad d'in dakanshi?
Hmm kedai bari,,,nan yakwashe duk yadda sukayi yafad'a mata.
Salallami tafara yi tace yanzu shi Ahmad zai fifita matarshi akanka bayan kai d'an uwanshine kuma dan cin fuska a gaban idanunka yace ya mallaka mata wannan dank'areren gidan wai company ya ba d'iyarshi watau mu haka yakeso mudauwaba mu da bakomai nashiba.
K'wafa Mu'azu yayi yace kibarni da shi nasan abinda zanyi dan dama baisan ya kaini wuya ba tuni.
Ai wallahi Alhaji k'ara kad'auki mataki tun kan yarabe masu dukiyarshi muna nan zaune.
"ai wannan dole ne ind'auka dan wallahi bazan ta6a bari yarabe masuba ni yabarni nan baki a sake ina hamma,,,yana fad'in haka yawuce yafita.
Abbu bayan angama wannan fita yayi yaje yasamu lauya d'inshi yafad'a mashi komai yabashi copy d'aya daga cikin takardun inda yaje yasamu abokanshi biyu yadamk'a masu copy d'aid'aya dan suzama shaida ya mallaka ma matarshi gidan da yagina sai companynshi ya mallaka ma d'iyarshi.
Da dare suna shirin bacci Ammi cike da damuwa tace Alhaji dan Allah kataimaka kasasanta tsakaninka da d'an uwanka kar hakan ya'bata maku zumunci.
Murmushi yayi yace kar kidamu babu abinda zai ta6a zumuncinmu yanzu haka akwai wani gida da nikeso insiya inmallaka mashi kinga shikenan haka ya yi ko?
Murmushi Ammi tayi tace Eh Alhaji yayi Allah yasaka da alkhairi.
Intak'aice maka tun daga wannan ranar Abba Mu'azu bai sake yi ma d'an uwanshi magana ba koda shi ya yi mashi shiko d'auke kai yake baima Amsawa ahaka har sukaci wata d'aya.
Wata ranar lahadi Abbu yaje yasamu abba Mu'azu yaso suzauna sutattauna akan fushin da yake da shi ammah yak'i yace Indai har yanaso suzauna toh dole sai ya janye kyautar da yayi ma matarshi da d'iyarshi shikuma Abbu yace gaskiya bazai iyaba shima akwai wani gida da yasa aka gyara suje yagani zai mallaka mashi shi.
Abba yace baisan da wannan ba dan yasan bazai kai na Ammi kyauba saidai ayi musanya yabata nashi shi kuma yabashi nata.
Abba yace gaskiya bazai iyaba.
Abun ya yi ma Abba Mu'azu ciwo sosai.
A daren ranar Abbu duk damuwa tadameshi har sun kwanta bacci yafad'a ma Ammi abinda yake faruwa tace dan Allah yabashi gidan Indai har hakan zaisa asamu zaman lafiya, Abbu yace toh shikenan bari sai zuwa safe sai muga yadda za'ayi.
Ashe Abbu nah bazai kai safen ba cikin dare suna bacci wasu Katti ukku suka shigo cikin gidan babu wanda yasan shigowarsu wajen k'arfe biyun dare sai ji su Abbu sukayi ana