Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
ran zata tashi.
Su dukansu d'aga bulalen hannunsu sukayi suka dinga shaud'a mata ta ko'ina suke dukanta ammah ko kad'an bata motsaba kanta yana sunkuye k'asa ta runtse idanunta gam bugunta suke kamar sun samu jakka lokaci guda tasulale k'asa tafad'i saida suka ga bata iya motsi sannan suka barta nan mutum biyu yakamata suka tafi da ita d'akinta ana zuwa aka wurgata suka rufe k'ofar nan wajen tayi kwance idanuwanta a rufe gashin kanta duk ya baje mata fuska ahankali tad'ago hannunta tadafe kanta daga haka bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Ruwan sanyin da aka makaka mata a jiki ne yasa tayi saurin bud'e idanuwanta d'aya daga cikin masu tsaronsu ce abinci ta ajiye mata cikin wani d'an k'aramin kwano duka abincin bai wuce ayi loma biyar yak'are ba, a wulak'ance tace ga abincinki nan.
Tashi tayi zaune tana kallonta da idanuwanta da suke lumshewa saboda wahala har matar tajuya tatafi.
Maimakon taci abincin sai ma rarrafawa da tayi dakyar taje chan k'arshen ginin d'akin tad'age wani dutsi dan babba babba dayake ajiye cikin d'akin nata tad'auko wani d'an k'aramin littafi duk ya cumimiye me kama da diary tabud'e hannunta yana rawa tad'auko wata biro still dai hannunta yana rawa tafara rubutu chan kuma tarufe tamaida inda tad'auko tatashi tana tafiya tana rangaji takoma chan wajen da abincin yake tazauna d'aukowa tayi zata ci wata irin iska me karfi tataso a cikin d'akin k'ara jawahir tasaki nan tasulale tasume.
Barr Faruk zuwa yayi yasamu Alk'ali sukayi magana Alk'ali Jinjina ma maganar tashi yayi yace anya barrister zaka iya wannan aikin? Nifa yarinyar chan hankalina bai kwanta da itaba.
Murmushi Barr Faruk yayi yace Allah yagafarta malam hankalina ne bai kwanta da abinda ake zarginta akaiba nafiso inyi bincike intabbatar da gaskiya idan dai har nagano akwai sa hannunta a ciki toh zan janye daga tsaya mata.
Alk'ali yace toh shikenan tunda ka ce haka Allah ubangiji yataimaka.
Barr Faruk yace Ameen zanje insamu registrar muyi magana inyaso kafin azauna court a karo nagama ingama bincike akanta.
Jinjina kai Alk'ali yayi yace hakane.
Barr Faruk yana komawa gida a harabar gate d'in gidansu yaga wata irin dank'areriyar mota ko kallon motar baiyiba yazo zai wuce nan driver yai saurin fitowa yaje yalek'a ta window d'in motar daidai da Barr Faruk yayi horn dan abud'e mashi gate.
Juyowa yayi yakalli driver d'in da yace ranka yadad'e d'alla'bai ne yake son magana da kai.
'Bata fuska yayi yace wanene kuma haka?
Bud'e motar da akayi aka fitone yasa yajuya yakalli wanda yafito daga cikin motar Alhaji Mani yagani nan yak'ara had'e fuska har ya iso wajen daga saitin motar yatsaya sannu Barrister.
Batare da ya juyoba ya amsa da yauwa.
Alhaji Mani yace ina fata kaga sak'o na jiya dan ina ta Kiran wayarka inji daga gareka ammah baka d'auka.
Cikin nuna rashin damuwa yace Eh nagani kawai dai bazan iya tsaya makaba so yakamata kasamo wani lauyan.
Cikin d'aga murya yace haba Faruk meyasa zakayi min haka? Toh tsaya fad'i kud'in da kakeso inbiyaka kasan dai banda matsalar kud'i.
Wani irin kallo Barr Faruk yayi mashi kafin daga baya yaja motarshi yashige cikin gate d'in da megadi tuni ya bud'e mashi.
Alhaji Mani tsaye yayi yana bin motar da kallo cike da bak'in ciki da takaici Jinjina kai yayi tare da cize le6e yace tabbas bakasan wanene niba ammah zan fahimtar da kai,,,,juyawa yayi cikin 6acin rai yanufi wajen motarshi inda driver yai saurin binshi yaje yabud'e mashi k'ofa yashiga.
Washe gari bayan azuhur Barr Faruk yakira Bilal a waya yace yana son ganinshi a office d'inshi.
Bayan ya zo ne Barr Faruk yace yana so yarakashi gidan yari dan yagana da Jawahir.
Hankalin Bilal ba k'aramin tashi yayiba gabad'aya yanemi nutsuwarshi yarasa ji yake kamar yace bazaijeba saidai baya iya yi ma Ogan nashi musu dan haka saida yahad'e wani wahalallen miyau sannan ya amsa da toh.
Barr Faruk saida yagama wani aiki da yake sannan yakira shugaban gidan yarin sukayi magana akan zuwan da zaiyi yagana da Jawahir a matsayin shi na lauyanta meson kareta.
Bayan sun gama wayar yamik'e yace ma Bilal suje.
A cikin motar shi suka shiga suka kama hanyar prison na mata su dukansu shuru sukayi babu me magana kasancewar shi dama Barr Faruk ba me yawan magana bane, shi ko Bilal tsoro ne yataru yai mashi yawa ahaka har suka isa.
Suna isa daidai zasu shiga k'ofar Barr Faruk bai ko tsaya yi ma masu gadi magana ba yanemi yawuce su dukansu tasowa sukayi suna cewa malam Lafiya ina zakaje? Wa kake nema?
Batare da ya basu amsar tambayoyinsu ba yad'ago ID card d'inshi yanuna masu cikin sauri duk sukaja baya yawuce matan da suke zaune suna aiki nan duk suka zuba masu idanu suna kallonsu duk inda suka gifta binsu suke da ido wad'anda suke cikin Ceil ma haka suka dinga lek'osu k'ofa k'ofa suka dinga shiga duk inda aka nemi a tsaidasu Barr Faruk ID Card kawai yake nuna masu baya tsayawa dogon bayani da su, wasu ko basu tsaida su kasancewar sun san Barr Bilal ahaka har suka kai wajen wani d'aki inda me gadi na musamman akasa yana tsaron k'ofar inda daga gefen d'akinta d'akin wasu mata ne su ukku a ciki, Barr Bilal cike da tsoro yajuyo yakalli Barr Faruk yace Oga nan ne take.
Cikin nuna rashin damuwa yace toh muje girgiza kai yayi yace a'a zan jiraka a daidai nan kaje kadawo ganin yadda yatsorata yasa yace shikenan nan yawuce zai tafi megadin d'akin yayi saurin mik'ewa yanufo wajenshi yace malam wa kake nema?
ID Card din hannunshi yanuna mashi nan yai saurin bud'e mashi yana shirin shiga Megadin yace saidai ranka yadad'e...sai kuma yayi shuru Barr Faruk yana jin haka yaciro wayoyinshi daga cikin suit d'inshi yamik'a ma megadin sannan yawuce yashiga, tsaye yayi bakin karfunan k'ofar yana bin cikin da kallo wani d'an k'aramin kurkuku ne baida girma sosai kuma babu wadataccen haske a ciki Juyowa yayi yakalli me gadin yace ina buk'atar haske.
Megadi zuwa yayi yad'auko wata torch light me haske sosai yahaska d'akin nan Haske yagauraya a d'akin wucewa Barr Faruk yayi yashiga tsakiyar d'akin yahangeta zaune kanta sadde a k'asa inda gashi yabaje mata fuska tsaye yayi yana kallonta kafin daga bisani yataka ya isa wajen da take tsugunnawa yayi gabanta ganin har lokacin bata d'ago ba yasa yace Jawahir .
Shuru tayi tak'yaleshi kokad'an bata motsaba sake kiran sunanta yayi ahankali tad'ago kai takalleshi ta cikin gashinta da yake baje a fuskarta idanuwanta yakalla da sukayi jajir kamar garwashi inda fuskarta take a tamke babu fara'a ko kad'an wani irin kallo takeyi mashi,
Barr Faruk tsugunne yayi shima yana binta da kallo a karo na ukku yakira sunanta.
Cikin wata irin murya cike da k'araji tace kabar nan wajen!! tana fad'in haka ta sadda kanta k'asa inda gashin ya ida baje mata fuska.
Mik'ewa Barrister yayi cikin sanyin jiki yawuce zai fita dan tabbas baiga alamun zai samu abinda yake son samuba daga gareta saidai me yake faruwa da ita da gabad'aya tacanza anya kuwa mutum ce ita? Sake juyawa yayi yakalleta yaga still dai kanta yana sunkuye dan haka yawuce yafita, tsaye yayi a daidai k'ofar d'akin yana kallonta ta jikin k'arfunan.
Megadin wajen ne yazo yarufe k'ofar sannan yatsaya gefen Barrister Faruk yace 'Dallab'ai daman nasan mawuyacine a wannan irin lokacin ta iya yi maka magana dan lokutta da dama tana shiga cikin wannan yanayin.
Juyowa Barr Faruk yayi yakalleshi yace in ba damuwa inason samun wasu bayanai daga gareka game da ita.
Barr Bilal da yake mak'ale gefe d'aya yace a'a Oga da dai ka hak'ura kawai mun tafi.
Shareshi Barr Faruk yayi yacigaba da cewa duk abinda kasani a game da ita nakeson ji daga gareka.
Jinjina kai megadin yayi sannan yawuce yakoma wajen zamanshi nan Barr Faruk yabi bayanshi kujera yanuna mashi yazauna nan suka fara juyo sautin kukanta Barr Faruk har zai mik'e nan megadin yace a'a Barrister kar kaje dan kusan kullum sai tayi wannan kukan.
Cike da mamaki yake kallonshi yace toh minene dalilinta na kukan?
Girgiza kai yayi yace wannan ne dai ban saniba abinda dai kawai nasani a game da ita shine....
Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604 FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number d'in 09035938246_
_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_
_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_
_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/5, 15:59] Sis Nerja'art👰🏻: https://www.facebook.com/105966804349754/posts/105967661016335/?sfnsn=mo
*......FANSAN RAI.......*
_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_
*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]
_*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*_
*PAGE THREE*
Tun lokacin da aka kawo ta nan aka rufe a lokacin akwai wasu mata guda biyu masu irin laifinta na kisa an ke'bance su nan su kad'ai aka had'e su d'aki d'aya kasancewar duk wadda zakaga ankawo nan toh ta aikata babban laifi ne wanda za'ayi mata d'aurin rai da rai dan ba'a had'asu da k'ananun masu laifi, tun da aka kawota ban ta6a jin tayi magana da sauran matan biyun da aka had'esu ba dan ina lura da su sosai saidai ita take'be kanta ita kad'ai taraku'be wani lokacin tadinga kuka sosai abinda yafi bani mamaki shine idan dare yayi duk baccin da zanyi infarka sai na ganta zaune idanuwanta suna kallon wacchan yar k'aramar tagar da ke cikin d'akin kafin kaga ta kwanta bacci dawuya, yawanci zakaga ta baza gashin kanta ya rufe mata fuska kamar yadda kashiga kaganta.
sauran matan biyu ganin bata biye masu yasa suka dinga tsangwamarta ammah bata biyesu idan ma aka kawo masu abinci saidai sudauka sucinye subarta bata ta'ba d'aga kai takallesu ba nikuma ganin haka yasa nafad'a ma masu kawo abincin saboda haka ne aka dinga fitar mata da nata daban, akwai wani lokaci da aka kawo masu abinci nan abokan zaman suka cinye nasu daidai ita kuma ta d'auko nata zata ci kawai suka taso suka zo zasu janye Kwanon abincin nata sai tarik'e batare da ta kallesuba ganin haka yasa suka kalli juna suka kwashe da dariya babbar wadda daga ganinta ba alamun imani atare da ita ne tanemi tafizge kwanon da k'arfi ammah sai takasa abun ya basu mamaki ganin da hannu d'aya tarik'e kwanon ammah ta kasa k'wacewa kanta dai yana sunkuye a k'asa a fusace babbar tawanka mata mari.
Ba shiri tad'ago takalleta batare da ta saki kwanon ba ganin batada niyar saki yasa gudar tazo nan suka rufeta da duka suna bugunta ta ko'ina saida mukazo muka janyeta nan aka yi masu bulala akan laifin bugunta da sukayi saidai me wannan bulalar bata shigesuba dan sunji haushin bugun da akayi masu akanta dan haka da dare ma suka k'ara dukanta kafin su kwanta bacci kwanciyar nan da sukayi washe gari ba'a tashi dasuba koda akazo za'a fitar da su wajen aiki me tsanani da ake sakasu nan aka samesu kwance sun mutu ita kuma tana chan zaune k'arshen bango ta had'e kai da gwiwa kowa ya yi mamakin mutuwarsu nan aka fara zargin ko tana da hannu a ciki aka dinga dukanta ana tambayarta tafad'i yadda akayi suka mutu cikin k'araji tace ni ban kashesu ba, cigaba akayi da dukanta saida akayi mata jinajina sannan aka fitar da ita aka yankar mata wani k'aton fili akace tashare ko awa d'aya batayi ana zuwa aka samu wajen fes nan aka bata wanki dayawa akace tayi shima bata d'au lokaci ba aka samu ta gama saboda haka akayi tunanin ko wasu ke tayata dan haka aka tafi da ita kitchen aka bata nik'an markaden da za'a girki tunda tarik'e tafara juya kayan miyar bata tsayaba saida suka nuk'u duk mutanen wajen sukaita mamakin ganin ko alamar gajiya babu tare da ita bayan ak'alla duk rana mutum biyu akesawa sunuka ammah itako ita kadai tayi.
Haka aka dinga bata aiki iri-iri duk dan tafad'i yadda akayi suka mutu ammah tak'i akayi duk binciken da yadace ammah ba'a gane dalilin dayasa suka mutuba kuma babu kwakkwarar shedar da tanuna itace tayi kisan dan haka aka kyaleta, kasan abinda yafi bani mamaki wani lokacin ko da ankawo mata abincin yadda aka ajiyeshi haka ake zuwa a d'auka bata ta'bashi ba kuma anrasa me takeci ni kaina nasha inyi la'be ko naga abincin da takeci ammah ban gani gashi duk yadda zakaso tayi magana batayi inma tayi toh ba wata me tsawo bace,
Akwai wani lokaci da aka fita da ita za'a kaita wajen da zata gana da lauyanta Barr Mubarak ana fita tashak'e wata 'Yar aikin gidan nan da take matsa mata sosai dakyar aka samu aka k'waceta duk kacar da aka d'aureta da ita ammah nema tayi tagudu saboda haka ne aka hana fitowa da ita daga cikin d'akinta akace adinga barinta ko da lauyanta ya zo saidai yashiga yagana da ita a ciki, inba court za'ajeba ba'a fitowa da ita sai yau da naga anfito da ita ankaita ta yi aiki bansan dalilin hakan ba, ammah na fi tunanin dan ma'aikatan suna jin haushin yadda ita ake barinta bata aiki.
Ko kad'an baka ta'ba jin maganarta dan hatta lauyoyinta ma haka zasuzo suyi ta faman mata tambayoyi ammah bata basu amsa daga k'arshe ma duk sai rasasu akayi saboda hakane nafara tunanin anya mutum ce.
Ajiyar zuciya Barr Faruk yasafke tare da juyawa yakalli Ceil din da Jawahir take ciki sannan yamik'e yace nagode sosai Baba kuma ni insha Allahu zanyi k'ok'ari wajen ganin ta bani duk wata amsar da tadace.
A'a Barrister kabi ahankali dan akwai had'ari acikin rayuwarta.
Murmushi yayi yace kar kadamu Nan yajuya suka tafi Barr Bilal yana biye da shi yace barrister ka dai ji Komai da kunnenka ina fata yanzu zaka janye kudurinka nason ganin ka taimaka mata.
Girgiza kai yayi yace ina nan akan bakana zan taimaka mata.
Zaro ido yayi yace zaka taimaka mata? Toh nidai ba da niba dan ba abinda zaisa inshiga rayuwarta.
Tsayawa Barr Faruk yayi yajuyo yakalleshi yace ni zan shiga rayuwarta kuma kaima dole kashiga yana fad'in haka yajuya yawuce yanufi chan wajen motarsu.
Tsaye Barr Bilal yayi yabishi da kallo kafin daga baya yabi bayanshi suka shiga mota suna shirin tafiya wani ma'aikacin gidan yazo suka gaisa da su Barr Faruk yace Oga ya sanar da ni zuwanku ina ta jira ashe har kunzo.
'Dan guntun murmushi Barr Faruk yayi yace Eh munzo ai daman ya fad'a min baya nan toh kuma na kira wayarka ban samuba saidai shi ya yi ma sauran ma'aikatan bayanin zuwana saisa ban samu matsala ba.
Yace Eh ai sun san da zuwanka da abinda zai kawoka dafatan dai ka gama?
Eh toh kusan haka ammah zan dawo dan ban samu abinsa nake son samuba.
"Toh shikenan idan ka dawo sai kata'bo ni, godiya barr faruk yayi mashi nan sukayi sallama yaja motar sukabar gidan yarin.
Tunda yakoma gida tunanin labarin da megadi yabashi da yanayin da yaga jawahir a ciki yake tabbas har cikin ranshi yana da niyar taimakonta saidai me shima ya fara tantama akan hakan.
Wayarshi yad'auko yakira shugaban me kula da gidan yarin yace gobe zai dawo zai tattauna da Jawahir dan yanason more information game da case d'inta sannan asa agyarata asa tayi wanka wannan gashin nata agyara mata shi.
Dariya Mahadi yayi yace toh Barrister angama ammah wannan gashin nata ko angyara shi dakanta take yamitse abunta ammah shikenan za'ayi.
Bayan sun gama wayar fitowa yayi yasamu Hajiya Nuratu a parlor tana waya zuwa yayi yazauna a gefenta har tagama wayar takalleshi tana murmushi tace Son ka fito?
Murmushi yayi yace Eh Momcy d'azu ai na shigo lokacin kina sallah
Ohk ina fatan dai ka ci abinci.
Yatsina fuska yayi yace Eh Momcy na ci.
Ba dan ta yarda da maganarshiba tace Allah dai yasa dagaske kake dan nasanka bakason cin abinci.
Allah first love na ci.
"Toh shikenan na yarda d'azu mukayi waya da Nasiba ta ce kwana biyu baka je wajentaba meyasa?
Dan guntun murmushi yayi yace Momcy aiki ne yaimin yawa wata shara'a ce tasha min kai sosai saisa ma yanzu kikaga kullum ina gida ammah zan kirata a waya.
Gyad'a kai tayi tace toh shikenan Allah dai yataimaka yashige mana gaba.
Barr Faruk yace Ameen Momcy Daddy ya dawo ne?
"A'a ya dai ce min yau zai dawo idan tafiyar ta samu inko bata samuba sai jibi"
Allah yamaidoshi lafiya Momcy bari inje ina wani aikine in d'an ida.
Toh Son badamuwa Allah yataimaka.
Ameen Momcy.
Washe gari wajen k'arfe sha d'aya kasancewar weekend ne yashirya yaje gidan yari dan yagana da Jawahir a office d'in shugaban yasafka kasancewar abonki shi ne sosai bayan sun gaisa ne Mahadi yace Barrister wai dagaske zaka tsaya ma Jawahir maikudi a wannan shara'ar tata?
Murmushi yayi yace Eh insha Allahu ina da burin haka.
Shuru yayi sai chan yace kuma kana gani babu wata matsala.
Ta'be baki yayi yace bana tunanin haka.
Shikenan bari insa akawo maka ita nan,,,wayarshi yad'auko yakira wata ma'aikaciyarsu suna gama wayar yakalli Barr Faruk yace abokina gatanan za'a kawota bari ind'an fita ana jirana a waje zan turo ma'aikacinmu ko akwai abinda kake buk'ata kafin intafi?
Murmushi yayi yace bana buk'atar komai maybe kafin kadawo na gama abinda nake na tafi.
Mahadi yace Eh gaskiya ina tunanin haka dan zan dad'e ammah kakula.
Hannu yamik'a mashi sukayi musabaha yatafi.
Barr Faruk wayarshi yashiga latsawa chan yajiyo yanayin tafiya kamar ana jan mutum d'ago kai yayi yakalli k'ofar wasu matane biyu jaye da wata yarinya andaureta da kaca hannuwa da k'afafuwa dakyar take tafiya har suka shigo da ita, ido Barr Faruk yazuba mata yana kallonta cikin ranshi yace wacece wannan?
Matan ne