Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 10*
....Har lokacin zaman mu kotu yayi mukazo babu lauyan da zai tsaya min ana ta surutu akan na kashe lauyana, duk yadda akaso in amsa laifin kisan nan ammah nak'i amsawa saboda haka ne alk'ali yasake d'aga shara'ar nan da wata ukku masu zuwa inda yabada umurni da acigaba da sani aiki me tsanani a gidan yari.
Duk tsawon lokacin da nad'auka a gidan kaso muna zaune d'aki d'aya da wad'annan matan biyu watau Raliya da Rufaida har lokacin magana bata ta'ba had'ani da su ba koda daman suna nuna min tsana duk lokacin da za'a kawo mana abinci saidai sucinye har nawa, ahaka wata rana mukayi fad'a akan abincina da aka kawo min koda wannan fad'an ma Ammi ce sukayi da ita a lokacin tana jikina wanda yakaisu har suka dakeni a k'arshe ma suka yanke shawarar kasheni a cikin dare, ita kuma Ammi ganin haka yasa takashesu da daren dasafe aka tashi basu da rai,,wannan dalilin ne yasa aka maido ni wannan d'akin ni kad'ai ina cigaba da rayuwata, ana azabtar da ni aka hana adinga fita da ni aiki saidai batare da sanin shugaban gidan ba suke fita da ni suna sakani dan a ganinsu bazasu iya barina incigaba da zama haka ba kamar anmin gata ne.
Ana saura wata d'aya musake komawa kotu a lokacin ne Barr Muhsin yazo a matsayin lauyan da zai kareni ko kad'an banyi mamaki da ganinshi ba dan daman na sanshi a matsayinshi na lauyan mahaifina wanda yasan duk wani sirrin duniyarshi ta ciki da waje, tunda yazo ban ta'ba ce mashi uffan ba ya yi juyin duniya inyi mashi magana ammah na k'i har lokacin komawarmu kotu yayi muka koma haka aka gabatar da shara'a suka fafata shida Barr MB, yana k'ok'arin kareni saidai kawai inbisu da idanu har akayi aka gama inda aka k'ara d'aga shara'ar tamu zuwa wasu watanni biyu masu zuwa, nan aka maidoni gidan yari da alokacin yazame min gida idan da sabo na saba saidai duk lokacin da za'a fita da ni zuwa kotu ina jin wani irin yanayi a duk lokacin da muka fara tafiya cikin mota ina kallon mutane masu wucewa.
Haka dai Barr Muhsin yayi ta bina ammah bai samu yadda yakeso ba har aka sake wani zaman da yakasance na biyun k'arshe dan har lokacin baida k'wak'warar hujjar da zai kareni, a nan ma sake d'aga shara'ar akayi zuwa wasu watannin biyu masu zuwa a lokacin ne Barr Muhsin da aka maido ni gidan yari yazo yasameni kallona yake cike da mamaki yace Jawahir narasa meyasa kwatakwata kin kasa sakin jiki da ni nifa ba da niyar cutarwa nazo makiba taimakonki nakeson yi ammah kin kasa gane haka.
Murmushi nayi nace gane hakan abu ne mewuya domin mutane abun tsoro ne.
A cikin idanunshi naga mamaki k'arara koda mamakin bai nuna akan maganata ta farko da nayi agareshi ba saidai hakan ya faru ne saboda maganar da nayi bai zaci hakan ba, jinjina kai yayi yace hakane ammah jawahir ai kin sanni kinsan bazan zo da niyar cutar da ke ba.
Matsowa tayi kusa da shi sannan ahankali tace cutarwa ta nawa kuma? Shin ka mance lokacin da katsaya ma Abba akan kunaso kuk'wace kamfani na ta k'arfin tsiya? Ko baku bane kuka bugo jabun takardu akan kamfanin dan kawai kuga kun rabamu da su, hatta gidan Ammina kaine katsaya ma Abba wajen ganin ya k'waceshi ta karfin tsiya, idan ko haka ne cutarwa ta nawa zakayi min!....
Da mamaki yake kallonta har takai aya sannan yace jawahir duk wa yafad'a miki wannan? Wallahi ba gaskiya bane ko kad'an ban ta'ba tunanin cutar da ku ba.
Murmushi jawahir tayi a karo na biyu sannan tace ba ma wannan kad'ai ba hatta abinda kake da niyar aikatawa na sani.
Kasa cemata komai yayi yana binta da kallo kafin daga bisani yawuce yatafi.
Tun wannan zuwan bai sake dawowa ba sai bayan kwana ukku, koda yazo aka fiddo mashi ita dan sugana kallonshi tayi tace ashe zaka k'ara dawowa da ace zaka taimaka ma kanka da ka hak'ura da zuwa wajena dan bana buk'atar taimakonka.
Cikin ran Barr Muhsin yace wannan na rasa wace irin yarinya ce anya zata amince musamu abinda mukeso cikin ruwan sanyi? Chan kuma a fili yace zuwana shine daidai idan har ban taimaka makiba tabbas zan kasance acikin masu butulci mutanen gari zasu zageni a matsayina na lauyan mahaifinki ace na kasa kareki.
Cikin d'aga murya tace kaje kanuna tausayawarka ga wasu ba dai ga ni ba domin ni bana buk'atar hakan.
Jinjina kai yayi cike da mamakin maganganunta cikin ranshi yace lallai yarinyar nan da ace babu abinda nake nema a gareta da bazan ta'ba tsayawa tana min wannan wulak'ancin ba....
Jawahir tana zuwa nan a labarinta kallon Barr Faruk tayi da har lokacin yake tsaye ya tsareta da idanu d'an guntun murmushi tayi tace Barr muhsin tun bayan rasuwar Ammina baya k'asar zan iya cewa sai ma bayan mutuwar Barr Mubarak ne sannan yadawo kuma su Alh Tanimu ne suka turoshi ko ma ince Alhaji Tanimu ne yahad'a shi da sauran mutanen da sukeso suga sun mallake dukiyata koda yagane nice sukeson yin aiki a kaina ya yi farin ciki sosai domin shima akwai abinda yake buk'ata a wajena.
Wannan abun da mukayi da Barr Muhsin yasa sai bayan sati d'aya yasake dawowa bayan anfiddoni yad'auko wani Atm yanuna min yace wannan mallakin mahaifinkine yana da kud'ad'e a cikinshi kuma gab ake da arufe account d'in saboda ya kwana biyu ba'ayi amfani da shi ba kuma ba kowane yasan yana da wannan account d'inba tunda ya fi amfani da wanchan gudan, wannan ya bud'e shi ne saboda masu biyanshi bashi idan ya basu koda duk yarjejeniyar da suke akan bada bashi yana sanar da ni a matsayina na lauyanshi dan mahaifinki baya abu sai ya samu mesheda, wannan dalilin ne yasa nasan komai akan wannan Atm d'in da sabon account d'inshi.
Ta'be baki tayi tace nasan haka saidai bakasan Pin d'in da zaka ciro kud'in ba wannan dalilin ne yasa kasanar da ni?
Yanayin yadda take magana har mamaki take bashi dan tana da saurin fahimtar abu saidai bai nuna mata mamakinshi ba yace hakane inda zaki amince kisanar da ni da naje ancire kud'ad'en kafin arufe account d'in.
Kallonshi tayi a wulak'ance tace wannan ne bazai yuwu ba Barrister zanfi farin ciki ace sun rufe account d'in da dai ace kaine zaka ciro kud'in nan dan nasan kai zasu amfana.
Maganata ta 'bata mashi rai sosai ahaka yatafi yabarni.
Ya fad'a ma abokan nashi na k'i amincewa dan ina da wayo sosai koda k'arancin shekaru na, wanda yake jagoran su bayan tafiyar Alhaji Tanimu ne yazauna yatsara masu wata dubara inda suka samu wani k'wararre a wajen rubutu wanda yake da baiwa duk rubutun da yagani zai iya yin irinshi haka suka bashi irin rubutun mahaifina yayi masu, yarjejeniya ce suka rubuta akan wannan filayen da suke kawo min files d'insu insa hannu nak'i, sun kashe kud'ad'e sosai akan aikin inda Barr Muhsin yataimaka masu suka zauna har kotu akan cewa mahaifina ya siyar ma da Alhaji Tanimu filin kasancewar ansan Barr Muhsin shine lauyan mahaifina kuma ga sheda angani ta rubutu da komai yasa aka basu filayen sunyi farin ciki sosai da wannan nasarar da suka samu nan suka sanar da Alhaji Tanimu ta waya shi kuma yabasu dama da su saida ma gwamnati filayen biyu daman itace tabuk'aci hakan saboda filayen yana da girma sosai dan duk cikin filayen mahaifina babu me girmansu nan aka basu mak'udan kud'i sukaje suka raba a tsakaninsu.
Dalilin mutuwar Barr Muhsin kuma ganin bai ci nasarar samun Pin d'in a wajena ba yasa yashirya yaje wajen boka yai mashi bayanin duk abinda yakeso nan bokan yabashi wani kwalli yace da ya shafa yazo wajena duk abinda yakeso zanyi mashi nan yayi ta murna har yayanke shawarar hatta babban account d'in Abbu sai yasa nayi mashi signing ya fitar da kud'i, toh akan hanyar shine tadawowa Ammi takasheshi acikin motarshi aka tsinci gawarshi, shine dalilin da yasa ake cewa shima ni nakasheshi dan kawai ya tsaya min.....tana zuwa nan a labarin sai ganin wata irin guguwa sukayi me k'arfi tana shigowa cikin d'an kurkukun d'akin ta k'aramar tagar nan cikin sauri jawahir tamik'e tatsaya gaban Barr Faruk, su dukansu idanu suka zuba ma guguwar har tagama shigowa nan tahad'e waje guda sai ga wannan tsohuwar ta bayyana, tana bayyana tabushe da dariya.
Barr Faruk da mamaki yake kallonta tabbas itace wannan tsohuwar da yata'ba gani kuma itace yake yawan gani a mafarkin shi, muryar jawahir ce yaji ta ce Ammi menene dalilinki na zuwa nan a wannan lokacin?
Ci gaba tayi da dariyarta marar dad'in saurare me kama da haniniyar doki saida tayi me isarta sannan tadogara sandarta tafara takowa ahankali inda suke tsaye jawahir saurin cewa tayi a'a kar kimatso nan kitsaya nan!
Bata musaba taja tatsaya tana me kallon Barr Faruk da yake tsaye bayan Jawahir kamar wanda ruwa yacinunashi tayi da yatsa cikin shak'ak'k'ar murya da bata fita sosai tace kai kai kana shiga hurumina dayawa, ina gargad'inka da kadaina inko ba haka ba rayuwarka zata zama tarihi.
Saurin tarar numfashinta jawahir tayi tace baidace kisake aikata kuskure ba a karo na biyu Ammi, shin shi kinga ya yi maki kama da mugayen mutane ne? Meyasa kin cika son kanki dayawa?
Bushewa tayi da dariya akaro na biyu sannan tace tunda har ya iya zuwa yad'auko memory d'innan tabbas ya aikata kuskure sannan nice kad'ai nake da ikon iya fitar da ke daga gidan nan ammah sai kinyi nadamar maganarki.
Cikin d'aga murya tace wannan ne kuma bazai ta'ba faruwa ba Ammi kece dai yakamata kiyi nadamar kashe yaya umar da kikayi!!
Bushewa tasake yi da dariyar mugunta sannan tace kisanar da shi yayi gaugawar maida Memory Card d'innan dan wannan shine umurni na.
Fitowa Barr Faruk yayi daga bayan Jawahir har ya bud'e baki zaiyi magana nan jawahir tayi mashi nuni da yayi shuru bai musaba yaja bakinshi yayi shuru, nan tsohuwar ta d'age kanta sama nan wani farin haske yabayyana wanda daga jawahir har Faruk idanunsu suka kasa jure kallon hasken dan kar yayi masu illa, su dukansu sukayi saurin runtse idanunsu har saida jawahir taji alamun bacewarta sannan tabud'e idanunta ajiyar zuciya tasafke tare da juyawa takalli Faruk da yabud'e idanunshi a daidai wannan lokacin tace yanzu aiki ya ganka sai ka yi da gaske sannan zaka iya tseratar da kanka daga Ammi daman wannan dalilin ne yasa tun farko nakasa fad'a maka komai dan nasan Ammi bazata ta'ba barinka cikin kwanciyar hankali ba ni kaina ba barina takeba kullum cikin azabtar da ni take.
Faruk da yazuba mata idanu sai a lokacin yayi magana yace ammah jawahir meyasa take cutar da ke bayan da fari tana taimakonki, miyasa tabari har aka kawo ki nan gidan kaso kina rayuwa marar 'yanci bayan ta san duk itace me laifi ba ke ba?
Juyawa tayi takalli gefe d'aya tare da yin guntun murmushi sannan tace dalili d'aya ne yasa duk take min haka ba wai komai bane sai dan kawai na furta mata kalmar tsana sannan nanuna inaso tarabu da ni ammah a maimakon tarabu da ni shine take wahalar da ni, nikuma hankalina baya kwanciya idan har tana cigaba da kasancewa tare da ni domin gani nake duk wanda yara'beni sai ta ga bayanshi, haka taso taga bayan wata ma'aikaciyar gidan nan akan matsa ma rayuwata da tayi saida nayi mata dagaske nanuna zan kashe kaina idan har tayi mata wani abu sannan tafasa saidai duk da haka saida tatsorata ta, taimako guda ne kawai nake buk'ata daga Ammina shine kad'ai yasa nake buk'atar kasancewarta tare da ni, ina jin dad'in d'aukar fansar da take tayani bana nadamar wannan domin shine hukuncin da yadace da azzalumai irinsu Alhaji Tanimu, ko a yanzu haka aka kasheni bazan ta'ba nadama ba dan na cika burina saidai abinda ba a rasaba ammah in da so samune ace na cika gabad'aya burin nawa,,, rintse idanunta tayi wasu siraran hawaye suka gangaro mata.
Faruk rasa abinda zaice mata yayi sunyi kusan minti biyar a haka sannan yace Jawahir kikwantar da hankalinki kamar yadda nayi maki alk'awali insha Allahu zan taimaka maki yanzu dai abu d'aya yarage kisanar da ni suwanene sauran mutanen da suke da hannu a mutuwar su Abbu insha Allahu ni kuma zanyi abinda yadace, sannan zanyi k'ok'arin had'a duk wata sheda waje guda kafin lokacin zaman k'arshe yayi a kotu ammah kafin nan ina zan samu Ummah? Sannan Megadin gidanku shima ina zan sameshi?
Ahankali tabud'e idanunta tasafkesu akan fuskarshi sannan tace Ummah tana chan asibiti kwance saboda tashin hankalin da tashiga jininta ya hau sosai sannan ga mutuwar 'barin jikin dama da takamu da shi (paralyse), na ji ance har yanzu batasan inda hankalinta yakeba bata magana da kowa saidai tabi mutane da kallo.
"Ammah toh wane asibiti ne aka kaita?"
Girgiza kai tayi tace nima ban saniba kawai dai abinda nasani ina nan gidan kaso wani lokaci Ammi da tazo wajena nan take nuna min abinda yafaru na ga komai a cikin tafin hannunta Ummah tana kwance bata iya komai likitoci suna ta k'ok'ari akanta saidai har tsawon wannan lokacin bata san inda kanta yakeba, saidai duk wannan abun da nagani ban gane wane asibiti bane, sannan megadin gidan mu buzu ne ainafin shi d'an k'asar Nijar ne bayan faruwar haka yagudu yakoma gida bamu san inda yake zaune ba a chan, Alk'ali ma saida yanemi akawoshi kotu dan amsa wasu tambayoyi saidai akazo aka fad'a mashi ya gudu kuma hakan ya faru ne saboda tsananin tsoratar da yayi akan kisan da akayi ma mutanen gidan kar shima abun yashafeshi.
Barr Faruk yace shikenan jawahir kikwantar da hankalinki ni na san yadda zanyi, zanje intattara duk wani bayanai da suke wajena saidai abu d'aya da ace zan sake samun wani abu da zai k'ara taimaka min da zanfi buk'atar hakan.
Shuru jawahir tayi kamar me tunanin wani abu sai kuma chan tace akwai abu d'aya da zaka iya samu saidai samunshi kamar ba abune me sauk'i ba.
Barr Faruk yace kar kidamu fad'a min shi koma menene zanyi bakin k'ok'ari kamar yadda na iya d'auko memory d'innan.
Cikin sanyin jiki tace ba wai a wajen Ammi zaka same shi ba, wannan yana a gidan Alhaji Tanimu da ace kana da damar da zaka iya shiga gidan har d'akinshi da ka samo wayar Abba da take hannunshi dan a lokacin da aka kamani sunyi amfani da wani key da suka sata sun shiga gidanmu sun yaye duk dukiyar Abba da k'addarorin shi, hatta wayarshi ma tana wajen Alhaji Tanimu saboda duk wayar da Abba zaiyi da mutum tana recording din maganar da sukayi tsawon wani lokaci kafin voice d'in yagoge indai har ba shi Abba yagoge ba toh yana cikin wayar, har sai and'an kwana biyu sannan maganar take gogewa , sannan wayar da yake kiransu da itace a wajen Alhaji Tanimu, ahakane nake gani zaka iya samun duk wasu bayanai da kake nema saboda maganganun da sukayi yana ciki wannan dalilin ne yasa yad'auke wayar ya adanata a cikin gidanshi batare da sanin kowa ba wannan itace kad'ai zata taimaka maka kagane sauran mutanen da Abba yake tare da su.
"Ammah jawahir wannan zai yi wuya gaskiya dan bana tunanin abu ne me sauk'i shiga cikin gidanshi har inje d'akinshi inyi bincike inma zan sanar da hukuma na tabbata babu wanda zai bani goyon bayan hakan gaskiya saidai kawai muyi hak'uri da wayar nan, toh ammah idan har sai cikinta zamu samu abinda muke buk'ata taya zamu iya hak'ura da ita?,,, kanshi ne yayi ma tambayar sai kuma yasafke ajiyar zuciya tare da kallon jawahir da tatsareshi da idanu yace bansan ta yadda zan iya shiga gidanba, ya kike gani ya dace?
" Nima bansan yadda za'ayi ba saidai kawai ahak'ura"
"A'a jawahir baza'a hak'ura ba zan je inyi tunani inga hanyar da yadace inbi dan inaso ingane ko suwanene suke da hannu a ciki kafin Amminki takashesu, bari intafi koma menene zaki ji ni zanyi k'ok'ari wajen ganin na samo mafita a cikin kwana biyu bazan dawo wajenki ba har sai na samo wayar na gane suwanene suke da hannu a ciki, saidai to wayar wace iri ce yadda zan ganeta?.
Tsayawa tayi tana tunani sai chan tace fara ce zaka ganta a cikin wardrope d'inshi ta gefen dama daga chan k'asan kayanshi nan zaka ganta.
Da mamaki yake kallontwa yace Jawahir duk ya akayi kika san wannan bayan ke kina nan cikin gidan kaso? Ko kema ba mutum bace!
Murmushi tayi har saida hak'oranta suka bayyana sannan tace zan sanar da kai ammah ba yanzu ba, sannan ni mutum ce kamar kowa, kaje kawai ina maka fatan samun nasara.
Juyawa yayi yatafi cikin sanyi jiki, daga nan office d'in Alhaji Mahadi yawuce yasameshi zaune ankawo mashi wasu mata sabbin zuwa guda biyu wad'anda suke da case na kashe mijinsu ganin Barr Faruk ya shigo yasa yace ma mataimakiyarshi atafi da su asasu cikin kurkukun d'akin nan k'arami wanda wasu mata ukku suke a cikin shi amsawa tayi nan taba wasu ma'aikata biyu umurni aka tafi da su.
Bayan suk sun fita Alhaji Mahadi yace bismillah Barrister kazauna.
Bai musaba yaja kujera yazauna.
Kallonshi Alhaji Mahadi yayi yana murmushi yace ya dai barrister na ga duk ka yi sanyi dayawa ko duk case d'in jawahir d'inne yake gwagwata ka?
Ajiyar zuciya yasafke yace ba ma haka ba abokina wani taimako nakeso DPO yayi min ammah ban san yanayin kirkin shi ba ko zai fahimci abinda nakeso.
Indai akan Jawahir ne bazai ta'ba fahimta ba dan ka san laifin da aka kamata da shi, kuma indai DPO ne bana tunani zai amince maka koma menene dan yana da tsatstsauran ra'ayi da ganin shi wani ne, musamman ma da yaga