Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar RAI Complete 1&2 Complete Hausa Novel by SIS Nerja'art

Author :  SIS NERJA'ART Category :  African Stories & Novels

Chapter   25 / 74

72K to 75K   out of 220.3K words

wani wajen suje suyi kisa saboda k'auran sunan da sukayi yasa mutane suke tsoron dajin.



'Yan fashin zaune suke suna zuk'ar shisha inda iskan da ke cikin dajin yake kad'asu, daga chan gaba da su kad'an ogansune zaune a bisa kujera hannunshi rik'e da k'walbar giya ya kame yana sha, su dukansu sun duk'ufa suna sharholiyarsu nan suka fara jiyo k'arar tafiya kamar ana tun karo wajen da suke, saurin ajiye shishir sukayi kowa yad'auko makaminshi yarik'e a hannu, inda ogansu yanuna ko inkula hankalinshi kwance yana ta shan giyarshi, suna nan a tsaye suna ta mazurai suna jira suga wane me k'arancin kwananne zai kawo kanshi, sun dad'e tsaye a haka sai ganin 'bullowar wata kyakkyawar budurwa sukayi basusan lokacin da suka saki baki suna kallonta ba, sanye take cikin wata gown wadda takama jikinta sosai inda gashin kanta yake baje a tsakiyar bayanta kyakkyawar fuskarnan tata ta sha makeup tafiya take ta jan hankali tatunkarosu tana masu murmushi me jan hankali su dukansu sun shagala suna kallonta har saida takusa isowa wajen da suke sannan sukayi saurin nunata da bindiga sukace kitsaya nan idan har kika matso zamu harbeki.
Cikin nuna rashin damuwa taja tatsaya tare da waigawa takallo ogansu da yake zaune har lokacin yana shan giya, fuskannan tata d'auke da murmushi tabud'e baki cikin siririyar murya me dad'in saurare tace idan ba damuwa inaso kubani dama inyi magana da oganku.
Juyawa sukayi suka kalli ogan suna shirin yin magana sai jin muryarshi sukayi ya ce kubarta ta iso muji da me tazo.
Saurin matsawa sukayi suka bata hanya tawuce tana karairaya duk suka bita da kallo suna lasar le'be, tana isa gabanshi taja tatsaya idanu yazuba mata yana kallonta daga sama har k'asa ganin haka yasa tajuya baya sannan tajuyo, ajiye kwalbar giyar yayi cikin muryar maye yace wacece ke? Me yake tafe da ke wajena?

Maimakon tabashi amsa sai fad'awa da tayi jikinshi tazauna tana cigaba da yi mashi murmushin nan nata me saurin rikita mutun.
Ganin haka yasa yabushe da dariya yace da alama wannan 'yar hannu ce tamuce.
Ganin haka yasa su ma suka bushe da dariya sannan suka koma suka zauna, hannu yakai yafara shafa gashin kanta yace gaskiya kina da kyau sosai,
Fari tayi mashi da idanu tace nagode.
Ajiyar zuciya yasafke yace lallai ke d'in ta dabance, hannunshi yad'aura bisa wuyanta tayi saurin janye wuyanta, gashinta yadamk'o dak'arfi yana shirin tura fuskarshi a wuyanta tureshi tayi da dukkan k'arfinta tamik'e tsaye tana jifanshi da wani mugun kallo.
Kyalkyacewa yayi da wata muguwar dariya yace tunda har kika kawo kanki ya zama dole kiyi abinda nakeso, hannu yakai zaya jawo ta tayi saurin yin baya tare da girgiza kai.
Gyatsa yayi sannan yajuya yakalli yaranshi da suke tsaye cirko cirko cikin muryar maye yace kukaimin ita cikin bukkata, su dukansu suka kwashe da dariya sukace angama oga ashe har muma yau zamu yagi rabonmu daman mun kwana biyu bamu samu namaba, juyawa tayi takallesu taga sun nufota gadan gadan nan tanuna su da hannunta sai ga wata irin iska ta tashi me kama da guguwa su dukansu saida suka tsorata sukayi saurin sa hannu suka rufe idanunsu dan kar ta shiga, bud'e baki tayi tasaki wata irin razanannar k'ara wadda tasa gabad'ayansu saida suka firgita suka juya zasu bar wajen sai ganin wani haske sukayi a gabansu dan haka suka had'e waje guda kowa yana raba idanu, ogansu kuma yunk'urin tashi yayi daga kujerar da yake zaune nan iska tajashi da k'arfi sai gashi a kusa da sauran 'yan uwanshi 'yan fashi,
Nuni tayi da hannunta a sama tafara karanto wasu irin d'alasimai sai ga wata k'atuwar macijiya ta bayyana a wajen su dukansu saida suka tsorata suka san yau sun gamu da gamonsu, bushewa tasakeyi da dariya nan tayi girgiza tazama wata k'atuwar dodanniya, murya suka fara jiyowa wadda tasa gabad'aya dajin yadinga amsawa ji sukayi ana cewa kuuuu azzalumai ban zo wajenku domin komai ba sai dan d'aukar *FANSAR RAI* zan kasheku kamar yadda kukaga bayana ku d'in azzalumai ne bazan ta'ba barinku ba.

Su dukansu tsaye suke sunaso suyi magana ammah tsoro ya hana babu wanda bai saki zawoba a wajen da suke tsaye, macijiyar ce sukaga tana tunkaro inda suke tsaye dukkansu yunk'urin guduwa sukayi ammah sai ji sukayi kasala ta safkar masu har macijiyar ta iso wajensu tana zuwa tasakar masu tsartuwa nan duk suka zube k'asa kowa yana jijjiga suna safke numfashi.

Ganin haka yasa tasake bushewa da wata razanannar dariya me kama da kukan hadari, sannan tanunasu da hannunta sai ga wasu k'ananun macizzai sun fito daga bakin wannan babbar macijiyar suna fitowa suka nufi wajen da mutanen nan suke kwance suna zuwa suka fara sarinsu, nan 'yanfashin suka fara ihu hayak'i yana fita daga jikinsu, sun dad'e a haka kafin daga bisani duk suka mace, saida tatabbatar da babu me motsi a cikinsu sannan lokaci guda ta'bace ita da macizzan.



***** *****
Barr Faruk tunda yabaro gidan Alhaji Sufyan cikin 'bacin rai ya isa gida saidai duk da haka baiyi nadamar hakan ba saboda akowane lokaci ashirye yake dan ganin ya tafiyar da aikinshi yadda yakamata, yana isa a k'ofar gate gidansu sai ganin motar Barr MB yayi anfaka ta, tsayar da motarshi yayi tare da fitowa yajingina a jikinta yana jira yaji da me yazo.
Ganin haka yasa Barr MB yafito yanufo wajen da Faruk yake tsaye yana murmushi yace ashe na zo a daidai yanzu nake shirin kiran wayarka sai gaka.
Shima murmushin yayi yace gaskiya ka taki sa'a.
Hannu Barr Mahamud Bello yamik'a mashi sukayi musabaha sannan yace ya aiki?
Murmushi yayi yace Alhamdulillah gashinan muna ta tayi.
Ajiyar zuciya yasafke yace hakane saidai nasan ka yi mamakin zuwana wajenka ko?
Ta'be baki Faruk yayi yace ko d'aya dan nasan zuwanka yana da nasaba da Alhaji Mansur a matsayinka na lauyanshi da wad'anda suke k'ara.

Jinjina kai yayi yace tabbas hakane ammah Barrister ka bani mamaki ace wai kaine da kanka kake zarginsu abun kunyanma har da surukinka dan kawai sun hanaka auren d'iyarsu, hakan bai dace da kai ba dan duk garin nan inzaka kewaye babu wanda bai san arzik'in nan nasu bane ko da Alhaji Muhammad yana da kud'i ammah bayada kud'in da zasu nemi suci dukiyarshi ya kamata kasan irin abinda yake fitowa daga bakinka a matsayinka na lauyan wadda ake k'ara.
Murmushi ne yabayyana a fuskar Barr Faruk yazuba mashi idanu yana kallo har saida yakai aya sannan yace dakyau Barrister aikinka yana kyau, saidai maganar da kayi akwai gyara a cikinta dan ko da ace kowa zai yarda da cewa dukiyarsu ce toh ni bazan ta'ba yarda da hakan ba dan nasan ba dukanta bace dukiyarsu, kaidai kawai katsaya a matsayinka baka san komai ba akai kabarni da su kawai dan duk abinda zaka fad'a ba zan ta'ba yarda ba dan ni nasan abinda baka saniba, am ina da abunyi idan babu sauran abinda yakawoka zaka iya tafiya saidai ince sai munhad'u a kotu.
Murmushi Barr Mahamud Bello yayi yace toh shikenan tunda ka ce haka ammah Barrister ya kamata kabi a sannu akan su Alhaji Mansur gudun kar wani abu yafaru.
Jinjina kai kawai yayi yabud'e motarshi yashiga sannan yayi horn megadi yazo yahangeme mashi gate d'in gidansu yacinna motarshi a ciki inda Barr Mb yashiga tashi motar yakama gabanshi......







_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*



*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]

_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_


_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_


_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_




*PAGE 15*

Alhaji Mansur da yake manne da waya a kunnenshi duk ya saurari komai su Barr Faruk suka tattauna kasancewar sa Barr MB yayi yakirashi a waya yadda zai saurari hirar tasu, yana gama saurare wurgi yayi da wayar tare da komawa yazauna yace lallai yaron chan ya cika taurin kai idan har bai janye k'udurinshi ba ya zama dole inyi wani abu akanshi dan bai isa ya'bata min duk wani shirye shirye na ba.
Toh ammah ta ya yakamata in'bullo mashi? Shuru yayi yana tunani sai kuma chan yayi murmushi yace idan ka san wata bakasan wata ba nan yatashi yad'auko wayarshi.







Washe gari yana office d'inshi zaune ya d'age kanshi sama yana kallon ceiling a ka ga yanayinhi ka san tunani yake, yana nan a haka sai ji yayi anturo k'ofar d'akin anshigo.
'Dago kai yayi dan ganin wanene yashigo batare da annemi iziniba karaf suka had'a idanu da Nasiba yanayin yadda tashigo babu alamun fara'a a fuskarta yasa yagane akwai wata a k'asa, zaune yayi yana kallonta har ta iso wajen table d'in da yake gabanshi, kujera yanuna mata yace bismillah kizauna.
Zare glass d'in da yake fuskarta tayi tare da yatsina fuska tace ba wannan yakawoni wajenka ba Faruk.
Murmushi yayi cikin ranshi yace na san za'a rina,,, ajiye jakkarta tayi saman table d'in sannan tace na zo ne inyi maka godiya akan abinda kayi ma mahaifina Faruk tabbas kai butulu ne ban ta'ba sanin haka ba sai a yanzu, na yi da nasani da har na amince namallaka maka zuciyata, ina maka kallon mutumin kirki wanda nakeso yakasance abokin rayuwata ashe har akwai ranar da zakaje kakalli tsabar idanun mahaifina kaci mashi mutunci har kazargeshi akan kisan wani.
Dafe kanshi yayi da hannuwanshi duka biyu jin tana neman tak'ara mashi wani zafin da yake saman kanshi, muryarta yaji ta fashe da kuka dan haka yad'ago kanshi cikin sanyin murya yace haba Nasiba meyasa zakice haka bayan ke bakisan abinda yake faruwaba.
Cikin d'aga murya tace taya zan san abinda yake faruwa bayan ka ci mana mutunci tabbas kai butulu ne Faruk kuma insha Allahu kamar yadda kaso katozarta mahaifina ubangiji bazai ta'ba baka daman haka ba, na yi nadamar saninka a rayuwata Faruk.
Saurin mik'ewa yayi tsaye yace wai wace irin maganace kikeyi haka Nasiba baidace kice hakaba ni fa akan aikina nake ba wai tozarta mahaifinki nakeson yi ba.

Koma me zakace kafad'a Faruk nima kaina ban wuce matsayin da zaka tozartani ba, ashe wannan dalilin ne yasa kace insamo maka number d'in Alhaji Mansur dan kawai sun hanaka aurena shine zaka 'bullo masu ta wannan hanyar har kana ik'irarin cewa gidan mahaifina ba nashi bane, wai me yake damunka ne haka faruk!?
Ajiyar zuciya yasafke yace Nasiba yakamata kifamceni duk yadda kike tunani ba haka bane.
'Daga mashi hannu tayi fuskarta sha'be sha'be da hawaye tace babu abinda zanji daga gareka bayan wanda kayi ahakan ma nagode Faruk a yanzu na ida tabbatarwa kai d'in ba masoyina bane mutum ne meson tozarta ni, ashe nikad'ai nake haukana na d'auki soyayyata na baka da zuciya d'aya kaikuma a wajenka ba hakaba nagode sosai Faruk na tayaka murna da kayi silar zubar da hawayena sannan kayi yadda kakeso rayuwace ubangiji yana sane da duk abinda kake aikatawa, na barka lafiya, jakkarta tad'auka cikin sauri tajuya tafita tabar d'akin.

Dunk'ule hannuwanshi yayi yabuga a jikin table d'in da yake gabanshi yace meyasa haka Nasiba? Meyasa bazaki saurareni ba? Hannu yasa yashafa kanshi tare da wucewa cike da tashin hankali yakoma bayan kujerarshi yatsaya nan yafuzgar da wata irin iska me zafi daga bakinshi kan kace mi ya fara zufa, wayarshi ce tafara ringing ammah ko kallon wajen da take ajiye baiyi ba, komawa yayi yazauna tare da dafe kanshi da dukkan hannuwanshi biyu cikin d'aga murya yace daman nasan ba kowane zai fahimceni ba tabbas wannan shine matsalar da jawahir take ji min tsoron inshiga, na rasa masoyiyata adalilin case d'inta ammah ya zama dole inyi abinda yadace dasannu zan maido da martabar soyayyata, nasiba bazan ta'ba bari inrasaki ba zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin kowa ya fahimceni, ya fi awa d'aya a nan zaune yana ta 'yan tunane tunane kafin daga baya yadanna k'ararrawa masinja yashigo wasu files ne yad'auko yamik'a mashi yace wad'annan kakaisu office d'in Director sannan yamik'e yahad'a duk abinda yake buk'ata yafita, tunda yafito daga office d'in yanufi harabar da motocinsu suke wata bak'ar mota ce Jeep yaga a kusa da tashi motar saboda glass d'in bak'ine yasa bai lura da mutanen da suke cikiba saidai bai ta'ba ganin wani ma'aikacinsu a cikin motar ba, ganin ta d'an tare mashi hanya yasa yanufi wajen zaiyi knocking d'in glass dan amatsa yafitar da tashi motar, tun kan ya isa sai gani yayi anja motar antafi dan haka shima yashiga tashi yakama gabanshi.


Yana cikin tuk'i Daddynshi yakirashi a waya yace kazo gida kasameni yanzu murmushi yayi yace toh Daddy ganinan zuwa ina hanya.
Bayan sun gama wayar cikin ranshi yace Allah yasa dai lafiya.
Yana isa yasameshi a parlornshi zaune ganinshi yasa yanuna mashi waje alamun yazo yazauna.
Fuskarshi d'auke da murmushi yace toh Dad, kallon drink d'in da yake saman table yayi ganin haka yasa Dad yad'auko cup yatsiyaya yamik'a mashi, amsa yayi tare da yin godiya sannan yafara sha.
Gyaran murya Alhaji Sani yayi sannan yace Faruk me yahad'aka da Alhaji Sufyan.
Saurin janye kofin yayi daga bakinshi yace na'am Dad.
'Daga kai yayi yace na san ka ji abinda nace.
Shuru yayi cikin ranshi yace watau har ya sanar da Dad,, muryar Dad yaji ya ce kai nake saurare.
'Dagowa yayi yakalli mahaifin nashi yace babu komai Dad.
A'a bazakace babu komai ba kaga Faruk banson rigima kafita harkar Alhaji Sufyan dan shi ba abokin yinka bane nayi mamaki sosai da naji wai kaine kaje har gida kaci mashi mutunci har kana fad'a mashi cewa wai gidanshi ba mallakinshi bane, wa ya aikeka ko ma ince ina kaji hakan?
Jikin shi sanyi yayi sosai yace kayi hak'uri Dad ina akan aikina ne.
"Dakata banason irin haka kar insake ji ka shiga harkarshi dan shi d'an siyasa ne ka san yana da kud'in da zai mallaki fiye da wannan gidan, sannan katsaya iya aikinka babu ruwanka da duk abinda bai shafeka ba.
Har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan ya san ba lallai ne Dad yafahimci abinda zai fad'a ba, Dad yace ka yi shuru.
Toh Dad insha Allahu.

Yauwa haka nakeson ji Son.
Murmushi yayi yace toh Dad.
Kallon agogo Dad yayi yace bari intashi daman fita zanyi natsaya jiranka.
Shikenan Dad sai ka dawo.

Zaune yayi wajen har mahaifin nashi yatashi yatafi sai kuma chan shima yamik'e yakoma part d'inshi, yana jin babu dad'i a cikin ranshi.



______Da dare yana kwance yana ta tunanin yadda zai 'bullo ma lamarin dan hankalinshi ya tashi sosai da aka saka mahaifinshi a ciki saboda indai dan shine kar mahaifansa susan komai a game da wannan case d'in, yana nan kwance bai saniba har k'arfe d'aya tagota, dariya ce yafara jiyowa a falon d'akinshi tana tashi, saurin tashi yayi zaune cikin ranshi yace wannan dariyar fa?
Ji yayi ancigaba da yi babu k'ak'k'autawa dan haka yakunna fitila tare da mik'ewa tsaye yanufi hanyar fita, yana bud'e k'ofar bedroom d'in sai yaji kamar takun mutum ana tafiya a chan babban parlor sautin dariyar yana cigaba da tashi kasancewar da k'arfi akeyinta, ji yayi kamar yajuya yakoma bedroom d'inshi sai kuma yafasa dan yanaso yaga me yin dariyar dan haka yabud'e k'ofa yafita daga saman matattakalar bene yatsaya yaji ana cigaba da taku na tafiya ammah baiga kowaba dan haka yagane Ammin jawahir ce har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa saboda kar su Dad sujiyo dan haka yajuya yakoma part d'inshi, yana shiga bedroom yamaida yarufe juyowar da zaiyi sai ganinta yayi a tsaye bayanshi cikin siffar da tasaba bayyana saidai wannan karon gashin nan nata farine kal har yana ta'ba k'asa saboda tsawonshi tana tsaye da 'yar sandarta tana kallonshi da k'wala k'walan idanunta wanda girmansu sun kai na goruba saurin jingine jikinshi yayi a jikin k'ofa cikin dakiya yace mi yakawo ki wajena?
Bushewa tayi da dariya wadda tasa gabad'aya d'akin saida ya amsa, saida tayi me isarta sannan tabud'e baki cikin kakkausar murya tace aduk lokacin da naso ganin mutum ina bayyana a gareshi kuma kaima ka san haka, bana neman umurni bare har abani izini,,, dogara sandarta tayi tana tafiya a dudduk'e har saida taje tsakiyar d'akin sannan tatsaya tare da juyowa takalleshi yana nan tsaye a inda yake, sake bushewa tayi da wata dariyar tayi wadda ta wannan karon ta sha bambam da ta farko da wannan jinta yayi kamar kukan jaki saboda rashin dad'inta saida tayi me isarta sannan tace babu abinda zaka iya yi akan case d'in su Alhaji Mansur domin wuk'a da nama duk suna a hannu na sai na kashesu kamar yadda sukayi silar barina duniya ni da mijina sannan zan tseratar da d'iyata daga gidan kaso da kaina.
Cikin nuna rashin tsoro yace wannan ne bazaki iyaba domin tun farko yakamata kitseratar da ita ammah kika kasa, sannan maganar su Alhaji Mansur na riga na maido case d'in a hannuna ni yadace inwanke jawahir a idanun duniya sannan inyi silar da zaisa arufesu a gidan yari ayi masu d'aurin rai da rai.
Sake bushewa tayi da dariya sannan tace bakada iko a wannan hurumin domin nice me power, ina sake gargad'inka akan kajanye hannunka a cikin case d'in nan domin tseratar da kanta daga bala'o'in da suke tunkarar rayuwarka, su Alhaji Mansur bazasu ta'ba barinka ba zasuyi k'ok'arin ganin sunga bayanka ammah idan har ka za'bi mutuwarka akan komai toh shikenan saidai duk wannan abun da kake bai ta'ba burgeni ba dan nasan wuk'a da nama suna a hannuna.

Nunata yayi da yatsaya yace ke d'in azzalluma ce bawai kina taimakon jawahir bane kawai dai kina cutar da rayuwarta ne gashinan ta dalilinki kowa guje mata yake.

Wata irin razanannar k'ara tasaki wadda tasa har saida akayi k'aramar girgizar k'asa a cikin d'akin.
Saurin toshe kunnuwanshi yayi har saida k'arar talafa sannan yasakesu.

Nunashi tayi da yatsanta cikin 'bacin rai tace idan har kacigaba da jifata da munanan kalamai zan d'and'ana maka azabata.
Bud'e baki yayi zaiyi magana sai ji yayi kamar anrik'e bakin nashi, juyawa tayi baya tace bana buk'atar jin komai daga gareka, nan tafara takawa tink'is tink'is tanufi wajen da ya ajiye

25 / 74