Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
dan ak'wato mana hak'k'inmu.
Barr Faruk kallon Barr Nas yayi da shima yake kallonshi su dukansu sukayi shuru aka rasa wanda zaiyi magana daidai lokacin akayi sallama aka shigo su dukansu suka juya suka kalli k'ofa tare da amsawa wata dattijuwa ce tashigo nan duk suka gaisheta bayan ta amsa ne tace Nazir ina key d'in bedroom d'in Abbanku zamu d'auko sauran lemuna a ciki.
Aunty Amina kinsan dai anhana bud'ewa nima kaina dak'yar nasamu Ummah tabani key d'in nashigo parlor.
Harararshi tayi tace kai ni dallah bani ind'auko abinda zan d'auko sai inmaido maka kayi ta tseguminka saikace wata uwa abu zan d'auka a ciki.
Ganin yadda tafara d'aga murya tana fad'a yasa yaciro keys d'in acikin aljihu yamik'a mata amsawa tayi taje tabud'e tashiga.
Barr Faruk kallon kallo suka fara da Barr Nas sai kuma suka maida hankalinsu ga k'ofar bedroom d'in da tabud'e, Faruk ji yake kamar yayi tsalle yashige saidai hakan bazai ta'ba yuwuwa suna kallo tagama d'auko lemunan tarufe d'akin tamik'o ma Nazir key d'in, sannan tafara jidar lemunan tana fita da su.
Nazir a gefen da yake zaune ya d'age wani throw pillow ya ajiye Keys d'in a wajen yace muma ai yanzu zamu fita tun kan azo afara yi mana surutu tace da dai ya fi maku.
Faruk yana kallo nan ya ida sarewa yatabbatar bazai samu yadda yake so ba.
Bayan ta fita nan Barr Nas da Nazir suka fara hira inda shi kuma Barr Faruk yayi shuru abin duniya duk ya isheshi, Nazir bai damu da shurun da yayi ba dan yana ganin yanayinshi yagane shi d'in ba mutum bane me son hayaniya sosai ba, suna cikin hirar nan wayar Nazir tafara ringing d'aukowa yayi yai picking tare da yin sallama, basuji abinda akace mashi ba saidai ji sukayi yana cewa toh shikenan Kawu ganinan zuwa ai dama ina cikin gidan bari infito, kashe wayar yayi yakallesu yace bari ind'anje indawo wasu abokan Abba sukazo mana gaisuwa daga Kaduna, ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke kafin Nas yayi magana shi yayi saurin cewa Allah Sarki toh shikenan babu damuwa sai ka dawo.
Nas dai murmushi yayi dan ya san dalilin Faruk na cewa haka.
Mik'ewa Nazir yayi yafita lokacin da aka sake kiranshi waya, yana barin d'akin cikin sauri Faruk yamik'e yanufi wajen kujerar da yazauna yana zuwa yahankad'e pillow yad'auko keys d'in wani irin farin ciki yaji a ranshi yajuya yakalli Nas da yakeyi mashi kallon mamaki ganin babu wani alamun tsoro a tare da shi har ya iya d'aukar key d'in, murmushi yasakar mashi tare da cewa ina zuwa bari inyi sauri inje ind'auko bazan 'bata lokaci ba.
Cikin sanyin jiki yace a'a Faruk ina jin tsoro.
Batare da ya tanka shi ba yawuce yanufi hanyar Bedroom d'in yana zuwa yasa key d'in da yaga Nazir ya nuna ma matar nan, yana murzawa sai ga k'ofa ta bud'e juyowa yayi yakalli Barr Nas da yagama tsorata sannan yazare key d'in yashiga cikin bedroom d'in yamaida k'ofa yarufe, tsaye yayi a bakin k'ofar yana bin d'akin da kallo komai na ciki ya ji sosai za'a iya cewa aljannar duniya kenan, ta'be baki Faruk yayi sannan cikin sauri yanufi wajen wardrobe d'in yana zuwa baiyi wata wata ba yabud'e yafara bincike cikin sauri dubawa yadinga yi ammah baiji wayar ba saida yaduba kusan sau ukku baiga komai ba nan hankalinshi yafara tashi yace shikenan and'auketa daga wajen toh ammah tana ina? Ko dai Jawahir batasan inda takeba daman haka nan tace min tana cikin wardrobe d'inshi?.
Tsaye yayi wajen, jikinshi duk ya yi sanyi sosai chan kuma yatuna da irin matsalar da zai shiga dan haka yajuyo cikin sauri zai fito yabar d'akin.
Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yamzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mufito mukoma setting room.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:13 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Award Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 12*
Barr Nas da yake zaune tsoro duk ya gama cikashi Allah Allah kawai yake Faruk yafito kafin dawowar Nazir yana cikin haka kawai sai jiyo muryar Nazir yayi ya tunkaro d'akin yana waya yana cewa shikenan Ummah ganinan yanzu zan kawo maki keys d'in daman sun tafi yanzu ina tare da su Nas ne kuma shi dai d'an gidane babu damuwa sai mukoma setting room.
Wayyoooo kar kuso kuga Nas a lokacin zufa ce tafara kwarara daga jikinshi yana jin kamar yanutse cikin kujera, tsoro da fargaba duk suka d'arsu a cikin zuciyarshi, Nazir na gama wayar ya ida shigowa cikin d'akin yana shigowa yakalleshi yace ya naga kana zufa? Sorry bari ak'ara Ac d'in daman d'azu muka rageta.
Shi dai da idanu yabishi kawai cikin ranshi yana cewa shikenan Faruk ya ja min, muryar Nazir yajiyo yana cewa ina abokin naka ba dai ya tafi ba?
Dabarbarcewa yayi yarasa abinda zaice sai chan cikin rawan murya yace am ya je waje zai amsa waya ne.
Toh shikenan bari mujira yadawo sai mukoma chan setting room ko kuma mutafi muhad'e da shi dan Ummah ta fara fad'a wai inkawo mata key d'in d'akin Abba saboda ba'a so ana shigowa yanzu za'a fara surutu.
'Yan cikin Nas saida suka kad'a yarasa abinda zaice ma Nazir sai chan cikin dauriya yace Nazir ko zaka taimaka min da ruwa insha kafin yadawo kaga kar mufita yadawo kuma bamu nan baisan inda muka nufa ba.
Mik'ewa Nazir yayi yace hakane kuma bari inje inkawo maka ruwan dan na nan ciki basuda sanyi inyaso in nagamu da shi sai infad'a mashi.
'Daga kai kawai yayi dan baya ji a yanzu zai iya magana saboda tsananin tsoron da yashiga juyawa Nazir yayi yafita dan samo ma abokin nashi ruwa.
Yana fita Nas yana son yamik'e ammah yakasa jikinshi ssi rawa yake yana nan zaune sai ga Faruk ya fito yana fitowa cikin sauri yarufe d'alkin, jin motsin tafiya yasa yawurgo ma Nas key d'in yayi saurin juyawa tare da kanga wayarshi a kunne kamar yana waya.
Nas tura key d'in yayi a k'ark'ashin throw pillow d'in da Nazir ya ajiye key d'in daidai lokacin Nazir yashigo yana cewa na sa yanzu za'a kawo maka.
Ajiyar zuciya Nas yasafke ganin asirinsu bai tonuba.
Nazir kallon Faruk yayi da yajuya yana waya yace ashe ya dawo ai da nafita ban ganshiba.
Murmushi Nas yayi yace Eh kana fita yadawo kuma aka sake kiranshi waya shine yamatsa chan yana yi.
Nazir yace Allah sarki yanzu kuzo mukoma setting room na san sun ragu gashi fitarnan da nayi andameni infito inrufo d'akin.
Murmushi Nas yayi yace haba ba damuwa ai mu ba bak'i bane, daidai lokacin Faruk yajuyo yana murmushi yace bakomai ai yanzu ma zamu tafi dan daga wajen aiki ake min neman gaggawa.
Nazir yace tun yanzu maimakon kubari sai anjima.
Kar kadamu muma munso mubari sai da anjima dan dai kiran gaggawar da akayi min ammah zamu dawo wani lokacin.
'Dauko key d'in Nazir yayi yace toh shikenan sai mufita gabad'aya in mik'a masu key d'in inhuta.
Faruk yana lura da Nas da yake ta yi mashi kallon tuhuma ammah yak'i kulashi ahaka har suka fita.
Saida suka jirashi yafara mik'a key d'in wa Ummanshi sannan suka tafi yarakasu har wajen mota yayi masu godiya suka shiga suka tafi, suna fara tafiya Nas yajuyo yakalleshi yace wai ya dai Faruk sai alama nake ta tambaya kuma ka gane nufina ammah kashareni wallahi hankalina ya tashi sosai Allah ya taimaka guy d'in nan bai gane komai ba.
Murmushi Faruk yayi yace daman ya gane da kai zaka fi kwana ciki tunda abokinka ne.
Au haka ma kace ko?
"Toh me kakeso ince?
Yanzu dai fad'a min shin ka d'auko wayar ko kuwa hakanan kafito baka gantaba?
Murmushi yayi yace Eh toh banga wayar ba.
Kana nufin baka gantaba hakanan kafito?,, Nas yatambayeshi cike da mamaki.
Juyawa yayi yakalli taga sannan yace ina nufin ban gantaba a inda jawahir ta fad'a min saidai na ganta a wani wajen na daban.
Ajiyar zuciya Barr Nas yasafke yace Alhamdulillah na ji dad'in haka gaskiya Barrister kai d'in nadaban ne saisa ko a school nake jinjina maka dan k'walwarka tana ja sosai.
Juyowa Faruk yayi yakalleshi tare da fiddo wayar daga cikin aljihunshi yana murmushi yace tabbas ina farin ciki Nas ko ba komai wayar nan zata taimaka min wajen samun duk wani abu da nakeso, yanzu dai mu wuce gidana kasafkeni dan ko motsta bazan d'auko gidanka ba.
Kallonshi Nas yayi yace ban gane insafkeka ba malam, muje dai ind'auko su Madam inmaidasu gida inyaso kaga sai muwuce gidan naka ko ba haka ba?
Hakan ya yi abokina ai duk yadda kakeso haka za'ayi dan yau ba k'aramin taimako kayi min ba.
" yoh ba dolena intaimakeka ba tunda nima ka taimaka min wajen samo soyayyar madam a school"
Su dukansu dariya sukasa nan Faruk yagirgiza kai tare da juyawa yana cigaba da kallon taga.
Bayan sunyi sallar magrib a cikin anguwarsu Faruk sannan suka wuce gidanshi a parlor suka zauna Faruk yaso yakunna wayar ammah yajita a kashe alamun ba charge dan haka yatashi yajonata sunayin sallar isha'i Barr Nas yace shi zai wuce gida koma menene inyaso gobe zasu had'u.
Barr Faruk yace babu damuwa nan yarakashi har wajen mota yana tsokanarshi tashin hankalin da yaga ya shiga lokacin da yafito cikin d'akin.
Barr Nas yana dariya yace ka ma yi sa'a da bakaga na saki zawo ba dan wallahi har na hango makomata gaskiya na yi kasada dayawa Allah dai ne yacecemu.
Hakane Nas ni fa daman kai nafi ji ba kainaba dan banaso inja maka wani abu yasameka.
Hmm toh yanzu ya za'ayi idan zaka maida wayar?
Barr Faruk yace a'a bazan maidata ba tunda shima ba tashi bace idan nagama bincikena zansan yadda zanyi da ita.
Toh shikenan Barrister Allah dai yataimaka sai dai goben idan na shigo.
Toh Allah yakaimu.
Bayan tafiyarshi Faruk wanka yayi yashirya wajen k'arfe tara yacire wayar daga charge yafara bincika abubuwan da suke cikinta ya samu shaidu sosai dan hatta recordings ya samu na wayar da akayi har da wanda alamu yanuna anyi recording antura ma wani ya saurara, wata murya da yaji anyi waya da me ita saida yaji kamar ya san muryar ammah yakasa tantanceta.
Cikin contacts yashiga yafara binciken numbobin ciki nan yaci karo da number d'in da tad'aga mashi hankali saurin d'auko wayarshi yayi yasaka number d'in yayi dialing a nan ya ida tabbatarwa da tabbas number d'ince hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba, ajiye wayar yayi tare da dafe kanshi ji yayi komai ya tsaya mashi, chan kuma yamik'e yafara zagaye d'akin yana zuwa yana dawowa hannuwanshi suna a bayanshi ya rik'esu tunowa yafara yi da lokacin da jawahir take ce mashi zaka taimaka min kana nufin komai kusancinka da mutum idan har yana da hannu a ciki bazaka ta'ba barinshi ba?
Cize le'be yayi a hankali sannan yakoma yazauna yak'ara d'auko number yasake dubawa tabbas idanunshi ba gizo sukeyi mashi ba toh ammah me hakan yake nufi kenan shima akwai hannuwanshi acikin mutuwar mahaifan Jawahir? A'a kodai abokinshi ne kawai ammah baida hannu acikin mutuwarsu, toh ammah call recording d'in da naji fa tabbas akwai na muryarshi ya ji shi, sake kunno recording d'in yayi yasaurara muryarce yaji tana cewa Hello kana jina ya kamata kayi k'ok'ari wajen ganin ka samo mana file d'in filin nan dan da alama zaiyi kud'i sosai ni na san yadda za'ayi asiyar da shi batare da kowa ya ganeba dan nima kaga wannan filin da kabarmin gwamnati nasiyar mawa kuma ta siya da kud'ad'e masu tsoka.
Toh shikenan Alhaji koma me kenan nasan hanyar da zanbi insamo dan dama maganar da muka gama yi da Alhaji tanimu kenan dan shine jagoran komai, da ace akwai hanyar da zanbi da a yau d'innan sai naga bayan yarinyar nan kowa yahuta dan na san idan har tamutu dole abarmin gadonta gabad'aya tunda ni kad'ai ne d'an uwan mahaifinta,,, Cewar Alhaji Mu'azu.
Daga chan 'bangaren dariya akayi akace kaidai kabi komai a hankali ko da baka kasheta ba zaka iya yin amfani da damarka wajen ganin mun samo dukiyar Alhaji Muhammad, inyaso idan har mun gama samun yadda mukeso zaka iya kasheta saidai kuma idan har zaka rufe ma mutane baki dan kar ayi zargin wani abu kamar yadda mukayi bayan munsa ankashe Alhaji Muhammad da matarshi.
Dariya Alhaji Mu'azu yayi yace ai fiye da hakan ma zan iya sa wa ayi mata dan ni ban had'a komai da kud'iba abokina, yanzu dai zuwa anjima zan kiraka idan har nagama tattara bayanan filin inyaso sai muje musiyar da shi.
Yauwa mutumina kayi k'ok'arin haka sai na ji daga gareka.
Ana zuwa nan recording d'in yak'are.
Wani kuma yasake kunnowa nan ma yaji muryar mutumin yana cewa, Hello Alhaji Mu'azu ina jinka d'azu ka kirani bana kusa.
Eh Wallahi abokina cewa nayi ta samu fa a yanzu ga wani gida nan na Alhaji Muhammad da nagano yana da shi batare da sanin kowaba sai yanzu naga takardun gidan na je na ganshi kuma antabbatar min da nashine.
Daga chan 'bangaren dariya akayi akace lallai Alhaji Muhammadu wayonshi ya yi yawa watau yana da gida batare da sanin ka ba, toh bari zan zo inje muga gidan idan har yana da girma sosai ni zan sayeshi dan dama inaso mutashi da iyalina daga nan, kace abu ya zo gidan sauk'i ai wallahi mutuwar nan tashi dad'i tayi min dan ko bakomai munsan muma mun mori dukiyarshi.
Alhaji Mu'azu ma dariya yayi yace kaidai bari a yanzu gashinan ina ta facaka da kud'i yadda nakeso ba kamar lokacin da yake raye ba, ka san mutuwarshi ko kad'an bata d'aga min hankali ba sai waje d'aya lokacin da kabani layarnan insaka mashi a baki toh a nan ne nad'an tsorata dan ko da su Alhaji Mannir suka shigo gidan zasu kasheshi ban wani d'aga hankaliba dan na san zamuyi nasara.
Katseshi yayi yace a'a Alhaji Mu'azu kayi shuru kar ajiyo ka asirinmu yatonu agane mune muka kasheshi abar maganar kawai zan zo yanzun nan muje inga gidan dan ka san bana wasa da kud'i,,, su dukansu dariya sukayi.
Hakayayi ta kunno recording d'in me muryar yana saurare
________Yana gama sauraren recording d'in ajiyar zuciya yasafke tare da kwantar da kanshi saman gadon inda k'afafuwanshi suna a k'asa ahankali yace tabbas biri ya yi kama da mutum toh ammah ta wace hanya zanbi wajen ganin na kamasu da laifin da nake zarginsu, dan shi kad'ai ne yagane muryarshi bai gane muryoyin sauran da yaji ba saidai ya gane ta mutane biyar saboda sunansu da Alhaji Mu'azu yake ambata a cikin wayar saidai mutum biyu ne bai ganeba toh ammah su wanene? Shin suna raye ko su ma ankashesu? Kanshi ne yajefa ma tambayoyin.
Kasa runtsawa yayi dan kwatakwata daman bai sa ma ranshi yin bacci a lokacin ba nan yayi kwance yana ta 'yan tunane tunane tare da neman hanyar da zai 'bullo wajen ganin ya kamashi da laifin da yake zarginshi da shi, tashi yayi yad'auko wayarshi yana tura duk recording d'in da yake so masu alak'a da case d'in ya dad'e yana turawa dan suna da yawa sosai saida yaza'bi iya wanda yakeso, a cikin kunnuwanshi akayi kiran sallar asuba.
Wajen k'arfe goma yagama shirin shi yaje wajen aiki kasancewar litinin ce yana zaune yana aikinshi nan aka kirashi a waya dubawa yayi ganin private number ne yasa yashare baiyi picking ba wani kiran yasake shigowa a karo na biyu, tsaki yayi sannan yad'auko wayar zai kashe ta gabad'aya dan kar tahanashi yin aikinshi sai kuma yafasa yayi picking batare da yayi magana ba.
Daga chan 'bangaren akace Hello kana ji?
Shuru yayi yana sauraren muryar kamar ya ta'ba jinta k'ara jefo mashi tambaya akayi "wai ko ba Barr Faruk bane"
Saurin d'ago wayar yayi daga kunnenshi yadanna inda zatayi mashi recording d'in maganar sannan yace Hello ina ji.
Au daman kana ji shine zakayi shuru watau har rainin hankalinka ya kai ga haka,,, tsaki yaji anja sannan aka kashe wayar.
Bai damu da hakan ba ya ajiye wayar yacigaba da aikinshi.
Saida yatashi daga aiki sannan yaje yasamu Jawahir tana ganinshi murmushi tasakar mashi tace ina tayaka murna.
Shima murmushin yayi yace murnar me kenan?
"yanayinka da nagani ya sa na gane ka samo wayar"
Matsowa yayi kusa da ita yace Eh hakane na samo kuma duk na saurara saidai mafi yawansu sun mutu dan naji maganarsu da sunan su da aka kira acikin recording d'in.
Fara'ar da take fuskarta ce tagushe tace tabbas hakane duk sun mutu dan dama mutane takwas ne kuma a yanzu shidda daga cikinsu sun mutu, Yaya Aliyu baya cikinsu kawai dai Ammi ta d'auki fansar kasheta da yake da hannu a ciki da kuma niyarshi ta ganin bayana, Mijina Umar ma baya da hannu a ciki, su Abba da abokanshi ne.
Jinjina kai yayi yace na fahimci haka Jawahir saidai akwai wani taimako da nakeso kiyi min.
Taimako kuma? Wane irin taimako ne?,, tajefa mashi tambaya.
"Kar kidamu yanzu zan sanar da ke koma menene.....
_____________
Bayan kwana biyu Faruk yana kwance a d'akinshi Mom tashigo tasameshi zama tayi daga gefenshi tace ya dai Faruk ba dai tunani kake ba?
Murmushi yayi tare da tashi zaune yace No Momcy bacci natashi ne.
Ohk, ina fatan babu wata matsala.
Kallon Mom d'in tashi yayi cike da k'aunarta dan ya san bata son ganinshi cikin kowace irin matsala, girgiza kai yayi yace babu komai Momcy.
Yauwa haka nakeson ji da anjima idan zaka fita zan baka sak'o kabiya kakaima Hajiya Maijidda.
Da mamaki yake