Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   68 / 74

201K to 204K   out of 220.3K words

Ya kamata kizo kafin bikki dan wata d'aya kinga yarage.
Kicin kicin tayi da fuska tace zan zo sai mun gama exams islamiyya dan next week zamu fara.
Toh menene na had'e fuska? na ji ba damuwa idan kun gama sai azo kinga ayi hidimar bikki k'anwar ango tana kusa.
Murmushi tayi tace hakane yayana.

Faruk janta yayi da hira sukaita yi har wajen k'arfe biyar sannan sukayi sallama kud'i yafiddo sosai yabata yace ta sayi abinda takeso tunda baiyo tsara ba, da dafari har ta k'i amsa tace akwai kud'i a wajenta shareta yayi yabar mata su nan sannan yaje sukayi sallama da su inna da Baba Malam su ma ya ajiye masu kud'i sosai su Yaya Nura ne suka kaishi airport yabi jirgin k'arfe biyar da rabi yakoma katsina.

Jawahir ta yi farin ciki sosai da zuwanshi haka taje talabarta ma khausar zuwan yayan nata da kud'in da yabata dan su Baba Malam taba su k'in amsa sukayi, a wajensu taga invitation d'in Faruk na d'aurin aure nan tayi Allah yasa alkhairi dan daman ya fad'a mata ba'a kaida bugo IV na 'yanmata ba lokacin da yazo saisa bai tafo mata da nata ba, batama yi tunanin anbugo na d'aurin aureba saida taganshi.




*BAYAN SATI UKKU*

Gidajen biyu aka fara hidima sosai inda kud'ad'e aka dinga ruwanu dan ma amarya ta ce ba wani program d'in da zatayi saboda yanayin da suke ciki saidai wa'azi kawai ta amince ayi.

Amarya Nasiba ta sha gyara ta yi gwanin kyau sai salk'i take da kaganta kaga amarya saboda kyaun da tayi na amare.


Ana saura kwana ukku bikki suna zaune a harabar gidansu suna hira da Faruk tace Lovely wai dan Allah Jawahir ta zo garin nan ne?
Girgiza kai yayi yace a'a.
Cike da mamaki take kallonshi tace meyasa toh sai yaushe zata zo? Zata dai halarci bikkinmu ko?
Toh wannan ne ban dai saniba dan ance min suna exams a islamiyya kinga kenan ba damar tazo.
Cikin nuna tausayi tace Allah sarki Jawahir baiwar Allah wallahi yarinyar nan tana bani tausayi gata mutuniyar kirki,, k'walla ce tacika mata idanu tace duk su Daddy sune silar jefata cikin wannan yanayin ta rasa kowa nata wace irin rayuwace wannan, taya zata kasance cikin farin ciki?

Ganin yadda tafara hawaye yasa cikin sanyin jiki yace Nasiba duk abinda kikaga ya samu bawa to daga ubangiji ne babu wanda ya isa yatsallake k'addararshi, kuma a yanzu Jawahir tana rayuwa me dad'i a wajen dangin mahaifiyarta.
Duk da haka Lovely ta yi rashi.
Kinga Nasiba kidaina sa damuwa a ranki Jawahir batada matsalar komai, mubar wannan maganar yanzu kud'in da naturo maki sun isa ko kuna buk'atar k'ari.

Girgiza kai tayi tace bana buk'atar k'ari na wajena sun isheni dan ni ba wani taron da zanyi.
Shikenan rabin ran duk yadda kikeso haka za'ayi.
Murmushi tayi tace nagode sosai Lovely.

Hirarsu suka cigaba da yi cike da shauk'i da k'aunar juna har saida aka fara kiran sallar magrib sannan sukayi sallama yatafi gida.


Ranar alhamis aka gabatar da wa'azi wanda mutane d'aid'ayane suka halarta sakamakon rashin gayyar da amarya tayi ko ma ace ita da danginta sukayi duka abokanta mutum ukku tagayyata sai 'yan uwa, amarya ta yi kyau sosai anyi wa'azi me ratsa jiki inda aka ci aka sha.

Ranar juma'a kuma akayi ma amarya lalle, inda ranar asabar aka d'aura auren faruk Sani Maishadda da amaryarshi Nasiba Sufyan Mai Nasara akan sadaki mafi daraja wanda dubban mutane suka halarci d'aurin auren kasancewarsu 'ya'yan manya yasa aurensu yazagaye cikin garin katsina da gidajen yad'a labarai ko da rabi da kwatan mutanen duk na 'bangaren ango ne dan amarya basu wani yi gayyaba saidai dangi, abokan mahaifinta ma wasu sun halarci d'aurin auren, ango baki k'in rufuwa yayi saboda farin ciki ga jama'a da suka dinga mashi Allah yasa alkhairi su Barr Nas da Barr Junaid manyan abokan ango sin sha babbar riga sune suka dinga haba haba da jama'a.



Gidajen biyu cike suke da jama'a ana ta hidima abunka da bikkin masu kud'i haka aka dinga fiddo naira.

Mutanen Kebbi tun ranar juma'a suka iso Katsina ammah banda su Jawahir da suke jarabawa a islamiyya itama ta so zuwa saidai Exams d'in tahana dan an d'aga masu ita ne da tuni sun gama a lokacin baifi guda hud'u sugama ba, Mom bataji dad'iba koda sukayi waya tace tazauna tayi jarabawarta inyaso idan sun gama sai tazo tayi masu hutu da hakan Jawahir ta mince, saidai takira ango tayi mashi Allah yasa alkhairi.


A 'bangaren Nasiba ta sha kyau har ta gaji dan gyarane ta sha shi saidai da kaganta ka san tana cikin damuwa wanda ba komai yaja hakanba sai tunanin rabuwa da gida da zatayi tafuskanci sabuwar rayuwa, Nasiha iri iri tasha a wajen mahaifiyarta da dangin iyayenta.

Da marece angwaye suka zo da motoci aka d'auki amarya aka kaita a chan gidan angonta da ke chan Goruba Road, gida ne na gani na fad'a dan tun daga tsarin ginin zuwa kayan da aka zuba mashi komai ya ji, shi kanshi Faruk part d'inshi iyayenshi sun tsara mashi sosai dan duk kayan da suke ciki saida aka kwashe aka canza mashi sabbi abunka da d'an gata.

'Yan kawo amarya sunyi santin gidan da tsarinshi inda wasu daga cikinsu suka dinga ma gidan vedio, Nasiba dai tana zaune a tsakiyar royal bed d'inta k'udundune cikin mayafinta inba hawaye ba babu abinda take.

Bayan sallar magrib jama'a suka fara watsewa yarage daga amarya sai yayyenta da k'awarta d'aya me suna Amrah, Amrah aminiyar Nasiba ce tun tashinsu hatta karatunsu tare sukayi a school guda babanta wani hamshak'in me kud'i ne zama a iya cewa yana cikin mak'arraban gwamnati, su suka sake gyara mata gida tas aka kunna turaren wuta.

Sai wajen k'arfe tara su angwaye sukazo tun kafin su shigo su Aunty Sadiya suka sa'be suka tafi aka barta tadinga kuka hatta Amrah tafiya tayi saboda kiran da aka dinga mata a gida.

Nasiba kuka tadinga yi har angwaye suka shigo duk surutan da suka dinga bata ma san abinda suke cewa ba dan hankalinta baya wajensu, Faruk ko rawar jiki yadinga yi yanaso sutafi subar mashi amaryarshi ammah suka k'i saida yaja Barr Nas gefe yace ya kamata yace sutafi hakanan dare yakeyi, shi ko Barr Nas mi zaiyi inba dariya ba koda suka dawo yakalli su Barr Junaid yace toh ku sai kuzo mutafi tun kan ango yabiyomu da ta'barya su dukansu dariya sukayi Barr Junaid yace ai naga alama angon nan ya k'agara mutafi dan ina lura da irin kallon da yake mana, toh arufe mana taro da addu'a kafin muwatse tunda mun rako ango gidanshi lafiya.
Faruk shuru yayi yak'yalesu suka dinga mashi shak'iyanci.

Cikin abokansu ne d'aya daga ciki yayi masu addu'ar zaman lafiya sannan sukayi masu sallama suka tafi Faruk yarakasu saida suka bar gidan sannan yarufe yadawo yasamu amaryarshi a inda yabarta har lokacin k'udundune take cikin mayafi tana sheshek'ar kuka.
Daga gefenta yazauna tare da yin sallama ahankali, jin shuru yasa yakai hannu yayaye mayafin nan tayi saurin runtse idanunta yace haba Hearty miye abun kuka a ciki yau fa ranar farin ciki ce agaremu godiyarmu yakamata mununa ma ubangiji akan wannan ranar da yanuna mana.
Shuru tayi nan yad'ago fuskarta yana goge mata hawaye saida yatabbatar ta daina kukan sannan yasata taje tayi alwallah sukayi sallah bayan sun gama sunyi duk abinda yadace daga nan yafita yakoma part d'inshi dan haka Nasiba tasamu damar yin wanka koda d'ar d'ar kawai take gabanta yana ta fad'uwa tana fitowa tashirya cikin sauri tagama duk abinda zatayi tahaye gadonta takwanta bata dad'e da kwanciya ba taji Faruk ya bud'e k'ofa ya shigo saurin runtse idanu tayi kamar me bacci tana ji yahau gadon yakwanta gefenta muryarshi taji saitin kunnenta yana cewa Hearty ba dai kinyi bacci ba?.
Shuru tayi nan yai murmushi tare da janyota jikinshi yana cewa ban yarda ayi wannan baccinba dan yau ranar farin ciki ne agaremu ya kamata mununa ma juna irin son da muke fad'a muna yi ma juna, shafata yafara yi
Saurin tura kanta tayi cikin k'irjinshi nan yai murmushi tare da kai hannu yakashe bedside lamp daga nan wasa yacanza.....



Washe gari Faruk lalla'bata yadinga yi nan tadinga narke mashi tana zuba shagwa'ba, breakfast daga gidansu Faruk aka aiko masu da shi tun kan sutashi bacci, tare sukayi wanka suka shirya sannan suka fito sukayi breakfast Nasiba tana ta narkewa shi ko sai rawar jiki yakeyi akanta.


A ranar bai lek'a ko k'ofar gida ba yana nan manne da matarshi indai ba masallaci zai je ba, sai magrib sannan yafita nan Nasiba tasamu damar shirya kayanta.


Bayan sallar isha'i Faruk yadawo gida nan sukayi wanka suka yi dinner sannan suka zauna a parlornshi suna kallo, Nasiba manne mashi tayi a jiki inda shi kuma idanunshi suke a lumshe kamar me bacci gabad'ayansu babu ma meyin kallon, fuskarshi taji ya tura cikin gashin kanta tare da k'ara matseta a jikinshi nan itama tak'ara narke mashi, muryarshi taji ahankali kamar me jin bacci yana cewa Hearty ina k'aunarki da dukkan zuciyata tabbas sonki a cikin jinin jikina yake ji nake kamar a mafarki yau nine tare da wadda nafi k'auna a matsayin mata agareni.
'Dago kanta tayi takalleshi tana murmushin jin dad'i tace tabbas nima ina cikin farin ciki sosai da ubangiji yamallaka min kai a matsayin miji agareni ina ji a raina na fi kowace mace dace da samun miji irinka,
shima idanu yazuba mata yana mata wani shu'umin kallo.
Saurin maida kanta tayi takwantar a k'irjinshi nan yashafa bayanta yace Nasiba indai har zaki kula da ni toh ni kuma zan nuna maki cewa babu wata mace a cikin duniyar zuciyar Faruk indai ba ke ba.

Wani irin dad'ine taji sosai dan kalamanshi sun ratsata, ahankali tace inko hakane zan baka kulawa wadda babu namijin da yata'ba samun irinshi, fiye da yadda uwa take son d'anta, zan nuna maka tattalin so da k'auna zallah dan Allah Faruk karik'eni amana.
Bakida damuwa da wannan matata yanzu sai kitashi muje anuna min son da ake min wanda yafi wanda uwa take ma d'anta.
Tun kan yarufe baki tayi saurin d'ago kai ta kalleshi, d'aga mata kira yayi nan taturo baki tace nidai a'a.
Kallon agogo yayi yace tunda dai har kika fad'a ya zama dole in gani a ido domin gani ya kori ji kinga ma yanzu dare ya yi muje kawai malama.

K'walla ce tacika mata idanu tace dan Allah kayi hak'uri kaga fa ban warkeba.
Cak yad'auketa yace ai aikin lada ne zakiyi muje kawai amaryata.
Nasiba ji take kamar tafashe da kuka dan ita kad'ai tasan irin wahalar da tasha hannunshi jiya, a bedroom d'inshi yawuce da ita saidai ji tayi ya safketa saman gadonshi nan shima yahau, cike da tsoro kamar zatayi kuka tace dan Allah kar kayi min komai Allah ciwo nake ji.
Shareta yayi yakashe bedside lamp sannan yajanyota jikinshi yarungume, ahankali cikin kunnenta yarad'a mata cewa kikwantar da hankalinki hearty babu abinda zanyi maki bacci kawai zamuyi dan nima ina tausayinki Allah dai yayi maki albarka domin kin faranta min.
Murmushin jin dad'i tayi nan hankalinta yakwanta tagyara kwanciyarta a cikin kunnenta taji yana rad'a mata kalamai masu ratsa gangar jiki ahaka har bacci yayi awon gaba da ita.



____________

Khausar kallon Jawahir tayi da take kwance ta d'age kai sama tana kallon ceiling tace wai ke sister tunanin me kike tun d'azu.
'Dagowa jawahir tayi takalleta tace ni ba tunani nakeba kawai dai ina tunanin rayuwane.
Uhm ko kuma kina tunanin zuwa Katsina dan na ji kince ma Mom da anyi hutun islamiyya zakije masu hutu.
Cikin sanyin jiki tace Khausar bazanje katsina ba a nan zanyi hutuna tunda hutun sati biyu ne aka bamu.
Kai Sister ammah dai da baki kyauta ba kinga ko bikkin Barrister bakije ba muna jarabawa lokacin, kuma yanzu sai kik'i zuwa kiyi masu Allah yasa alkhairi ko d'an man shanu musha, dan ma naga Barrister yanzu tunda yayi aure tsawon kwana biyu baku gaisaba ko fushi yake da rashin zuwanki bikkinshi.

Jawahir runtse idanunta tayi dan itama kanta abun yana damunta ta yi tunanin dalilin dai rashin zuwanta ne yasa tun ranar d'aurin aure da takirashi tayi mashi Allah yasa alkhairi basu sake wayaba, toh ko dai yana fushin da ni dagaske?

Muryar Khausar taji tana cewa yoh wa yasanar maki sai kikira kitambayeshi.
Shuru tayi bata sake cewa komai ba dan bata d'auka a fili tayi maganar ba.



A ranar da marece tana cikin game da wayarta kiran Faruk yashigo tsayawa tayi tana kallon wayar cike da mamaki cikin ranta tace yau kuma antuna da ni kenan.
Har saida takusan tsinkewa sannan tayi picking tare da yin sallama, daga chan 'bangaren Faruk da yake kwance saman cinyar Nasiba amsa mata yayi tare da cewa k'anwata fushi nake da ke.
Murmushi Jawahir tayi tace kayi hak'uri yayana na san na yi laifi kuma na baka uzurina.
'Dago kai yayi yakalli Nasiba da itama take kallonshi nan suka sakar ma juna murmushi sannan yace anya kuwa uzurin nan naki zai kar'bu bayan bakizo kika ga amaryata ba.
Daga chan 'bangaren Jawahir murmushi tayi tace Allah sarki ni, dan Allah Yayana ayi min hak'uri zan zo.
Nasiba ce tace bazan hak'uraba k'anwata har sai kinzo kin goge laifinki.
Murmushi Jawahir tayi dan ta jiyo abinda tace, Faruk ne yace kindai ji abinda tace ko? Bari ma inbaki ita kuyi magana.
Cikin jin kunya tace a'a Yaya Faruk Allah kunyarta nakeji.
Dariya yayi yace nidai babu ruwana gatanan sai k'anwar lauya tasan yadda zata kare kanta,,, wayar yamik'a Nasiba da take ta dariya.
Itama Jawahir 'yar dariyar tayi jin Nasiba ta yi sallama yasa ta amsa tare da cewa Auntyna ina wuni?
"Uhm bazan amsaba fushi nake"
Marairaicewa tayi tace dan Allah kiyi hak'uri wallahi ina son zuwa lokacin exams muke a islamiyya ammah zan zo.
Toh shikenan k'anwata na kar'bi uzurinki ya dai kamata kizo idan kun gama dan ga d'aki nan mun ware nakine kinga sai kiyi mana hutun nan kafin akoma.
Dariya Jawahir tayi tace d'aki kuma Auntyna.
Eh man mu dai muna jiranki.
Faruk ne yace kibarta hearty idan tayi wasa dakanmu zamuje har chan KEBBI mud'aukota.
Jawahir rage fara'ar fuskarta tayi tace zan zo insha Allahu Yayana ayi hak'uri.
Toh shikenan Jawahir sai kinzo muna godiya sosai.
Bakomai Auntyna nima nagode nan sukayi sallama takashe wayar, ta'be baki tayi ta ajiye wayar sannan tamik'e tafito tsakar gida tasamu Inna Mairo zaune tana cin k'uriga nan itama tazauna gefenta tad'iba tafara ci.


Faruk kallon Nasiba yayi da take rik'e da wayarshi yace k'anwarnan tawa gudun garin nan take na lura da ita bata son zuwa.
Cikin sanyin jiki Nasiba tace wallahi Lovely banga laifinta ba saboda abinda su Daddy sukayi mata basu kyautaba sun cutar da rayuwarta sun rabata da duk wani farin cikinta ni wallahi har kunyarta nakeji,,, k'walla ce tacika mata idanu ganin haka yasa Faruk yace Nasiba haka ubangiji yak'addara babu wanda ya isa yacanza k'addararshi.
Cikin muryar kuka tace kaduba kagani lovely duka yarinyar nan nawa take ammah ace jawarci take.
Kinga Nasiba banaso kiyi min 'barnar hawayenki komai yasamu bawa daga ubangiji ne banason kina shiga damuwa
Goge hawayenta tayi nan Faruk yafara lalla'bata yana lallashinta cikin dabara yasamu yarabata daga damuwar da tashiga.

___∆∆∆∆∆____

Dad kud'ad'e yafitar akayo order d'in duk kayan aikin da ake buk'ata inda yazuba ma'aikata sosai a cikin companyn Jawahir aka fara gudanar da aiki nan da nan company yafara ha'b'bakowa dan shi Dad mutum ne mekula sosai da sanin makamar aiki.



A cikin gidan Kaso su Alhaji Mansur da Alhaji Sufyan aiki ake saka su sosai ana wahalar da su babu wanda zai ce ga matsayinsu a da, sunyi nadamar abinda suka aikata sosai dan basusan rayuwa zata juye masu hakaba gashi gabad'ayansu babu wanda iyalanshi yazo dubashi, sunyi bak'k'i sun rame duk sun fita hayyacinsu kullum cikin aibata junansu suke da da sun sani kuka ko ba'a magana musamman idan suka tuna akwai ranar da ma za'a rabasu da rayuwarsu gabad'ayanta.

****** *******

Jawahir bayan ta dawo daga gidan kitso ganin Baba Malam tayi zaune shi kad'ai a bisa 'yar kujerarshi a k'ofar gida yana sauraren radio, wajenshi tanufa tatsugunna tagaisheshi yace Jawahir har an dawo?.
Eh Baba Malam.
Toh sannunki.
Yauwa Baba.
Ganin yadda tayi yasa yagane akwai magana a bakinta dan haka yace Jawahir kisanar da ni duk abinda yake cikin ranki kar kidamu zan fahimceki.
Ahankali tace am daman Baba wata 'yar alfarmar nake nema a wajenku.
Toh ina saurarenki.
Shuru tayi sai kuma chan tace dan Allah idan ba zan takura maku ba inaso ataimaka asamo min makaranta incigaba da karatuna.
Shuru yayi yana saurarenta ganin daga nan bata sake cewa komai ba yasa yace toh jawahir bazank'i ta takiba ammah da son samune zan fi so ace aure kikayi tunda kinga wanchan mijin naki ya rasu aure shine mutuncinki ammah zaki iya fara karatun kafin Allah yakawo mijin inyaso sai ki ida karatun a gidanki dan ni kinga gaskiya babu d'iyar da nake bari tayi karatu a gidan nan saidai tafara ta ida a gidan mijinta, yanzu haka kinga Khausar da Rashida an tsaida ranar aurensu watanni ukku suka rage ayi bikkin, idan hakan ya yi maki ba matsala.

Jikinta sanyi yayi cikin ranta tace chakwakiya kenan ni ina naga wani manemin aure ni da babu ma aure agabana yanzu na fi son inyi karatu inyaso daga baya idan da rabo zanyi aure.
Ganin ta yi shuru yasa yace Jawahir rayuwarki ta fi had'ari tunda kin ta'ba aure saisa nafison kiyi aure saidai komai lokacine idan Allah ya kawo maki mijin sai ayi auren.
Cike da ladabi tace toh Baba Malam nagode sosai insha Allahu zan kasance me biyayya agareku.
Cikin jin dad'i yace yauwa Jawahir Allah yayi maki albarka.
Amsawa tayi da Ameen tace atashi lafiya sannan tamik'e cikin sanyin jiki tashiga cikin gida, 'bangarensu Khausar tawuce tasameta kwance tana bacci dan haka tafito takoma 'bangarensu.
Tunda tazauna tunanin maganar Baba Malam kawai take wai ya fi son tayi aure ita kuma a yanzu bata shirya ma aureba a tsarin rayuwarta ta fi so tayi karatu tazama wani abu wadda za'ayi alfahari da ita, ammah yanzu taya ma zata iya fara yarda tayi soyayya koda ta san d'an zamanta a garin mutanen da suka dinga zuwa wajenta da sunan so suna da yawa.
Wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata ahankali tace Abba kun cuceni duk kune

68 / 74