Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   28 / 74

81K to 84K   out of 220.3K words

sunan wanda ake cigiyane yasa tayi saurin d'ago kai tamaida kallonta ga TV gabanta wani irin mummanan fad'uwa yayi tace na shiga ukku Daddy Mummy kuduba min wallahi Faruk ne ake cigiya me yafaru da shi?.
Murmushi Alhaji Sufyan yayi yace tabbas wannan Faruk ne ikon Allah ko ya akayi haka, yanzu haka wajen iya yin shi ne yayi ma wad'anda suka kasa hak'uri suka d'aukeshi ko kuma wannan yarinyar takasheshi.
Hajiya Maijidda rik'e baki tayi tace na shiga ukku yanzu Faruk d'inne ya'bata tun shekaran jiya?
Nasiba da tayi mutuwar zaune hankalinta ya tashi sosai kasa cema iyayen nata komai tayi tana ta kallon hotunanshi da ake dallawa a TV ana cigiya chan sai ga hawaye sun fara fita nan tasa ma iyayenta kuka.
Su dukansu kallonta sukayi cike da mamaki sukace ke kuma kukan me kikeyi?
Cikin kuka tace Daddy Faruk d'ina ba'a ganshi ba ya 'bace .
Daddynka fusata yayi yadaka mata tsawa yace ke bana son shashancin banza ai ba ubanki bane ya'bace da zaki ma mutane kuka kuma yaushe Faruk d'in yazama naki wannan azzalumin maci amana, inma banda abinki miye abun tada hankali kan 'bacewar wanchan butulun?
Cikin sheshek'ar kuka tace wallahi Daddy Faruk ba mugu bane mutumin kirkine bana son wani abu yasameshi dan Allah muje nemanshi.

Mummynta ce takai hannu tabuge mata maki tace ke dai shashasha ce miye abun tada hankali ga 'bacewar wanda yaso yatozarta mahaifinki yanzu haka rashin mutuncin yayi ma wasu sukaji basu iya hak'uri,

K'ara sautin kukanta tayi tana jin wani irin haushi akan maganar da iyayenta suke marar dad'i akan Faruk dan ita ta san har yanzu tana jinshi a ranta.


Mahaifinta ne yace kibarta kawai Hajiya sai tayi ta yi tunda ita batasan ciwon kanta ba bata kishina duk cin zarafin da yake mana bata gani ni wallahi dad'i ma naji yanzu ai iyayenshi zasu gane abinda muke fad'a masu akan abubuwan da d'an nasu yakeyi tunda su basu iya hanasu.

Mik'ewa Nasiba tayi cikin sauri tajuya tafita daga parlorn tana cigaba da kuka.

Mummynta ce tace oh ni yau naga ikon Allah watau Alhaji yarinyar chan dai da alama bata hak'ura da yaron chan ba.

Cikin 'bacin rai yace kibarta ko kukan jini zatayi bazata ta'ba auren Faruk ba ko da ace yana nan bare ma baya nan dan bazan ta'ba ba irinshi auren d'iyataba.

Shuru Mummyn Nasiba tayi dan ita babu abinda tatsana sama da 'bacin ran d'iyartata dan ma ba hali da ta je ta lallasheta.


Nasiba kuka tadinga yi kamar wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa wani irin tausayin Faruk ne taji ya d'arsu a zuciyarta, wayarta tad'auko takira numbers d'inshi dukansu a kashe nan tacigaba da rusa kuka daga k'arshe tatashi tad'auko mayafinta tazari key d'in motarta tabi ta k'ofar baya taficce batare da sanin iyayenta ba.

Tuk'i take ammah kuka takeyi ahaka har ta isa gidansu Faruk, tana isa ko tsayawa rufe motar batayi ba tashiga gidan da gudu, duk mutane ne zazzaune anyi cirko cirko kowa yana jimamin 'bacewarshi tsawon kwana biyu, a parlor tasamu Mom zaune tana ta matsar hawaye ana lallashinta tana zuwa tafad'a jikinta tare da fashewa da wani irin kuka me ban tausayi, cikin kuka tadinga cewa Mom dan Allah ina Faruk? Dagaske ne ya 'bace? Dan Allah Mom kice min Faruk d'ina yana d'akinshi wallahi ina sonshi bana so inrasa shi.
Mom kamar jira take nan itama d'in tafashe da kuka, k'ok'arin k'wace Nasiba akayi daga jikin Mom ammah tarik'eta gam.
Dakyar aka samu aka 'ban'bareta nan takwanta a k'asa tana cigaba da rusa kuka, aka rasa wanda za'a lallasa ita da Mom.

Alhaji Sani Maishadda da abokan Faruk ne suka dinga k'ok'arin zuwa wajaje nemanshi inda a chan garin daura kakanshi yasa aka dinga safkar alk'ur'ani ana sadaka....








_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 18*

Mummyn Nasiba saida tafaki idanun mijin nata sannan tanufi d'akin d'iyartata dan talallashi abunta sai gani tayi wayam babu ita nemanta tafara yi tana dubawa a parking space taga babu motarta dan haka tasan ta fita dawowa tayi tasamu mijin nata tace oh ni Alhaji watau yarinyar chan fita tayi daga gidan nan.

Da mamaki yake kallonta yace kina nufin bata nan?
Eh na duba d'akinta kuma naga motarta bata nan.
K'wafa yayi yace watau gidansu Faruk taje dan bata jin magana kibarni da ita zata dawo gidan tasameni.


Har dare Nasiba tana gidansu Faruk hawayen idanunta sun kasa tsayawa fuskarnan duk ta kumbura saboda tsananin kukan da tasha tana zaune gefen Mom koda aka kawo masu abinci daga ita har Mom k'in ci sukayi saida akayi da gaske sannan suka d'an ci, suna nan a haka Barr Junaid da Nas suka shigo saurin mik'ewa tayi tanufi wajen da yake tun kan yayi magana tatari numfashinshi tace Junaid anga Faruk d'ina ko?
Junaid kallon Nas yayi su dukansu jikinsu ya yi sanyi sannan yakalli Nasiba tare da girgiza mata kai.

Ja tafara yi da baya nan wasu hawayen suka wanke mata fuska tace shikenan tunda ku bazaku iya ganoshi ba ni zan je innemeshi da kaina, ni zan iya dawowa da shi.
Barr Nas ne yayi k'arfin halin cewa kiyi hak'uri Nasiba muna bakin k'ok'arinmu ammah har yanzu Allah baisa andaceba insha Allahu zamu gano Faruk kikwantar da hankalinki.

Wajen Mom takoma tatsugunna kusa da kujerar da take zaune tace Mom kin gani ko basu ganoshi ba kidaina kuka ni zanje in nemeshi.

Ganin yadda take magana kamar zararra yasa mom ta girgiza kai tace a'a Nasiba babu inda zakije insha Allahu zasu gano mana shi.
Fashewa tayi da kuka tace Mom har sai yaushe?
Kwantar mata da kanta saman cinyarta tayi nan tafara lallashinta dan batasan abinda zatace mata ba.
Kuka tadinga yi sosai har saida Dad yadawo nan yasamu yalallasheta tadaina kukan ganin har tara ta yi yasa yace tatashi tatafi gida, da fari ta ce babu inda zataje har sai Faruk ya dawo saida Dad yadinga lalla'bata sannan tahak'ura tatashi tatafi.


Tana isa gida a parlor tasamu iyayen nata mahaifinta sai kaiwa da kawowa yake tana shigowa yace daga ina kike?
Batare da ta damu da yanayin da taganshi ba tace daga gidan su Faruk nake...bata rufe baki ba taji ya wanka mata bari.
Saurin dafe kuncinta tayi tare da kallon mahaifin nata cike da mamaki dan wannan shine karo na farko a rayuwarta da yata'ba marinta.
Nunata yayu da yatsaya yace ke har kin isa kitsallake maganata? Da izininwa kika fita daga gidan nan?
Shuru tayi tare da sadda kanta k'asa tana hawaye kanta yayo zai rufeta da duka Hajiya Maijidda tayi saurin shan gabanshi tace a'a Alhaji dan Allah kar kabugeta yarinya ce Nasiba batasan komai ba sai andinga kwatanta mata.
Wata uwar harara yawurga mata yace Nasibar ce yarinya?
Shuru tayi tana kallonshi.
Cigaba yayi da cewa toh wallahi duk lokacin da tak'ara barin gidan nan sai na mugun sa'ba mata ban yarda ko nan da waje tasake fitaba.
Wucewa Nasiba tayi sumi sumi tanufi d'akinta tana ji yana cewa ka ga 'yar iskar yarinya ni zaki maida banza watau ke ga shugabar soyayya ko?

Mummyn Nasiba ce tace Alhaji ayi hak'uri.
Tsaki yaja sannan yawuce a fusace yakoma d'akinshi.


Bayan d'iyartata tabi tana zuwa tasameta zaune saman gado ta dafe kuncinta tana ta kuka, zuwa tayi tazauna kusa da ita tace haba Nasiba meyasa bakiji yanzu gashinan kinja ya doke ki.
'Dago kai tayi takalli mahaifiyartata cikin sheshekar kuka tace Mummy fad'a min menene laifina a ciki? Dan kawai ina son Faruk, ai bani nadasa ma kaina son nashi ba meyasa ake ganin laifina?
Matsowa Mummy tayi kusa da ita tare da dafata tace haba Nasiba kidaina cewa haka kinga kema baki kyautaba ya kamata zuwa yanzu ace kin cireshi a ranki ko dan saboda tozarcin da yaso yayi ma mahaifinki kinga a yanzu mahaifinki yana fushi da ke saboda abinda kikayi baki kyautaba.
Girgiza kai tashiga yi cikin kuka tace Mummy kune zakuga rashin kyautawa ta ammah ni zuciyata gani take hakan shine daidai dan saboda tana son Faruk, indai har abinda nayi a wajenku ba daidai bane to kuyafe min na ji ni me laifi ce saidai bazan ta'ba iya cire son shi ba ammah ina fatan inyi k'ok'arin cireshi a raina ko da ace hakan zai zama sanadiyar mutuwata indai har hakan zaisa infaranta maku.
Rungumeta jikinta Hajiya Maijidda tayi tace a'a Nasiba kidaina cewa haka dan bamuso murasaki munason ki sosai.
'Dagowa tayi takalleta tare da yin murmushi wanda yafi kuka ciwo sannan tace indai har kuna so na to ya kamata kubarni incigaba da kasancewa da soyayyar Faruk dan zuciyata tana sonshi hakan kawai zakuyi min ingane cewa kuna k'aunata.
Da mamaki take kallon d'iyartata da soyayya ta gama rufe mata idanu cikin sanyin jiki tace Nasiba kinsan dai duk duniyar nan babu wanda yakaimu k'aunarki saboda mu mune iyayenki saidai mahaifinki nakeji kinsan idan har yafad'i magana to baya canzata.
Ruk'o hannuwan mahaifiyartata tayi tana kallonta da idanuwanta da suka kumbura saboda tsananin kuka tace Mommy dan Allah ke kikasance da ni domin ke uwace na tabbata ke kad'ai zaki iya fahimtata.
Rungumeta tayi tare da shafa bayanta tace ina tare da ke d'iyata tabbas nice kad'ai yafi dacewa infara fahimtarki, kidaina kukan mucigaba da addu'a insha Allahu Faruk zai bayyana.
Ajiyar zuciya tasafke tace nagode sosai Mummyna.
Bakomai d'iyata yanzu dai kidaina kukan nan bari inje inkawo maki abinci kici kiwatsa ruwa kikwanta ko?
Goge hawayenta tayi tare da yin murmushi tace nagode mummyna.



***** *****

A chan 'bangaren Faruk yana chan da mutanen nan a cikin d'akin a d'aure dan a yanzu ma ya samu ansafkeshi daga saman kujerar a saman gado aka d'aureshi indai har zaiyi wata buk'atar kusan mutum ukku suke rakashi wajen toilet yashiga yagama abinda zaiyi sannan sumaidoshi sud'aure Alhaji Mansur kusan kullum sau ukku yake zuwa yadubasu yakawo masu abinci koda shi a wulak'ance ake bashi abinci kuma ba ci yakeyi ba sai yaga yunwa ta cishi sosai sannan yaci, wulak'anci da cin mutunci kala-kala yake sha a wajensu Alhaji Mansur da mutanenshi saidai shi duk wannan bai dameshiba abu d'aya ne yake d'aga mashi hankali halin da iyayenshi suka shiga sai kuma case d'in jawahir baisan yadda zai kasanceba ita kanta ya san sai ta zargi wani abu kar ma tad'auka yaudararta yayi.



A yau ma yana zaune a inda aka d'aureshi hankalinshi a tashe yana tunanin kotun da za'a zauna gobe sai gani yayi anwurgo mashi takeaway a saman jikinshi, kallo d'aya yayi mashi yad'auke kai, d'aya daga cikinsu ne yataso yana cewa watau sai ma kad'auke kai idan bazaka ci abincin ba sai kayi magana ba sai na kwanceka ba.
Shuru yayi kamar baiji abinda yace ba.
Cikin 'bacin rai yace kai wai wane irin banzan mutum ne ayita maka magana kayi shuru kak'yale mutane ka san kabi a sannu inba hakaba zan nakasaka a wajen nan nace zaka ci abincin ko ka k'oshi.
Nan ma shuru yayi yaba bango ajiyarshi.
A fusace yad'aga bindigar da take hannunshi yabuga mashi a kai, Faruk saida yasaki k'ara saboda zafin bugun.

'Dago mashi kai yayi dak'arfi yace idan har kacigaba da mana taurin kai sai mun azabtar da kai a gidan nan, kalleka dan Allah a yanzu gakanan a wulak'ance a wajenmu duk wannan jin kan nan da tak'ama babu su.
Wani daga cikin sauran da suke zaune ne yace cinnaka ni ko naga ba jin kai kaga fa yadda yake taka k'asa kamar irin baya so d'innan shi a dole ga me kud'i barrister sai ga rayuwar barrister ta k'are a hannunmu ya koma wani k'ask'antacce.

Su dukansu dariya sukasa suna cewa dan Allah jibarshi, duk ina dukiyar yanzu.

Bud'e baki Faruk yayi ahankali yace koma me zakuce bazan ta'ba damuwa ba saidai inaso kusani a duk ranar da nayi nasarar barin gidan nan gabad'ayanku sai na sa and'aureku.
Kan bindiga wanda aka kira da cinnaka yasake buga mashi a fuska har saida jini yafito daga hancinshi, runtse idanu yayi dak'arfi yana jin rad'ad'in bugun.
'Daya daga cikin wad'anda suke zaune ne yace a'a Cinnaka kadaina dukanshi ka ga Alhaji bai ce mubugeshi ba kabari abani izini sannan mucasashi tunda shi har yana ma tunanin zaya fita daga nan har yasa ad'auremu, wayyoo Allah har ma na d'an tsorata dan Allah kutaimaka min zasu kamani wallahi tsoron zaman gidan kaso nakeji......su dukansu kwashewa sukayi da dariya, wani kuma yace ahaka wai shashashan yake gani zamu barshi yafita lallai da sauranka.

Haka sukaita tsokanarshi shi dai yayi shuru bai sake cewa komai ba saboda rad'ad'in da yakeji a fuskarshi.
Yana ji Cinnaka yakoma yazauna batare da ya kwance mashi hannuwa ba koda daman shima ba yunwar yake ji ba inma yana ji sai ta cishi sannan yake cin abincin da suke bashi.





Jawahir da take zaune a d'an kurkukun d'akinta tun bata damu da rashin zuwan Barrister ba har abun yazo yafara damunta dan bai ta'ba d'aukar wannan lokacin bai zoba gashi ma abun tashin hankalin gobe ne zama na k'arshe da zasuyi a kotu,,, mik'ewa tayi tsaye tare da jingine jikinta a jikin bango ahankali tace ko dai Barrister ya janye ne shima bazai iya taimakona ba? Girgiza kai tayi tace ah'ah ko kuma wani abu yafaru da shi?
Hannu tasa tatoshe bakinta nan k'wallah ta cika mata idanu tace na shiga ukku ba dai akaina wani abu yafaru da shi ba, idan ko hakane ya zanyi, nice sila,,,
Tana nan tsaye a haka akazo aka bud'e d'akin juyowa tayi dan ganin wanda zai shigo sai taga ma'aikaciyar gidan ce, ajiyar zuciya tasafke
Kallonta matar tayi a wulak'ance tace ke zo muje ana son ganinki.
Nuna kanta tayi tace ni?
Harararta tayi tace akwai wani ne cikin d'akin?
Batare da ta bata amsaba tad'auko kallabinta tad'aure kanta sannan tabi bayanta suka fita, da mamaki take kallon inda suka nufa tabbas wajen da ake kaisune idan wani ya zo ganawa da su.
Suna zuwa sai jin matar tayi ta ce kawo hannunki, mik'awa tayi nan taga ansa mata ankwa sannan matar tace kishiga ciki d'allabai yana ciki.
Tambayar kanta tayi tace Faruk kenan yazo ganawa da ni ammah kuma yau bai shigo wajenaba sai nan....Daka mata tsawa matar tayi tace me kika tsaya jira?

Shiga tayi d'akin da mamaki take kallon wanda yake tsaye.
Murmushi yasakar mata yace sannu d'iyata ina fata kina lafiya? Wannan dai mahaifin bai kyautaba da baya zuwa ganin d'iyarnan tashi.
'Daure fuska tayu tace menene dalilinka na zuwa wajena?
Matsowa yayi kusa da ita yana murmushi yace kikwantar da hankalinki na zo ne kawai duba lafiyarki sannan injajanta maki 'bacewar da akace Barrister Farukya yi tsawon kwana ukku.

Zaro idanu tayi waje da mamaki take kallonshi tace kana nufin Barrister ya 'bace?

Alhaji Mansur dariya yasake yi yace ya naga kin tsorata, nima dai haka naji ban saniba ko akan wani case aka saceshi gashi mu kuma gobe ce ranar shara'a ta k'arshe.
Idanu tazuba mashi tana kallonshi cikin ranta tace ko dai akan case d'ina ne?
Ya kikayi shuru ko kina tsoron makomarki ta gobe?
Sai a lokacin tayi murmushi tace ban damu da makomata ba saidai na san duk abinda yafaru da Faruk ku ne sila, shin ko shima kun kasheshi kamar yadda kuka kashe iyayena?
Tarar numfashinta yayi yace ko kuma kin kasheshi kamar yadda kika kashe sauran lauyoyinki, shin taya ma gobe za'a barki bayan kin kashe lauyoyi ukku.

'Daga murya tayi tace idan har kuka bari wani abu yafaru da Barrister bazan ta'ba barinku ba da duk wanda yake da hannu a ciki sai naga bayanshi, kukyaleshi yayi rayuwarshi domin shi baida laifi a ciki nice me laifin kuma idan har saboda ni kuka kamashi kusakeshi ni na amince akasheni ammah kar ku kashe wanda baisan komai ba a kai.

"Jawahir mu bamu kamashi ba dan baya hannunmu kece ma nayi tunanin kin kasheshi ammah dai shikenan ke kad'ai kikasan wannan sirrin dan nasan daman ba fad'a min gaskiya zakiyiba nima daman jaje nazo maki, ni zan tafi ko ma mekenan sai munhad'e a kotu gobe ina fata zaki kasance cikin bak'in ciki kasancewar yau itace ranarki ta k'arshe gobe kamar yanzu kina cikin k'abarinki, na barki lafiya.

Hawaye ne suka gangaro mata a kuncinta ganin ya juya zai tafi yasa cikin d'aga murya tace na fad'a maka kar kabari wani abu yafaru da rayuwar Barrister wallahi idan har kakasheshi nima sai naga bayanka kafin nima akasheni.
Bai tsaya bata amsaba yawuce yatafi.


Dafe kanta tayi da hannuwanta da suke da ankwa, matar ce tazo tatisata gaba tamaidata chan d'akinta tamaida tarufe.
Tana shiga sulalewa tayi k'asa tazauna tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka, cikin kuka tadinga cewa Ammi kizo gareni ina buk'atar taimakonki ko da ace wannan shine taimako na k'arshe da zakiyi min a duniya dan Allah kizo gareni......bata rufe baki ba sai ga wani farin haske ya bayyana a gabanta, saurin mik'ewa tayi tana kallon haskenan nan yafara komawa siffar mutum kafin k'iftawar idanu sai ga tsohuwarnan ta bayyana.
Bud'e baki tayi zatayi magana tatari numfashinta tace tabbas Barrister yana cikin mawuyacin hali dan yana hannunsu sun kamashi saidai bazan ta'ba taimaka mashi ba.
Saurin zamewa tayi k'asa tatsugunna tare da had'e hannuwanta biyu waje guda cikin muryar kuka tace dan Allah Ammi kitaimaka min kitseratar da shi domin rayuwarshi tana da muhimmanci sosai bai dace ace wani abu ya sameshi ba a dalilina ni k'wara akasheni dan tawa rayuwar batada sauran amfani.

Dariya matar tayi sannan tace Jawahir yau gaki a gabana tsugunne kina rok'ona bayan da baki ta'ba hakan ba, saidai tsanar da kikayi min ammah yau kece a haka dubeki.

Fashewa tayi da kuka tace tabbas ni k'ask'antatta ce kar kiyi duba da abinda yafaru dan Allah kiceci wannan bawan Allahn banaso sukasheshi.

Zureren hannunta tad'ago tace kiyi duba zuwa nan jawahir.
Saurin d'ago kanta tayi tadubi hannun Barrister Faruk ne tagani zaune an d'aureshi idanunshi

28 / 74