Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 74

21K to 24K   out of 220.3K words

karo na biyu yace baizama dole hakan yakasance ba sai kabari sai antabbatar da itace d'in sannan kace haka.
Ko da ban tabbatar ba nasan itace, kai na lura bakasan matsayina ba agarin nan saisa nake fad'a kana fad'a.
Wani irin kallo Barr Faruk yayi mashi yace ban damu da matsayinka ba dan ni ina akan aikina,,,yana fad'in haka yabud'e motarshi yashiga yaja dabaya yacanza hanya,,,ta'ba hannu da Nasiba tayi yasa yai firgit yad'ago yakalleta.
Lafiya lovely naga duk ka canza wai ma tunanin me kakeyi?
Dan guntun murmushi yayi yace bakomai
Wani irin kallo tayi mashi tace ban yardaba kaidai kafad'a min damuwarka.

Dagaske sweetheart babu komai ina fata kina farin ciki sosai akan sa ranar aurenmu da za'ayi gobe?
Hannu biyu tasa tarufe fuskarta sannan tad'aga mashi kai alamun Eh.
Murmushi Barr Faruk yayi yace nima haka sweetheart, duba agogon da take manne a tsintsiyar hannunshi yayi yace Sweety bari intashi intafi kinga magrib ta gabato.
Bud'e fuska tayi cikin shagwaba tace kai lovely tun yanzu? Duka yaushe kazo da har zaka tafi.
Cike da kulawa yace kiyi hak'uri Sweety wallahi nima naso inshigo da wuri dan dai wani aiki da najene ammah gobe au jibi ashe gobe gidan cike yake jama'a.
Dariya tayi tace toh bazaka zo da dare ba?
"Eh toh zan duba ingani.
Marairaicewa tayi tace dan Allah kashigo.
Mik'ewa tsaye yayi yace shikenan Sweety insha Allahu zan shigo.
Cikin jin dad'i itama tamik'e tace yauwa lovely zanyi farin ciki sosai idan kazo,,,
Kallonta yayi yace me zaki ajiye min?
Juya idanu tayi tace abu me dad'i.
Murmushi yayi yace Toh shikenan sai na shigo,,,,rakashi tayi har wajen mota saida yashiga yatafi sannan takoma cikin gida.


Alhaji mansur dake zaune a setting room d'in aminin nashi kallonshi yayi yana murmushi bayan sun gama gaisawa yace abokina wai wanda nagani tare da Nasiba a nan waje ko shine wanda zata aura?
Oh Faruk Eh shine.
Jinjina kai yayi yace Dakyau ashe ta kwana gidan sauk'i.
Cikin nuna rashin fahimta yace ban fahimta ba minene yakwana gidan sauk'i?
Murmushi yayi nan yakwashe duk yadda sukayi da Barr Faruk yafad'a mashi.
Baki Alhaji Sufyan yasaki yana kallonshi yace yanzu Faruk d'inne yace haka? Ya akayi ma har yatsaya mata a matsayin lauya?
Hmm kaidai bari abokina nima dai ban saniba ai yaron nan baida kunya.
Jinjina kai yayi yace kabarshi mun san ta inda zamu 6ullo mashi.
Hannu yabashi suka kashe suna dariya...


*Free Page*

_Wannan littafin na kud'i ne ga duk me buk'ata zai biya d'ari biyu N200 Kacal zai turo MTN card ta wannan number d'in 09035938246 ko katuro 200 ta account number d'innan 5330055604, *NANA HALLIRU* FIDELITY BANK, idan katura ka aiko da screen shot na transaction ta wannan number 09035938246_

_Ga mutanen Niger zasu tura 300f ta wannan number d'in +22794775574_
_Gareku masoyan gaskiya_


_*GARA B'ASA! GARA B'ASA!! GARA B'ASA!!!* wannan gara'basa anyi tane kad'ai ga duk wanda keson karanta littafin *FANSAR RAI* da *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shaharariyar marubuciyar nan watau *AMINA ABBA UMAR* ga duk mai bukatar karanta duka novel's d'in biyu zai biya *N300* kadai domin samun damar karantasu cikin aminci, gareku masoyan gaskiya muna jiran ku nuna mana k'aunarku ta hanyar biyan *N300* kad'ai, idan duka biyun kakeso zaka turo kud'i ta wannan account number d'in 3092292135 FIRST BANK, ko kuma katin waya Mtn na d'aya daga cikin Numbers d'in nan 09035938246 ko kuma 07030792790, ko 07036073670, sai ka aiko da shedar biya ta d'aya daga cikin numbers d'in, sai munji daga gareku masoyanmu_






_Sis Nerja'art✍🏻_
[3/12, 19:43] Sis Nerja'art👰🏻: *......FANSAR RAI.......*



_*STORY AND WRITTEN BY SIS NERJA'ART✍🏻*_



*INTELLIGENT WRITERS ASSO....®*
[On Ward Together]


*DEDICATED TO ZM CHUBA'DO*



*PAGE TEN*

Barr Faruk bayan ya koma gida da ka ganshi kasan yana cikin tashin hankali bakomai ne yad'aga mashi hankali ba sai dan yasan kallon da Alhaji Mansur yayi mashi akwai alamar tambaya a ciki, fatan shi dai kar yazame mashi matsala a cikin maganar aurenshi.
Haka yakasance gabad'aya yakasa sukuni har dare wajen k'arfe tara yakira Nasiba a waya har suka gama hirarsu bata nuna mashi akwai wata matsala ba saboda haka yad'an saki ranshi.


Wajen k'arfe d'ayan dare farkawa yayi daga baccin da yake a razane saboda mummunan mafarkin da yayi na wannan tsohuwar da yasaba mafarki da ita ce tazo mashi a saman iska tana rik'e da wata zandamemiyar wuk'a wadda tsawonta baya misultuwa sai shek'i wuk'ar takeyi ta nufo shi shikuma yana ta gudu har takusa taddoshi nan yayi tuntu6e yafad'i gabad'aya tatafo da dukkan k'arfinta zata caka mashi sai ganin wata matashiyar yarinya yayi ta zo ta rik'e wuk'ar gashinta duk ya baje mata fuska tana cewa yatashi yaruga,,,yana zuwa daidai nan yafarka daga baccin nashi gumi kawai yake had'awa, ya dad'e a zaune yana k'ara tariyo mafarkin a cikin ranshi kafin daga bisani yamik'e yaje yayi alwallah yai sallah raka'a biyu yayi addu'a yakoma yakwanta dakyar yakoma baccin nashi.


Washe gari koda yatashi yashirya fitowa yayi parlor yasamu su momcy suna breakfast, Daddy ne yace son ka fito?murmushi yayi yace Eh Daddy nan yagaishesu sannan yaja kujera yazauna momcy dakanta tahad'a mashi nashi breakfast d'inshi nan shima yazauna yayi, ya d'an ci ba laifi yamik'e momcy tace ba dai har ka k'oshi ba?
Murmushi yayi yace wallahi momcy cikina ya cika.
"Hmm daman ai haka kake bakason cin abinci saisa gakanan sai k'arewa kakeyi.
Daddy ajiye cup d'in tea d'in da yake a hannunshi yayi yace Son kasan dai banaso kana fita da yunwa.
Marairaicewa yayi yace Allah Daddy na k'oshi kaga fa naci sosai.
Daddy yace toh shikenan yanzu zuwa anjima zan kira Alhaji Sufyan muji yadda za'ayi akan baikon ku da za'ayi subamu lokacin da zamuje dan munyi magana da abokaina su Alhaji Salisu da Alhaji Abu.
Cikin nuna jin kunya yace toh Daddy.
Momcy ce tace ina ruwan son nasan dai kana murna da ranar nan dan tunda kafito baki ya k'i rufuwa.
Cike da jin kunya Faruk yawuce yabarsu.
Yana jiyosu suna mashi dariya, bayan tafiyarshi daddy yace ma momcy Hajiya munyi magana da malam ya nuna farin cikin shi sosai dan shima daman ya damu Faruk yayi aure dan da cewa yayi yaje cikin 'ya'yan gwaggonshi yaza6a dan ya gaji da ganinshi babu aure saida nace mashi ai ya samu mata sannan.
Dariya momcy tayi tace ina ruwan malam ai yanaso yaga auren Faruk, Itama Gwaggo Harira da nafad'a mata bakaga yadda tanuna farin cikiba da tace zatazo sai nace mata ai mazane zasu sa bikkin ba mataba.
Daddy yace Allah sarki, Allah dai yanuna mana ranar bikkin nan dan kowa murna yake.
Ameen dai,,cewar momcy.


Barr Faruk yana komawa part d'inshi key d'in motarshi yad'auko da dukkan wayoyinshi sai system d'in aikinshi yafito d'aya daga cikin motocin da suke a harabar gidan yashiga Secretary yakira a waya yafad'a mashi bazai samu shigowa ba yau yasanar da su dan akwai aikin da zaije yi.

Bayan sun gama wayar tada motar yayi dagudu yabar gidan cikin k'ank'anin lokaci ya isa prison, yana isa office d'in shugaban yasafka nan suka gaisa sannan yace ya zo akan maganar fitarsu da jawahir.
Shuru shugaban yayi sai chan yace toh shikenan barrister ammah bari ahad'aku da 'yan sanda suyi maku rakiya.
A'a ba sai ka had'ani da wasu yan sanda ba naga hankalinka ya d'an tashi toh kakwantar da shi zan maido maku jawahir lafiya kamar yadda kuka ban ita.
Ajiyar zuciya yasafke yace shikenan barrister ammah dan Allah Kakula kasan yarinyar nan tana da hatsari.
Yar dariya yayi yace ku dai kuka san haka insha Allahu kamar yadda dai nayi maka alk'awali zan maidota.

Alhaji Mahadi wayarshi yad'auko yakira wata mata yace sukawo mashi jawahir yanzu.


Aiko suna gama wayar ko minti ishirin ba'ayiba sai ga jawahir ankawo, kallon Barr Faruk tayi da shima yake kallonta nan matan suka k'watsa mata tsawa sukace bazata tsugunna ba.
A maimakon tatsugunna sai ma dai zama da tayi a k'asa tare da sunkuyar da kanta tagaishesu nan duk suka amsa mata.
Alhaji Mahadi nuna Barr Faruk yayi yace nasan dai kinsan wannan lauya d'in wanda yake k'ok'arin tsaya maki toh gashinan yanaso kufita na amince mashi saboda matsayinshi ammah da badan hakaba bazaki ta'ba barin gidan nan ba har sai angama shara'a, sannan zan ja kunnenki idan kuka fita kar kisaki kiyi tunanin guduwa domin duk inda kikaje sai munsa ankamoki, ina fata kinji ni?
D'aga kai kawai jawahir tayi alamun toh batare da ta kalleshiba sawa yayi aka cire mata ankwar da take a hannunta da kafafunta.

Mik'ewa Barr Faruk yayi yace toh Alhaji bari muje.
Shikenan barrister dan Allah kakula
Murmushi yayi yace babu matsala insha Allahu.

Wucewa yayi a gaba matan suka bishi suna rik'e da jawahir ahaka har suka fito sukaje wajen motarshi bayan mota matan suka bud'e mata tashiga Barr Faruk baidamu da hakan ba yabud'e mazaunin driver yashiga, matan ne sukaje suka fad'a ma masu gadi akan oga ne yace afita da Jawahir sannan suka bud'e mashi gate.


Tunda yafara tuk'i yana kallonta ta cikin mirror tana kallon window babu wanda yatanka ma wani har suka hau titi saida sukayi nisa a tafiyar sannan Barr Faruk yace ina yakamata muje ko inkaiki gidana?
Girgiza kai kawai tayi alamun a'a.
Jin haka yasa Shima yayi shuru baisake cewa komai ba, a daidai wani shagon kaya yayi parking d'in motarshi yace minti biyu nan yafito yashiga bai dad'eba yadawo da wata Leda yabud'e gaban mota yasaka sannan yazaya yashiga yatada, ta mirror yakalleta yaga ta jingine kanta a jikin kan sit d'in da take zaune ta lumshe idanunta haka yacigaba da tafiya chan jawahir tace muje hotel.
Kallonta yayi yaga still idanuwanta suna a lumshe dan haka yakama hanyar wani babban hotel dake cikin garin katsina wanda sai d'an wane da wane yake zuwa suna isa wajen da ake parking d'in motoci yaje yai parking d'in tashi sannan yajuyo yakalli jawahir da har lokacin idanunta suna a lumshe yace kifito mushiga, ahankali tabud'e idanunta da sukayi jawur yanayinta zaka kalla kagane cewa ba wai bacci tayiba dakyar tabud'e murfin motar tafita nan shima yabud'e yafita tare da zagayawa yad'auko ledar sannan yawuce a gaba tana bayanshi har suka isa cikin hotel d'in suka tsaya a reception d'aki Barr Faruk yakama masu mai kyau da tsada na kwana d'aya koda wuni zasuyi ammah kud'in kwana d'aya yabiya sannan ya amshi key d'in d'akin.
Kallon jawahir yayi yace muje, wucewa tayi gaba yana binta a baya suka haura step sukaje wasu manyan d'akuna wad'anda suka fi na k'asan kyau room 5 yabud'e jawahir tsaye tayi tak'i shiga saida yace bismillah kishiga man sannan tashiga, a parlour tatsaya tana kallon makeken parlorn daidai lokacin da shima yashigo yarufe d'akin yawuce bedroom yabud'e shima komai fes Fitowa yayi yasamu jawahir a wajen da yabarta a tsaye ledar da yashigo da ita yamik'a mata yace ga wannan rigace kishiga ciki kiyi wanka kisaka sai kikawo wad'annan kayan naki abada awanke maki kafin mutashi tafita sun bushe, bata musaba takar6i ledar tawuce bedroom d'in cikin sauri tana shiga tamurza key sannan tafara zagaya d'akin tana binshi da kallo lokaci guda hawaye suka fara fita daga idanunta saurin goge hawayen tayi tai saurin fad'awa bathroom, ruwa tahad'a masu gumi tayi wanka saida tatisa wanka ya kai sau biyar tawanke kanta tas hatta kayan da tacire dakanta tawanke ita kanta saida taji wani iri da taga yadda sukayi, bayan ta gama a cikin toilet d'in tashanyasu tafito, wani irin sanyi ne taji yana ratsata da tayi wankan ledar da Barr Faruk yabata tabud'e taga jallabiya ce me gyale a ciki nan tad'auka tasaka saida tagyara kanta sannan tayi sallah bayan ta gama zuwa tayi tabud'e k'ofar takoma saman gado takwanta tare da runtse idanunta jinta take duk wata iri.

Barr Faruk da bayan shigarta zama yayi a parlorn har saida yaji anfara kiran sallar azuhur sannan yatashi yarufe d'akin da key yaje masallaci bayan ya dawo kiran waya yayi yasa akawo masu abinci koda aka kawo nan yazauna yaci nashi yabar ma jawahir nata idan tafito taci ammah har yagama bata fitoba dan haka yad'auka yanufi bedroom d'in knocking yayi da mamaki yaji k'ofar a bud'e turawa yayi a hankali yashiga sai ganinta yayi kwance saman gado tayi rufa da blanket kanta ne kawai a waje, kallo d'aya yayi mata yad'auke kai yaje saman bedside ya ajiye mata abincinta yawuce zai tafi har ya juya sai jin muryarta yayi ta ce bana buk'atar abincin, juyowa yayi yakalleta still dai idanuwanta a rufe yace kina nufin haka zaki zauna da yunwa bazaki ci komai ba.
'Dan guntun murmushi tayi tace kar kadamu da cina kaje kawai kaci idan ka gama sai kazo inbaka tarihin nawa.

Cike da zumud'i yace ni na gama Indai kin shirya toh sai mufara,,zuwa yayi yazauna bisa wata 1 seater dake opposite d'in gadon, shuru jawahir tayi tak'i bud'e idanunta bare yasa ran zata tashi tafara,,cikin ranshi yace anya kuwa zata fara yanzu? Bai gama tunanin ba yaji ta ce ka k'osa infara ko?
Da mamaki yake kallonta kamar tasan abinda yake cikin ranshi.

Bud'e idanunta tayi tasafkesu akanshi tace dafatan ka shirya yanzu infara maka.

D'auko jakkar laptop d'inshi yayi yafiddota a ciki yakunna sannan yace na shirya.

'Dan guntun murmushi tayi tare da d'aga kanta tana kallon ceiling tace dafarko dai kamar yadda kaji ko kasani mahaifina ba 6oyayya bane a garin nan nasan kana jin sunanshi Alhaji Muhammad Maikudi,,,

Alhaji Muhammad mai kud'i dan asalin garin funtua ne dake cikin nan k'aramar hukumar katsina, Malam Sani da Malama Ramatu sune iyayensu, 'ya'ya biyu ubangiji yabasu a duniya daga Mu'azu shine babba sai k'anenshi Muhammad watau mahaifina.
Mahaifinsu Malam Sani yana da rufin asirinshi ba laifi dan d'an kasuwa ne yana da d'an shagonshi da yake siyar da yan kayan miya Alhamdulillah yana samu sosai dan zan iya cewa duk yawancin yan ungunwarsu wajen malam Sani me kayan miya suke siya har ma da yan k'etaren unguwar dan kayan miyarshi suna da sauk'i ga kyau,

Tun tashin Muhammad yakasance mai son karatun arabi da na zamani inda kuma d'an uwanshi yakasance akasin haka baison karatu, mahaifinsu malam Sani kullum cikin nasiha yakeyi mashi akan yadaure yayi karatu kamar yadda d'an uwanshi yakeyi, ba dan ya soba ya amince yashiga makaranta suka kasance aji d'aya da k'anenshi saidai hakan baisa yadinga karatun ba dan duk gwajin da za'ayi masu baya wani ci sosai sa6anin k'anenshi da yake maida hankali dan dama shi yana da burin karatun a ranshi duk wata kyauta da za'a bada Tun daga primary har secondary yana cikin wad'anda za'a ba saboda k'ok'arinshi da maida hankali a karatunshi saboda haka ne yasa yayanshi yatsaneshi kiri Kiri yake nuna mashi bak'in ciki a fili shikuma dayake Allah ya yi shi mai hak'uri da son d'an uwan nashi dan haka cikin kyautukan da yake samu yadinga bashi wasu ko yaraba rabi yabashi duk dan azauna lafiya.

Bayan sun gama secondary school takardun Muhammadu sunyi kyau sosai inda shikuma Mu'azu nashi zaiyi gyara mahaifinsu ya nuna bak'in cikinshi da rashin cin d'an nashi Mu'azu ammah da yake shi mutum ne mai yadda da k'addara dan haka yace zai sake biya mashi yagyara shiko yace inaa bazaiyi ba babu wani karatu da zai k'ara yi yanzu dan shi ya gama nashi kasuwanci yake da burin yi dan haka malam Sani yasama mashi shagon haya acikin kasuwa yazuba mashi yan provision inda shikuma Muhammadu yanuna karatu yakeson cigaba dan haka mahaifinsu yasama mashi admission na Degree a A.B.U Zariya yaje chan yana karatunshi hankali kwance.

Mu'azu ko ya maida hankalinshi da Sana'ar shi har yasamu budurwa wadda yakeso yace ma Mahaifin nasu shi aure yakeson yi, da fari da Mahaifin ya ce yabari yak'ara tara yan kud'i sannan yayi maganar aure ammah fafur yanuna a'a dan haka Mahaifinnasu ya amince akaje akayi magana gidansu Fatima aka tsayar da ranar aure.

Shiko Malam Sani baida buri akowane lokaci sai na son aika ma danshi Muhammad kud'i da ya d'an tara dan saboda ya san bazai ta'ba zuwa yanema ba dan shi yana da zurfin ciki ko da yana son abu toh zai barshi bazai nuna ba saidai idan ya ga yazama dole ne makaranta ake buk'ata sannan zaiyi ma Mahaifin nashi magana yatura mashi.

Ahaka har yaje aji biyu a karatunshi inda shikuma Mu'azu akasha shagalin bikkinsu amaryarshi tatare a wani gidan haya da yakama masu, Muhammad lokacin ya so yazo bikkin nashi saidai suna exams ne dan haka yahak'ura saida suka gama yadawo gida.


Yana aji ukku ne Allah yayi ma Alhaji Sani rasuwa ta dalilin hadarin mota da sukayi akan hanyarshi tadawowa daga k'aramar hukumar ajiwa lokacin ya je dubiyar wani abokin kasuwancinshi da baida lafiya sukayi accident saidai aka maido gawarshi gida, ba k'aramin tashin hankali iyalanshi suka shiga ba dan ita Inna Ramatu har suma saida tayi, shiko Muhammad gani yake ya fi kowa shiga damuwa da burinshi bai cikaba mutuwa tarabashi da mahaifinshi dan ya ci burin yagama karatu yasamu aiki iyayenshi suci moriyar wahalar da suke sha wajen karatunshi.

Tunda yadawo gida saida akayi arba'in lokacin mutuwar ta lafa sannan Inna Ramatu tamatsa mashi yakoma makaranta da zai tafi tatura shi gidan yayan nashi yafad'a mashi zai koma ammah Mu'azu babu abinda yabashi saidai cewa da yayi Allah yakiyaye.
Yan kud'in da Inna Ramatu tahad'a mashi dasu yakoma makaranta, basu je mashi ko inaba suka k'are dan ko da siyan handout akabar mutum ya wahala,

Koda yakoma makaranta baifi wata d'aya ba 'yan kud'in da yaje da su suka k'are ganin yanayin da suke ciki shi da mahaifiyarshi na rashi yasa kawai yafara shiga kasuwar garin duk ranar da take ci yana zuwa yayi dako yasamu d'an abinda zai rufa ma kanshi asiri saida yahad'a da tsaron shagon wani idan sun tashi lecturer yake zuwa ahaka har yasamu da cukucuku ya had'a degree d'inshi dan yayanshi bai taimaka mashi da ko kud'in mota inma Inna Ramatu tamatsa mashi yatambayeshi ko ya tambaya saidai yace baida kud'i da dai ace ya yi mashi magana dawuri da ya bashi yanzu hidima tayi yawa.
Haka sukaitayi har yagama karatunshi bai ta6a d'aukar Naira d'aya yabashiba kuma shima bai ta6a damuwa ba.

Bayan ya gama Mahaifiyarsu ta so yafara neman aikin gwamnati ammah yace a'a sai ya yi masters d'inshi, Yaya Mu'azu fad'a yadinga yi yace haka zai k'are wajen bauta ma boko Maimakon yakama aiki yayi aure dan shi a lokacin har matarshi ta haihu d'anta namijii ya ci suna Umar,,,wasu siraran hawaye ne suka gangaro

8 / 74