Author : SIS NERJA'ART Category : African Stories & Novels
briefcase d'inshi ganin haka yasa Faruk cikin sauri yanufi wajen da take, juyowa tayi ahankali tare da nunashi da hannunta nan wata irin iska tataso sai ji yayi and'aukeshi anyi wurgi da shi gefe d'aya ya fad'i kanshi ya bugu da k'asa.
Jawahir da take k'wance a cikin d'an kurkukun d'akinta tana bacci cikin daren nan, lokaci guda tafarka tare da fasa k'ara da dukkan k'arfinta wadda tasa saida duk mutanen da suke kusa da d'akin da take suka farka, hatta shi kanshi megadin saida yafarka rik'e kanta tayi tare da jan gashinta da dukkan k'arfinta ahankali tace a'a Ammi kar ki aikata haka ya kamata kibar Barr Faruk kar kiyi mashi komai bai chanchanci hakan daga garekiba, bazan ta'ba bari kiyi mashi wani abu ba,
'Daga murya tayi tace a'a Ammi na ce kar kiyiiiii!! waige waige tafara yi chan kuma tamik'e cikin sauri tanufi wajen bango tana zuwa tabuga kanta da k'arfi, wani irin zafi ne taji ammah ahaka tasake bugawa nan take jini yawanke mata fuska tasulale k'asa a hankali tare da furta sunan Amminta.
Daidai lokacin maigadi ya iso d'akin yadallota da fitila ganinta a kwance shame shame yasa yayi saurin bud'e k'ofar yashiga.
Ammi ko da komai yafaru a cikin kunnenta ta jiyo sautin d'iyartata tsayawa tayi chak a inda take tsaye tare da fasa k'arar da tasa saida Faruk yafarfad'o daga suman da yayi, cikin d'aga murya tace a'a jawahir bazan ta'ba bari wani abu yasameki ba, nan take tayi girgiza ta'bace.
Yunk'urin tashi yayi daga inda yake kwance ammah yakasa jin jikinshi yayi duk yana yi mashi ciwo saboda buguwar da yayi, dafe kanshi yayi da hannunshi sai a lokacin yasamu damar fara karanto addu'o'i sannan yasamu yamik'e dak'yar yanufi toilet, ruwan zafi yahad'a yagasa jikinshi bayan ya fito ne yanufi wajen briefcase d'inshi yabud'e ajiyar zuciya yasafke ganin bata ta'ba mashi komai ba saidai me ya jiyo lokacin da tafurta sunan jawahir to me yafaru da ita?
Jin k'arar bugawar agogo alamun k'arfe ukku yasa yakwanta yana jin jikinshi duk yana mashi ciwo ahaka yasamu yayi bacci.
____
Megadi yana shiga d'akin tsaye yayi a wajen kan jawahir cike da mamaki ganin ko kad'an bata motsi ga jini yana fita daga goshinta hakan yasa yayi saurin fita yad'auko wayarshi yakira shugaban su yasanar da shi halin da ake ciki, nan da nan aka kira First Aid Member na prison d'in sukazo suka fara mata dressing ammah jinin bai tsayaba, ruwa aka d'ebo aka watsa mata bata farfad'o ba daga suman da tayi sunyi kusan minti talatin akanta ganin har lokacin bata farfad'oba yasa suka kira shugaban suka sanar da shi yace to suyi k'ok'ari sutsayar da jinin da yake zuban kafin zuwa safe idan har bata farfad'oba sai akaita asibiti.
Haka ko akayi har asuba bata farfad'oba dan haka ana yin sallah aka d'auketa aka saka cikin mota aka nufi asibiti da ita inda motocin 'yansanda biyu suka rakasu har babban asibiti da ke cikin garin, a emergency unit aka wuce da ita a lokacin cike yake babu gado dan haka aka kama mata d'aki a aminity aka kwantar da ita nan likitoci suka yo kanta ganin daga gidan yari akazo da ita, dubata sukayi sannan suka nad'e mata kai da bandage bayan sunyi mata dressing sannan suka sa mata drip, daga k'ofar d'akinta 'yansanda biyar ne tsaye suna kaiwa da kawowa.
Sai wajen k'arfe goma sha biyu sannan tafarfad'o daga suman da tayi.
Tana bud'e idanunta taganta kwance a wani wajen na daban mamakine yakamata tace ina ne nake nan?
Yunk'urin tashi tayi sai kuma takasa, hannu tasa tafizge drip d'in da aka sa mata tatashi zaune tare da dafe kanta da taji kamar zai cire saboda tsananin ciwon da yakeyi mata, daidai lokacin doctor yashigo yana ganinta yayi saurin nufo inda take yace lafiya me yafaru?
Runtse idanunta tayi tana ji kamar zai fad'o nan yazo yarik'eta takoma takwanta yamaida mata drip d'in sannan yafita yarubuta wata allura yace aje asamo yanzu zaiyi mata ita.
Ba a dad'eba aka kawo allurar yayi mata sannan yafita yace kar wanda yashiga abarta tana buk'atar samun hutu tsawon awanni bakwai, nan suka amsa da toh sannan yawuce, d'aya daga cikin police d'inne yabud'e d'akin yalek'a ganinta a kwance yasa yamaida k'ofar yarufe.....
_Sis Nerja'art✍🏻_
[7/24, 11:14 PM] Sis Nerja'art 2: *......FANSAR RAI......*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSO....®*
[On Ward Together]
_Follow me on Wattpad: *Sis-nerja*_
_Wannan Littafin na kud'i ne domin karantawa cikin aminci da yarda ga duk me buk'ata zai turo katin Mtn na d'ari biyu N200 kacal ta wannan number d'in 09035938246, ko ta account number 5330055604, Idan katura ka aiko da screen shot na transaction a wannan number d'in 09035938246_
_Akwai gara'basar *RESHE YA JUYE DA MUJIYA* na shahararriyar marubuciyar nan *AMEENA ABBA UMAR* tare da novel d'in *FANSAR RAI* akan farashin N300 kacal, ko da kud'in ka sai da rabonka_
*PAGE 16*
...Yana gama shirin shi ko wajen aiki bai biyaba yau yawuce gidan kaso dan yana so yaga halin da jawahir take ciki yana isa yasamu labarin abinda yafaru dan haka daga nan yawuce asibitin, yana isa likita yana fitowa daga d'akin yatabbatar masu da har lokacin bacci take.
Awanta biyar tana baccin lokaci guda tabud'e idanunta tafara waresu a cikin d'akin ganin babu kowa yasa tatashi zaune hannunta takalla wanda aka sa ma kanula tasa gudan hannun tafizgeta sannan tayi saurin safkowa daga saman gadon, fara takawa tayi ahankali tanufi wajen taga, d'an d'age labule tayi talek'a ganinsu tayi tsaye wasu zazzauna a k'ofar d'akin, ganin wani yana shirin kallon tagar yasa tayi saurin sakin labulen tare da komawa takwanta tana ji suka bud'e d'akin suka lek'ota sannan suka maida suka rufe, tana jin sun rufe tatashi zaune tana bin d'akin da kallo kamar me neman wani abu sai kuma chan tamik'e wasu kaya tahango ajiye saman 'yar k'aramar drowar da take cikin d'akin cikin sauri taje tad'auka tashiga toilet nan tatsaya tana bin toilet d'in da kallo, 'yar tagar da tagani ne yasa tayi murmushi ajiye kayan tayi sannan tataka drum talek'a tagar, ganin wajene bayan d'akin yasa tasafko tad'auki kayan tasaka nan tafara tunanin ta yadda zata iya fita, juyowa tayi taje tarufe k'ofar toilet d'in ahankali sannan tataka drum d'in taja ragar (net) d'in tagar da k'arfi ammah tak'i 'balluwa dan haka tasa bakinta tafara ciccirewa da hak'oranta abinda zai baka mamaki kamar ba hak'oran mutum ba yanayin yadda take cire ragar da su saida tafara cire na 'bari guda sannan tasa hannunta taja dak'arfi sai gashi ta 'ba'b'bakota gabad'aya, koda tagar ba wani girma gareta ba ammah ahaka tatura kanta tafitar da shi saida taga babu motsin kowa a wajen sannan ta ida fidda jikinta dakyar tadira bayan ginin, gyalen kayanta tasa tarufe fuskarta da shi sannan cikin sauri tawuce zata zagaya tana 'bullowa sai ganin 'yansandar tayi tsaye a gaban d'akin suna kaiwa da kawowa dan haka sai tak'ara jan mayafinta a fuskarta sannan tacanza hanya cikin sauri tafita tabar asibitin tana fita tasamu me napep tatsaida tafad'a mata anguwar da zai kaita cikin sauri tashiga tace suje dan haka yajata suka tafi, tana yi tana kallon agogon da ke manne a gaban napep d'in har suka isa inda tace yakaita, suna isa tafita daga napep d'in tajuya zata tafi me keke napep d'in yace Hajiya kud'ina.
Tsayawa tayi cak tare da juyowa dan ita ta ma mance da zata biya wasu kud'i gashi batada su, k'ara maimaita mata yayi.
Ahankali tace kud'i? A'a kayi hak'uri banda su.
Harara yawurga mata yace da kinsan bakida kud'in shine zaki shigo min napep.
Ganin wani mutum ya nufo wajen yasa tad'aga murya tace dan Allah kayi hak'uri wallahi a rud'e nake saisa ban tsaya d'auko kud'i ba, fitowa yayi daga cikin napep d'in yace wallahi babu inda zakije sai kin biyani kud'ina.
Ganin haka yasa mutumin yanufo wajen yana cewa lafiya me yafaru?
Cikin fushi me napep d'in yace wannan yarinyar ce dan rainin wayo zata shigo min napep bayan na kawota inda takeso sai tace min batada kud'i.
Kallonta mutumin yayi yace haka akayi?
'Daga kai tayi alamun Eh.
Toh shikenan ni zan biya nawa ne kud'in naka?
Jawahir tana jin haka sai tayi murmushi tace nagode sosai sannan tajuya tatafi cikin sauri, tana zuwa k'ofar gate d'in gidan taja tatsaya kamar tayi knocking sai kuma tafasa, tura k'ofar gidan tayi ahankali sai jin motsi tayi a toilet na wajen k'ofar alamun megadin yana ciki dan haka tatura tashiga tamaida tarufe sannan tafara takawa sad'af sad'af ahaka tanufi hanyar cikin gidan tana shiga nan ma shuru batare da wani tsoro ba tafara taka matattakalar benen ahaka tahau sannan tamurd'a k'ofar wani d'aki jinta a bud'e yasa tad'an bud'e ahankali sai gani tayi babu kowa a ciki, k'arar shower tajiyo a toilet dan haka tabud'e d'akin ahankali tashiga tana lalla'bawa dan kar ajiyo k'arar takun ta, daga tsakiyar d'akin tatsaya tana binshi da kallo sai kuma chan tanufi wajen bedside tana zuwa tajawo drower k'asa tajita a datse dan haka tabud'e ta saman taji ita kuma a bud'e, lalubawa tafara yi sai ga key ta gani tafiddo cikin sauri tabud'e ta k'asar tana jawowa sai ga wasu files a ciki fiddosu tayi gabad'aya tafara dubawa daidai lokacin taji anrage k'arfin shower d'in, bubbud'ewa tayi cikin sauri tana dubawa tad'auko wasu files guda biyu tamaida sauran tarufe drower sannan tad'auka, jiyo murya tayi a cikin toilet d'in ana cewa Hajiya ke ce ganinan ina wanka, mik'o min towel.
Kallon k'ofar toilet d'in tayi sannan tawuce cikin sauri tafita tarufe d'akin, dagudu tasfka daga saman benen, hayaniya tafara jiyowa a gudan d'akin na mutanen gidan dan haka cikin sauri tafita, a filin gidan tasamu megadi tsaye saita nutsuwarta tayi sannan tawuce zata fita, kallonta yayi ammah ita ko bata kalli inda yakeba tana ji yace sannu Hajiya dan ya d'auka ko k'awar d'iyar gidan ce, amsawa tayi sannan yabud'e mata k'ofa taficce.
Tana fita ajiyar zuciya tasafke dan ita kanta ta san ba k'aramin namijin k'ok'ari tayiba da har tayi kasadar shiga cikin gidan, takawa tafara yi har tasamu napep tashiga sannan tafad'a mashi inda zai kaita ranta fal da farin ciki ta yi nasarar samo abinda takeso, ahaka har suka isa asibitin, suna isa talaluba dan tabashi kud'i sai taji wayam ba jakka ajiyar zuciya tasafke cikin ranta tace da da yanzu ba d'aya bane, muryar dattijon taji ya ce d'iyata munzo.
Cikin sanyin jiki tace kayi hak'uri baba ina tunanin kud'in da zan biyaka ne ashe babu kud'i atare da ni.
Juyowa yayi yakalleta yace kamar ya bakida kud'i ai bakiyi kama da marassa kud'iba d'iyata.
Cikin sanyin jiki tace dagaske nake Baba wallahi banda su.
Gyad'a kai yayi yace toh shikenan jeki kawai na yafe.
Godiya tayi mashi cikin jin dad'i sannan tafita, tafiya tafara yi bata ankaraba sai gata ta gaban 'yansandan nan cikin sauri tajawo gyalen tasake rufe fuskarta, murya Barr Faruk tajuyo da bai dad'e da dawowa asibitin ba alamun yana waya dan haka tadake tawuce tazagaya baya babu wanda yaganeta daga cikinsu, tsayawa tayi saida taga wasu mutane sun wuce sannan tataka dakali tawurga files d'in ta cikin tagar sannan itama tasamu tahau tadira aciki, tana dirawa tayi saurin cire kayan jikinta ta ajiye a nan cikin toilet d'in tad'auko unifoam d'inta na gidan yari tasaka sannan tad'auko files d'in, saida tad'an kanga kunnenta a wajen k'ofa jin ba motsin kowa yasa tabud'e ahankali tashiga, saurin jawo 'yar k'aramar drower da take ajiye cikin room d'in tayi wadda aka ajiye saboda ajiye ma patient kaya, tasaka files d'in.
Doctor ne yatafo yana cewa bari inshiga yanzu lokacin farkawarta ya yi idan har mukaga ta farka babu wani ciwo atare da ita sai mu sallameku, d'aya daga cikin masu kula da gidan yarin ne yace tabbas hakan yakamata Doctor dan yarinyar chan tana da had'ari zamanta a gidan yari shine kwanciyar hankalinmu, shidai bai fahimci abinda yake nufiba saidai yayi murmushi yabud'e k'ofar yashiga.
Kwance yasameta ta lulle'be har fuskarta yana isa yajanye mayafin ahankali tabud'e idanunta, murmushi yayi yace ashe kin farka ai na d'auka yanzu ne yakamata ace allurar ta sakeki, shuru tayi tana binshi da kallo, kallon hannunta yayi yaga ba kanula yace ya akayi kika cire?
Kallon hannun nata tayi sannan tace am daman daman na ji yana min zafi ne.
Ohk, akwai inda yake maki ciwo yanzu?
Girgiza kai tayi, nan yasake dubata yace saidai na san har yanzu kina jin ciwon kan ammah zasu dinga maki dressing d'in ciwon naki.
Batace komai ba saima kallonshi da takeyi ganin haka yasa yarubuta mata sallama tare da magungunan da za'a siya mata bayan ya gama yafita yasanar da su dan haka wasu police mata biyu suka shigo tana a nan inda take kwance suka saka mata ankwa a hannu, kallon hannuwanta tayi sannan tatashi suka izata a gaba suka fita da ita d'akin nan duk 'yansandar suka rufa masu baya, juyawa tayi takalli Faruk da yake waya har lokacin shima ya juyo yana kallonta, motsa baki tayi alamun tana son yin magana sai kuma tafasa sai tayi mashi nuni da idanu alamun yazo yaji.
Kashe wayar yayi yatako wajen yana zuwa yatsaya yace har an sallameta sukace eh,
Bakinta takai saitin kunnenshi tarad'a mashi wani abu wanda babu wanda yaji abinda tace sannan tawuce aka tafi da ita.
Tsayawa yayi a wajen har suka wuce sannan yaje yashiga d'akin yaduba drower yafiddo files d'in, tsaye yayi yana kallon files d'in mamaki duk ya cikashi cikin ranshi yace ita kuma ina tasamosu ko dai ta fita daga gidan kason nan? Kallon d'akin yayi yace ammah kuma ai ba hanyar da zata fita batare da ansaniba, wayarshi ce da tafara ringing yasa yayi saurin fita daga d'akin tare da kanga wayar a kunnenshi yanufi wajen motarshi.
Yana komawa gida zama yayi yabud'e files d'in yana dubawa cikin ranshi duk mamaki ya gama cikashi ganin yadda akayi tasamesu, chan kuma yayi murmushi yace wannan aikin naki ya yi sosai Jawahir, toh ammah idan yazama Amminta ce tad'auko su fa? Girgiza kai yayi yace wannan ne kuma bansaniba ko ma ya akayi na ji dad'in samunsu sosai.
Wayarshi yad'auko yad'auki files d'in hoto sannan ya ajiye yashiga shigar da su acikin laptop d'inshi bayan ya gama ne yakira Barr Nas a waya suka tattauna daga nan kuma yatashi yafara shirin fita.
A chan 'bangaren Alhaji Mansur hankalinshi a tashe yake sosai akan yadda Barr Faruk yakeson ganin ya tona masu asirin da yake binne babu wanda yasan da shi dan haka yafara tunanin yadda zai 'bullo mashi.
Ranar wata talata Barr Faruk yana gida da marece Alhaji Mansur yakirashi a waya, ya yi mamakin ganin kiran nashi sosai kamar ba zai d'agaba har tatsinke yana tunanin kiran me yakeyi mashi chan sai wani kiran yasake shigowa dan haka yayi picking batare da yayi magana ba.
Jin anyi picking yasa Alhaji Mansur yakalli nakusa da shi yayi murmushi sannan yace Barrister ina fatan kana jina?
Daga chan 'bangaren Faruk yace Eh ina ji.
Mik'ewa yayi tsaye sannan yace idan babu damuwa inaso yanzu muhad'u da kai a gida akwai maganar da nakeso muyi.
Shuru Faruk yayi baice komai ba.
Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ko bai yarda da shi ba dan haka yace inma bazaka zo ba toh kafad'i inda yadace muhad'u.
Cikin gadara da nuna isa yace idan zaka iya zamu had'u a chan Rahama Restuarent.
Toh shikenan nan da rabin awa zaka sameni a chan.
Batare da ya amsaba yakashe wayar.
Tsaki Alhaji Mansur yayi yace yaron nan ya cika jin kan tsiya shi gani yake kamar shi wanine ammah bakomai zan safke mashi girman kan nan nashi bari inje inshirya intafi duk yadda mukayi da shi zaka ji.
Suna gama wayar yatashi yashiga wanka yashirya yafita.
Yana isa Rahama Restuarent babu mutane sosai a ciki yaja kujera yazauna nan yabada umurni akawo mashi coffee yana cikin sha ne Alhaji Mansur ya iso yafara ware idanu yana tunanin inda zai zauna kafin Faruk ya iso da mamakinshi sai hangoshi yayi zaune, murmushi yayi sannan yanufi wajen yaja kujera yazauna yace ashe har ka iso.
Batare da ya kalleshiba yace Eh, me kake buk'ata akawo maka?
Yatsina fuska yayi yace bana buk'atar komai.
Batare da ya ce komai ba yacigaba da shan cofee d'inshi, Alhaji mansur hannu yasa a aljihu yazaro cheque ya ajiye mashi a gabanshi yana murmushi yace gashi
Batare da ya kalli cheque d'inba yace menene wannan?
'Yar dariya yayi sannan yace abokan rayuwa ne mana kakalla kagani.
Kallon cheque d'in yayi yai murmushi sannan yacigaba da shan coffeen shi.
Ganin haka yasa Alhaji Mansur yayi tunanin ya yi nasara yace wannan gabad'aya na mallaka maka su kaje kacire inma basu ishekaba kayi min magana ink'ara maka wasu.
Sai a lokacin ya ajiye coffeen yad'auko cheque d'in yaduba murmushi yayi yace 5billions, me kakeso inyi maka ne?
Bushewa Alhaji Mansur yayi da dariya yace dakyau haka akeso kud'i masu canza kowa, gyara zamanshi yayi yace yauwa ka yi tambaya mekyau abu d'aya nakeso kayi shine kajanye daga case d'in yarinyar chan, idan har kayi haka ni kuma zan k'ara maka linkin wad'annan kud'in.
Jinjina kai Faruk yayi yana murmushi yace wannan ne daman dalilin kiran da kayi min.
Eh shine kaga sai mutaru murufa ma juna asiri kai kaci dukiya ita kuma akasheta, kai kowane lokaci ma kaji kana son kud'i kakirani ni kuma zan aiko maka da su batare da 'bata lokaci ba.
K'ara duba cheque d'in yayi gaba da baya sannan yayageshi yawurga mashi.
Baki Alhaji Mansur yasaki yana kallonshi cike da mamaki yace kai kana da hankali kuwa? Ka san abinda ka aikata?
Mik'ewa yayi tsaye lokaci guda fara'ar da take fuskarshi tagushe cikin d'aga murya yace ni ko nasan abinda na aikata dan ni ba irin sakarkarun lauyoyin da ake siya bane, idan har kanaso kaga 'bacin raina toh kace zaka siyeni da kud'i, ka kalli kanka kai ba abun kunya bane kakalli kamata kace zaka siyeni da kud'i? Ko ka mance wannan Barr Faruk Sani Maishadda ne lauyan gaskiya?
K'ut Alhaji Mansur yahad'iye wani wahalallen yawu duk idanu suka raina fata dan bai d'auka zai ga haka daga wajen Faruk ba.
Girgiza kai yayi yace bazaka ta'ba samun hakan daga gareniba dan ni aikina gaskiya nake karewa bana d'aure ma k'arya gindi dan haka kawai kasaurari nan da kwana biyar zamanmu a kotu, yana fad'in haka yajuya a fusace zai tafi sai jin muryar Alhaji Mansur